Showing 33001 words to 35375 words out of 35375 words

Chapter 12 - Aure Da Haihuwa Book Complete Hausa Novels by Surbajo.txt

30 Nov 2024

1529

badan yasoba ya miƙe yaje ya ɗauko mata ya kawo mata,yakoma yaci gaba da baccinsa me daɗi.


Cikin bacci yaji ta kuma ɗaka masa dukan,a firgice ya farka,wannan karon wiper akasa shi miƙowa akan madubin again😄


Kwanciya yakumayi yaci gaba da baccin,can cikin baccinsa yakuma jin ta ɗaka masa wani dukan,yana buɗe ido yace "mezan miƙo muku?"ya faɗi cikin takaici.


Murmushi tayi sannan tace"dama zan nuna maka murmushin da yake ne yana bacci,wallahi harda É—an sauti murmushin"ta faÉ—in cike da nishaÉ—i.


Gwajab ya koma ya kwanta,ya lumshe ido,bece mata komai,ba haushi taji dan haka wani dukan ta sake kwaɗa masa tace"kai kaji haushi,kar ka kalla ɗin"😄


Ranar farhan seda yayi danasani tafi dubu na kwana a É—akin na Shehnaz,dan in motsi yaron yayi seta tasheshi ta nuna masa,kan gari ya waye kuwa an sauya wa yaron kaya so uku,wai datti suke shiyasa take sauyawa.


Asubar fari Farhan ya fice a É—akin idonsa cike da baccin da be samu damar yi ba


Muje zuwa


Surbajo for life
11/29/21, 1:15 PM - Ummi Tandama😇: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������


*Zahra Surbajo*


*52*


Shehnaz ko ko baccin ma bata ji,ita data kwana azaune.
Farhan be fito ba se misalin ƙarfe goma na safe,yayi wanka ya kimtsa,idanunsa har yanzu akwai ragowar kumburi na sauran bacci.


Ɗakin shehnaz ɗin yafara shiga,a tsaye take saɓe da ɗanta a kafaɗa tana ɗan masa waƙoƙi cikin harshen larabci,tana ganinshi tace"yauwa habibi jeka gun Safna kace ta baka soson wankan baby zan masa wanka,"


Dama yasan zaa rina ko gaisawa bata bari sunyi ba ta fara aykenshi.
Haka ya juya zuwa part É—in safna yana mita.


Safna na ganinshi ta taso ta rungumeshi,fuskarta É—auke da faraa.
Duban tsanaki tai masa sannan tace"Me kuma yafaru naganka da ido luhu luhu kamar fanke?"


Tsaki yayi sannan yace"nifa kin haɗani da jidali wallahi,ita bata huta ba nima bata barni na huta ba"daga haka ya kwashe bidirin da akayi jiya,amma banda ƙin yarda ya kusanceta sabida wannan sirrinsune,ya sanar da safna.


Safna dan dariya har ƙwarewa takeyi,farhan ne ya katseta da cewa"yanzuma aykoni tayi,tace kibada sabulu"


Dariyarce ta sake kubcewa safna wannan karon harda tari take dan dariya.


Haka ta ɗauko ta miƙa masa tace"to Abu musaddiq,agaida ummu musaddiq"


"zan kamaki ne"ya faÉ—i sanda ya fice daga É—akin.


Inda ya barta nan ya sameta ya miƙa mata sabulun ya nufi kujera da niyar zama da sauri ta dakatar dashi da cewa.


"Habibi ina towel É—in babyn fa?"


"sabulu kawai kikace"yabata amsa.


"to kai yaro ne da zakace sena lissafo komai,ay kasan akai wanka zaa tsane jiki,ni dan Allah kai sauri ka amso min"


Wayyo Farhan yaga takanshi,juyawa yayi yakoma gun safnar,yana buɗe ƙofar ya tsaya bece komai ba.


Dariya tayi sannan tace"Abu musaddiq me ummu musaddiq É—in tace abaka?"


"towel"ya bata amsa agajarce.


Zuwa tayi ta É—auko ta bashi tana gimtse dariya dan taga acike yake taf.


Yana zuwa yasamu ta cire masa pampers tun kan ya zauna ta miƙo masa yakai dustbin🤣


Bece komai ba ya amsa ya fice,basuyi aune ba sejin ƙarar motarshi sukayi ya fice daga gidan😄dan abun ya isheshi.


Banida caji ne se anjima zaku jini


Muje zuwa


Surbajo for life
11/29/21, 1:18 PM - Ummi Tandama😇: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������


*Zahra Surbajo*


*Page 53*


A karo na farko da shehnaz da safna suka zauna guri guda suna hira har da dariya.
Zaune suke a babban falon gidan suna hira,bayan sallar la'asar.


Yaran kuma suna ɗaki suna bacci,shehnaz da ƙyar ta iya baro nata ɗan aɗakin,hankalinta gaba ɗaya yana gunshi.


Sallama Farhan yayi ya shigo falon,amsawa sukayi gamida masa sannu da zuwa,


Fuska a haɗe yaje ya nemi guri ya zauna,ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana mazurai.itade safna tun shigowarshi takeson yin dariya take dannewa sarai farhan ya lura da ita amma se yayi kamar beganiba.


Shehnaz ce tace"yauwa habibi,ɗazu daka fita musaddiq..."ay be jira ta ƙarasa ba ya miƙe da sauri yabar falon,zuwa part ɗinshi,wato ita bata ma fahimci fushi yakeba,wani laifin ma take shirin ɗorawa.


Ganin ya bar gurin ne safna ma ta miƙe zuwa sashinta,shehnaz tafi kowa murna da watsewar dan ita kamar akan ƙaya take tafison zama kusa da ɗanta.


Farhan be sauraresu ba se tara na dare,É—akin safna ya fara shiga.akan gado take yayin da Ayman da Aymana,ke baccinsu acikin gadajensu.


Dariya ta shiga ɓoyewa dan tana ganinshi dariyar ta taso mata.
Ayko kanta yayi ya wawurota,tsilli tsilli tayi da ido,
Hadeta yayi da jikinshi sannan yace"mahaukaci na koma ko,?shiyasa kikemin dariya,kinga baby wallahi ki fita idona in rufe"


Kwantar da kanta tayi a ƙirjinshi,sannan ta sa masa kukan kirsa.
KiÉ—imewa yayi yashiga rarrashinta,a ruÉ—e yace"kune kuka cajamin kaina yau,ita ta aykoni ke kisani agaba kina dariya,da wanne zanji "


Ƙara shiga jikinshi tayi tana kukan,taƙi magana.rasa yadda zeyi da ita yayi dan haka janta yayi suka kwanta agadon,yashiga ayka mata sakonni masu wiyar fassarawa.lib tayi ajikinshi,kuka ya ƙare,seda ya tabbatar ta ware sannan ya ƙyaleta,ya gyara kwanciyarshi akan gadon ya janyota jikinshi.


Ganin sha É—aya na dare ta wuce ne yasa safna cewa"dare fa yayi Abban musaddiq,kaje tana jiranka"


"ay shehnaz in zan shekara ban jeba bazata damuba matuƙar musaddiq na tare da ita,kuma in naje wallahi bazata barni in runtsa ba,kawai ki barni in kwana anan,dan mu dama bamusan wani wai baa kwana ɗakin mejego ba se tayi arba'in"


Duk yadda safna taso yatafi ƙin yarda yayi dole ta ƙyaleshi.


A nan ya kwana baccinshi harda munshari,ita ko shehnaz rashin zuwan nashi sosai yay mata daÉ—i,dan ita yanzu a matsayin takura take kallon zuwanshi gunta,tafiso taganta ita kaÉ—ai da babinta.


Haka rayuwarsu taci gaba da garawa cikin so da ƙaunar juna,


Yaran nada shekara guda,Farhan ya shirya musu tafiya zuwa nigeria,harda shehnaz da junior da Ayman da Aymana,da safna,da musaddiq É—an gidan mummy kamar yadda suke masa kirari sabida son da shehnaz take nuna masa.


Tuni doctor Amina tayi booking na maaikata guda biyar ta turasu sabon gidan da farhan ya gina dominshi da iyalinsa a garin na Abuja,domin su fara gyaran gidan.


Safna tafi kowa murna da tafiyar kodan taje gun baffanta da dangin mahaifiyarta.


Da misalin ƙarfe bakwai na safuyar yau jirginsu ya ɗaga zuwa nigeria,


Muje zuwa


Surbajo for life.
11/29/21, 1:18 PM - Ummi Tandama😇: ��������
*AURE DA HAIHUWA*
��������


*Zahra Surbajo*


*Billy shantally tawa ni kaɗai,alharin Allah ya kai miki keda ahalinki baki ɗaya,ina ƙaunarki nima sosai,Allah ya barmu tare cikin aminci*


*Page 54*


Koda suka iso,doctor Amina suka samu tazo ɗaukarsu a danƙareriyar mota jeep babba,se motocin jamian tsaro daga gomnati,kasancewar Farhan yarima me jiran gadon mulki.


Doctor Amina rungume safna tayi tana kukan farincikin sauyin data gani tattare da safnar,dan yanzu gaba ɗaya ma hausarta ta koma kamar tame koyon hausar,dan tun zuwanta dubai inde ba waya zatayi dasu baffa ba to zata iya ƙirga hausa ko sau nawa tayita,sabida babu mejin yaren se ita kaɗai


Gidan su aka kaisu wanda ya gaji da haÉ—uwa,Bayan kowa yayi wanka ya kimtsa,sukaci abinci sannan doctor tai musu sallama kan gobe zata dawo,ay ga mamakin doctor tana fitowa wajen gidan motar Rayhan tagani a fake yayinda shi kuma yake tsaye yana jiran fitowarta.
Da kamar ta wuce shi amma seta tsaya ƙarasowa yayi da gudunshi.


Buɗe ƙofar tayi ta fito fuskarta ba yabo ba fallasa.


"barka da safiya likita"cewar rayhan yana murmushi.


"barka de Rayhan,ya gari,me kakeyi anan ne?"doctor ta buƙata.


"Likita ke na biyo sabida naga tahowarku dasu Safna tundaga airport,naje raka iyalina zata umara,zan juyo naganku,shine na biyoku,don Allah doctor ki taimaka ki haɗani da safna da mijinta in nemi yafiyarsu badan ni ba doctor"ya ƙarasa maganar hawaye na bin kumatunsa.


Sosai tausayinshi yakama doctor,dan haka cewa tayi ya jirata,ita kuma ta juya cikin gidan.


Su safna sunyi mamakin ganin ta sabida ta musu sallama ta tafi.
Farhan ne ya dubeta yana murmushi,yayinda musaddiq ke kan ƙafarsa yana wasa yace"sarkin mantuwa me aka manta kuma?"


Ɗan yaƙe tayi sannan tace "kana da baƙo a ƙofar gida"


Sosai Farhan yayi mamakin maganar amma be kawo komai ba ya miƙe bayan ya sauke musaddiq ɗin yabi bayanta suka fita.


Besan Rayhan ba,dan haka be gane ko waye ba seda suka iso gabanshi,doctor tace"am very sorry ranka ya daɗe,wannan shine tsohon mijin safna wato rayhan"bata ƙarasa ba Annurin dake fuskar Farhan ya kauce,da sauri Rayhan ya zube agabanshi ya riƙe ƙafafunsa yana kuka yace"don Allah ku barni haka base kun hukuntaniba,Allah yagama muku sakayya tun tuni,gafararku nazo nema kaida matarka,bana nufinku da kowanne irin sharri"kukan dayaci ƙarfinsane yasa yakasa ci gaba da maganar.


Tausayinshine ya mamaye zuciyar farhan,hannu yasa ya kamoshi ya rungumeshi ajikinshi yana dukan bayansa alamun rarrashi.


Ganin kowa yazo shigewa kallonsu ake ne yasa yaja hannun Rayhan É—in zuwa cikin gida,doctor na binsu abaya.


Kai tsaye falon gidan ya nufa dashi,bakunansu ɗauke da sallama,Azabure safna ta miƙe jikinta ɓari yake kamar ɗan mazari,tsorone ƙarara a fuskarta dan haka cikin kuka take faɗin"me kazo yi gurin mijina,me nayi maka,don Allah karka rusa min farincikin daban taɓa mafarkin samu ba,kabar rayuwata nima na jima da barin taka kamar yadda ɗa ke baro cikin mahaifiyarsa,ina ƙaunar mijina,wallahi ka zamo sanadin rabani dashi bazan yafe maka ba"Farhan ne ya ƙarasa inda take ya janyota jikinshi,ta kwantar da kanta a ƙirjinshi tana faɗin"baby banida alaƙa dashi,wallahi ban gayyatoshi nan ba"


Bayanta yake shafawa a hankali dan ya lura duk a firgice take,"calm down baby,ba wani abu ya kawoshi ba haƙuri yazo baki ki natsu pls"


Se a lokacin safna tasamu natsuwa,dan ita da tunaninta É—an auran nata yazo ya girgiÉ—e mata.


Rayhan wanda kishin ganin safna ajikin wani ba shiba ya gama nuƙurƙusar zuciyarsa duƙawa yayi agabanta yace hawaye na bin idonshi.


"safna ki gafarceni,na cutar dake gashi cikin ruwan sanyi Allah na miki sakayya,nayi aure amna likitoci sun tabbatar mana da cewa daga ni har matata bazamu haihuba,sabida bamuda kwayoyin haihuwa,tun muna magani har mun haƙura,don Allah ku gafarceni ko zan samu sassauci azuciyata"


Farhan wani tausayin Rayhan dinne ya mamaye ko ina na jikinshi,tabbas rashin haihuwa,masiface dake hana bawa runtsawa,sabida shima yashiga wannan halin abaya shi kaÉ—ai yasan ya yaji a lokacin.


"Nayafemaka duniya da lahira,Allah ya yafe mana baki É—aya,haihuwa kuma ina muku adduar Allah ya baku"cewar safna.


Farhan kamo hannun ayman da aymana da junior yayi ya tsayar dasu gaban Rayhan,yace"wainnan ƴaƴanane da Safna ta haifa min,harda wancan( ya nuna musaddiq wanda shehnaz ta ɗauke abunta ta riƙe tunda taga ya fara kami yaran)a cikinsu ka ɗauki guda ɗaya na baka duniya da lahira"


A kiÉ—ime Rayhan yake kallon Farhan,yanaso ya tabbatar da abinda kunnuwansa suka jiyo masa.gyaÉ—a masa kai yayi gamida sake tura yaran gabanshi .


Rayhan bin kyawawan yaran yayi da kallo,hawaye na bin idonshi,a hankali ya É—ora hannunsa akan junior gami da jansa jikinshi ya rungume,shima junior É—in rungumeshi yayi,yana faÉ—in "Abba kadena kuka,babba baya kuka inji ummina"cikin harshen turanci.


Ƙara rungumeshi yayi ajikinshi yana wani sabon kukan akaron farko ankirashi da sunan mahaifi saɓanin uncle daya saba ji abakin ƴaƴan kannensa dana abokansa.


"dama nakane,dan haka kaje da kayanka mun bar maka duniya da lahira,kaddarace ta gifta wacce kuma ta wuce"cewar farhan yana murmushi.


Rayhan kama ƙafar Farhan yayi yana kuka yakasa magana,ganin hakanne yasa Farhan ɗaukar junior ya miƙa masa yace"Tashi kuje Allah tayaka ruƙo"asanyaye ya miƙe ya ɗauki junior,wanda se farinciki yake ko alamun damuwa babu aranshi.bare ayi zaton zeyi kuka.


Koda ya É—ago ya dubi safna wacce ke kuka,bece komai ba illa haÉ—a hannayensa dayayi guri guda alamun godiya.


Haka ya fice É—auke da junior ajikinshi,doctor Amina na binsa a baya.


faÉ—awa kan kujera safna tayi ta rushe da kuka me tsuma zuciya,Allah ne kaÉ—ai yasan son da takewa junior,gashi yanzi anrabasu.


Shikanshi Farhan É—in dauriya yayi dan kaf Æ´aÆ´ansa yafison junior,amma dama haka Allah tace in zakayi kyauta kayi da abunda kafi so.


ÆŠaukarta yayi cak suka wuce É—aki,tana rusa masa kuka,shehnaz kanta tausayin safnar taji,dan haka jan ayman da aymana da musaddiq tayi suka wuce nata É—akin.


É—akinshi ya nufa da ita,se cigaba take da kuka tana kiran junior É—inta.


Akan gado ya ajiyeta sannan shima yahau gadon ya janyota jikinshi yayi mata rungumar da zatayi shuru dan kanta,ayko baa jima ba tayi shuru ta koma se lumshe ido take,a hankali ya dubeta yace"Allah ya miki baywa ta koina,mw isa akan ƙaramin abu zaki tashi hankalinki,nasan Rayhan baze taɓa cutar miki da ɗa ba to meye abun kukan,ni kinma bani kunya,ke da nakewa kallon jaruma ta"ya ƙarasa maganar yana lakace mata hanci.


"to ni baby ay kyautar ce kayi bakayi shawara dani ba"tayi maganar a ashagwaɓance.


"sanda kika kyautar da musaddiq shawara kikayi dani?"ya tambaya yana ƙoƙarin zuge zif ɗin rigarta.


Murmushi tayi bata bashi amsa ba ta koma ta kwanta akan gadon ta sakar masa linzamin.


Cire rigar yayi,ya janyota jikinshi ya shiga shafa boobs ɗinta ta gefe,yayinda ya manna bakinshi akansu,yashiga surcking ɗinsu,ba tun yau ba ta hanashi ganin shayarwa take amma fafur yaƙi denawa.


Hannu yakai can ƙasan marar ta ya shiga ayka mata sako me wiyar fassara,safna kukan daɗi tasa mishi a haka tashiga rage masa kayan jikinshi,itama sakon tafara tura masa ta hanyar kamo joy stick ɗinsa tana ɗan mulmulawa,gamida pressing,gaba ɗaya ta birkita masa lissafi,kamar yadda shima ya birkita nata,shi kuka ita kuka ahaka ya cilla kwallonsa araga.


Basu samu natsuwa ba seda suka kwashe awa guda da rabi suna abu É—aya,dan Farhan akwai dogon zango,tun safna na raki har ya koyar da ita ta saba.


Kwanansu biyu da zuwa suka nufi ƙauyen sara.


Babu wanda beyi murna da zuwanta ba,har matan babanta,kowa nan nan yake dasu,
Baffa har kuka yayi da ganin safnar wacce tazamo silar arziƙinsa.


Babu inda basu zaga ba adangin na safna,kyaututtuka suka rabawa kowa,ga maƙudan kuɗaɗe da suka rabawa jamaar gari,kowa se son barka.


Satinsu guda suka koma Abuja cike da kewar juna,dan maimuna da kuka suka rabu da safnar.


Rayhan kusan kullum seya kawo junior,amma abun mamaki shi junior É—in beson zuwa,yafison yakaishi gurin iyayen shi Rayhan É—in.


Iyayen Rayhan da Æ´an uwansa har gida sukazo sukayiwa Safna godiya da Farhan.
Zumuncine ya ƙullu atsakaninsu,ranar da jameela ta dawo daga umara tasamu labarin sunyi ɗa har suma seda tayi dan farinciki.


Har gida yakaita tayi musu godiya.


Rayhan da jamila ko ƙuda basa so ya taɓa junior,in kana ƙaunar ɓacin ransu to kataɓashi,ko office Rayhan yaje be iya zama har yatashi be dawo gida yaga junior ba sannan ya koma.


Watan su safna biyu a nigeria suka koma dubai,safna ɗauke da ɗan ƙaramin cikinta,wanda farhan ya ɗauki son duniya ya ɗora masa kamar baa taɓa masa haihuwa ba.


Ayman da Aymana kuwa gidan iyayen Farhan É—in aka kaisu,dama sosai suka ji É—acin kyautar musu da junior da yayi.


To muma Anan muna fatan Allah yasauki safna lafiya da sauran mata masu ciki amin summa ammin.


*ALHAMDULILLAHI*


A nan wannan littafi na AURE DA HAIHUWA ya kawo ƙarshe,
Darasin dake ciki Allah bamu ikon ayki dashi.


Kuskuren dake ciki Allah yabamu ikon gujewa aykatashi.


mu kasance tare cikin sabon littafina me suna TAYI MIN ƘAƘANTA dan ganin wainar da ake toyawa.


Taku har kullum


Zahra Surbajo.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login