Showing 15001 words to 18000 words out of 41742 words

Chapter 6 - Alheri Danko ne completed by Ummi Aisha .txt

29 Nov 2024

1364

yasamu tafida kwance adakinsu ga ledar ruwa nan ana kara masa ashe duk wannan wayar da yake yimasa karfin hali kawai yakeyi shima yana kwance, sannu tafida yau likita ne dakansa ake kara masa ruwa? Murmushi tafida yayi faisal ya kukayi da hanfa? Cikin fara'a faisal yace an bata gado aiki zasuyi mata nan da kwana 3 fatan dai Allah yasa adace amin faisal nagode Allah yabar zumunci, haba tafida duk abinda nayi maka ai kaina nayiwa Allah yabaku lafiya, tashi yayi yafita saboda tsabar tausayin dan uwansa da ya shigeshi.
[9:54AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Acikin kwanakin kullum sai faisal yaje garin disina yayinda shikuma tafida yana nan akwance yana jinya jininsa ne yahau over gashi tunda yake bai taba yin hawan jini ba sai a wannan lokacin, ranar da za ayiwa hanfa aikin aranar faisal yatafi da sassafe dama duk abinda suke bukata shi yake kai musu, yana zuwa asibitin ya samu za ashiga da ita dakin da za ayi mata aikin ga iyayenta agefe ko wannensu zuciyoyinsu babu dadi haka shima faisal yatsaya suna nan tsaye har tsawon awa 2 sannan aka fito da ita kai daga ganinta kasan tawahala mutuka wani daki aka zarce da ita amma da alama ba ayi nasara ba, sai bakar wuya da tasha domin sai da aka fara yimata fanfo sannan aka yimata wankin kunne kai wuya dai kala kala tashata amma bata samu lafiya ba domin sauki daga Allah yake nan mamanta tafashe da kuka shi kansa faisal ji yake kamar yayi kukan domin bai san halinda tafida zai shiga ba idan yaji cewa bata warke ba, tashi yayi yashiga office din likitan dan neman karin bayani anan likitan yake sanar dashi cewa sunyi iya bakin kokarinsu amma ba adace ba kuma amma kunnenta lafiya lau yake dan haka agobe ma zasu iya tafiya gida godiya faisal yayi masa yafito yazo yasamu iyayenta yayi musu bayanin abinda likita yace, babu komai Allah yasa haka shine yafi alheri mahaifin hanfa yafada alokacin faisal yayi musu sallama yakama hanyar misau yana zuwa ya tarar da tafida yana jiransa nan ya zauna yafada masa dukkan abinda ya wakana, cikin damuwa tafida yace babu komai ni dama ita nakeso ba wani abu nata ba amma yanzu abinda nakeso dakai faisal dan Allah kaciri kudi gobe kaje kasiya musu gida mai kyau ka zuba musu furnitures kasiya musu kayan abinci domin babu amfanin ni ina zaune awuri mai kyau ina cin mai kyau amma matata tana cikin kuncin rayuwa kai faisal yadaga hakane Allah yakaimu goben. Acikin kankanin lokaci faisal yaje garin disina yasiyawa su hanfa hadadden gida mai kyau wanda yadace da zamani yazuba musu furnitures dama unguwar ba unguwace mai hayaniya ba babu bata lokaci suka koma gidan nan iyayenta da ita kanta suka shiga yiwa faisal addu'a domin duk atunanisu shine yake yi musu wannan hidimar, lokacin da faisal yadawo gida ya sanar da tafida ba karamin dadi yajiba anan yake sanar da faisal cewa an hadashi da wani malamin addini wanda yake taimakawa mutane dan haka zaije ya duba hanfa ko Allah zai sa adace, hakan kuwa akayi faisal yaje yadauki malami suka tafi gidansu hanfa, suna zuwa malamin yace taje tadauro alwala sannan ya bukaci da abashi ruwan zamzam original ba jabun ba nan faisal yatashi yaje wani Islamic chemist anan cikin garin ya siyo yakawo, ruwan zamzam din malamin yajuye acikin wani koko yafara addu'a yana watsawa akan fuskar hanfa take tafadi akasa, cigaba da watsawar yayi yanayi yana addu'a har aka kwashe tsawon lokuta alokacin yafara yiwa su faisal bayanin cewa hakika hanfa tana fama da matsala ta jinnu kuma kurame ne gashi sunfi wahalar sha'ani amma aci gaba da addu'a, nan faisal ya zauna agarin bai tafi misau ba sai dai suna yin waya da tafida. Kwana uku malamin nan yayi yana yiwa hanfa magani amma shiru sai akwana na hudune Allah yabada nasara jinnun sukayi magana amma da hannu suke nuni da haka malamin yace sufita daga jikinta amma da yake masu taurin kaine sai da suka sha wahala sannan suka fita.
[9:56AM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Sai da malamin yaja musu kunnen cewa su sakar mata kunnenta da bakinta kafin su fita, suna fita tayi wata irin atishawa mai karfin gaske, Allahu akhbar hakika sauki da rashinsa daga Allah suke tuni tafara wani bacci mai nauyi, malamin ne yajiyo gasu faisal yace wato abinda yafaru shine ruwan zafi ita wannan baiwar Allah ta zuba musu to shine suka shiga jikinta amma insha Allahu yanzu tasamu waraka farin cikine ya mamaye zukatansu asannan mamanta tayi magana tace dama lokacin taliya tadafa tana tacewa tashekar da ruwan shikenan tun daga lokacin tafara jinya, girgiza kai malamin yayi shiyasa ba aso azubar da ruwan zafi akasa dan haka sai akiyaye nan suka zazzauna suna jiran farkawarta sai da ta dade tana bacci sannan ta farka bakinta dauke da addu'a nan fa ta kalli mamanta tace mama! Wato masu karatu ni ummi Aisha sauran kadan nasaki wayata tafadi taci screen saboda tsananin zakin muryar hanfa danaji wata irin zazzakar murya ce da ita shi kansa faisal ji yayi kamar wata balarabiya balarabiya tazama maida kallonta tayi ga faisal tace nagode Allah yasaka da alheri tana gama fadin haka tatashi hawaye suna bin kumatunta tashiga daki tayi alwala tafara salla domin nuna godiyar ta ga Allah yayinda shi kuma faisal yadauki malam suka koma misau suna zuwa yafara yiwa tafida albishir ai tafida bai san lokacin da yadiro daga kan gado ba yazo ya rungume faisal tuni yaji jikinshi yaware nan yafara tambayar faisal nawa za abawa malam? Yace duk abinda yasamu domin shi bai yanke ba, ok to zan bashi dubu dari biyar da mota daya da gida guda daya take shima tafida yafada bathroom yadauro alwala yazo yafara nuna godiyarsa ga Allah. Bayan hanfa ta warware ne tafara shirin komawa makaranta nanfa tafida yayi siyayya mai tarin yawa yabawa faisal ya kaimata duk abinda yasan zata bukata sai da yasai mata kayan kwalliya da kayan abinci da drinks kala kala hatta pad sai da ya siya mata ga turarruka masu tsada nan iyayenta da ita suka shiga godiya bayan tafiyar faisal mahaifinta yake ta yabon faisal sannan yabata labarin cin mutuncin da dan uwan faisal din yayi masa wato mijinta tafida tun daga nan taji ta tsani tafidan tun kafin ta ganshi. Ranar Monday ta shirya tadawo makaranta nanfa yan makaranta suka shiga mamaki jin hanfa bebiya tawarke yayinda wasu kuma suke cewa ai babu mamaki da sha'anin Allah, ranar data dawo makaranta ranar tafida yafara zuwa office bai dawo ba sai 5 tunda yadawo yaci abinci yayi wanka yafita shida babban zaginsa da sarkin mota yana daga baya azaune yace musu school of nursing zasuje haka kuwa minti kadan sai gasu acikin makarantar suna shiga suka fara tafiya ahankali har sukaje gaban wani hall inda dalibai ke tsattsaye group group da alama daga lecture suka fito nanfa daliban suka fara bin motar tafida da kallo wata babbar jeep ce kirar kamfanin crotoure baka mai bakin gilasai an rubuta tafida 4 ajiki, ba aganin wanda yake ciki, ido tafida yafara budewa yana kallon daliban can ya hangota da uniform ajikinta da dan karamin hijabi iya kafadarta tayi wani kyau sosai tana tsaye cikin maza sunfi biyar da modern biology a hannunta da alama bayani take musu nanfa yaji ransa ya sosu, babban zaginsa ya cewa yaje yakira masa ita koda yaje hanfa bata kulashiba sai ma gurmuda baki da tayi duk abinda tayi akan idon tafida yana kallonta ta glass din motar dan haka koda babban zagi yadawo bai jira bayaninsa ba yabude motar yafita nanfa kallo yakoma kansa yatsuke cikin bakar riga mai gajeren hannu ajikin rigar an rubuta big guy da jan fenti yasa jan trouser da jan takalmi irin nasu na sarauta hatta belt din da yadaura ja ce yadora bakar jacket asama ahankali yafara tafiya yana zuwa yajiyo da ita yaja hannunta nanfa tafara turjewa ganin haka yasa tafida fizgota jikinsa ya rungumeta nan fa su babban zagi da sarkin mota suka fito da gudu suka zo inda suke suka baza babbar rigarsu sukayi musu runfa suka lullubesu ahankali tafida yadago kanta yasa bakinsa akan nata yafara zagaye lips dinta da harshensa,tofa muje zuwa dai masu karatu.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [5:39PM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikin sauri hanfa ta bude idanuwanta ta fara kallon fuskarsa bakinsa kan nata gashi ya wani kankameta duk kamshin turarensa na fogg ya cika hancinta ras! Taji gabanta ya fadi, jan hannunta yayi yakaita cikin mota yabude gidan baya yasata shima yashiga sukuma su babban zagi suka zauna daga waje, yayinda dalibai suka yi cirko cirko suna tattauna wannan lamari da ya afku wasu kuma ba karamin burgesu tafida yayi ba, suna shiga cikin mota hanfa tafara matsawa yana binta, tana matsawa yana matsowa har taje jikin kofa daidai lokacin ya karasa matsowa kusa da ita kallon fuskarsa tayi yawani rankwafo jikinta, jikinsa yana gogar nata hatta numfashinsa akan fuskarta yake sauka, tunani tafara yi, yana yi mata kama da faisal sosai sai dai yafi faisal kyau, komai nashi ya tsaru sai kace shi yayi kansa dan kyau, to kodai shine tafidan? Duk yadda akayi wannan shine tafida mijina sannan kuma still dr din da ya dubani a asibiti tafada acikin ranta, hakika taji dadin kasancewarsa a matsajin mijinta amma kuma sai ta wanashi ta nuna masa kuskurensa na ciwa mahaifinta mutunci da yayi domin tana son ta nuna masa cewa iyayenta suna da martaba da kima a idonta, iska ya hura mata akan fuskarta take tajiyo wani kamshin strawberry me hade da splash ya fito daga bakinsa, ahankali kamar meyin rada yace kin gama gudun? Kallonsa tayi tadauke kanta tafara kiciniyar bude kofar motar amma bataga wurin budewar ba saboda tsananin tsaruwar da motar tayi, hannunsa mai mutukar laushi yasa yajiyo da fuskarta madam! Kijiyo kiji abinda zan fada miki, ko bakya ji? Well dama ni basai naji muryarki ba tunda nasan kina jina shikenan, nayi mutukar farin cikin kasancewarki mata ta hakanne ma yasa nayi alqawarin kyautata miki domin na nuna godiyata ga mahaifinki akan aura min ke da yayi, wannan dalilin ne yasa nima na himmantu har sai da kika samu lafiya tareda taimakon dan uwana, abokina, aminina faisal, wanda banida kamarsa aduniya, dam taji dama shine yasa faisal ya yimata dukkan abinda yayi mata? Shiru tayi tana sauraren taushashshiyar muryarsa tun da take bata taba jin muryar namiji mai dadi kamar tasa ba.
ALHERI DANKO NE!
4⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Mahaifinki yayi min alheri mai yawan gaske shiyasa nima na daura aniyar yi masa alheri ta hanyar sama miki lafiya domin shi ALHERI DANKO NE sai alokacin ta kalli fuskarsa idonsa tarr akan fuskarta, yatsina fuska tayi takawar da kanta, meyasa kika shiga cikin maza kika tsaya? Ko baki san ina kishinki ba? Shiru tayi bata bashi amsaba amma tajiyo takalleshi daidai lokacin da yake lasar lebenshi wanda ya kasance ja kamar ya shafa jan baki mai duhu, juya kanta tayi ta kalli window ahankali taji yakama hannunta yatsun hannunta ya zubawa ido fatarta bakace amma ga gashi nan kwance sai kace jikin namiji, kallon hannun nata yayi yai murmushi ai bakar mace tayi arayuwa dama shi can bakar mace yakeda ra'ayin aura, dayan hannun nasa yasa yafara shafa gashin hannunta, wani irin shock tafara ji amma sai ta maze, ahankali yace haka kike da gashin nan duk jikinki ko iya hannun ne? Sai alokacin tayi masa magana dubawa zakayi sai kaga, wani darr yaji acikin kunnensa saboda jin sautin muryarta.
[6:13PM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
4⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Kamar wani sakali haka tafida ya zuba mata ido yana kallonta ashe tasan muryar ta tahadu shiyasa tatsaya ja masa aji sai da tagama yangarta sannan tayi masa magana, wani sanyin dadi yaji acikin ransa hakika hanfa tana daya daga cikin matan da Allah ya horewa baiwar murya zazzaka, kallonta yayi ya lumshe manyan idonsa ya budesu akan fuskarta, kafar wandonta yakama yadago kafarta yadan janye shi sama nan yaga gashi kwance mamakine yakama hanfa shi wannan be san gatse ba, dan tace yaduba yagani shine zai duba din, hannunsa yasa yashafa kwaurinta nanma akwai gashin har cinyarki? Shiru tayi hannunsa yadauke daga kwaurinta ya ajiye kafar tata akasa yafara kokarin saka hannunsa acikin rigarta nanfa tayi caraf tarike hannunsa me zakayi? Cikinki zan duba naga ko nanma akwai gashin, to babu tafada tana buntsira baki, ni kika buntsirawa baki? Kefa kika ce dubawa zanyi sai nagani kuma ya zan duba zaki hanani? Bata bashi amsaba, kin san me nakeso dake daga yau kar nasake ganinki acikin maza kin gane? Buntsira baki tasake yi, yana ganin haka yakai bakinsa kan nata yahada yatsoti lebenta.
ALHERI DANKO NE!
4⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Bakinta ta kwace ta tofar da yawu tasaka bayan hannunta tafara goge bakinta wannan wanne irin kazanta ne haka? Tafada tana hararsa aranta kuma tana cewa wato kai ga mai mata ko shine harda wani biyoni school, kallonta ya danyi kyankyami na kike yi? Wannan abin ne kazanta? Zakiga kazanta kuwa wannan ba kazanta kika gani ba, yana gama fadin haka yajanyota jikinsa ya fara kokarin saka bakinsa cikin nata amma taki ta damke bakinta yanda bakinsa bazai shiga nataba, murmushi yayi wlhi ko ki bude bakinki ko kuma nayi maganinki yanzu, hannunshi yazira cikin rigarta ta baya bashiri ta yi magana, meye haka? Dan mitsitsin bakinta yakalla ga fararen hakoranta siri siri ajere gata da yar wishirya nan da nan yaji yawunsa ya tsinke, bakinsa yahada da nata yakama harshenta yarike yafara dura mata yawun bakinsa mutsu mutsu tafarayi tana tuttureshi amma yaki cikata, haka tarinka shanye yawunsa yana dura mata wani sannan yafara lasar harshen bakinta yana tandar lips dinta sai da yashafe samada minti 20 sannan yasaki bakinta, hannunta tasa akan bakinta tana tofar da yawu tuf tuf, dariya tafida yayi wadda har saida beautiful point dinsa yafito fararen hakoransa suka bayyana, yarinya zancen yaushe kuma ai kin riga da kinsha yawu na sai dai kiyi hakuri ki kiyayi gaba amma yanzu kan kin ga kazanta iya kazanta ko? Harararsa tayi mugu kawai, ni kike cewa mugu? Zakiga muganta yarinya.
[8:30PM, 11/19/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
5⃣0⃣
Na A'ISHA (ummi)
Baki hanfa ta murguda kawai saboda tsabar kazanta zaka wani bani yawunka nasha, wannan ai kazanta ne, wani malalacin murmushi tafida yayi mata ai dan kinsha yawuna ba wani abu bane tunda zan zuba miki abinda yafishi ajikinki, wa? Allah ya kiyaye tafada tana harararsa tareda fara idonta wai nanfa ta kara saka tafida a wani yanayi, hannunta ya kama shidai hannunta yana burgeshi gashi da tsananin taushi kamar auduga ga laushi da tsantsi, farcenta yafara murzawa sannan yakai hannun bakinshi yayi kissing dinsa yasa dan yatsanta abakinshi ya fara lasar farcenta yana tsotsar dan yatsan, cike da mamaki ta kalleshi hannun hagun ne fa, to meye? Kece kike kyankyamina ni bana kyankya minki kanta takawar daka kallonsa, sai alokacin idonsa yakai kan agogon hannunsa dake daure akan tsintsiyar hannunsa karfe 6:20 har anfara kiraye kirayen sallar magrib sannan yawancin daliban dake harabar area classes din sun tattafi hostel sai daidaiku, dan yatsanta yadan ciza duk da taji zafi amma bata nuna masa ba, cire yatsan nata yayi daga bakinsa yace kije kitafi hostel amma ga zarah can nahango ta ki turo min ita, shiru tayi aranta tana cewa gaskiya kam kai dan sarauta ne ace magana tarinka yiwa mutum wahala kanata yimin magana kamar me yin rada kana magana dakyar,ni ummi A'isha nace dan hanfa bata san tafida bane amma ahakanma ita dakarfi yake yi mata magana, wani abu ya taba take kofar motar tabude, hannunta ya saki ba dan yasoba yace kitafi sai dasafe amma gobema zan dawo, bata bashi amsa ba tafice tanufi inda su zahara'u sulaiman suke tsattsaye tana zuwa tace zarah kije yana kiranki, dasauri xarah tatafi inda yake, tana zuwa yasauke glass din motar tafara gaisheshi, cikin sakin fuska ya amsa yace zarah ga amanata nan nabaki ki kular min da ita fiyeda yadda zaki kula dakanki, compliment card dinsa yamika mata ga wannan akwai phone number dina ajiki idan da wani abu sai ki kirani domin ita bazan bata phone yanzu ba.
hausa novel blog
‹ › Home
View web version
Thursday, 22 December 2016
aisha ummi at 01:26
ALHERI DANK'O NE 51-END
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [8:20PM, 11/20/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE❗
5⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Murmushi zarah tayi insha Allahu zaka sameni mai tsananin rikon amana, yawwa zarah nagode ai tafada miki nine mijinta ko? Murmushi zarah tasake yi wlh tafada min kuma nayi murna sosai Allah yabar kauna, amin zarah nagode juyawa zarah tayi tatafi sukuma su babban zagi sukazo suka shiga motar sarkin mota yaja suka tafi. Zara'u tana zuwa inda su hanfa take tasamesu tsaye hanfa tana yi musu bayanin wani zanen skeleton dake zane ajikin littafi nan zarah tajirata tagama domin hanfa akwai brain kusan tafi kowa ja a yan lab science, kuma wani abin burgewar mahaddaciyar alqur'ani ce dan da ka take dori batare da ta buda alqur'anin ba wow inama ummi aisha ce, tana gama yi musu bayanin suka tafi hostel itada zarah, cikeda zolaya zarah tace hanfa mijin nan naki dan love ne dan naga ko kunyar dalibai baiji ba yawani rungumeki, dan karamin tsaki hanfa tayi ai kibari kawai zarah namiji bai san kunya ba yanzu dan Allah in banda rashin kunya meye nashi na hugging dina agaban mutane? Ai kuwa kinyi sa'ar miji dan ni ina son namijin da ya iya soyayya, um hanfa tafada aranta kuma tana cewa idan wannan ne ai har ya isheki ma dahaka suka karasa hostel suka shiga room 2 kasancewar nanne dakinsu kuma komai nasu ahade yake su 2.
ALHERI DANKO NE❗
5⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Shikuwa tafida tsintar kansa yayi cikin farin ciki marar misaltuwa gaba daya hanfa yau tagama tafiya da imaninsa ko yaya ya lumshe idonsa ita yake gani da wannan tunanin suka je gida abakin gate suka hadu da mutuminsa faisal kowannensu ya fito daga cikin mota, suka bawa juna hannu dai dai lokacin suka shiga cikin gida anan suka hango mai martaba yafito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login