Showing 21001 words to 24000 words out of 35375 words

Chapter 8 - Aure Da Haihuwa Book Complete Hausa Novels by Surbajo.txt

30 Nov 2024

1526

kimtsa junior, ta nufi gidan maimunan.


Bayan sun gaisa,maimuna ta dubi Safna cikin damuwa tace"Safna in fa ka rasa mafadi kai kaiwa kanka,ke kinga yadda kika koma kuwa,kinyi baki kin rame, akan namijin daba mijin aurankiba,yakamata fa kiyiwa kanki fada"


Wasu hawayene masu zafi suka zubo mata,ta dubi maimuna cikin raunin murya tace"Maimuna su baffa basu fahimceni bane,Rayhan na bukatar kulawa ta macen shi ta Aure,ki duba kulawar daya ba mahaifiyata tun daga ciwonta har zuwa mutuwarta,Rayhan ya kula da komai nawa,kuma shi wannan abun da yamin shike nuna cewa shi Dan Adam ne,Tara yake be cika goma ba,Rayhan ya bani ilimin da Nike takama dashi,ki duba lamarin nan,yanzu shi Farhan fisabilillahi me yayimin, da ya cancanci in wulakanta Rayhan akanshi,kowanne da na halak fa baya mance halacci kuma duk Wanda ya tallafi mahaifanka kamar nasa ji kake duniya kaf ba kamar sa "ta karasa maganar tana kuka me tsuma zuciya.




Shuru maimuna tayi tana nazarin maganar ta Safna can ta nisa,tace"komai kika fadi Safna gaskiya ne,Rayhan yakai ki soshi,sede abinda nakeso ki gane, Rayhan yana da kazamin kishi Wanda idonsa ke rufewa har ke ya wulakanta,kuma koda yanzu kin koma gareshi bazaku zauna lafiya ba,sabida baze so danki ba,kuma ke bazaki yarda ya nuna masa kiyayyaba,bama haka ba,Farhan amsar dansa zeyi,shin kina da tabbacin haifar wani Dan Bayan junior din,?Rayhan mutumin kirki ne amma beda zuciya me karfin daukar kaddara,yanzu kike rayuwa baasan wacce kaddarace nan gaba zata kara fada miki ba"


"To baki ga shi farhan din wulakancin da yay min ba,tafiya fa yayi ya bar ni, kuma ko nemana baya yi,bare Dan shi"ta yi maganar cikin nuna takaicin abinda yayi matan.


Murmushi maimuna tayi sannan tace "to Safna so kike yasa a daureki asa masa a mota,kefa kika karade gari da ihu kan ba kya sonshi,to laifine Dan ya tafi yabarki da masoyin naki?"


Harara ta jefawa maimuna sannan tace"baki fahimceni ba,ay da ya rarrasheni,da zan bishi,zuciya fa yayi yatafi,da sona yake,ay da ya rarrasheni"


Dariya maimuna takeyi kamar cikinta zeyi ciwo,dakyar ta tsagaita tace"Safna ko de kin fara kewar mijin naki me jajayen kunnuwanne?"


Duka Safna ta kaiwa maimuna sannan tace"to laifine,jiki da jini da lafiya in kasa kewar mijina?"


Wata uwar shewa,Maimuna tayi ta kwashe da dariya gamida rangada guda.


"To ko bikon Farhan ya kama ki,Dan wallahi baze dawo nemanki ba,Dan shima naga alamar akwai kishi,sede me tsabta Dan wlh da Rayhan ne sakin ki zeyi,daga baya yazo yana danasani"


Harara Safna ke zabgawa maimuna kamar idonta ze fado.




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/15/21, 12:08 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*






*Number danasa akan littafin nan,ta business ce kamar yadda na fadi,ko anmin mgn kan inturo littafi ko insa mutum a group bazan bada amsa ba,haka nace, amma salon de ace ga abinda kayi aji haushinka wasunku na tamin mgnr da bata shafi kasuwancin ba,pls yakamata kusan uzurin mutum don Allah*




*Page 33*




To tunda Safna tabar gidan maimuna lissafinta ya kubce,sosai take kewar mijin Nata, Dan ta kai ta kawo ko bacci bata iyayi.


Gaba daya tayi baki, ta lalace, bame ganin ta ya dauka itace.


Tayi kuka tayi addua kan Allah ya kawo Farhan din gareta,amma,shuru kamar an shuka dusa.


Tsawon watanni shida kenan,da tafiyarsa,hankalin Safna in yayi dubu ya tashi,yanzu ta yarda Dari bisa Dari tana matukar kaunar mijinta kuma tana kewarshi.


Ganin da tayi shurun baze mata bane yasa ta tuntubi maimuna da Neman shawara.


"Kije gun doctor Amina mana,ko kije gun yar uwarsa Sarah a Kaduna su nemoshi"cewar maimuna.


Cikin damuwa Safna tace"bazan iya zuwa gun Sarah ba maimuna a duniya ba abinda take so sama da Farhan, nasan ranta be mata dadiba kan abinda nai masa,sede ko doctor Amina din"


"To kije gareta nasan insha Allahu zata karbeki,ta kuma hadaki da mijin ki"


Da wannan shawarar suka rabu,zuciyar Safna cike da kwarin guiwa, tabbas gobe zata tafi Abuja Dan haduwa da doctor Amina.


A nashi bangaren Farhan kusan kullum seya kira doctor Amina yaji,ko Safna ta fara nemansa,"doctor ina kewar matata bazan boye miki ba"cewar Farhan cikin damuwa.


"Kayi hakuri ka daure, kabar,komai har zuwa ta nemeka,"cewar doctor


Tsaki yayi sannan yace"yarinyar fa Sam bata da hankali kina fa ganin abinda tamin"cewar Farhan cikin damuwa.


"A kara hakuri yallabai,duk inda Safna take nasan tana cike da kewarka"


Da irin wainnan kalamun doctor ke rarrashin Farhan Dan bata so yafara sakkowa Safna ta raina shi.


Yau Safna tun asuba ta gama shirya kayanta,ta kimtsa junior itama ta kimtsa, sannan ta nufi dakin baffa tai sallama ya amsa mata gami da bada izinin shigowa.


Koda tashi ga gaisheshi tayi,sannan ta ce "baffa dama kudin mota nakeso abani,zani Abuja gun doctor Amina, inason magana da ita"ta fadi cike da tsoron me ze biyo baya.


Murmushi baffa yayi,sannan yace"zaki gun doctor Amina ko de zaki Neman Farhan?"


Da sauri Safna ta cukuikuye fuskarta cikin hijabi,Dan sosai taji kunya.


"A baya kin batamin rai amma yau kin farantamin kuma naji dadi,Allah yay miki albarka,kizamo me biyayya da hakuri da mijinki,rashin kunya duk ba naki bane,a ka ida Safna senayi bincike kan in aurar dake ga Farhan amma gamsuwa da nayi da hankalin sa yasa nabashi ke,kuma insha Allahu babu danasani awannan auran,Safna kiyi wa Aure biyayya.kuma yanzu ki kiramin innar taki tazo ta shirya mu biki Abujar Dan ganin gidan doctor Aminar"


Safna sabida tsananin farin ciki har kuka takeyi,bata taba tsammanin baffa zema saurareta ba.


Godiya tai masa sosai,sannan, ta mike taje ta kira masa matar tasa.


Da misalin karfe biyu na rana,Safna suka isa Asibitin doctor Amina,


Basu jima da zuwa ba doctor ta fito daga zagayen marasa lafiya, sanda taga Safna dasu baffa ba karamin dadine yakamata ba,Safna ko se kunyar hada ido takeyi da ita.




Bata ko zauna ba,ta kwashe su a mota zuwa gidan ta,ji take kamar tai tsalle Dan murna.


Koda suka isa gidan sosai kan safna ya kwance,ganin hotunan Farhan ta ko ina acikin gidan,wai meye alakar Farhan da doctor Amina ne?tana son sanin wannan amsar.


Abinci doctor ta gabatar musu,me rai da lafiya, Bayan sun ci sun sha, taba su baffa masaukinsu,sannan taba Safna ma Nata.


Seda dare yayi suka samu damar zantawa da doctor inda baffa yafara da cewa"mude Amina,ke muka Sani dangin Farhan, amanar Safna gaba daya mun baki, Safna ta gane kurenta,gatanan munkawota ki sada ta da mijin ta"


Murmushi doctor tayi,sannan ta dubi Safna cikin sigar zolaya tace"baffa banaso ayi mata dole,ya kamata ayi hakuri Ku koma da ita Dan da bakinta ta shaida mishi bata sonshi,kaga.."safna ce ta katseta da hanzari tana kuka tana fadin.


"Wallahi bazan koma Sara ba,ni gurin mijina zaki kaini,ay kece kika zugashi ya aureni shine zaku wani tafi Ku barni sekace bazawara,wlh se kin kaini gun mijina,nagaji"ta karasa maganar cikin kuka.


Ba doctor ba,hatta baffa da inna dariya suke mata,se alokacin Safna ta kula da katobarar da tayi Dan haka da gudu tabar gurin zuwa dakinta da doctor ta sauketa..


Haka de su baffa suka gama magana da doctor karshe Farhan ta kira,suka yi magana dashi,sosai,yaji dadin sakkowar Safna godiya yakewa su baffa, doctor na fassara musu.


Makudan kudi yasa doctor ta basu in zasu koma.


Washegari da wuri su baffa suka tafi,Safna har kuka tayi na rabuwarsu.




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/16/21, 11:09 PM - Ummi Tandama😇: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*






*Page 34*




Bayan doctor Amina takai su baffa airport kamar yadda Farhan ya bukata,kai tsaye gida ta dawo gurin Safna.


A dakinta ta sameta,Safna na ganinta kunya ta kamata tayi kasa da kanta,murmushi doctor tayi sannan ta karasa kusa da ita ta zauna,sannan ta dafo kafadarta,ta fara magana cikin tattausan lafazi.


"Safna tun da wannan kaddara ta fada miki Allah ya jarabceni da sonki,ina kallonki tamkar kanwata wacce muka fito ciki daya,batu na gaskiya Safna kin bata ran Farhan fiye da tunanin ki,dami ne kika tsinta a kala amma kikeso ki banzatar,ta koina Farhan ba tsaranki bane,amma ya nuna miki ke yake kauna kika watsa masa kasa a ido,akwai ayki agabanki,Dan gaskiya in yayi fushi irin haka yana da wiyar sakkowa"


Idon safna ne ya kawo kwalla,cikin hardewar murya tace"ki bashi hakuri ,ni wlh bansan meyasa nayi hakanba,amma yanzu na gane kuskurena"ta karasa maganar cikin kuka.


Murmushi doctor tayi sannan tace "ze sakko amma bada wuri ba,se kin zage damtse sosai sannan kinyi hakuri kamin kiyi Nasara,bama wannan ba,kinga Farhan yana da mata,maana kina da kishiya,kuma itama Balarabiyace, Dan haka bazan kaiki gareshi ba har se na kimtsaki,Dan kanki har yanzu akwai kura,dole a kakkabeta".


Shuru Safna tayi tana nazarin maganganun doctor din,Farhan Nada mata wayyo Allah ita ta shiga uku,taya zata iya kishi da Balarabiya,anya ba hakura zatayi da auran ba kuwa?


Haka de doctor taita kokarin wayar mata da kai akan lamarin zama da kishiya,da kuma abubuwa da tasan Farhan din naso da Wanda be so.


Wasa wasa Safna seda ta kwashe tsawon watanni biyu a gidan doctor tana tsumata da magunguna,sannan tana koyar da ita darussan aure.


Sosai Safna tayi kyau ta murje tayi wata kiba, ta musamman wacce ta kara fito da kyanta.


Ga wani fari da tayi,Wanda in ba magana tayi ba dauka zakayi itama Balarabiyarce.


Babu ta inda doctor bata gyara Safna ba ciki da waje,ita kanta bata gajiya da kallon safnar.


Yau da wuri ta dawo daga Asibiti, zamanta a falo kenan,wayar ta ta hau kara da sauri ta daga ganin Farhan ne ke kiranta,


Gaisawa suka yi cikin girmamawa,kamar yadda suka saba,sannan Farhan yace"wai Amina ko de ke na aurowa yarinyar nan ne,?nasa miki ido inga iya gudun ruwanki,amma naga baki gane ba,kinga ki sakomin matata a jirgi,tazo tasameni,ina kewar yarona,sosai"


Dariya doctor tayi,sannan tace"tuba nake yallabai,last week da mukayi waya cewa kayi private jet zaka turo mana in mun shirya, to kai muke jira"


"Na kira Abdallah(mijin doctor) a waya dazu yace yana Lagos,so nakira Taufeeq nasa yashirya muku komai,gobe jirgin zezo mun samu izinin haka,Dan haka banda bata lokaci jirgin safene"cewar Farhan a tsanake.


"Insha Allahu angon Safna gobe muna tafe da yardar Allah"


Murmushi yayi me sauti,alamun yaji dadin sunan data kirashi.


Sallama sukayi kamar kullum yauma be bukaci jin muryar Safna ba.


Safna dake gefe zaune ranta sosai ya baci amma ta daure,Dan bataso doctor ta gane tana jin haushin kin nemanta da Farhan din yakeyi.




Washe gari da wuri suka kimtsa,kayansu,inda doctor tayiwa Safna Jaka Jaka na magungunan mata masu kyau da nagarta,


Sun isa airport akan lokaci, karfe Tara na safe jirginsu ya daga zuwa kasar ta Dubai, Safna na kukan bankwana da kasarta,wacce batasan ranar da zata zo ba.




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/19/21, 1:10 AM - Ummi Tandama😇: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*




*Page 35*






Sun sauka lafiya, inda suka samu direba yazo daukarsu a wata Dan kareriyar mota,


Bayan ansa komai nasu a motar suka shiga aka jasu zuwa gidan na Farhan, Safna duk ranta a bace,sabida Farhan be zo tarbarsu da kanshi ba,a ganinta wulakanci ne yay mata a matsayin ta na amaryar shi.


Koda suka tunkaro get din gidan Safna baki ta bude tana kallon sarautar Allah girma da kyau na gidan ya isa da isarsa,babuce kawai babu a gidan,ga garden nan tamfatsetse,me cike da yawan shuke shuke.


Har suka tsaya a harabar ajiye motoci Safna bakinta a bude ike tana kallon gidan.


Sai da doctor ta tabota sannan ta dawo hayyacinta,suka fito daga motar zuwa cikin gidan.


Koda suka shiga falon gidan Safna kusan suman tsaye tayi sabida kyawun falon,haka tasaki baki tana kallo.


Da sallamar su suka shiga falon,shehnaz ce zaune ta harde kafafu wata Yar matashiyar yarinya na matsa mata kafafun,cikin sakin fuska ta waigo da niyyar amsa sallamarsu,sede ganin fuskokinsu ne, yasa taja wani uban tsaki,Dan farin Sani tasan Safna sabida sunsha kai ruwa rana da farhan sabida hotunanta da ya ajiye a wayarshi Wanda da yawa batasan ma ya dauketa.


Doctor Amina ko kallonta batayi ba,ta Ciro waya ta kira farhan ta shaida mishi sun iso,


"Sorry Amina,Abi ne ya kirani,kiran gaggawa,amma ganinan zuwa"yana fadin haka ya kashe wayar.


Sunanan zaune ya iso falon cikin shiga ta alfarma, fuskarshi dauke da murmushi, yasamu guri ya zauna,nan ko junior yace dawa Allah ya hadashi badashi ba,ya dinga zullo a jikin Safna dole ta saukeshi,kasa ya rarrafa,gurin Farhan yana fadin,"Dada "cikin muryar Yara masu koyon magana.


Tun kan ya karaso Farhan din ya karaso gurinshi ya sureshi wani farin ciki na ratsa shi na ganin gudan jinin nasa,kiss yakewa yaron ta koina yana rungume shi.


Guri yasamu ya zauna dauke da junior din,gaisawa sukayi da doctor yayi mata ya hanya,bayan sun gaisa dinne doctor ta karya wuya tace"Ranka ya Dade ga Safna na kawo maka,don Allah kayi hakuri da abinda ya faru,yanzu ta gane kuskuren ta kai mata afuwa"


"No problem"Farhan kawai yace,sannan yamike yana fadin"muje Amina kiga masaukin,inaso inje in dawo ne"yafadi yayi gaba,doctor na binshi a baya,Dan ta fahimci bangaren Safna ze nuna mata.amma fushin da yake da ita baze bari,ya ambaci sunanta ba.


Koda suka isa bangaren doctor batai mamaki ba Dan tasan ze iya yin abinda yafi haka.sosai ta yaba da komai na bangaren, dakuna hudu ne,acikin falon, daya na Safna daya na baki,daya nashi,daya na yara,Wanda kowanne ya gaji da haduwa da kayan kyale kyalen duniya.


Dakin safna bango guda glass ne kuma yana fuskantar lambun gidan ga wata royan din doguwar kujera da aka ajiye ajikin gurin,kai abinda se Wanda kagani.




Bayan ya nuna mata be dawo ta babban falon ba yabi. Ta karamar hanya zuwa nashi bangaren rungume da junior.


Doctor gun Safna ta koma ta kamota zuwa bangareta,Safna se share hawayen bakin cikin tarbar da angon nata yay mata ...






Muje zuwa






Surbajo for life.
11/19/21, 11:53 AM - Ummi Tandama😇: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*




*page 36*




Rarrashinta doctor takeyi da duk wata kalma me dadi da tazo bakinta,tare da sake koyar da ita dabarun zaman Aure.


Shuru Safna tayi,Dan ta gamsu da bayanan na doctor.
.suna zaune masu aykin da Farhan yasa sui musu abinci suka shigo musu dashi.


Bayan sun ci sun koshi,kowa wanka yayi,ya rama sallah,sannan suka shirya kayayyakin da suka zo dasu. A inda yadace.


Da misalin karfe takwas,doctor tayiwa Safna sallama, Dan ba a gidan zata Kwana ba,gidan iyayen Farhan din zata,Dan tunda mahaifiyarsa taji zuwanta take ta kiranta kan tazo gidan su.


Da kuka suka rabu da Safna, bayan ta kara ja mata kunne kan duk abinda ta koyar da ita.


Safna toilet ta shiga ta sake yin sabon wanka,kwalliya me sauki tayi,sannan ta nemo,wani wando three quarter fari me kama jiki,ta saka,sosai mazaunanta suka fito acikin wandon,kasancewar rubber ne,koya ta motsa rawa sukeyi,sannan tasa wata Yar yaloluwar Riga pink,wacce itama ta kama ta, bata wahal da kanta sa bresier ba,ta kama gashin kanta da ribbon pink.


Falonta ta dawo ta zauna,ta kunna tv, tana kallo Dan ta debewa kanta kewa,gashi tunda suka zo ya tafi da junior be kawoshi ba,kewarshi duk ta dameshi.


Turo kofar falon akayi,da sauri takai dubanta gurin,Farhan ne rungume da junior, alamun kamar tare dashi yafita kai doctor Amina gidan nasu.


Mikewa tsaye tayi tana kallonshi,shima ita yake kallon tun daga sama har kasa.


Takawa yayi a hankali zuwa gabanta,junior ya mika mata a hankali tasa hannu zata karbeshi,hannunta tasa a kasan na Farhan din, cikin salon da doctor ta koya mata,tayi hakan,da sauri Farhan ya dago ido yana kallonta,ita shi take jefawa wani shuumin kallo,tana wasa da idanuwanta.


Be ce mata komai ba ya zare hannayensa,ya matsa daga kusa da ita.


Juya tayi cikin takun daukar hankali, Wanda koya ta motsa mazaunanta rawa suke ta nufi daki domin kwantar da junior.


Farhan a yadda ya tsara,junior din kawai ze bata ya baro sashin Nata, amma tafiyar ta Safna tasa kafafunsa sun kasa daukarsa,kan kujerar data tashi ya je ya zauna, Wanda shi kanshi besan zaman na menene ba.


Tana kwantar dashi,ta dauko wata shuumar humrar ta ta shafa,sannan ta dawo falon,cikin salon tafiyar da ko ina na jikinta rawar yakeyi.


Tunda ta fito Farhan ya jingina bayanshi da jikin kujerar ya lumshe idonsa kamar yana bacci amma fes yake kallonta.


Koda ta karaso,tsayawa tayi agabanshi,tana yan waige waige alamun tana Neman wani Abu ,zuwa can ta hangi remote din asaman kujerar setin saman kansa.


Hankali kwance,ta ware kafafunta,ta haye kan cinyarshi,ta zauna,😄war Farhan ya bude idanunsa,yana kallonta,be gama mamakin karfin halin na safna ba,yaga ta Dan mika hannu saman kansa,gamida manna masa boobs dinta a fuska,tana kokarin dauko remote,ga wani Dan jujjuyawa da takeyi a jikin nasa .


Chaiiiiii😄




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/19/21, 12:27 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*






*page 37*






Dauko remote din tayi,sannan ta sakalo hannayenta,a wuyansa,suka fuskanci juna,gaba daya ta gama daga mai hankali amma ko kusa be nuna hakanba,cikin wata shuumar murya wacce ko Rayhan besan tana da ita ba ta lankwasar da kai,tace "Abban junior kayi hakuri mana haka,dan Allah,wallahi na tuba fa"ta karasa maganar hawaye


Shanyayyun idanunsa ya lumshe, ya jingina bayansa da jikin kujerar.


Safna ganin beda niyyar mata magana ne yasa ta kwantar da kanta a kirjinsa ta soma rera kukanta kamar wacce aka Zane.


Sosai kukan ke taba masa zuciya, Dan ko kadan beson damuwarta,ji yake kamar zuciyarshi zata fito,sabida zafin da take masa.


Ganin bata da niyyar dena kukan ne yasa Farhan sa hannu ya dagota daga kirjin nashi, ya kureta da ido,itama( ido kamar na malekin kwarto),shi din take kallon,cikin sigar fada yace"wai ke bakya jin dadin rayuwarki ne,se kin sa mutum a shiga uku,narasa me nai miki kikemin duk wannan abubuwan?"karasa maganar yayi cikin bacin rai.


Safna sosai ta tsorata da yanayin nasa amma daurewa tayi,tace"kayi hakuri Abban junior don Allah na gane kuskuren da nayima ka yafemin"wasu hawayen suka sake yo ambaliya daga idon Nata.


"Look Safna, shi wannan kukan na menene?da zaki zo han kan laps dina kina yimin,?dukan ki nayi?"


Da sauri ta girgiza masa kai,tana rufe bakinta,sakamakon wani kuka dake kokarin kwace mata.


Wani takaici ne ya lullubeshi ganin shifa tayiwa laifi sannan tasashi agaba tana kuka.


"Dagani zanje in kwanta"cewar Farhan yana kokarin mikewa.


Safna taga biyayyar bazata kaita ba,Dan haka,cikin zafinta tace "baza'a daga din ba malam"tasake nanikeshi 😄


Iko se Allahu, Farhan dariya ce taso kubce masa amma seya maze,be taba ganin mutum Dan daru irin safna ba,kai da jikinka ace bazaa daga ka ba.


Kyaleta yayi ya maida hankalin shi kan tv Dan ya lura ta juye dayan sashin dayafi so nata wato tsiwa.


Safna zaune rashe rashe akan cinyarshi,yayinda ta zagayeshi da hannayenta ta kwantar da kanta a kirjinshi.


A haka bacci yay awon gaba dasu su duka,farhan hannu yasa cikin baccin ya rungumo ta,suka shiga yin kayansu.in kowa yaji kamar ze fadi seya zabura ya sake kankame Dan uwansa😄.


Kiran sallah ne ya farkar da Farhan A hankali yakai dubansa gun rigamammiyar matar tashi,dake bacci akan shi hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login