Showing 6001 words to 9000 words out of 41742 words

Chapter 3 - Alheri Danko ne completed by Ummi Aisha .txt

29 Nov 2024

1359

course dinshi anan faisal yazo yasameshi abokina dama kana ciki, eh gani kaganni kuwa, akusa dashi faisal yazauna me kakeyi? Wlh wani course zan tafi na 5 months, kai dazakayi aure wanne course kuma zakatafi bayan ga babban course zaka samu duka tafida yakaiwa faisal yace zan yimaka rashin mutunci wlh, dariya faisal yayi duk tsiyarka dai ana daura maka aure kazama bazawari,waya fada maka? Wlh karya kake kaine bazawari amma ni virgin ne dariya faisal yayi ai mun kusa muga karshen virgin domin virgin zai koma disvirgin dariya tafida yayi yace ka karaci iskancinka kagama akwai ranar ramuko. Tuni aka fara shirye shirye agidan mai martaba har an hada kayan aure irin na al'ada dana zamani ankai gidansu amarya kullum bushe bushe da raye raye akeyi agarin mai girma tafida zai angwance,ni ummi Aisha hannuna asama nace Allah yaja zamanin mai girma tafida, tunda aka fara shirin biki tafida baya shiga sabgar kowa agidan tsakaninsa da kowa gaisuwa ce daga angaisa shikenan dama can shi ba mai magana ba da faisal kawai yanzu yake magana mai tsawo shima faisal din dan bazai iya fushi dashi bane saboda sun shaku sosai, amma ko inno da mai martaba tsakaninsu gaisuwa ce yadda suke fushi dashi shima haka yake fushi dasu, ana igobe za afara gudanar da biki yafara shirye shiryen tafiyarsa India domin nan da sati 2 zasu fara gudanar da course din mai taken yaki da cutar sankarar mama (cancer),shi dai faisal shine yazama tamkar angon domin komai wanda ango yakeyi shine yayi, shikuma tafida hakan ko ajikinsa tashi yayi yaje wurin mai martaba yayi masa maganar tafiyarsa India maimartaba bai damuba yace babu matsala dama itama amaryar taka karatu takeyi koda tana nanma nace babu maganar tarewarta yanzu tunda bakaso duk lokacin dakaso ta tare nan gaba, dukar da kai tafida yayi yace godiya nake mai martaba Allah yakara nisan kwana yatashi yafita.
[8:41PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana fita yayi kicibus da faisal kallon faisal yayi yadauke kai domin yafuskanci faisal ya zake akan auran nan, cikeda dariya faisal yaja hannunsa mutumina ya akayi? Shiru yayi kamar baijishi ba cikin zolaya faisal yace wai kai duk dokin zaka samu hanyar ne ya hanaka magana? Sai alokacin tafida yayi murmushi wlh kai wannan yadama ni yanzu ba wannan ne agabana ba, dariya faisal yayi zo muje abokina kaji hannunsa yakama suka nufi cikin gida har dakinsu suka zazzauna faisal ya dubeshi yace dan Allah tafida ka tsaya ka nutsu ka rungumi matarka shifa aure mukaddari ne, cikin jin haushi tafida yace me zai hana kai ka rungumi kaddarar ka aureta? Dariya faisal yayi ai ni ba abani bane amma kai kaga da yake dan gatane aure za ayi maka kasha sha'aninka tsaki tafida yayi yajawo earphone dinsa yajona ajikin wayarsa yafara shan sauti dariya faisal yayi yace kadai kusa ka zama bazawari, jin shiru tafida bai amsa ba yasashi gane cewa bai ji abinda yace ba domin dayaji da sai ya bashi kyakkyawar amsa domin babu abinda yatsana irin yaji yakirashi da bazawari tashi faisal yayi yafita yana dariya. Shirye shiryen biki ya kankama yayinda shi kuma tafida yaketa shirye shiryen barin kasar, ranar alhamis aka sanya amarya a lalle faisal shine yake tsaye akan komai kullum baya samun lokacin kansa daga nan zai yi nan gidan mai martaba kuwa ya cika yayi dam da al'umma garin in banda kade kade da raye raye babu abinda akeyi domin sarki zai aurar da dan autansa kuma dan gaban goshinsa amma shi tafida in banda fushi babu abinda yakeyi gaba daya yadaina walwala yazama marar fara'a gashi kullum sai sunyi fada da faisal, ranar juma'a aka fara niyyar daura auren tafida amma kememe yaki kirshayawa.
[9:05PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣0⃣
Na A'ISHA (UMMI)
Babu yadda faisal bai yi da tafida ba kan ya shirya su fita domin da misalin karfe 1:30 za adaura auren amma yaki yarda yatashi ya shirya tun faisal yana yimasa cikin lallami har yafara fada shiru tafida yayi masa bai tanka masa ba, ganin haka yasa faisal yakara tunzura ya hasala yafita daga dakin, lokacin har su mai martaba sun tafi inda za adaura suren, faisal shi kadai yatafi yasha fararen kaya masu tsada yana zuwa lokacin wurin yacika makil amma haka yasamu ya kutsa ya isa wurin mai martaba sarki yana ganinsa yafara tambayarsa ina tafida cikeda damuwa yace ranka yadade bashida lafiya ne bazai iya zuwa ba, cikin fushi mai martaba yace yayi daidai kuma rashin zuwansa bashine zai sani nafasa yimasa wannan auren da nayi niyya ba, hakuri faisal yafara bawa sarki tuba muke ya mai martaba ayi mana uzuri,galadima ne ya matso yace ranka yadade ni ina ganin afasa daura auren nan da tafida abawa faisal, girgiza kai sarki yayi a'a galadima banki ta takaba amma nidai da tafida zan daura auren nan, nan aka fara daurin aure waliyyan amarya sunzo aka daura auren tafida da amaryarsa akan sadaki naira dubu dari, ana gama daurin aure sarki yakira uban amarya gefe yafara yimasa bayani kan cewar amarya ba yanzu za akawota ba sai lokacin da yayi magana gyada kai mahaifin amaryar yayi tareda yiwa mai martaba godiya, ana kammalawa faisal ya koma gida afalo ya taradda tafida kwance yana danna wayarsa dariya faisal yafara yi yamikawa tafida hannu assalamu alaikum mr ango harara tafida ya cilla masa yayi tsaki wata dariya faisal yayi mr ango asamo hanya lafiya amma banda rashin imani dan wlh idan kayi mata takarfi zaka iya kasheta, tashi zaune tafida yayi wlh faisal kar ka kaini bango, ya isheka, murmushi tafida yayi daga fadar gaskiya? Allah yabaka hakuri gyara kayanka baya zama sauke mu raba, murmushi tafida yayi yau kam yazama amma kabari duk lokacin dana nemi hanyar narasa zan nemi taimakonka, zama faisal yayi bawani nan dama can kasan inda take, wai kai sau nawa zan fada maka ne? Wlh Allah ni ban san ta inda take ba kai nifa ko haihuwa idan zan karba bana tsayawa naduba kawai aikina nakeyi dariya Faisal yayi to congratulations yanzu zaka gane ta inda take sallamar jakadiya ce ta katse musu hirar tasu.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:27PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Har cikin falon jakadiya tashigo tarussuna barkanku da hutawa samarin kwarai tafida ta kalla ranka yadade mai martaba yana kira tana gama fadin haka tajuya tana cewa afito lafiya, tashi tafida yayi yafita shikuma faisal bai bishi ba domin yasan fada zaisha awurin mai martaba yana tsoron kar yaje ahada dashi, tafida yana isa dakin mai martaba yasameshi shida inno da momcy zazzaune gabansa wuri yasamu yazauna gabansa yanata harbawa, cikin fada mai martaba yafara magana ibrahim ka raina kowa agidan nanko? Kanuna mana mu bamu isa dakai ba kenan tunda har za muyi maka umarni amma kasa kafa ka shure, saboda baka daukemu da daraja ba shine zaka ki halattar daurin aurenka ko? To ka kyauta kuma duk abinda kayi daidai ne domin ahalin yanzu sai dai kanemi wani uban amma baniba aure kuma nayi maka shi sai dai zaka iya nunawa duniya rashin matsayina ta hanyar sakin matar, nanfa inno itama tadauka ya saketa mana shiyasani kuma mutumin banza kawai kai in banda tsabar raini har ayi maka umarni ka ki bi? Yaran yanzu bakuda kunya kota sisin kobo muda aurenma basai an tare zakaga matar ba,waye zai tsaya jin ra'ayin mutum, hakuri momcy tafara basu hajiya inno ayi hakuri dai, mai martaba dana yayi kuskure amma ayi hakuri ayi masa gafara ayafe masa kar yashiga cikin wani hali dan Allah aduba kokena, tashi inno tayi tafita tanata fada shima mai martaba tashi yayi yafice yatafi fada, kallonsa momcy tayi tafida baka kyauta ba meyasa zakaki zuwa wurin daurin auren? Cikin kasala yace momcy ni auren ne bana so, 27 years nayi aure? Is too early wlh,murmushi momcy tayi babu komai yanzu abinda nakeso dakai anjima da daddare kuzo kaida faisal kubawa sarki hakuri kaji? Naji momcy, yawwa Allah yayi maka albarka, tashi yayi shima yafita.
[9:47PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Da daddare faisal yasaka tafida agaba sukaje wurin sarki suka bashi hakuri amma sai dakyar suka samu ya sauko sa'arsu daya su yan lelensa ne domin badan hakaba da zai dade yana fushin bai huceba, daga nan sashen inno suka shiga itama suka bata hakuri tsakanin da da uwa sai Allah nan itama ta huce tace tahakura suna dawowa dakinsu faisal yafara bawa tafida shawara, abokina kafin katafi India yakamata kaje kaga amaryarka kayi mata sallama, tsaki tafida yayi naji zanje, yawwa mutumina yakamata kaje. Abangaren gidansu amarya kuwa koda mahaifinta yaje musu da batun rashin tariya dawuri nan dangi suka fara kace nace wasu kuma mamakine ya kamasu wannan wanne irin aure ne kodan anga basuda kudi shiyasa za araina musu wayo? Shidai uban amarya baice komai ba kuma zancen da nake yimuku har yau nidai ummi Aisha banga kalar amaryar tafida ba balle na zayyano muku yanda take, kasancewar sarki mutum ne mai adalci yasa ya aikawa da gidansu amarya kayan abinci kala kala yace arinka ciyar da amarya kuma duk lokacin da yakare zai aiko wani sannan duk wata bukata tata arinka sanar dashi hakan da yayi ba Karamin dadi gidansu amaryar sukaji ba. Tafida shirin tafiya yagamu domin yau saura kwana 2 yabar kasar, wanka yayi ya shirya yadau kwalliya cikin bakin danyen boyel yasa bakar hula takalmin kafarsa ma baki yaafito sai zuba kamshin turare yake take fadawansa suka bude masa motarsa yashiga suka rufa masa baya driver yaja sai disina, suna zuwa suka zarce wani dan madaidaicin gida daga ganin gidan gidan talakawa ne masu rufin asiri, cikeda yatsina fuska tafida yafito daga motarsa yanufi cikin gidan fadawansa suna take masa baya, babu ko sallama yakutsa kai cikin gidan yana rayawa aransa wai dan abin kunya nanne gidan sirikansa kai Allah ya kiyaye, atsakar gida yahango mahaifin matarsa da mahaifiyarta tana hura wuta, kafarsa yasa yayi bol da wata buta ta farin karfe atsakar gidan da alama butar mai gidan ce, dayake gwanine wurin kwallo take butar tawuce tasaman kan mai gidan taje tadaki bango tadawo baya tafadi atsakar gidan ta tankwashe yanda bazata moruba har abada.
[10:07PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikin tashin hankali mahaifiyar matarsa tafara magana suwaye ku? Me kukazo yi anan gidan? Cikin yayyatsina fuska tafida yadubi wannan mitumin yace bawan Allah yadda kasa aka daura min aure da yarka to tun wuri kaje kasa awarwareshi domin bazan zauna da itaba kuma bazan taba sonta ba, banda tsabar son zuciya tayaya zaka dauki yarka ka kaiwa mai martaba rallarta har alika min ita, to bana sonta kuma sai nasaketa sai asannan suka gane ashe shine mijin yarsu sirikinsu duk cikinsu babu wadda yayi masa magana kawai tsayawa sukayi suna kallonsa fadawansa kuwa sai fadi suke hutawarka lafiya tafida wannan sako naka ya je inda kakeso yaje, abi tafida a zauna lafiya tafida buhun karangiya ko an zazzage dole sai ya makale, gaba salamun baya salamun dan sarki jikan sarki, gunbar dotse, icen kan kabari titi kafi karfin a tsallakaka dole sai an waiga, takawarka lafiya toron giwa dawisu da ado aka sanka, ragayar dutse namijin fama, juyawa tafida yayi yafita daga cikin gidan fadawansa suka rufa masa baya kai tsaye fadarsa yawuce inda wakilinsa yake, anan ya tambayi wakilin nasa wacce gonace tafi kowacce girma agarin? Cikin washewar baki wakili yace ranka yadade gonar sirikinka malam faduluddeen gonarsa tafi takowa girma cikin rashin damuwa tafida yace ok to inaso nan da sati mai zuwa agyara min domin zan turo masu aiki zasuyi min ginin gidan shakatawata awurin, cikin mamaki wakili yace yallabai sirikinka fa, ka iya bakinka wakili fadawa suka fada lokaci daya, shiru wakili yayi yace tuba nake yallabai tashi tafida yayi yana bawa sarkin fada sallahun ginin da za azo ayi masa, cikeda farin ciki yakoma gida domin yasan abinda yayiwa mahaifan matarsa dole zasuji haushi kuma kila zasu samu sarki suce yasashi yasakar musu yarsu amma abin mamaki shiru yaji ba wani batu alokacin har ansoma fara yimasa ginin gidan da yabada umarni acikin yanayin yashirya yanufi kasar india yana cikeda haushin auren da yake kansa.
[10:45PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Lokacin da tafida ya tafi india ya samu damar mantawa da auren dayake lankaye akansa sai dai kusan kullum idan sunyi waya da faisal yana yawan yimasa maganar amaryarsa dariya kawai tafida yakeyi domin yanzu ya daina damuwa idan faisal yana yimasa tsiya, cikin ikon Allah yasamu yagudanar da course dinsa cikin kwanciyar hankali da nasara wata 5 daidai yayi yafara shiri ysdawo Nigeria. Ranar da yadawo ranar fada ta cika makil da yan sannu da zuwa faisal kuwa sai zolayarsa yakeyi amma yashareshi har sai da suka koma daki sannan yakalli faisal yace mekake cewa dazu? Dariya faisal yayi abokina kayifa kyau sosai kayi fresh kodai kabi hanyar ne? Tsaki tafida yayi kai wai baka da wata magana sai kwaya daya? Ai ni nafada maka ko zanbi hanyar da kake fada to ba yanzu zan bitaba, dariya faisal yayi to malam yakamata fa kasan inda dare yayi maka dan wlh nakusa korarka daga dakin nan? Wazaka kora? Kai zan kora tunda yanzu Kai magidancine so sai kakoma wurin iyalinka, kamanta zurriyya ba iyaliba tafida yafada tareda mikewa yafara cire rigar jikinsa domin shiga wanka. Washe garin ranar da tafida yadawo yakwanta yayi baccinsa ranar bai je office ba sai wurin 11 sannan yashirya cikin suit milk colour yasa milk colour din takalmi yasha turare yafito dan zuwa asibitinsu yana so yaje yakai report, agidan baya yazauna acikin motarsa fadawansa suna tareda shi har asibitin yana fitowa daga mota wasu yanmata wanda zasu kai kimanin su 20 suna sanye da unifoam suka fara kallonsa da alama yan practical ne aka turosu asibitin duk cikinsu babu wadda tafida bai tafi da imaninta ba nanfa suka fara tattauna maganar a tsakaninsu. Sai da tafida yayi hutun sati 2 sannan yafara zuwa office aranar dayaje yana tsaye acikin office dinsa yana daddanna wayarsa wata nurse tashigo masa office akidime pls sir ka taimaka mana munada patient wadda take neman taimakon gaggawa kamar baijiba yayi har saida ta sake maimaitawa sannan yace yaji yabi bayanta har zuwa female ward can gadon karshe takaishi tace gata sir wannan ce, gaban gadon yakarasa wata yar budurwa yagani wanda shekarunta zasu kai 23 aduniya tana sanye da farar riga da bakin dark blue din wando daga gani yar practical ce domin yaganta da unifoam din yan lab science.
[11:12PM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Kallon fuskar ta yayi kyakkyawa ce ta daukar hankali shidai yana ganin mata masu kyau amma baiga wadda ta kai wannan kyau ba duk kuwa da cewa baka ce amma bakinta mai kyau ne har wani shining take kallon nurse din yayi me yasameta? Cikin inda inda tace let me go and call her friend she's d one dat brought her here, dasauri tafita Jim kadan sai gata dawata budurwa itama tana sanye da uniform irin na wadda take kwancen kallonta tafida yayi meya sameta? Dr wlh kawai muna zaune mukaga tafadi, sai alokacin yasa hannunsa yatabata amma da bai taba koda hannunta ba ya salam! Yafada saboda jin laushin fatar jikinta, nan yafara jin wani yanayi ajikinsa daurewa yayi yafara checking dinta anan yasamu yagano matsalar tata yayi mata allurai har guda hudu alokaci guda, kallo yabita dashi dama wannan ai dole tasamu matsala saboda tahadu sosai shiyasa takamu da ciwon mara mai tsanani wanda bazata taba warkewa ba har sai tasadu da namiji, fita yayi yakoma office dinsa sai 3 yashiga round yana shiga yan practical suka fara gulmarsa wannan likitan duk asibitin nan yafi kowa kyau, ai duk misau ma babu mai kyanshi inji wata aciki, yana tafiya yana duba patient har yazo gadon karshe inda yanmatan nan suke, waje yace sufita yafara duba patient dinshi wadda har ta wartsake kallonta yayi doguwa ce baka tanada manyan idanuwa da dogon hanci gata da dan tsukakken karamin baki, gashin girarta mai yawane batada kiba dayawa amma tana hips da cikar kirji sosai, yanmata kin tashi? Ya tambayeta, biron hannunsa ta karba da takarda tayi masa rubutu kamar haka, bana jin abinda kafada ni bebiyace kuma kurma ce, mika masa tayi yakarba ya karanta cikeda mamaki ya rubuta mata, ayya sannu, amma ko kin san ke kyakkyawa ce? Mika mata yayi takarba tagani takaranta tayi masa reply nagode amma Kayi hakuri ni matar wanice, karba yayi yai murmushi nima mijin watane, murmushi tayi wlh inada aure, bai gasgata ta ba saboda yaga tana fama da matsalar ciwon mara sperm yataru dayawa a mararta gashi har ya haifar mata da ciwo shi kuma yasan da ace tanada aure da hakan bazata faruba kallonta yasakeyi waye zai mallaki wannan a matsayin mata yatsaya yazuba mata ido yana kallonta? Kai karyane gaskiya budurwa ce cikakkiya kuma.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Wani tsadadden murmushi tafida yayi mata yace ok koma dai menene bari na rubuta miki maganin dazai taimaka miki, wata yar takarda yadauka ya fara rubutu yana gamawa ya mika mata gashi Allah yabaki lfy, duk wadannan maganganun da yakeyi bata jinshi murmushi yayi mata kinyi min kinyi daidai da tsarina hannunta tadaga tayi mai nuni ma'ana me yake nufi, murmushi ya sakeyi wanda har sai da fararen hakoransa suka bayyana kumatunsa na dama ya lotsa kusan ko magana yakeyi sai yadan lotsa kallonsa tayi taji gabanta yafadi wannan likitan yanada kyau tafada acikin zuciyarta astagfurullah tayi saurin tuba saboda tunowa datayi itafa matar aure ce, fuskarsa ta kalla lokacin da yake yin rubutu ajikin takarda yadan dunkuyar da kansa yanayi yana lasar lebenshi nakasa wanda suke jaja jaja duhu duhu domin tabar wiwin da yakesha tahadu da jan lebensa sai tabada wata irin kala mai kyau kamar yana shafa jan baki gashi farinsa irin mai dan jan nanne kura masa ido tayi kai wannan saurayin yana yimata kama da Seth rollins dan wrestling domin har tsayinsu ma zai zo daya gashi manyan idanuwansa ma irin nasane sak, dagowa yayi yana murmushi yamiko mata takardar yayi mata wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login