Showing 9001 words to 12000 words out of 35375 words

Chapter 4 - Aure Da Haihuwa Book Complete Hausa Novels by Surbajo.txt

30 Nov 2024

1524

jin karar motarshi alamun ya fice,fitowa tayi ta nufi kitchen, Dan samawa kanta abin da zata karya.


Ga mamakin ta kitchen din arufe yake se wata takarda da ya manna ajikin kofar,dauke da rubutu kamar haka,


"Bazan iya ciyar da Dan da ba nawa ba,ki nemi ubansa ya baku abinci"


Zubewa tayi agurin tana kuka,bata taba tsammanin Rayhan ze mata haka ba ko a wasa.




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/14/21, 12:45 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*






*Page 13*






Mikewa tayi ta koma dakin ta, kudi ta dauko tasa hijabi,ta nufi gun megadi,yana hango ta nufo shi yataso da sauri yadan risina yace "barka da safiya hajiya,me kike da bukata?"amsawa tayi cikin sakin fuska tace"baba don Allah cefane nakeso kayomin,a wuse market,"


"To badamuwa ranki ya Dade kawo aje ayo miki"


Lissafa masa komai tayi sannan ta bashi kudin kimanin dubu tamanin,yatafi .


Kulle gidan tayi ta ciki sannan ta koma cikin gida,wanka ta shiga sannan ta shirya ta dawo falo zaman jiran akawo mata cefanen.


Baa jima sosai ba megadi yashigo mata da sakonta bayan ta bude masa gidan,sosai tai masa godiya sannan ta kwashe komai takai dakinta.


Dan karamin gas din datasa ya siyo mata ta kunna ta daurayo tukunyar daya siyo mata tazo ta hada komai ta Dora indomie acikin dakin Nata.
Dan duk abinda zata bukata seda tasa ya siyo mata.


Haka taci gaba da gudanar da rayuwarta a kulle acikin daki,koda wasa batason ganin Rayhan, shiyasa ta kulle kanta aciki,sabida akwai toilet acikin dakin Nata,


A nashi bangaren Rayhan ko tunda ya fice yabar gidan,kotu yaje ya shigar da karar doctor Amina sakamakon abinda sukawa matarsa,inda alkali yabada sati biyu su hallara agabansa.


Lokacin da sakon ya riski doctor Amina,tashin hankalin data shiga,bashida adadi.Neman Farhan take a waya tun lokacin data ga su Rayhan din amma bata shiga,wannan shine yakara daga hankalinta.


Ranar shiga kotun da safe Rayhan yaje kofar dakin na safna yace cikin dakewar murya.
"Ki bude kofa ki fito mu tafi kotu Dan yau alkali yabada mu hallara agabanshi ina jiranki a mota"yana kaiwa nan yayi fucewarsa abunsa


Safna jin maganar tayi kamar saukar Aradu,yau itace Rayhan yakai kara kotu?wannan wacce irin masiface.
Tunda ya fada tasan dagaske yakeyi,Dan karya bata daya daga cikin halayensa.


Jiki asanyaye ta janyo hijab tasaka,ta zura takalmi ta fito.bayan ta kulle dakinta.


A motar ta sameshi yana cika yana batsewa,ba me cewa shine Rayhan din ta me yawan murmushi.


A harabar kotun suka samu doctor Amina ma ta iso ita da maaikatan da suka gudanar da aykin.


Karasawa gunta Safna tayi suka gaisa,inda doctor Amina tace"Safna kinga kaddara ko?"
Hawaye ne suka gangaro daga idon Safna masu zafi sannan tace"doctor ina cikin tashin hankali"


Karasowar Rayhan gurin ne ya katse musu hirar,inda ya dakawa Safna tsawa da cewa "wuce mutafi".ba musu tabishi abaya suka shiga cikin kotun.


Bayan kowa ya hallara ne me gabatar da kara yatashi ya gabatar da karar da Rayhan Hashim ya shigar agabanta,yana me kalubalantar doctor Amina,da sauya kwayoyin halittarsa Dana wani ta sawa matarsa,Wanda hakan ya janyo matarsa ta dauki ciki,yana me rokon kotu datasa matarsa ta zubar da cikin,kuma yanaso kotu me adalci da ta bi masa hakkinsa.


Bayan an gabatar da kara ne alkali ya bukaci ganin doctor Amina,jiki asanyaye ta karasa inda aka tanada domun tsayuwar Wanda ake tuhuma taje ta tsaya.


"Munaso ki gabatar mana da kanki"cewar alkali,


"Sunana Amina Galadima,likita,kuma mamallakiyar Asibitin Galadima special hospital"


"Kinji korafin da aka shigar akanki shin haka akayi koko kina da ja game da hakan?"alkali yasake jefo mata tambayar.


"Duk abinda aka fadi ranka ya Dade haka ne,sede ba nice da kaina na gudanar da aykinba, kuma kuskuren suna aka samu ta hanyar kamanceceniyar suna,ina me rokon kotu datai mana sassauci".ta kwashe komai ta sanar da kotu gamida mika takaddu na bincike da kuma duk wani Abu daya shafi dashen tun kan ayi har zuwa bayan anyi,


Alkali ya bukaci maaikatan da suka gudanar da aykin dasu gabato gabansa,suma suka amsa sune suka yi,


Bayan dogon rubutu alkali yafara magana,"Bayan nazari da bincike,wainda ake tuhuma basu wahalar da sharia ba kotu ta gamsu da duk bayanan kowanne bangare,kuskurene babba suka aykata,Wanda dole ay musu hukunci,Na farko,kotu ta yankewa doctor Amina hukuncin biyan Tara ta dubu Dari,bisa laifin daukar maaikatan da suke sakaci da aykinsu,su kuma wainda suka aykata laifin,kotu na umartar da akaisu gidan gyaran hali na tsawon wata guda,ko zabin Tara,ta dubu goma goma"kotunce ta hargitse da surutu,kamin alkali ya tsawatar akai shuru, sannan yaci gaba


"Kotu na kira ga Rayhan da yayi hakuri bisa faruwar wannan Lamari,sabida kotu bazata sa Safna ta zubar da cikiba, Wanda aykata hakan zunubine,kuma shi wannan Abu daya faru,shima kuskuren ne babba, duba da tabbaci da aka samu daga bakunan maaikatan na cewa cikin an sameshi bada kwayoyin halittarka ba,kuma kamin ayi an tabbatar da bata da ciki,bayan anyi kuma baka kusanceta ba seda aka tabbatar da ta samu cikin,hakan ya tabbatar da cewa cikin jikinta ba naka bane,Dan haka kotu ta sallami wannan karar"


Gaba daya kotun ta kaure da hayaniya,Safna kuka take kamar ranta ze fita, wannan kaddara dame tai kama.


Haka ta mike tabi bayan Rayhan din daya fita afusace,


Sede kamin ta karaso tuni yaja motar sa yabar harabar gurin,Dan shi Sam ba haka yaso ba,so yayi asa safna ta zubar da cikin, sannan adaure doctor Amina, amma gaba daya ba hakan akayiba,


Hakanne yasa shi tunanin anya ma kuwa alkalin yasan aykinshi?




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/14/21, 12:45 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������






*Zahra Surbajo*






*Inna Ibrahim kime alkhairin Allah yakai miki, ina alfahari da haduwa dake arayuwata.*


*14*




Doctor Amina ce ta karaso inda take ta dafata, da sauri ta waiga taga waye,
Ganinta ne yasa ta rushe da kuka ta fada jikinta tana fadin,"doctor ki taimakeni banason rasa aurena,Ina son mijina sosai"tayi shuru sakamakon kukan dayaci karfinta.


Jan ta zuwa mota doctor tayi sabida jamaa sun fara taruwa akansu,da gudu ta fice daga harabar kotun.


Safna ko se aykin kuka take,har suka iso kofar gidan Rayhan din,bude mata kofa tayi ta fito,sannan tace"gobe zan dawo in mijinki ya fita Dan musan yadda zaa bullowa da abun ki kwantar da hankalin ki"


Jiki ba kwari ta tura kofar get din tashiga ita kuma doctor taja motarta ta bar gurin.


A harabar gidan tasameshi tsaye yana huci,kamar wani maciji,bata bi takanshi ba tayi hanyar shiga ciki,wata tsawa ya daka mata sai da cikinta yayi juyi ta waigo a firgice,.


Tsayawa tayi cak a inda take,har ya karaso,cikin fushi yake magana "Safna koda wasa ban dauka zaki ketare maganata ba,nadauka son da kikemin na gaskene,shiyasa na baki umarnin zubar da ciki amma kika ki,to ni bazan iya zama dake ina kwasar bakin ciki ba,Dan haka zan baki zabi wallahi sede ki zaba ni ko cikin jikin ki?"ya wurga mata tambayar batare da shayin komai ba,


Cikin kuka Safna ta tsuguna agabanshi tafara bashi hakuri"don Allah Rayhan kayi hakuri, kasan ina sonka, wlh nafi sonka akan cikin jikina,fushin Allah ne kawai banason na fada,sakamakon zubar da cikin,don Allah ka fahimceni"ta karasa maganar cikin kuka.


"Zabi na baki malama ni ko cikin jikin ki?"yafadi batare daya tausaya mata ba.


Rokonshi take da duk iyawarta kan yayi hakuri amma fafur ya kafe,ganin bata da mafitane yasa ta mike tsaye ta share hawayen ta tace asanyaye "na zabi cikin jikina Rayhan"


Kallon mamaki yay mata sannan yace "to kije na sauwake miki aurena dake kanki,na sakeki saki daya"ya yi saurin barin gurin sakamakon kukan dakeson kubce masa,yana son matarsa,yayi iya yinsa Dan yaso abinda ke cikinta amma yakasa,shiyasa ya sake ta gudun kar zuciya takai shi halaka.


Safna ji tayi duniyar tai mata nauyi,rasa abun yi tayi kawai seta kife agurin tana kuka,ta jima tana kukan kamin ta rarrashi kanta ta mike,ta shiga cikin gidan,dakinta ta shiga,ta hada kayanta na sawa se Jakarta ta hannu,


Ta janyo akwatin ta fice,daga falon tana kuka.


Shima dake tsaye ta window yana kallonta kukan yake kamar yabita,sede hakan da yayi shine masalaha agareshi.


Tana fita, taxi ta dauka drop zuwa jabi park, tana isa motar Daura ta hau,fasinga daya dama suke jira Dan haka direba yaja motar suka nausa kan titi.




Muje zuwa




Surbajo for life
11/14/21, 12:46 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*








*Page 15*




Da laasar ta sauka a kofar gidan su,sede dandazon mutanen da ta gani ne a kofar gidan ya daure mata kai,tana kokarin Neman hanyar da zata sada ta ne da cikin gidan taci karo da mutane na fitowa daga gidan dauke da makara da gawa aciki.


Da sauri taja baya, tana binsu da ido,kanin babansu ne karshen fitowa,suna hada ido yace "Safina ya muka ji da hakuri,sabuwa kuma sai yayi,Allah yajikanta"


Safna daskarewa tayi a tsaye tanajin maganar kamar a mafarki,innarta ta rasu,.batasan sanda ta yanke jiki ta fadi agurin sumammiya ba.


Matan dake cikin gidan ne suka hango faduwarta,da sauri sukazo suka dauketa zuwa dakin mahaifiyarta, aka shiga yafa mata ruwa ana mata fifita,ta jima kamin ta farfado.


Wani kuka tasaki me tsuma zuciya, wannan wacce irin rayuwace,miji ya korota asanda take tsaka da bukatarsa,mahaifiyarta ta rasu a lokacin data iso gareta domin Neman mafaka.


Rarrashinta makwabtansu ketayi,dan su kishiyoyin mahaifiyarta ko ajikinsu sabgar gabansu kawai sukeyi.


To haka rayuwa taci gaba da garawa,har Safna ta dauki danganar mutuwar mahaifiyarta,


Matan babanta ne suka sata agaba da tambaya me yasa mijinta bezoba ita kuma bata koma ba shine ta shaida musu komai bata boye ba,


Ayko kan kace kwabo garin ya dauka Safna cikin shege tayi agidan mijinta ya korota,duk inda tabi zunde da munafuncinta akeyi.


Ta rasa ina zata sa ranta taji dadi, maimuna kawarta ce kawai ke tausarta,kasancewar katangarsu daya da gidan da tai Aure.


Rayuwa tayiwa Safna tsada,ga matan babanta ba me bata abinci se ta wahalta masa shima bame yawa ba zaa bata.
Maimuna ke ayko mata wani lokacin.


Tsawon watanni bakwai kenan da mutuwar Aurenta,Wanda tuni cikinta watan haihuwarsa ya kama.


Kullum cikin fargaba take amma ta fawwala Allah,Dan ba me taimaka mata,se shi din.


Cikin dare yau ta tashi da ciwon nakuda,tayi kukan ta kira sunayen matan gidan Kansu zo su taimaketa amma ina ba Wanda yabi takanta,


Cikin hukuncin Allah ta haifo danta santalele ita kadai adaki,gefe ta koma tana kallon shi kwance akasa cikin jini yana ta rusa kuka,yana cilla kafa,


Ahankali ta matsa kusa da akwatin kayanta ta bude ta dauko zani,ta dauki jinjirin da mahaifar duka tasaka aciki ta nannadeshi sabida rawar sanyin da yakeyi.


Jin dumin da yayi ne yasa ya dena kukan,ya koma yayi lub,jin shurun tayi yawane yasa Safna saurin bude masa fuska,ta haska da fitila,ido cikin ido suka hada ita da jinjirin Nata, ko a wasa bata taba ganin jinjiri me kyau irin nashi ba,hasalima tafi ganin irinshi a kasashen ketare.karewa Dan kallo take sonshi na shiga zuciyarta,tana tunanin waye ubansa,


Mikewa tayi dakyar taja wani zanin ta daura,sannan ta bude kofar ta fice rungume da danta.


Gidan su maimuna ta nufa,batare da tsoron komai ba,taita bugawa,har mijin maimuna yaji yazo ya bude mata ta shiga,


Tana shiga maimuna ta fito Dan taji muryarta,tana tambayar ta lafiya.


"Maimuna haihuwa nayi kuma baa yanke cibiya ba,su inna kuma sunki taimakamin"cewar Safna a sanyaye.


Da sauri maimuna ta amshi jinjirin daga hannunta ta kamata suka shige daki.


Reza ta dauko sabuwa da zare, ta yanke jibiyar,sannan, ta kwantar da Dan koda ta fito tsakar gida tuni mijinta yajima da hada wuta ya Dora ruwan wanka,tunda yaji duk hirar tasu.


Kamin asuba tuni maimuna ta kimtsa Safna da jinjirin ta,cikin kayan sanyin danta datake goyo. Ita kuma ta bata kayanta tasaka.


Dumamen tuwo ta bata me zafi,tasa mata manshanu ta bata taci ta koshi.


Allah sarki bingirewa tayi agurin tana baccin gajiya.


Maimuna jinjirin tasa agaba take kallo,tana tasbihi ga Allah sabida irin kyau da kyautata surarsa dayayi Wanda ko a mafarki bata taba ganin halitta me kyansa ba.




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/14/21, 12:46 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*




*Kwana biyu bani da lafiya ne shiyasa kuka jini shuru,kuyi hakuri,yanzunma de na daure ne kar shurun tai yawa*




*Page 16*






Bata farka ba se wajen karfe goma,baki ta wanke sannan maimuna tasake bata wani abincin taci.


Bayan ta kammala ne shima jinjirin ya fara kuka alamun yunwa yakeji.a sanyaye maimuna tace.


"Safna kibashi nono yasha tunda ya iso duniya be sha ba fa"


A hankali safna tace "To"
Ta mika hannu ta amsheshi,sannan ta Ciro nonon a kunyace ta bashi,ayko kamar me jira ya cafke yafara ahankali.


Duk da zafin da takeji amma bata hanashi ba,har seda ya cire Dan kanshi ya koma bacci.


Maimuna ta amsheshi sannan ta dubi Safna cikin tausayawa tace"Husna lokaci yayi da zaki nemi uban Dan nan,Dan wanke kanki,daga zargin da ake miki"


Hawayene ya zubo ma Safna sannan tace"a bayanin likitar ubansa ba Dan kasar nan bane, maimuna a ina zan gano shi Nide kawai na dauki kaddara"ta karasa maganar hawaye na bin fuskarta.


"Ki kwantar da hankalin ki,ki bari in kikai arbain seki je gun likitar acan Abujar ta fada miki inda yake "cewar maimuna tana rarrashinta.


A haka sukabar hirar,maimuna ta rakata gida,sabida son ganin kwakwaf matan gidan sukai ta shigowa kallon jinjirin,ayko kan magriba tuni kauyen ya dauka ta haifo Dan larabawa tabbacin shege ne.


Unguwa unguwa akai ta zuwa ganin Dan na safna wacce bakin ciki yasa ta goye Dan tasa hijab ta hana kowa ganin shi.


Haka akai ta tsine mata,masu dungure mata kai nayi,masu dukan kanta nayi wai tayi asarar rayuwa zina da balarabe.


Duk yadda Safna taso danne wannan tozarci takasa,tayi kukan tayi kukan har ta rasa hawayen a idonta ,ko ina ba dadi,har dare jamaa zuwa tsine mata ake,gashi ba Wanda ya hanasu shigowa,


Da misalin karfe daya na dare ta hada ina ta ina ta ta fice daga gidan goye da danta tana kuka batare da tasan ina zata nufa ba, ita de kawai ta fice.


Muje zuwa




Surbajo for life.
11/14/21, 12:47 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*




*Facebook group dina seda nace muku kuda WhatsApp akwai banbancin number karku share a can amma kun dauko kuna share din zaku rikirkita littafin in bazaku dena ba zan dakatar da posting a Facebook din har sena gama gaba daya,*




*Page 17*




Sannu a hankali take tafiya har ta iso titi,gaba daya tsoron barin zuciyarta yayi,Dan haka tsawon titin tabi taci gaba da tafiyarta.


Duk inda titin yay Kwana itama bi takeyi,tana share hawayen ta, tana adduar Allah ya dauki ranta ita da jinjirin su huta.


Abunka da titin kauye,ba motar dake wucewa,shiyasa tai tafiya me tsayi kanta sare ta nemi guri ta zauna hutawa.


Tunda ta zauna kasan wata bishiya batasan ya akayiba sejin hayaniyar motoci taji,da mutane, da sauri ta bude idonta, bacci ne ya dauketa me nauyi bata sani ba.


Mikewa tayi jiki ba kwari taja akwatin kayanta,zuwa gefen titin,


Wata mota tagani gefen titin an rubuta Daura to Kaduna, asamanta,Karen motar se kwalawa fasinja kira yake,tsallakawa tayi kawai taje tace musu Kaduna zata.
Ayko tashiga akasa kayanta a boot,mota ta cika akajasu zuwa jihar ta jamcy lahirar makwalota.Kaduna.


Jinjirinta daya farka ta sauke,tasa abunta a hijab taciro nono tana bashi kukan daya fara tuni yay shuru.




Sha biyu na safe suka iso Kawo garage dake Kaduna, babu kudi a hannunta sukenan ta biya kudin motar, Dan haka,napep kawai ta dauka tace yakaita kasuwa layin yan Dan kunnen zinari.


Me napep ko ya dauketa,har cikin centre market dake Kaduna, yanuna mata layin masu Dan kunnen,ta Ciro na kunnenta Wanda tun suna tare da Rayhan yasiya mata Wanda tuni tamance zinari ne akunnenta seda ta iso kadunan, badashi tayi aka gwada aka siya take kudinta dubu Dari da hamsin,ta biya me napep kudinsa tai masa godiya.


Ajiyar kayanta ta bada a shagon data saida Dan kunnen,ta dauki kayanta kala daya,da emtyn zani Dan goyo danta,sannan ta karasa gurin masu seda kayan sanyin Yara ta siyawa jinjirin ta,harda pampers.


Itama Audiga da pant tasiyawa kanta,tasiya karamin baho,da zata iya yiwa danta wanka,da sabulu da soso.sannan ta nufi gidan wankan da ta gani tun farkon shigowarsu kasuwar.


Koda taje cinikin ruwan zafi sukayi,aka bata,sannan aka bata bandakim da aka gama wankewa,ta shiga,yaronta ta sakko gwanin tausayi,duk yayi kashi yagama bata jikinshi,, cire masa kayan tayi sannan ta wanke masa kashin, tai masa wanka,da ike wankan yakeso ko kuka beyiba.


Tagama,a bayin ta kimtsashi,tasa masa kayan sanyisa,kyanshi,ya kara,fitowa.azani tasashi sannan ta daure zanin ajikin karfen shower din dake bayi,kamar lilo,sannan itama tai wankan ta gyara kanta,wata niima taji tana shigarta,Dan dama ji take kamar tai kuka sabida takurar da tayi.


Bayan ta kimtsa,ta kwashe kayan da suka cire tasa aleda ta Goya danta dake ta faman bacci,ta fito daga bayin.taje ta sayi abinci taci sannan ta koma ta dauko kayanta,ta dawo bakin titi tana ware ido,Dan ita batasan ina zata nufa ba,tsaye take kawai bakin titin tana karewa mutane da ababan hawa kallo.




Ganin ta rasa madafane,yasa ta yanke shawarar tsallakawa daya bangaren ta tambayi wata me abinci data hango,inda zata samu dakin haya.


Hankalinta gaba daya na kan me abincin Dan haka mancewa tayi titi zata tsallaka,shigarta tsakiyar titin yay Dede da dauketa da wata mota tayi,tai sama sannan ta fado kasa.goye da Dan jinjirin ta.wayyo Allah.






Muje zuwa


Surbajo for life.
11/14/21, 12:47 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������


*Zahra Surbajo*


*Page 18*


Mikewa tayi ta koma dakin ta, kudi ta dauko tasa hijabi,ta nufi gun megadi,yana hango ta nufo shi yataso da sauri yadan risina yace "barka da safiya hajiya,me kike da bukata?"amsawa tayi cikin sakin fuska tace"baba don Allah cefane nakeso kayomin,a wuse market,"


"To badamuwa ranki ya Dade kawo aje ayo miki"


Lissafa masa komai tayi sannan ta bashi kudin kimanin dubu tamanin,yatafi .


Kulle gidan tayi ta ciki sannan ta koma cikin gida,wanka ta shiga sannan ta shirya ta dawo falo zaman jiran akawo mata cefanen.


Baa jima sosai ba megadi yashigo mata da sakonta bayan ta bude masa gidan,sosai tai masa godiya sannan ta kwashe komai takai dakinta.


Dan karamin gas din datasa ya siyo mata ta kunna ta daurayo tukunyar daya siyo mata tazo ta hada komai ta Dora indomie acikin dakin Nata.
Dan duk abinda zata bukata seda tasa ya siyo mata.


Haka taci gaba da gudanar da rayuwarta a kulle acikin daki,koda wasa batason ganin Rayhan, shiyasa ta kulle kanta aciki,sabida akwai toilet acikin dakin Nata,


A nashi bangaren Rayhan ko tunda ya fice yabar gidan,kotu yaje ya shigar da karar doctor Amina sakamakon abinda sukawa matarsa,inda alkali yabada sati biyu su hallara agabansa.


Lokacin da sakon ya riski doctor Amina,tashin hankalin data shiga,bashida adadi.Neman Farhan take a waya tun lokacin data ga su Rayhan din amma bata shiga,wannan shine yakara daga hankalinta.


Ranar shiga kotun da safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login