Showing 9001 words to 12000 words out of 41742 words

Chapter 4 - Alheri Danko ne completed by Ummi Aisha .txt

29 Nov 2024

1366

kasalallen murmushi yajuya yafara tafiya ita dai nurse tana tsaye tana kallon ikon Allah domin tunda take acikin asibitin nan bata taba ganin dr tafida yayi irin haka da wata patient ba babu ruwansa da kowa tsakaninsa da kowa gaisuwa ce amma sai gashi yau har dasu bude hakora taf lallai wannan tacika mai nasara.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana juyawa marar lafiyar tafara kallonsa yahadu sosai ta kissima aranta sai da yafita tabude takardar da yabata tafara karantawa kamar haka Yake kyakkyawa agaskiya yau idona ya yi duban da be taba yiba hakika banyi kuskure ba idan nakiraki da suna tauraruwa kigodewa mahaliccinki domin ya tsara halittarki irin tsarin da har yau banga wadda takaiki ba, ina sonki zuciyata takamu da kaunarki alokaci guda,ina taredake aduk inda kike luv u! I. T. Tana gama karanta wasikar kawayenta suka shigo dukkaninsu kowacce tana sanye cikin unifoam nanfa wata daga ciki tafara yimata tambaya da hannu alamar meya ce mata murmushi kawai tayi bata fargaba taji sun fizge takardar hannunta karantawa sukayi take kuma bakin ciki ya mamaye zuciyoyinsu domin agaskiya wannan likitan bai dace da ita ba dasu yadace mutum dayace bataji haushin hakanba asalima murna tayi sukuwa sauran ji sukeyi kamar su shaketa dan haushi. Dr tafida yana fita daga female ward yanufi office dinsa zuciyarsa cikeda tunanin yarinyar da yagani sai dai yana jin tausayinta har cikin ransa domin abin atausaya matane gata budurwa har budurwa kyau iya kyau amma dayake Allah alhakimu ne sai ya iyota kurma kuma bebiya, duk da haka zuciyata tana sonki yanmata ni babu ruwana da jinki ko maganarki ke kawai naji ina so, zama yayi yafara kiran fadawansa minti kadan sai gasu kayansa yace su hada masa zai tafi gida babu bata lokaci suka harhada duk wasu abubuwa nasa suka fita,tashi yayi yacire bakar coat din jikinsa yabar iya tacikin wadda take light green mai dogon hannu da neck tie baki da green, ahannunsa yariko rigar idonsa yana sanye cikin farin glass yana tafe yana daddanna wayarsa.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Fadawansa na hango shi suka zabura suka zo suka fara take masa baya suna tafe suna zabga kirari, takawarka lafiya, alafiya dai tafidan alheri, gaba salamun baya salamun namijin fama, babban goro sai magogin karfe, karo da karo sai rago, wani Kaya sai amale wane jaki, buhun kaya kake mai daukarka sai wanda ya shirya, kogi ba ayi maka katanga, kaga katangar sukari kowa ya jingina sai ya lasa, sauka lafiya dan ahamadu jikan sani, farin wata sha kallo, lafiya dai mai dogon zamani, gaba salamun baya salamun,shi dai tafida tafiya kawai yakeyi yana yin waya da faisal amininsa kuma dan uwansa har ya isa gun motarsa suka bude masa ya shiga ya zauna, daliban nan duk akan idonsu hakan tafaru har motar tafida tafita daga cikin asibitin, daya daga cikinsu mai suna sakina itace ta tabe baki wai kuga haduwar wannan gayen amma yarasa wacce zai so sai waccan kurmar,bebiya dukansu baki suka tabe wayaga abinda rai keso inbanda haka me zaiyi da ita kuma kunji ma dan gidan sarki ne ashe, daya daga cikinsu ce ta katsesu haba sakina meye amfanin haka? Ina ruwanku dasu, wannan abun da kukeyi babu kyau hassada ce ita kuma hassada Annabi yayi hani da ita domin akwai wani ingantaccen hadisi da manzon Allah s.a.w yake cewa iyyakum wal hasadu, fa innal hasadu ta akulul hasanati kama ya akulul narul hadabe, ma'ana nahaneku da hassada domin ita hassada lallai tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cinye itatuwa ko kuma karare, dan haka wannan abin da kukeyi wlh bashida amfani ko kadan,soyayya ta Allah ce idan kukayi hakuri kuma zaku samu rabonku, tana gama fadin haka tabar wurin takoma cikin female ward, tsaki sakina taja wannan damuwarki ce amma wlh bazai yiyu ace mu masu baki da kunne yakimu yaso kurma ba. Tafida jinsa yake kamar bashiba har yaje gida,shidai bai taba soyayyaba asalima ko budurwa bai taba yiba saboda shi miskili ne nagaske kai kallon mata ma bai dameshi ba, baya hulda da mata ko kadan amma yau yayi gamo, gamo wanda za a iya cewa kyakkyawan gamo.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
2⃣9⃣
Na UMMI A'ISHA
Cikeda farin ciki ya isa gida sai wata walwala yakeyi marar kan gado domin babu wadda ya saba ganinshi cikin wannan yanayin su kansu fadawansa mamaki sukeyi yadda yau yake cikin nishadi da walwala, suna isa tangamemen gidansu yafito daga cikin mota fadawan dasuke tsaron kofar suka mimmike tsaye suka fara gyara kintsi gaba salamun baya salamun barka da shigowa tafidan zamani tafida ba akawo maka wargi, takawarka lafiya dan toron giwa, dan zaki kafi karfin rainon kura, ko kura ta mutu tafi karfin kare yaja gawarta, namijin dawa kake mai kayan alfarma, barka da shigowa zaki dangin sikari, tsawo dangin rama, takawarka lafiya gaba salamun baya salamun, cikeda jin dadi tafida yadaga musu hannu kamar yadda yasaba yanufi zauren dazai sadashi da lungun mai martaba yana zuwa kansa tsaye yawuce cikin dakin mai martaba yasameshi zaune yana kallon labarai atashar CNN zubewa yayi yafara diban gaisuwa, sannan yatashi yafita yanufi wurin inno itama a falonta ya taradda ita tana kishingide jikin tumtum ga bayi zagaye da ita sunayi mata firfita ka kayan motsa baki a gabanta shiga yayi yazauna a kan kujera bayinta suka tashi suka fiffita anan ya zamo kasa ya gaida ta yatashi yafita yau gaba daya jinsa yake kamar wani sabon mutum dan tsabar nishadi, yana isa dakinsu yashiga toilet yayi wanka yafito yasaka kayan yan kwallo jar riga mai number 1 ajikin rigar da wando dogo,adaki yayi salla yana idarwa yafito yanufi wurin dawakansa yasamu har an daura masa sirdi domin fita kilisa shi kadai kawai ake jira baiyi wata wata ba ya haye dokin shima sarkin fada yahau nasa da alama yau su biyu zasu fita kilisar, tafe suke ahankali kowannensu rikeda linzamin dokinsa har suka isa wasu manyan gonaki, tafida ne yayi yar magana ahankali kamar yadda yasaba, sarkin fada wannan gonar idan baka mantaba nataba fada muku zatayi daidai da tsarin danakeso wurin gina business suit dina, Allah ya taimakeka tafida sarkin fada ya fada,amma yallabai wani hanzari ba gudu ba wannan gonar itama ta sirikinka kace idan ban mantaba, yatsina fuska tafida yayi koma tawaye a cikin satin nan za afara yimin aiki, Allah yaja kwana,Allah yasa kafi haka, sarkin fada yafada amma acikin zuciyarsa cewa yake wannan wanne irin mutum ne ace duk gonakin sirikinka sai bi kakeyi kana karbewa kana gini marassa dalili.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Haka suka karaci shawaginsu suka koma gida lokacin magriba tana daf da kawo jiki, suna isa gida tafida yasauka daga dokinsa a gajiye ya shige gida afalonsu ya zube akan carpet ya kwanta gaba daya ya gama gajiya, jinsa yake kamar yayi wani gagarumin aiki, fuskar wannan yarinyar ya hango take yayi wani murmushi insha Allahu sai na auri wannan yarinyar yafada azuciyarsa domin kyakkyawa ce ajin karshe, amma mamakinsa shine yadda take karatun science alhalin kuma bata ji kuma bata magana hakika ta cika yar baiwa gashi komai nata mai kyaune tamkar ita tayi kanta saboda yadda halittar ta tatsaru sosai, lumshe manyan idanuwansa yayi oh ko meye sunanta? Tsabar yarude yamanta bai tambayi sunanta ba shigowar faisal cikin falon ne yasashi dago kansa yakalleshi abokina daga ina? Zama faisal yayi daga dambam nake kasan garin nawa kullum basa rabo da rikicin manoma da makiyaya, murmushi tafida yayi uhm dakyau hakimi, dariya faisal yayi kaima dai dadinta hakimin ne, murmushi tafida yayi masa wadda har saida faisal yayi masa magana yau naga kana ta fara'a kodai? Murmushi tafida yayi babu abinda yafaru amma nazo maka da albishir nasamo matar aure dariya faisal yafara yi bakada seti tafida yaushe kayi aure da har zaka fara neman wani? Tsaki tafida yayi kaga babu ruwanka malam ni namanta ma wlh da wani auren da mai martaba yayi min, kallonsa faisal yayi to wlh kafadawa yarinya gaskiya tunda wuri ka sanar da ita gaskiyar lamari kai bazawari ne ba saurayi ba dan kanada mata yakarasa maganar cikeda dariyar mugunta,shiru tafida yayi masa bai bashi amsaba amma yatsani faisal[truncated by WhatsApp]
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣1⃣
Kallon faisal yayi malam banida lokacinka yanzu yana gama fadin haka ya mike yanufi lungun inno zuciyarsa fes domin yana cikeda farin ciki a wannan rana. Daren ranar bacci kadan yayi domin alla alla yake gari ya waye yaje yaga wannan yarinyar, asuba tana yi yatashi yafita masallaci yayi salla yana dawowa ya dauko alqur'aninsa ya buda yafara karantawa har karfe 6 tayi sannan yaje yayi wanka yafito ya shirya cikin suit ash colour hatta takalmin kafarsa ash colour ne yadaura agogon Gucci na azurfa duk wannan budurin da yakeyi faisal yana kwance yana kallonsa sai da yagama shiryawa tsaf faisal yace gaskiya kayi kyau mitumina wlh babu wanda zai ganka yace kai ba saurayi bane kamar ba kayi aure ba, tsaki tafida yayi Allah yasa kaima asatin nan dai ayi maka auren inyaso muga ta tsiya, dariya faisal yayi gaskiya kam gara mai martaba ya taimaka min yayi min aure tunda gashi har Kanina zaiyi mata 2 ina zaune niko daya banyi ba dariya tafida yayi yajuya yafita bai ce komai ba yana fita yashiga gurin inno ya gaidata yafito yaje wurin mai martaba shima ya gaidashi sannan yayi haramar tafiya office lolacin karfe 8 saura minti 20. Yana zuwa office yazauna akan table dinsa yadauki yar farar takarda yayi rubutu yasa agaban rigarsa yafito yanufi female ward, yana shiga nurses suka fara gaisheshi morning sir! Morning kawai yake cewa yawuce, da haka har yaje last bed inda budurwar nan take, kallon kyakkyawar fuskarta yayi yai mata murmushi ita dinma shi take kalllo wata farar takarda ya miko mata takarba yana bata yajuya yafita dama abinda yakawo shi kenan, theatre ya hara dan yanada aiki acan, yana fita ta bude takardar tafara karantawa rubutunsa kyau kadai kamar wadda aka buga ajikin computer, sakon nasa takaranta kamar haka "some people hv a nice smile, some hv a nice eyes,and some hv a nice faces, you u hv all of them & nice heart Good morning & hv a nice day! I. T, tana gama karantawa sai kuma tasoma hawaye wanda nikaina ummi Aisha ban san ko na menene ba.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Kuka take sosai wannan wanne irin abune da aurenta ta rinka son wani mutum nadaban, istigfari tafara yi ba kakkautawa acikin yanayin kawarta zara'u sulaiman tazo ta sameta zama tayi gefen gadon tafara tambayarta da hannu meyafaru? Dakyar tadauki biro zara'u yau zan bar asibitin nan dama kin san acikin satin nan zan gama practical dina gida zan koma idan kingama naki ma hadu a sch dariya zara'u tayi to kijirani zanje nadawo tana gama rubuta mata ta tashi tafita, hawayenta tagoge tadauki takardar taboyeta acikin rigarta, tana nan zaune aka kawo wata mata marar lafiya agadon kusa da ita aka kwantar ta Jim kadan sai ga likitanta yazo wato dr tafida idonsa akanta yaje yagama duba matar nan yabata dukkan taimakon daya kamata sannan yadawo inda take, da ido yayi mata alama wai meya sameta idonta yayi ja, murmushi tayi takada hannu alamar babu komai takarda yadauka yarubuta mata meye sunanki? Da babban baki tabashi amsa sunana HANFA yana karantawa yayi murmushi meye ma'anar hanfa? Dan ni ban taba jin wannan sunan ba, murmushi tayi yakamata ka rinka bibiyar tarihi amma nabaka assignment go and find out d meaning of hanfa murmushi yayi yace zan kuwa baki mamaki domin zan samo miki ayau basai gobe ba yana gama rubutawa yabata yafita daga masu jinyar har nurses din kallonsu suke tayi to kodai sun san juna wannan abin mamaki ya isa domin ada ibrahim tafida (I.t) baya tsayawa yayi magana da patient amma gashi yau yatsaya yanata rubuce rubuce da kurma gulma nurses din suka fara yi agefe daya duk dai sun san ita wannan marar lafiyar yar practical ta hadu ta cancanci hakan.
[12:16PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Agurguje yagama abinda yakeyi ya koma gida abinda bai saba yiba tashi karfe biyu amma yau yayi saboda yana so yasamu damar binciko ma'anar sunan hanfa, yana zuwa gida yasamu sirikinsa yana fitowa daga fada ko kallonsa bayi ba balle yasa ran zai gaisheshi tafiyarsa yayi cikeda takama fadawa suna biye dashi suna takawarka lafiya dan toron giwa gaba salamun baya salamun dahaka yashige gida dakinsu yaje yabaje ya jawo laptop dinsa yafara searching din hanfa sai da yadade yana nema sannan ya samo cikeda farin ciki yatashi yaje dakin inno bata cikin dakin dan haka kan gadonta ya haye yayi dai dai yana tunanin hanfa ba shakka sunanta ya dace da ita kuma ya cancanceta ganin inno bata shigoba yasashi mikewa zai fita daga dakin sai gata kuma ta shigo,a'a tafida dama kana nanne? Kai yadaga mata ina nan inno ai tun dazu nadawo amma sake fita zanyi, to amma dai sai kaci abinci ko? Murmushi yadanyi to inno abani kadan naci dakanta tafita ta hado masa abinci takawo masa harda kayan marmari agefe zama yayi yadanci abincin kadan yatashi yafita yakoma dakinsu yayi wanka yafito yashirya tsaf cikin blue colour din jeans da riga dark brown mai gajeren hannu yana fitowa yahadu da faisal ya yau da wuri zaka fita kilisar ne abokina? Faisal ya tambaye shi, no zanje asibiti ne amma bazan wani jimaba zan dawo, ok sai kadawo faisal yafada yawuce ciki shi kuma tafida ya fita, yana zuwa su sarkin fada suka bude masa kofar mota ya shiga ya zauna sai asibitin kwararru na rasheed shekoni wanda yake da xango acikin garin misau.
[4:08PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Suna isa asibitin ya nufi female ward yashiga nurses din dake ciki sai fadi suke welcome sir! Last bed ya hanga amma babu kowa cikin rudewa ya tambayi daya daga cikin nurses din ina patient din dake last bed? Ahankali tace dr dazu tatafi, ahargitse ya kalleta are you mad? Danme zaku barta tatafi ban sallameta ba, meye amfaninku agurin? Wannan ya nuna min cewar baku san aikinku ba, sai kun karbi query saboda sam bakuda hankali hakuri suka soma bashi we are sorry sir! Ko kulasu bai yiba yafice daga cikin ward din, to shi yanzu ina yanufa? Tunda bai san inda yarinyar nan takeba sa'arsa daya yasan sunanta, fita yayi yashiga motarsa fadawansa suka rufa masa baya, ransa abace yake yau sanadiyar rashin ganin hanfa da wannan bacin rai suka karasa gida yana zuwa dakinsu ya fada akan gado ji yake kawai kamar ya fashe da kuka, tabar wiwi ya janyo ya kunna ya fara zuka nan fa ya turnuke dakin da hayaki kamar salansar babur, faisal dake kwance kusa dashi yana bacci ya bude ido yafara kallonsa dan ganye ka fara zuke zuken naka ne? Shiru tafida yayi masa domin bacin ran dayake ciki baxai barshi ya iya yin magana ba tabarsa yaci gaba da busawa batare da yace komai ba tuni idonsa ya kada yayi jajawur kamar jini ganin abin bana kare bane yasa faisal kwace sauran wiwin ya boye yana cewa kai meyasa wani lokacin baka da saiti ne? Sai kaje kajawa kanka wata cutar, kana likita amma baka san abinda zai illataka ba, dakyar tafida ya iya bude baki yace faisal ban ganta ba, wacece? Faisal ya tambayeshi yarinyar da nace maka nahadu da ita a asibiti, to kuma shine zakazo kayita shan wiwi? Ai kamata yayi katsaya ka nutsu ka binciko inda take amma baka zauna kayita bunkawa cikinka hayaki ba lumshe idanuwansa tafida yayi yace nagode abokina insha Allah zan kokarta kwanciya yayi yafara hango kyakkyawar fuskar hanfa, Allah sarki kowa da yadda Allah yake jarrabarsa ita kuma haka Allah ya halittota kurma sannan kuma bebiya amma ya tsara halittarta yadda bazai kwatantu ba, dan tsaki yaja ni ba muryarta nakeso ba kuma ba jin maganarta nakeso ba ita kanta nake so kuma insha Allahu sai na mallaketa.
[5:09PM, 11/16/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Zama jugum tafida yayi yana ta sake sake acikin ransa gamida tunanin yadda zai nemo sahibarsa hanfa daren ranar bashida wata walwala har gari ya waye, shiryawa yayi yadda yasaba cikin suit bakake yasa bakin takalmi yasa glass dinsa fari dan siriri yafito agurguje ya leka wurin mai martaba yafito yashiga wurin inno yana fitowa yanufi asibiti koda yaje tuni har ma'aikata sun firfito manyansu da kananansu, gakuma yan attachment suma duk sun fito, yana zuwa yawuce office dinsa yafito yashiga maternity jim kadan yafito yashiga female ward nanma bai fi minti biyar ba yafito yana fitowa yashiga antenatal,yana fitowa yadaga yan yatsunsa guda biyu yashiga office take dogarawansa suka furtsa aguje suka nufi office dinsa nanfa yan practical suka fara kace nace wato wannan daga yatsun dayayi ashe fadawansa yayiwa magana lalle sarauta sai me ita,basu farga ba sai ga wani bafade guda daya yazo inda suke yayi musu sallama yace wacece zara'u acikinku? Gani zara'u ta amsa, to kizo mai girma tafida yana son ganinki, hanzarta yanmata, tafida ikon Allah tafida mai jan doki, dasauri zara'u ta tashi tanufi office din dr tafida yayinda dogari yake biye da ita yana fadin takawarki lafiya yanmata, gyara kintsi bakuwar tafida alafiya dai gaba salamun baya salamun, ita dai zara'u gaba daya atsorace take domin bata san me zai biyo baya ba, yayinda kawayensu suna can suna ta gulmarta ita da hanfa to ko yanzu zara'u zai ce yana so? Inji wata acikinsu kudai jira muga dawowarta tukunna sakina tafada, zara'u suna zuwa office din tafida bafade yabude mata tashiga abinka ga jinin sarauta akishingide ta sameshi yana jiran zuwanta tana shiga yayi gyaran murya take fadawan sukayi waje suka ja musu kofa.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [6:39PM, 11/17/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
3⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Fadawansa na fita ya kalli zara'u yana daga kishingide yace hv a seat zarah, babu musu ta zauna akan kujerar dake nesa dashi, kallonta yayi ina hanfa take? Hanfa tatafi gida, a ina gidan yake? Ya tambayeta, acan disina gidansu yake, dagaske ne ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login