Showing 3001 words to 6000 words out of 35375 words

Chapter 2 - Aure Da Haihuwa Book Complete Hausa Novels by Surbajo.txt

30 Nov 2024

1523

agidan su maimunan sannan tasa doguwar rigarta ta shadda me ruwan hanta,wacce k'anwar innarta ta d'inko mata a daura d'inki ya dace da jikinta, bata d'aura d'ankwalin ba,illa kama gashinta me yawan gaske da tayi da ribbon sannan ta fesa turare,bame kallonta yace awannan kauyen take,sosai kyanta ya fito,bin jikinta da doguwar rigar tayi shi ya bayyana asirin kyawun dirinta,domin duk inda akeson mace safna takai.


Tana tsaka da fesa turaren ne wayarta tai k'ara a hankali tasa hannu ta d'aga Dan tasan me kiran,cikin siririyar muryarta tace"ranka ya Dad'e ya hanyar?"
"Hanya Alhamdulillahi beauty gani na iso inda muka had'u daku ranar farko "
"Barka da zuwa bari in turo a k'araso da ku,"sabida yashaida mata tare da abokinsa suka zo.


Cikin shagwab'a yace"beauty ke nake son fara gani please babu D'an ayke a tsakaninmu kizo da kanki"


Murmushi tayi sannan tace "to ganinan zuwa"daga haka suka kashe wayar.




Dubanta ta kai gun maimuna tace" taso muje mu iso dasu mutumim naki kwai rigima wai sede inzo da kaina in mai iso"


Dariya maimuna tayi sannan tace "wallahi k'awata Ina tayaki murnar samun Rayhan amatsayin masoyi Allah yasa har aure,nima kuma Allah ya bani nawa masoyin muyi aure mu huta da gorin garinnan"


Murmushi Safna tayi tace"amin k'awata"


Mayafi maimuna ta yafa bayan ta dan murza hoda,da ike itama farace kyakkyawa,Tass ta fito,bakin titin suka nufa.




Rayhan ne zaune a kan boot d'in motar yana latsa waya, yayin da abokinsa Haisam ke tsaye a gefenshi yana ta masa dariya yace"Ni wallahi gaba d'aya na raina ajin naka ace ka wuce turai,ka wuce Abuja ka wuce Kaduna ka wuce kano ka wuce katsina wai kazo wannan k'auyen anan ka gano matar aure,se wani kurantata kake yi se mutum ya ganta ya kusa amai" dariya Rayhan yayi sannan yace,"Safna tafi duk 'yanmatan wa'innan guraren daka ambata,ita ta dabance"hango su safnar ne ya katse masa hanzari.
Inda ya diro daga kan motar yana fad'in "tsarki ya tabbata ga mak'agin wannan sura"


Safna na hangoshi yana mata murmushi itama tai k'asa da kai tana masa murmushin,har suka k'araso gurin su bakin Rayhan yak'i rufuwa,sabida tayi masa kyau fiye da yadda ya ganta rannan.
.shi kanshi haisam ya gigita da ganin Safna Dan koda ya hangosu be dauka su bane.


A hankali ya kai dubansa gun Rayhan yace"abokina 1000%tayi"dariya sukai sannan maimuna ta gaida haisam.


Shiko Rayhan yasa Safna a gaba se zagayeta yake yana k'are mata kallo yana yaba kyan da Allah yay mata azuciyarshi,amma afili fad'i yake,"inyenba y'anmatana ta yi kyau"


Duk ya gama bata kunya,Dan haka a d'an shagwab'ance Wanda bata san sanda tayi ba,tace"ya isa haka kuzo mu k'arasa gida mana baffa yana gida yana jiran k'arasowarka"


Kusan suman tsaye yayi jin yadda tai maganar a shagwab'e.


Motar ya buk'aci da ta shiga su k'arasa, mak'ale kafad'a tayi tana murmushi Wanda hakan sosai ya burge Rayhan, Dan haka haisam ke binsu abaya da motar shi kuma suka jero tare da gimbiyar tashi da maimuna zuwa k'ofar gidan.






Muje zuwa




Surbajo for life
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*








*Page 6*






Tunda suka jero idon yan garin yayo Kansu,Rayhan ko a jikinshi,shi hakan ma wani alfahari ya k'ara masa.


A k'ofar gidan suka tsaya sannan Safna ta shiga d'akin soro,ta sanar da malam zuwan nashi.


Umarnin ta shigo dashi ciki yayi mata, sannan ya mik'e ya shige cikin gida.


Komowa tayi gunshi kanta a k'asa tace ku shigo ciki inji malam.


Shide kunyar ta na k'ara sa mishi sonta a zuciyarshi, ansawa yayi,sannan suka biyota a baya har zuwa d'akin.


Dardumai ne shimfid'e a ciki,Dan haka zama su kai,Maimuna dama tuni ta nufi gidan su tasa k'aninta ya kwaso kayan abincin shi da abokinshi suka kawo inda su Farhan d'in suke.


A kunyace Safna ta zuba musu abincin,sannan ta mik'a gabansu tace "ga abinci kuci kunsha hanya",


Murmushi Rayhan yayi sannan ya kishingid'a yace"Nide se in a baki za'a bani zanci in ba haka ba nak'oshi"


A kid'ime ta zaro ido tana kallonshi,kan kace kwabo idanun ta sun kawo ruwa,cikin shagwab'a da muryar kuka tace"ka rufamin asiri,bansan ya Nisan garin Ku yake ba, amma ana fad'in se an wuce jihohi uku kan aje,taya zaka yo wannan tafiya kace ba zaka ci abincina ba,kuma fa tun safe nake had'a maka"ta k'arasa maganar cikin turo D'an k'aramin bakinta gaba.


Tunda ta fara magana hankalin Rayhan gaba d'aya ya koma kanta,sonta da sha'awarta ke shawagi a zuciyarsa,yadda yake son matarshi ta aure ta kasance haka safnar sa take.cikin sigar rarrashi yace "is ok baby na,wasa fa nake miki ni na isa in k'i cin abincin gimbiyata,share hawayenki kar haisam ya raina min ke tun yanzu"


Dariyar da haisam ya yine yasa ta mik'e ta fice daga d'akin da D'an gudunta,bin bayanta Rayhan yayi da idanu,ji kake makwat ya had'iye wani miyau daya taru masa abaki.


Koda suka gama cin abincin alwala su kai suka je masallaci su kai sallah sannan suka jero da malam zuwa cikin gidan.d'akin soron suka shiga.


Cikin girmamawa suka gaisa da malam sannan suka gabatar da Kansu Wanda haisam ne kewa malam bayani shi Rayhan yayi shuru alamun jin kunya.


Bayan dogon bayani malam ya gano gidan kakannin Rayhan dake daura farin sani ya sansu,amma sabida jawa y'arsa k'ima se yace.


"Naji duk bayanin ku kuma na gamsu da shi,zan yi bincike game da hakan in na ga ba wata matsalar na amince in daura aurenka da mamana kamar yadda ka buk'ata zan sa ka turo magabatan ka bayan na kammala binciken,Allah yay muku albarka"


Amsawa sukai da "Amin baba mungode Allah ya k'ara girma"sallama yay musu sannan ya fice daga d'akin,


Bayan fitar malam ba'a jima ba safna ta shigo kanta a k'asa alamar jin kunya,fuskarta d'auke da murmushi.


Guri ta samu ta zauna,bata jima da zama ba maimuna ta shigo,suka shiga hira dasu haisam,cike da wayewa haisam yace"maimuna muje ki nunamin kan garinnan naku,ko nima zanyi arba da y'ar fillon da zata saci tawa zuciyar "murmushi maimuna tayi sannan ta mik:e suka fice daga d'akin.


Shuru ne ta ratsa d'akin tun bayan ficewar su haisam,Safna tayi k'asa da kanta se wasa take da abun hannunta.
Cikin tattausar murya yace"na takura ki da yawa ko baby na?"cikin murmushi ta girgiza kanta alamar ba haka bane,murmushi yayi ya mik'e daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna Wanda har jikinsu na tab'a juna,tsorone da firgici tsababa a idon safna,ya lura da hakan.


Murmushi yayi sannan ya sa hannu ya kamo hannunta,da sauri ta d'ago ido tana kallonshi,tana k'ok'arin kwace hannun Nata amma be bata damar hakan ba,a hankali ya furta,"Safna bazan tab'a cutar dake ba,ni din masoyinkine,amma naga ke kamar baki yarda dani ba,ko me yasa?"a hankali tace a d'an daburce "ba haka bane"


Matso da fuskarshi yayi sosai kusa da ta ta yana kallon idanuwan ta da shanyanyun idanuwan sa yace can k'asan mak'oshi "to yaya ne?"


Kasa magana tayi illa runtse idanun ta da tayi,Dan bazata iya jure kallon kwayar idanuwan sa ba


.murmushi yayi sannan ya saketa ya Dan matsa daga kusa da itan sannan yace "to oya bud'e idanun naki dodon ya matsa daga kusa dake"


Haka de yay ta jan ta da hira tun tana kin amsawa har tazo ta saki jiki dashi suka sha,hira.


Sai da aka idar da sallar isha'i sannan yay mata sallama bayan ya jibge mata kwalayen tsarabar da yayo mata,gami da bandir din kud'i dubu ashirin.duk yadda taso ya tafi da kud'in fafur yak'i,dole tasa ta amsa Dan har yayi fushi,.


Haka suka rabu cike da kewar juna,daura zasu su Kwana da safe su wuce abuja.




Muje zuwa




Surbajo for life
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra Surbajo*








*Page 7*








Cikin k'ank'anin lokaci Malam shi da Amininsa Baban maimuna suka je binciken waye Rayhan har garin Abuja.bayan sun gama binciken usulinsa na Daura.


Cikin ikon Allah ko ina beda nakasu,hakan sosai yayiwa malam dad'i Dan yana son Rayhan d'in.ya yaba da natsuwarsa.


Cikin sati guda mahaifin Rayhan da aminansa suka zo nemawa Rayhan d'in auren Safna, duk wani Abu na al'ada sun gabatar dashi inda aka sa ranar auren sati uku masu zuwa,Wanda shi Rayhan d'in Sam be so asa da nisa haka ba,Dan amatse yake da son mallakar matarshi.


Suko matan malam habaici da zagi da mugun fata game da auren na Safna ba Wanda basu yi ba,ita de Inna sabuwa ido tasa musu,a zuciyarta kuma ta na bin y'ar tata da addu'a.


Duk wani gyaran Amarya k'anwar innarta da ke daura ne tai mata,
Tuni Amarya ta fito a amaryarta.


Ko ina a garin na Sara gulmar auren na Safna ake yi,inda ake ta yamad'id'in auren kud'ine,shi yasa aka yi saurin tsaida lokaci.


Malam ma toshe kunnensa kawai yayi Dan maza ma ba'a barsu a baya ba gurin gulmar auren na 'yarsa


*********


Rayhan matashine D'an kimanin shekaru 33 da haihuwa,farine amma ba tas ba, dogo ne, me D'an jiki Wanda ba za'a kirashishi lukuti ba,dirarrene ta kowanne tsagi,
Fuskarshi zagaye take da kwantaccen sajen daya dace da zubin fuskarsa,


Rayhan mutum ne me ilimin boko da islamiyya sabida yayi dace da iyaye nagari Wanda suka bashi tarbiyya.


Ko kad'an sharholiya bata cikin tsarinsa a natse yake,shiyasa yake yawaita yin azumi Dan kame kansa




Mahaifinsa Alhaji Hashim D'an kwangilane,Wanda ya tara dukiya me yawa,matar sa D'aya,Hajiya Hafsa wacce takasance y'ar kasuwa dake saro kaya daga k'asashen waje ta kawo gida Nigeria ta siyar.
'Ya'yan su uku biyu mata d'aya namiji Wanda shine Rayhan d'in,kuma shine babba,sauran k'annensa ne,nuzula da jawahir,Wanda yanzu haka suna jami'a suna karatu.


Rayhan yayi karatu a k'asar England, inda yayi karatu a fannin kasuwanci,Wanda shine abinda yafi burgeshi shiyasa ya zabi fannin.


Koda ya kammala ya dawo gida, mahaifinshi mak'udan kud'ad'e ya bashi Dan ya fara gudanar da kasuwancin,in da be yi k'asa a guiwa ba yasa hannun jari a harkar saida man petur,sannan ya gina gidajen mai guda uku nashi nakanshi Dan jin dad'in gudanar da kasuwancin.


Tunda ya kammala karatu kullum burin iyayensa yayi Aure sabida shekarunsa na tafiya,shima yana da burin hakan se de wacce ze aura d'inne be gani ba.


Mahaifiyarsa da k'annensa sunfi kowa murna da jin ze yi aure,Dan haka suka shiga shirya lefe nagani na fad'a Wanda za'a kai gidan su Safna.


Wannan kenan


************


Ranar jumma'a dubban mutane suka halarci garin na Sara domin shaida auren Safna da Rayhan, Wanda ya kafa tarihi a garin na Sara.
.Wanda manyan 'yan kasuwa da jami'an gomnati,da masu fad'a aji suka halarci d'aurin Auren.


An d'aura auren akan sadaki naira dubu D'ari,Wanda ango Rayhan bakinsa Sam yak'i rufuwa ko ina ka waiga makad'a da marok'a ne ke ta aykinsu.


Tuni an gama shirya Amarya wacce tai kuka har ta godewa Allah, Dan tare da 'yan d'aurin Aure za'a tafi da ita,bayan malam yay mata nasiha game da zaman Aure.


Kuma malam ya hana kowa zuwa rakata,a cewarshi d'orawa mijinta d'awainiya za'a yi,


Haka aka fito da ita tana ta rusa kuka,motar da ango ke ciki aka sa ta,direba ya ja sauran motoci suka Mara musu baya.


Koda ta shiga motar d'ago ido tayi Dan taga waye a kusa da ita,carab idonta ya shiga nashi yana mata murmushi, fad'awa jikinshi tayi ta ci gaba da kukanta.


Rungumeta yayi sosai a jikinshi yana sakin wata ajiyar zuciya, wani Abu ke taso masa tun daga tafin k'afarsa zuwa tsakiyar kansa, a hankali ya shiga rarrashinta cikin murya me dad'i,yace"kukan na menene baby,haka?"cikin kukan take kai masa k'arar malam kan hana rakota da yayi.


Bayan ta ya shiga shafawa yana hura mata iska a kunne,Wanda sannu a hankali kukan ya gudu,sautin numfashinta da yaji ya sauya ne yasa ya fahimci bacci tayi.


Murmushi yayi sannan ya gyara mata kwanciyarta a jikinshi ta yadda ba zata wahala ba,sannan ya maida kallonsa gaban motar,ido suka had'a da haisam dake Jan motar ta glass, ayko ya tuntsire masa da dariya,sannan yace"baba kode transit zamu yi a hanya ne kad'an maida miyau kan mu wuce?"duka Rayhan ya kai masa. Ya goce dariyar dukansu sukeyi.




Muje zuwa


Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������






*Zahra Surbajo*






*Hauwa'u Muhammad Danjuma NBS keffi,Duk k'awar da ta dace da k'awa aminiya irinki to ta hau gado tai bacci,Dan inde da ranki da lfy bazaki bar damuwa ko b'acin rai ya iso gadon baccinta ba,Allah yasaka miki da Alkha'iri farin cikin da kike sakani ni da D'ana yusuf bamu da abun biyanki,Allah ya d'aukaka darajarki Dan halak be mance halacci akanki na tabbatar da haka*






*Page 8*




Da isha'i suka Iso gidan Rayhan dake Abuja, gidane na alfarma Wanda ko a mafarki Safna bata tab'a ganin kanta a cikinshi.
Ba kowa a gidan se su da suka shigo yanzu,Dan Abban Rayhan hana kowa zuwa yayi shima yace a bari se ta Kwana biyu a zo.


Haisam na sauke su yay musu sai da safe bayan ya mikawa Rayhan kaji da madarar da suka siyo a hanya, ya ja motar ya fice daga gidan,yana tsokanar Rayhan, Safna tsayawa tayi a harabar gidan duk se taji ranta ba dad'i ganin shima danginshi ba Wanda yazo tarbarta.
Rayhan d'inne ya matso inda take ya kama hannunta ya ja ta a hankali zuwa cikin gidan,inda take tafiya a hankali kamar bazata ba.


Be a jiyeta a ko ina ba se akan gadonta Wanda ya gaji da had'uwa,a sanyaye ta zauna kanta cikin mayafi a k'asa.


Muryarshi ce ta katseta daga tunanin da take inda yace "zani d'aki in kimtsa kema ki samu kid'an watsa ruwa kamin in dawo,ga toilet nan acikin d'akin"ya fad'i yana lek'a fuskarta, da sauri ta kara sunne kanta k'asa,lakace mata hanci yayi sannan ya fice daga d'akin.


Bayan fitar shi ta jima zaune sannan ta mik'e ta shige toilet d'in,suman tsaye tayi ta tsaya tana k'arewa toilet d'in kallo,,to in banda abun Rayhan taya zata iya amfani da toilet d'in,da ta rasa yadda zatayi kawai sai ta dawo d'aki tai zamanta.


Rayhan be jima ba sosai ya dawo sanye cikin farar jallabiya data bi fatar jikinshi ta kwanta lub.hannunshi rik'e da ledojin da suka shigo dasu d'azu,


Da sallamarsa ya shigo d'akin,sosai yay mamakin ganin ta inda ya barta tun d'azu,ajiye kayan hannunshi yayi,sannan a hankali ya taka ya isa gareta,gefenta ya zauna,sannan yasa hannu yacire mayafin dake kanta,da ike ba d'ankwali hakan yaba gashinta da yasha gyara damar bayyana se shek'i yake.


A hankali ya janyo ta jikinshi,yay mata mafaka a k'irjinshi,sannan yasa hannu a hankali ya cire ribbon d'in da aka kama mata gashin dashi,hakan yaba gashin damar bazuwa har kan k'irjinshi,wani niimtaccen kamshi yaji ya bugu hancinshi daga gashin Nata, zib d'in rigarta ya fara nema a hankali ya fara zuge shi,da sauri safna ta dago manyan idanuwanta tana kallonshi,hure mata idon yayi sannan yasa hannu ya gyara mata gashin kannata,daya zubo mata a fuska,yace yana d'aga mata gira, "wankan zan miki tunda nace kiyi kin k'i"
A kunyace tace"ba k'in yi nayi bafa,toilet d'in ne ban gane kanshi ba shiyasa"


Se alokacin ya tuna daga inda ya d'auko safna,dole bazata iya amfani da toilet d'in ba matukar ba bayani yay mata ba.


Murmushi yay mata sannan ya k'arasa zuge zib d'in,yana fad'in"ba komai ni ay tunda na dawo se in miki wankan"ya k'arasa maganar,yana cire mata hannayen rigar,Wanda hakan yaba albarkar k'irjinta damar bayyana,
Safna kasa hanashi tayi,sabida a fad'an da aka mata a gida ance yin hakan sab'awa Allah ne😄hakan ne yasa ta barshi yake yadda. Yaga dama da ita.


Rayhan Ido ya k'ura musu yana kallo,se yake ganin abun kamar a mafarki wai shine zaune da Safna ba Riga ajikinta,a matsayin mata da miji,a hankali ya mik'a hannu ya rungumota zuwa jikinshi yana sauke wata ajiyar zuciya,yace can kasan makoshi"baby komai naki me kyau ne,Allah yasani beauty inason mace me cikar halitta kuma se gashi Allah ya bani full options"sunne kanta tayi a k'irjinshi Dan ita gaba d'aya kunya ce fall idanunta.


Da kyar ya sake ta sannan yaja hannunta zuwa toilet d'in ya nuna mata komai sannan ya fito,nashi d'akin ya koma, yayi tsarki ya d'auro sabuwar alwala Dan ta d'azu ta lalace😄




Safna wanka tayi sannan ta d'aura alwala,ta d'auro tawul ta fito,Wanda fitowarta yay daidai da shigowarshi.


K'asa tai da kanta tana wasa da hannunta,kallo d'aya yay mata yaji yana shirin b'ata sabuwar alwalarshi yasa ya dauke kai da sauri.


Ma'ajiyar kayan sawa dake d'akin yaje ya bude ya d'auko mata wata rigar bacci Dede guiwa se dogon hijab na sallah da zani empty da zata d'aura.


Kayan maminshi ce tasa aka tanajesu tun kan su tare.


Gabanta yaje ya mik'a mata kayan sannan ya juya mata baya, rigar tasa sannan ta zame tawul d'in jikinta se rawa yake ta d'aura zanin ta saka hijab d'in,rab'awa tayi ta gefenshi ta wuce inda taga ya shimfid'a dardumar yin sallar.




Muje zuwa.






Surbajo for life.
11/14/21, 12:43 PM - MY MTN 2: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������




*Zahra surbajo*






*Page 9*






Bin bayanta yaje yayi suka tada sallar,
Koda suka idar addu'o'in zaman lafiya da samun zuri'a dayyiba yay musu sannan yajanyo ledojin da ya shigo dasu,yafito musu da nama da madarar dake ciki suka ci suka sha,Wanda safna tayi Nata da taimakon Rayhan d'in.


Safna brush tayi tazo ta kwanta,yayin da Rayhan seda yagama kashe wutar ko ina sannan yabi bayanta,


Ganin shi kwance daga shi se gajeren wando agefenta shi yafi komai sata rud'ewa,se mutsu-mutsu take a gadon ta kasa baccin.


Hannu ya mik'a ya janyota gaba d'aya jikinshi,,yay mata rumfa da faffad'an k'irjinshi, sannan yasa hannu yana gyara mata gashin kanta,a hankali yace
"Me ya hanaki baccin babyna?"


Akunyace tace "ba komai"


K'ara matsarta yayi yace"kode ni kike buk'ata ba?"
Da sauri tace"ni wallahi ba haka bane"tayi maganar kamar zatai kuka.


Murmushi yayi me taushi,sannan ya had'e bakinshi da nata ba tare daya ce komai ba.
A hankali yake tsotsar bakin Nata cikin salon da Safna ba zata iya jurewa ba,hakan yasa take ta mutsu mutsu,yayinda gefe guda kuma ta lumshe ido alamar tana amsar sakon.
A hankali ya cire bakin nashi akan nata yace cikin dusasshiyar murya yana kallon fuskarta,"baby ni bazakiyi kissing d'ina bane ko ko bakyason Wanda ni nake miki ne?"ya k'arasa maganar yana shafo gefen Boob's d'inta.
Girgiza masa kai tayi gami da b'oye fuskarta a k'irjinshi.


Kyaleta yayi yaci gaba da sarrafata yadda yake so,tun bata maida martani har tazo tana biye masa.


Wannan dare Safna ta gurzu a hannun Rayhan ta yadda ko hannu bata iya d'agawa,se ido dake zubda kwallar danasanin biye masa da tayi.


Da kanshi ya taimaka mata ta gyara jikinta,se lallab'ata yake kamar kwai,yana sa mata albarka.


Pain killer yabata,sannan ya d'auketa cak zuwa dakin shi inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login