Showing 1 words to 3000 words out of 35375 words

Chapter 1 - Aure Da Haihuwa Book Complete Hausa Novels by Surbajo.txt

30 Nov 2024

1521

*AURE DA HAIHUWA*








*Zahra Surbajo*


*Ina mai Baku hakurin jina shuru da kukayi,da sauyi da kuka samu game da yadda nasaba gudanar da lamurana,hakan ta farune sakamakon kaddarori da suka fadawa rayuwata Wanda banyi tsammaninsu ba,Wanda Alhamdulillahi da taimakon Allah na cinye su,ina godiya ga masoyana wainda basu yada ni ba,Allah saka da alkhairi,*


*Littafina na Hakki ne danake rubutawa watanni hudu kenan da yaci kasuwa,inda nasaida labarin ga wani marubuci Dan kasuwa ze wallafashi akasuwa,ayi hakuri don Allah hatimin nasara kowa ke nema shiyasa daya bukata na sallama ban sanar dakubane nabari se nadawo rubutun se in sanar da fatan zakui min uzuri,sabida tsawon watanni hudun nayisune ahali na rashin lafiya*


_wannan littafi nawa sabo ne me dauke da darussa masu maana,banyishi Dan cin zarafin wani ko wata ba,nayi ne domin fad'akarwa da nishad'antarwa,ga soyayayya me tab'a zuciyar me karatu,kuma kyauta ne bana kud'iba_


_Ku bishi ze k'ayatar daku_




*page 1*






I'd card d'in dake gaban rigarta ta gyara sannan ta gyara farin glass d'in dake fuskarta,cikin murmushi takai dubanta gareshi,tace cikin harshen turanci.


"Ranka ya Dad'e,bawai baze yiwu bane,ina de so ka gane ne wannan shine kwayoyin haihuwarka,da gwajin mu ke nuna mana na k'arshe ne, dole se anbi komai cikin kulawa da takatsantsan,inba haka ba,za'a iya rasa komai"cewar doctor Amina Galadima kamar yadda aka rubuta agaban rigarta.


Gyara zama yayi sannan yakai dubansa gefen matarsa dake ta cika tana batsewa, yayi murmushin k'arfin hali sannan yace,


"Doctor badamuwa na mik'a lamuran ga Allah, ko adace ko akasin hakan,Dan haka kiyi me yiwuwa kawai,kinsan yarda da nai dake ne kesawa in baro k'asata in zo gareki "be gama fad'in abinda yakeson fad'i ba,matar tashi ta katseshi da cewa cikin fad'a da harshen larabci.


"Farhan wannan shine karo na biyar da za'ai dashen kwayoyin halittarnan,wallahi matuk'ar ba'a daceba,to ni kuma zamanmu yazo k'arshe,taya in banda toshewar basira,kana zaune a k'asar Dubai, zaka wani taho Nigeria Neman haihuwa,shekara biyar kenan muna zuwa kullum ba sauyi,to Nide na fad'a maka"ta k'arasa maganar tana huci.


Jingina yayi da kujerar da yake zaune ya lumshe kyawawan idanuwanshi,yana sauraronta,harta gama,sannan ya budesu a hankali,ya zubesu akan matar tashi wacce yake ji inba ita baze iya rayuwaba.
Dubansa ya kai gun doctor Amina sannan yace cikin sark'akk'iyar murya,"doctor please do something meaningful to save my marriage"


Cike da tausayawa doctor Amina tace "insha Allah"


Sallama sukai mata suka wuce masaukinsu,bayan an amshi seamen sample d'inshi,ko a hanya matar tashi me suna shehnaz in banda masifa ba abinda take masa shide kallonta kawai yakeyi,Dan besan yaze mata ta fahimceshi ba.




Bayan wasu kwanaki doctor Amina ta buk'aci daya kawo matarsa Dan adasa mata D'an tayin acikinta.


Koda suka iso asibitin doctor ta shiga tiyatar gaggawa Dan haka d'aki na musamman aka basu su zauna domin jiran fitowarta.


A d'akin suka tarad da wasu mata da miji zaune suma daga dukkan alamu ita suke jira.
Sosai ma'auratan suka tafi da hankalin Farhan,kasancewar manne suke da junansu cikin so da k'auna,ya tsinkayo hirar da sukeyi cikin harshen turanci,inda mijin ke cewa.


"Baby ina fata da addu'ar Allah yasa in anyi dashennan mu dace da samun haihuwa"
murmushi matar tayi sannan ta shafi gefen fuskarshi tace"insha Allahu dear za'a dace jikina yabani hakan"ta fad'i cike da murna a fuskarta.


Sosai suka burgeshi duba da ganin yadda suka damu da junansu kowa k'ok'arin kwantar da hankalin d'an uwansa yake,sab'anin shi da tashi matar wacce keji kamar ta shak'eshi ya mutu ta huta.




Suna nan zaune doctor Amina ta shigo d'akin ita da wasu ma'aikata guda hud'u,daga kallon shigowar tata kai ba se an fad'a maka ba tana cikin tashin hankali,


Duk a firgice take,hakan yasa dukan su maida hankali kanta,cikin sauri sauri tace cikin harshen turanci."don Allah Ku gafarceni,Mahaifina ne Allah yayiwa rasuwa yanzu sakamakon hatsarin mota, zani gida yanzu,amma nayi musu bayanin komai,kuma zasu gudanar dashi cikin nasara"ta k'arasa maganar tana nuna ma'aikatan data shigo tare dasu.


A hankali Farhan yace"badamuwa doctor, Allah yajik'an mahaifinki,yasa ya huta"


Suma wa'incan ma'auratan ta'aziyyar su kai mata,amma banda shehnaz,wacce gaba d'aya ta d'auki tsanar duniya ta d'orawa doctor Amina sakamakon yarda da ita da mijinta yayi.


Cikin hanzari ta juya ta fice daga d'akin,ma'aikatan data shigo dasune suka buk'aci dasu taso su bisu.


Cikin nasara,kowacce an dasa mata sperm d'in a mahaifarta,se fatan Allah yasa adace.


Haka suka baro asibitin kowa na fatan dacewa gurin Allah.




Muje zuwa.




Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*




*page 2*








Tsawon sati biyu kenan da yin dashen,kuma tsawon kwanakin da doctor ta d'ibar musu kenan su dawo ay musu gwajin ciki Dan aga ko andace.


Misalin k'arfe takwas su Farhan suka shigo asibitin, zuciyarshi cike da zullumin abin da ze tarar.a waiting room suka zauna zaman jiran iso daga doctor Amina.


Ita ko doctor Amina nacan cikin office d'inta cikin matsanancin tashin hankalin da ta ma rasa ta yadda zata fuskanci matsalar.


Cikin tsananin bak'in ciki da tashin hankali ta kai duban ta gun ma'aikatan da ta sa su gudanar da dashen,tace,
"Me kuka yi kenan?,innalillahiwainnailaihirrajiun,da wanne bakin kuke son in yiwa mutanen nan bayani,?hankalin ku na ina lokacin Dana ware muku na kowa?,wannan wanne irin ganganci ne?,fisabilillahi ta ina Sunan Rayhan yazo d'aya da Farhan,ta Ina?"ta k'arasa maganar cikin zubowar wasu hawaye masu zafi data kasa tsaidasu.


Suko ma'aikatan motsin kirki cikinsu ba Wanda ya iya yi,Dan sunsan ba k'aramar b'arna suka aykata ba,Dan haka sun rasa ma kalma a bakunansu bare su furta,.


A raunane ta danna k'ararrawar kiran su,ba'a jima ba Farhan suka shigo shida shehnaz dake ta faman cika tana batsewa,doctor na had'a ido dasu wasu zafafan hawayen tausayinsu ya zubo mata ta runtse idon ta, Farhan na ganin hakan yasan ba'a dace ba,Dan haka addu'oi yay ta karantawa a zuciyarshi da zasu sanyaya zuciyarshi.


Bayan sun zauna doctor tayi k'ok'arin dedeta natsuwarta,sannan ta fara magana cikin rashin tabbas,tace"da farko de Farhan inaso ka yarda da k'addarar Allah, mekyau ko Mara kyau"
Murmushin k'arfin hali yayi sannan yace"karki damu Amina, nasan ba'a dace ba na bar komai a hannun Allah"


A raunane tace"Farhan wannan karon ba dacewa bane ba'a yiba,an dace sede an samu matsala daga ma'aikatanmu,akwai wani bawan Allah me suna Rayhan,shima ya zo nan da matarsa Safna, suma haihuwa suke nema,to rana d'aya muka amshi sample d'inku, ranar da za'ayi dashen ni kuma akamin rasuwa,nabar komai a hannun abokan aykina,sabida wajibine ayi dashen a wannan Rana, to matsalar da aka samu,se suka d'auki sample d'inka suka sama Safna,shikuma na Rayhan aka sawa shehnaz"ta k'arasa maganar cikin zubar da hawaye,


Runtse ido Farhan yayi yana karanto duk wata addu'a da tazo bakinsa,tashin hankalin daya shiga baze iya misaltuwa ba,sei da ya d'auki mintuna a haka sannan ya bud'e idanun nasa a hankali,yace,
"To yanzu ya akayi,shi Rayhan d'in ya san da wannan batun?"


Cikin dauriya doctor tace"be sani ba Farhan, sabida shekaran jiya ya kirani,yace yana son ya kawo Safna ay mata gwajin cikin Dan jiya da asuba zasu bar k'asar,tafiyar gaggawa ta taso masa,sun zo nan an mata gwajin kuma sakamakon ya tabbatar da tasamu cikin,ban duba b'arnar da suka yi ba se yau nay ta kiran number Rayhan d'in domin in sanar dashi bata zuwa"ta k'arasa maganar tana zubar da hawaye.


Kife kanshi yayi akan tebur d'in dake gabansu ya fara zubar da wasu hawaye masu zafi,duk yadda yaso ya jure amma ya kasa dole ya koka,wannan wacce irin mummunar kaddarace D'an wani a cikin matar wani,?ina zesa rayuwarsa,yana tsaka da wannan tunani ne ya tsinkayo muryar shehnaz na fad'in.


"Wannan ni ba matsalata bace kai ta shafa,Ni de fatana a gwadani yanzu Allah yasa bana d'auke da cikin wani gardi da ban sani ba"


Ba su da ta cewa dole doctor ta auna ta,abun mamaki,bata samu cikin ba,ita
ayko ana sanar da sakamakon ta mik'e,ta suri Jakarta,ta kai duban ta gun Farhan dake cikin tashin hankali tace a wulak'ance,"zuwa yanzu kasan aure ni da kai ya k'are,Dan bazan k'arar da rayuwata a gidan auren da ba albarkar aure ba,wato Haihuwa,Dan haka na tafi ka san inda zaka ayko min da takardata"tana kaiwa nan ta bud'e k'ofar ta fice a fusace.


Sake runtse ido Farhan yayi yana karanta duk addu'ar data zo bakinsa.


Iya tashin hankali doctor Amina ta shigeshi,Dan haka rarrashin Farhan d'in ta shiga yi da duk wata Kalmar rarrashi data zo bakinta,
A hankali ya d'ago ya kalli doctor sannan yace,"Amina inason abinda wannan mata zata Haifa,da dukkan rayuwata,fatana ki tabbatar da kin samo inda suke kin kuma shaida musu cewa d'ana ne a cikinta,hakan da zakiyi shine kawai yafiyata a gareki,Duk tsawon lokaci Amina ina Dubai Ina kallon hanyar da zaki kawomun gudan jinina,"yana kaiwa nan yamik'e ya fice daga office d'in,doctor Amina na binshi abaya,jiki asanyaye,har zuwa gun da ya ajiye lafiyayyiyar motarshi,ya bud'e ya shige,a hankali doctor ta dafa window motar tace murya na rawa.


"Farhan ka taimakeni lokuta da dama a rayuwata,Kaine silar matsayin da nake kai yanzu,kayimin alfarma so shurin masak'i,nayi maka alk'awarin nemo Safna da mijinta aduk inda suke afad'in k'asarnan,Dan tabbatar musu da cewa D'an dake cikinta ba nasu bane na mune,kuma in dawo dashi zuwa gareka"


Murmushi yayi me taushi,sannan yaja motar ya fice daga asibitin,


Ko takan shehnaz be biba Dan yasan tuni ta jima da barin garin na abuja,ta nufi Lego's Dan siyan ticket d'in daze sada ta da k'asarsu,


Dan haka gida ya wuce yayi wanka ya kintsa duk abinda ze bukata,sannan ya kira agent d'inshi aka tanadar masa private jet daze kaishi k'asarsa ta haihuwa wato Dubai.


Ba'a jima ba ya kirashi ya shaida masa komai yayi ready k'arfe shida zasu tashi na yamma.


Wuni yayi kwance ya rasa meke masa dad'i a rayuwarsa yana son matarsa shehnaz amma ita son da takewa haihuwa yafi son da take masa, gashi kuma ya samu haihuwar ta inda be tab'a tsammani ba,runtse ido yayi yana wa Allah kirari.


K'arfe biyar ya isa airport zuwa shida jirginshi ya d'aga dashi k'asarsa ta haihuwa,cike da kewar gudan jininsa.




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*






*page 3*






*TUSHEN LABARIN*




Safna Habu Sara shine sunanta,d'iyace ga malam habu,dake zaune a k'auyen Sara dake Zangon Daura ta Jihar Katsina,


Malam habu shine limamin garin sabida yana da tarin ilimin addini Dede gwargwado yasa dagacin garin nad'ashi limamin garin


Matanshi uku,inna hansai itace uwargida,se inna fure,se Amaryarsu jamila amma suna kiranta da Sabuwa.


Tunda malam habu ya auro jamila take fuskantar matsi da takura agurin sauran abokan zamanta,sun had'e mata kai sun wareta Wanda hakan ko kad'an be mata dad'i biyayya Dede gwargwado tana musu amma su Sam basa gani,acewa da ganin su duk na munafunci ne.


Inna hansai Nada Yara biyu,jummai,da Ladidi,se inna fure itama guda biyu gareta,akwai Abu se Zabba'u,inna sabuwa ce me guda d'aya wacce malam ya sawa sunan mahaifiyarshi Safina,




Yaran malam habu biyar duka mata Allah be bashi haihuwar d'a namiji ba,shi yasa ya duk'ufa wajen ganin ya basu tarbiya da ilimi ta yadda za ay alfahari da su.


Duk wani cin kashi na gidan akan jamila da 'yarta ake yinsa,an maidasu tamkar bayi,da ike jamila irin mutanen nan ne masu hak'uri ko kad'an bata cewa komai akan abinda ake musu ita da 'yarta.


Tun tasowar 'yanmatan na malam habu Allah yay musu farin jini, kasancewar dukan su da mahaifinsu suke kama,kyau kamar su sukai Kansu,kasancewarshi bafulatani,Safna ce ta kerewa kowa kyau acikinsu kasancewar ita ba iya kamannin malam d'in ta d'ebo ba harda na mahaifiyarta.Wanda hakan yasa ta fice zakka acikinsu.


Duk da tafisu kyau,wani ikon Allah ko kad'an ita bata da farin jinin samarin, kamar wata me bak'in jini,hakan ya sanya su inna fure yiwa sabuwa gorin 'yarta ba mashinshini.


Ita sabuwa abin be damunta Dan tasan aure lokacine,in yazo za ayi.


Wasa wasa har an kawo kud'in sauran 'ya'yan gidan amma Safna har yanzu ba me cewa yana sonta.




Suna Aji biyar a secondary school aka sha bikin sauran 'yan uwanta,inda kowacce ta tare a gidanta,aka bar Safna ita kad'ai a gida.


Zuwa lokacin lamarin yafara tab'a zuciyar sabuwa,amma ta duk'ufa da addu'a.


To bayan aurar da 'yanmatan gidan ne wahalhalu suka k'aru akan Safna, ita ce d'ebo ruwa,ba dabbobi abinci,shara wanke_wanke,girki,yo itace ,acewar matan gidan in bata yiba Wa ze mata.


Duk ta fice hayyacinta kullum mahaifiyarta kwarin guiwa take bata da cewa watarana se labari.




Muje zuwa




Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*






*page 4*








Yau tun asuba ta mik'e tayi duk aykace aykacenta,sabida yau ake taron sunan 'yar gidan inna hansai jummai ta haihu.


Ko da ta gama shiryawa,tuni su sabuwa da inna fure da sauran makwabtansu sun tafi gidan sunan,da ike a zango tai auren, Dan haka fitowa tayi cikin kwalliyarta ta nufi gidan su k'awarta Maimuna,dama tare zasu tafi gidan sunan.


Tana zuwa ta samu Maimunan ta shirya ita kawai take jira,Dan haka rankayawa sukai suka nufi titi Dan samun abun hawa da ze kaisu garin na zango.


Tsaye suke a bakin titin amma babu abun hawa,cikin damuwa Maimuna tace"yau fa alamu sun gwada 'yarfillo a k'afa zamuje zangon nan,kuma wallahi ga rana"


Murmushi Safna tayi daya k'ara fito da kyawun fuskarta,tace cikin siririyar muryarta,"da alama kuwa,kawai mu fara takawa,tunda ba wani nisa bane sosai,watak'ila a gaba mu samu"bata k'arasa maganar ba taji k'arar taka burki a gabansu,a tsorace dukan su suka dubi kan titin,wata shirgegiyar mota suka gani tana k'ok'arin gyara parking a gaban su,


Tana gama tsayawa na cikin motar ya fito,matashine kyakkyawa ajin farko,Wanda Hutu da ilimi suka samu masauki a jikinshi,sanye ike cikin farar shadda,tasha d'inkin zamani,kanshi ba hula se sumar daya Tara data dace da tsarin kwalliyar tashi.


Cikin takun burgewa ya k'araso gabansu fuskarshi d'auke da murmushi,yace"Amincin Allah ya tabbata a gareku,Ku gafarce ni firgitaku da nayi"ya k'arasa maganar yana had'e hannayensa guri guda.


Safna sarkin kunya,sunkuyar da kai tayi tana murmushi,yayin da maimuna tace"amin,mungode ba komai"


"In bazaki damuba Dan Allah kitaimaka min da sunan k'awar taki Dan naga kamar rowar magana gareta "yayi tambayar yana kallon fuskar Safna wacce har yanzu murmushi kawai take yi ba tace komai ba.


Murmushi maimuna tayi sannan tace "Safna sunanta dafatan ba zuwa sace ta kayi ba?"


Murmushi yayi yace"ita ta fara satoni,so shine nima nake so da taimakon ki ki tallafamin in saceta zuwa gidana na aure"


Da sauri Safna ta b'oye a bayan Maimuna,alamun taji kunya sosai,har zuwa lokacin murmushi be bar fuskarta ba.


"Se mun bincika tukuna in nagartarka ta kai a baka se ayi hakan sabida komai nufin Allah ne"


"Sunana Rayhan Hashim Daura,mahaifina Dan daura ne amma muna zaune a Abuja sabida yanayin Ayki,nazo bikin abokina ne nan yardaje,se kuma Allah ya had'ani da tawa amaryar a hanya"


Haka yay ta jansu da hira amma Safna ta gaza furta komai,har suka samu abun hawa,fafur suka k'i yarda su hau motarshi,gashi dukan su bame waya,Rayhan ganin zata kubce masa ne yasa ya d'auko wayarshi dank'areriya a gaban motarshi ya mik'awa Safna, yace "ba Dan na isa ba Dan Alfarmar Annabi ki amshi wayarnan,in muka rabu yanzu ban san ina zan sake ganinki ba,sabida yau zamu wuce gida,amma inda wayar a hannunki zan kira kimin kwatance"


Jiki a sanyaye Safna tasa hannu ta amshi wayar,se alokacin tace a tsorace murya na rawa,"zan zan...ajiyema in...muka had'u zaka amshi abunka"wani sanyine ya ratsa zuciyar Rayhan sakamakon jin muryarta da yayi.


"Na amince beauty semun had'un,"


Daga haka sukai sallama suka shiga mota shima ya shiga tashi,da ike hanya dayace haka yay ta bin su a baya har aka sauke su a zangon sannan yay musu hon yayi gaba.


Jikin Safna a sanyaye suka isa gidan sunan daya cika da jama'a.




Ko a gidan sunan seda aka mata habaicin ba mashinshini,ayko carab maimuna ta amshe zancen da cewa,"mashinshini de kam Safna Allah ya nufa ya shinshino ta,kuma insha Allahu se ya tsone idon mak'iyanta"


Ayko gaba d'aya gurin aka sa shewar zancen Nata.


Basu baro gidan sunan ba se isha'i sabida seda suka gyarawa mejego gida tukuna suka tafi.


A gajiye Safna take,Dan haka tana zuwa gida wanka tayi ta kintsa sannan ta Ciro wayar ta samu innarta tai mata bayanin komai game da had'uwarta da Rayhan yau.
Farincikine ya mamaye zuciyar innar ta,gami da yiwa Allah godiya daya fara haska tauraruwar 'yarta a idon manema sabida itama ta samu tai aure ta huta.


Nasiha da Jan kunne tai mata kan tade kama kanta da mutuncinta banda giggiwa,daga k'arshe tai fatan alkha'iri.


Muje zuwa




Surbajo for life
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*






*Page 5*






Safna shirin bacci tayi,tayi addu'a ta tofa tana kwanciya taji wani sauti me dad'i na tashi ak'asan fulonta,da har ta firgita can kuma ta tuna da wayar da Rayhan ya bata,Dan haka a tsanake ta d'auko wayar,bata wahalar gane kanta ba,sabida tana karatu,a hankali ta d'aga wayar ta kara a kunnenta,wata sassanyar ajiyar zuciya Rayhan ya saki wacce ta haddasawa Safna wani bak'on lamari ajikinta,sosai jikinta ya mutu,a hankali ta jiyo muryarshi yace a kasalance "beauty"sosai sunan da muryar da yay amfani da ita gurin kiran sunan Nata sukai mata dad'i,


ahankali cikin siririyar muryarta tace "ranka ya dad'e"


Rayhan kusan mirginowa yayi daga kan gadonshi Dan dad'in sunan da ta kira shi da shi,k'ara k'asa yay da murya sannan yace
"Kinyi kewa ta kuwa?"
Murmushi tayi me sauti sannan tace"gaskiya zan fad'ima ko k'arya?"


Yace "gaskiya"tace "to gaskiya d'aya banyi ba"


Shuru ya danyi sannan yace,"Ina sonki Safna shin kema kina sona kuwa?wallahi in har za'a bani ke safna nan da sati biyu na shirya auren ki,ba yaudarar ki nazo yi ba"


A hankali safna tace "Komai nufine na Allah, ganin farko zuciyata ta yarda da kai,ina fatan Allah ya baka ikon rik'eni amana,yasa akwai alkha'iri a tsakaninmu"


Cike da zumud'i yace "Amin beauty na"


Daga haka hira su kai ta abinda ya shafi karatu da nasaba,har zuwa sha d'ayan dare sannan su kai sallama yakashe.


Wasa wasa soyayya ce suke yinta me tsabta tsakanin Safna da Rayhan, sosai take jin son sa a zuciyarta,shima haka.


Tuni Inna Sabuwa ta sanar da Malam Habu komai sabida Safna bata b'oye mata komai tsakaninsu.


Yau Rayhan na hanyar zuwa gun masoyiyar tashi,shi murna ita murna,tun safe taje gidansu maimuna suka shiga girka abincin da zasu tarbe shi,Wanda Inna Sabuwace ta amso dubu uku gun malam ta bata,ayko wainar shinkafa sukai masa da miyar kaji Wanda malam yasa aka yanka zakaru manya guda biyu na tarbar sirikin nasa
Zob'o suka had'a suka siyo k'ank'ara suka sa,yayi sanyi gashi se k'amshin kayan k'amshi yake,fura da nono me kyau ta dama masa tasa k'ank'ara,sannan ta gurza kwakwa ta zuba aciki.


Acikin kulolin tarin auren maimuna aka jera komai,wanka tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login