Showing 3001 words to 6000 words out of 41742 words
Wani kallo tafida ya watsa masa ni zanyi aure amma ba yanzu ba sai nan da 3years dariya faisal yakumayi kasan Allah? Kai angone kakusa ganin hanya, wai kai waya fada maka aure zanyi ne? Uhm abokina bazaka yarda da abinda nake fada maka ba sai kaji kira daga wurin mai martaba sannan zaka gasgata ni, tsaki tafida yayi insha Allahu kai zai yiwa aure amma baniba,ni daba dan iska ba wa zaiyi min aure yanzu? Kai da kasan mata kake nemansu ai kai yadace ayiwa aure, dariya faisal yayi kasan Allah? Wlh kakusa zama ango kai barima kaji dazu daka zo kasamemu da mai martaba wlh maganar aurenka akeyi kuma nan da sati biyu za ayi, cikeda mamaki tafida ya kalleshi wai dagaske kake yi? Wlh Allah dagaske nake tafida wlh aure mai martaba zaiyi maka dazu akanka mukayi meeting da yamman nan kuma wani abin burgewar ma zaka samu virgin girl kamar yadda kake virgin boy, zumbur tafida yamike ni za ayiwa aure yanzu? Wanne laifin nayiwa mai martaba da zai hukantani ta wannan hanyar? Wa zai aura min? Yaya kamanninta suke? Girgiza kai faisal yayi wlh ban saniba abokina, to nima dai ummi Aisha ban saniba sai muci gaba da bibiyar tafida, masu karatu muje zuwa kubiyo Aisha.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [8:53PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣1⃣
Na UMMI A'ISHA
Kallon faisal tafida yayi ai kuwa wlh bazai taba yiyuwa ba nikadai ne da agidan? Akan me za ayi min wani aure yanzu kai ba gaka nan ba haba da Allah wlh bana so babu wanda zai rabani da gidan nan yanzu, kuma wlh duk yarinyar da tayi kuskure ta aureni sai ta raina kanta, dariya faisal yayi wadda takara kular da tafida kaga bani zaka fadawa ba kamata yayi kaje gurin mai martaba kayi masa wannan bayanin amma nidai ina tayaka murna sai dai shawarata agareka itace kasan mai martaba baya yin magana 2 daga yayi magana to yagamata so be careful kar kaje kajawa kanka, kaga mitumin nan nadazu daka samemu afada dashi? Shine mahaifin yarinyar wlh kayi dacen suruki cikeda bakin ciki tafida yace malam banfa tambayeka ba dan haka kayi min shiru banza kawai dariya faisal yaci gaba dayi ganin haka yasa tafida ficewa daga dakin yatasamma lungun inno wadda yake da dan tazara daga sashensa, yana shiga yatarar da bata cikin dakin sai kuyanginta suna gyara dakin kusan ko wanne lokaci dakin nata cikin gyaransa ake, shiyasa koda yaushe yake cikin tsafta tamkar dakin sabuwar amarya, suna ganinsa sukayi waje suka bar aikin da sukeyi, gadon inno ya dale yakwanta idan dasabo kowa agidan yasaba ganinsa akan gadon inno koda wanne lokaci yagadama zai zo yahaye yasha baccinsa akai kamar wani yaron goye.
[9:36PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣2⃣
Na UMMI A'ISHA
Rufe idanuwansa yayi amma yasan ba bacci zai iya yi ba maganganun faisal ne kawai suke dawo masa jiya jiyan nan kagama fadamin idan an baka mace baka san yadda zakayi da itaba sai gashi nan da sati 2 zaka zama ango an baka mata, zunbur ya tashi zaune jin abin yake kamar a mafarki aurefa? Daidai lokacin inno tashigo taganshi zaune akan gadonta, tafida ashe kana nan? Nima daga wurin mai martaba nake yakira ni yabani wani sako wurinka ras! Gabansa yafadi wato maganar faisal ta tabbata kenan ai kuwa tunda yake da mai martaba bai taba yimasa musu ba amma awannan karon dai zai yi, domin bai kamata ayi masa haka ba, abinda yafi cancanta shine abarshi ya zabi matarsa da kansa tunda sauran yayyensa ba haka akayi musu ba, maganar inno ce ta dawo dashi cikin hankalinsa mahaifinka yace nasanar dakai zai daura maka aure nan da sati 2 da wata yarinya yar gidan abokinsa amma ayadda naji yafada yarinyar ma ba lafiyayyiya bace, cikeda damuwa yace inno kuma ni za aurawa marar lfy? Haba inno yanzu mace ma an daina yimata auren dole balle namiji kuma naga sauran duk ba haka aka yimusu ba agaskiya nidai afasa maganar auren nan idan bahaka ba wlh za aji kunya, cikeda tashin hankali inno tace haba tafida mai martaba kake fadawa haka? Mahaifin naka zaka kunyata a idon duniya? To bari kaji wannan sakon naka yafi karfina sai dai yanzu katashi da kanka kaje ka sanar dashi bazakabi zabin da yayi maka ba, amma kasani mahaifinka ba yayin magana 2 magana daya yakeyi kuma aduk inda yasaka doka a garin nan ana bi balle agidansa dan haka ina baka shawara da kayiwa mahaifinka biyayya kar kajawo abinda zaiyi fushi dakai, shiru tafida yayi ransa duk yagama jagulewa wannan wanne irin abu ne? Shidai wlh wannan auren bada shiba, kallon inno yayi to inno abawa faisal mana amma sai ace ni za abawa? Wlh bana so ni babu auren da zanyi ban shirya yin aure yanzu ba kafin inno tayi magana jakadiya tashigo gafara dai ranki yadade barka da hutawa ayi min izini nashigo, kya iya shigowa jakadiya inno tafada tana kokarin kishingida.
[10:49PM, 11/12/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣3⃣
Na UMMI A'ISHA
Shigowar jakadiya ne yasa tafida dago dara daran idanuwansa yafara kallon jakadiya cikin girmamawa jakadiya ta durkusa ranki yadade barka da hutawa, Allah ya kareki uwar dakina sarki ya aikoni, kallonta ta maida kan tafida mai girma tafida sako daga mai martaba sarkin adalci sarki nakwarai yace kaje yana son ganinka cikeda damuwa batare da tafida yabata amsa ba yatashi yafita izuwa lungun sarki gaba daya jinsa yake kamar a mafarki, yana isa dakin sarki yaja yatsaya abakin kofa sakamakon ganin maga kofa dayayi toge akofar, cikin girmamawa maga kofa yafada dakin sarki yayiwa sarki bayanin zuwan tafida, yashigo sarki yafada atakaice, dasauri maga kofa yadawo yayiwa tafida iso suka karasa dakin sarki sannan maga kofa yafita yabasu wuri sunkuyar dakai tafida yayi Allah yaja zamaninka yanzu na samu kiranka daga wurin jakadiya,eh nine naturata takira min kai, ranka yadade na amsa kira, ibrahim! Mahaifin nasa yakira sunansa na'am, Allah yaja zamaninka, Allah yasa kafi haka tafida yafada kansa yana duke akasa, dalilin kiran da nayi maka shine kayi hakuri da abinda zakaji daga gareni, wato ibrahim aure zanyi maka nan damako biyu, ina fata zakayi dukkan wasu shirye shiryen dasuka dace nan da sati biyun, sannan ina so kayi hakuri da ita matar da zan aura maka domin ba lafiyayya bace kuma ga hotonta idan kana da bukatar gani, kansa akasa yace ya mai martaba ayi min adalci kuma asausauta min dan Allah afasa auren nan domin banida shirin tunkarar aure ahalin yanzu, kai! Wata tsawa mai martaba yadaka masa wadda ni kaina ummi Aisha sai da narazana, bafa shawararka nake nema ba umarnine nake baka, yanzu kai ibrahim har kayi girman da zan fada maka magana kayi min musu? Tuba nake ranka yadade, natuba mai zamani, ayi min afuwa hakika nayi kuskure amma ayafe min, cikin fada sarki yace to aure babu fashi zan daura shi inyaso aranar dana daura kana iya warwareshi ta hanyar sakin matar, ai kuwa zan sakenta tafida yafada acikin ransa.
[8:17AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣4⃣
Na UMMI A'ISHA
Tabbas ko wacece sai narabu da ita danme za ayi min auren dole bayan ga faisal nan shi ba ayi masa ba, kuma naga komai mai martaba zai yi tare yake yi mana nida faisal sai a wannan ne za a banbanta mu? Fadan mai martaba ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa, sanin kankane ni ba karamin mutum bane bare jama'ata su rainani, bana alqawari in saba sannan bana yin magana biyu dan haka dolenka ka amincewa umarnina domin ba kaine ka haifeni ba nine na haifeka idan hukuncin dana yanke maka yayi maka tsauri to ka mutu kabar duniyar inyaso sai ka huta da auren da zanyi maka, tuba nake ranka yadade, ayi min aikin gafara, tashi kabani wuri mutumin banza mutumin wofi, Allah ya huci zuciyarka ya mai martaba cikin hanzari tafida yatashi yafita gaba daya idanuwansa sun kada sunyi jajawur kamar gauta, ransa in yayi dubu yagama baci, dakin inno ya koma acan yaci karo da momcy bai iya yi mata magana ba yashiga dakin inno yazauna akusa da kafafunta, inno wai dan Allah laifin me nayi muku ne haka kuka tsaneni? Murmushi tayi irin nasu na manya haba tafida na, da daya tamkar da dubu, wlh tafida idan na rantse maka cewa dani da mai martaba munfi sonka fiyeda kowa acikin yayanmu ba zanyi kaffara ba, ni da mahaifinka duk cikin yayanmu munfi nuna maka so da kauna ba wai dan kasancewar ka dan auta ba a'a soyayyar daga Allah take haka nan Allah ya sanya mana sonka fiyeda sauran yan uwanka sannan nasan mahaifinka bazai taba cutar dakai ba, saboda idan kashiga damuwa sai yafika damuwar, dan Allah tafida ka kwantar da hankalinka kayiwa mahaifinka biyayya kaji? Shi wannan mutumin da zai baka yar tasa mutumin sarki ne tun suna yara, yayiwa sarki alherai da dayawa wadanda bazasu lissafu ba to kaga kuwa shi ALHERI DANKO NE! Baya faduwa kasa banza sannan kuma dadi musanye ne, abinda nakeso dakai kawai shine kayi biyayya, cikin kunar rai tafida yace amma inno ga ba faisal nan ba why not shi baza abashi ba? Sai ni za abawa danni aka tsana? Kai rufe min baki marar kunya inno tafada cikin fada dan kaga inata shawo kanka ina lallaminka da kalamai masu dadi shiyasa zaka fada min maganar banza? Anki abawa faisal din kai aka yi niyyar bawa in yaso aranar da aka daura auren ka saketa ko kuma idan ankaita gidan naka ka kasheta kaji? Fitsararren kawai in banda tsabar rashin kunya har sarki yabada umarni katsaya kana ja in ja da umarninsa? To sai gareka karka fasa, tashi maza kafice min daga daki kuma kar nasake ganin kafarka acikin dakina, da sauri tafida yatashi yafita bayi da kuyangu sai mamaki suke domin inno bata taba yiwa tafida irin wannan fadan ba kowa agidan yasan tafida shine dan lelen inno da mai martaba.
[8:41AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣5⃣
Na A'ISHA (UMMI)
Tafiya yake ahankali duk da cewa dama haka yasaba tafiya amma tafiyar yau tasha banbam data kullum lungun momcy mahaifiyar abokinsa faisal kuma dan uwansa najini yanufa yana shiga jakadiya tayi masa iso yakarasa dakin momcy tana zaune akan gado wata baiwa tana yimata firfita da muhucin kaba gefenta kuma wata baiwar ce take yi mata labarun ban dariya ko sallama bai iyayiba yashiga take bayin suka bar abinda sukeyi suka tashi suka fita, akan daddumar dake malale acikin dakin ya zauna yadukar da kai barka da hutawa ranki yadade, barka kadai tafida,cikin damuwa yace momcy ko kin samu labarin abinda zai faru dani? Cikin bacin rai tace nasamu tafida dazun nan jakadiya tazo min da labarin kuma inaji banyi kasa agwiwa ba natashi natafi wurin mai martaba domin jin sahihancin labarin anan ya tabbatar min da gaskiyar lamarin sai dai nayi takaici da ba abar min kai kazabi matarka da kanka ba kamar yadda aka yiwa sauran yan uwanka sai amma kirana gareka shine kar kayi jayayya da umarnin sarki domin hakan zai iya janyo maka fushin mai martaba akanka sanin kanka ne kuma fushin Allah yana daga cikin fushi na iyaye wannan hadisine ingantacce saga bakin annabinmu annabin rahma, kayi hakuri kayi biyayya idanuwansa jawur ya dago yadubi momcy dama momcy duk wanda kaji anbawa hakuri ai cutarsa akayi cikin damuwa tace babu komai tafida ni kaina narasa dalilin sarki nayimaka wannan irin aure acikin gaggawa amma babu komai kayi biyayya kawai ni naso ace ma wannan shashan dan uwan naka faisal za ayiwa auren, babu komai momcy nagode, tashi yayi yafita yanufi sashensu shida faisal yana shiga yasamu faisal kwance afalo cikin kujera cikeda damuwa yanemi wuri ya zauna faisal yana kallon fuskarsa yasan ya amsa kiran mai martaba tashi zaune yayi yadafa kafadar tafida abokina ya akayi? Kamar tafida zai yi kuka yace faisal wlh bana son auren nan bana so bana so, cikin damuwa faisal yace wlh tafida dazun nan lokacin da akeyin maganar tun alokacin nafara rokon sarki akan yayi hakuri nasan bazaka so auren nan ba amma yaya chiroma da baba galadima suka hayayyako min da fada wai nida kai mun raina kowa afada bama bin umarnin mai martaba saboda mu yan gata ne nida kai ne kawai sarki zai bawa umarni mu tsaya muna jayayya dashi ganin sun dauki zafi yasa nataso nabaro wurin amma dan Allah kar kadamu kanka, lallashin tafida faisal yayi tayi da kalamai masu sanyaya zuciya tareda nuna masa illar rashin bin umarnin iyaye.
[1/20, 11:29 AM] Ummi A'isha: [9:21AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣6⃣
Na UMMI A'ISHA
Shidai tafida yau rauni yafi gaban ciwo kallon faisal yayi kasan Allah? Ana daura auren nan sai nasaketa kowacece cikin sauri faisal yakatse shi kar kasoma yin haka abokina domin zaka aikata babban kuskure kar kazo kayi abinda mai martaba zaiyi fushi dakai, tashi tafida yayi yashige daki yabar faisal afalo cikeda damuwa domin damuwar tafida ta faisal ce.
***********************
Alhaji Ahmad Muhammad sani shine sarki na uku ajerin sarakunan garin misau ta jihar bauchi, garin misau babban gari ne sannan kuma babbar masarauta ce mai girman gaske, sarkin misau nayanzu shine sarki na uku yagaji sarautar ne ahannun mahaifinsa alh Muhammad sani nabiyu, alh Ahmad sani sarkin misau nayanzu yana da matan aure 2 hajiya kilishi (inno) da hajiya mabruka (momcy),hajiya Kilishi wadda akafi sani da inno itace uwar gida sunyi auren saurayi da budurwa ita da mai martaba lokacin baifi dan shekara 23 ba alokacin aka nadashi sarkin garin misau, Allah ya albarkacesu da yara guda 5 duka maza babban dan sarki shine chiroman misau alh Muhammad sani sai mai bimasa marafan misau alh adamu Ahmad sani sai turakin misau alh jamil ahmad sani sai barwan misau alh Mahmud ahmad sani sai kai gaman misau alh mannir ahmad sani daga nan sai dan autansu tafidan misau sannan hakimin disina alh ibrahim ahmad sani, amaryar mai martaba hajiya mabruka (momcy) yara biyu suka haifa da mai martaba babbar yarsu itace hajiya maryam (hajiya daso) sai kaninta alh faisal ahmad sani san turakin misau hakimin dambam, faisal da tafida tare suka taso adaki daya kasancewar babu yan ubanci agidan kowa yana kaunar dan uwansu bazaka taba iya banbance tsakanin dan hajiya inno da dan hajiya momcy ba saboda tsabar hadin kai, gaba daya yaran inno adakin momcy suke tasowa yayinda itama momcy ita ta aurar da hajiya daso kasancewar bata da ya mace, shi kuwa faisal da tafida kusan lokaci daya aka haifesu tsiransu kwana 5 ne atsakani shiyasa suka taso kamar wasu yan biyu sannan suka zama abokan juna dukkaninsu basuda wani aboki sai junansu tun suna yara haka suke kiran junansu kuma wani abin sha'awar shine bazaka taba jinsu sunyi fada ba kullum cikin zolayar junansu suke, gashi suna yar kama duk kuwa da cewar tafida yafi faisal kyau domin shi mahaifiyarsa ya dauko ita kuma bafulatana ce.
[10:03AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣7⃣
Na UMMI A'ISHA
Tunda suka taso basa rabuwa tare suke yin komai har suka zama samari shekarunsu daya tsayinsu daya kuma ko amakaranta ajinsu daya, tun lokacin da suka gama primary school suka tafi america acan sukayi karatunsu gaba daya suna gama degree suka jona masters dinsu, zaman da sukayi akasar waje anan tafida ya koyi shan ganye shikuma faisal yakoyi neman mata amma daga nan baya wata dabi'a shima tafida daga shan ganye baya komai mace kuwa babu abinda yake hadashi da ita sai asibiti idan bata da lafiya, tun akasar turai yan mata suke nuna masa maitarsu afili daga turawan har bakar fatar amma bai taba yadda ya kusanci kowacce mace ba neman mata sai dan uwansa faisal, suna kammala karatunsu suka dawo Nigeria kowannensu yakama aiki shi tafida kwararren likitane a fannin mata shikuma faisal auditor ne a ministry for local government, basu jima da fara aikiba akayi musu sarauta shi faisal sarautar sa san turakin misau hakimin dambam shikuma tafida sarautarsa tafidan misau hakimin disina,tun asali shi tafaida bamai yawan magana bane bashida surutu magana bata dameshi ba wannan dalilin ne yasa ake yimasa kallon mai girman kai yanmata dayawa kuma suke masa kollon mai takama dakyau basusan shi haka yakeba naturally.
***********************
Tafida yana shiga daki yakifa akan gado zuciyarsa sai tukuki take tamkar zata fasa kirjinsa tafito waje cikin damuwa faisal ya tashi yabishi cikin dakin yaci gaba da bashi baki amma tafida Ji yake kamar ya rushe da kuka, tashi yayi ysdauko ganye yafara busawa shikuma faisal ganin haka yasashi fara tsaki dalla malam kafita waje kagama busa hayakinka acan hararsa tafida yayi kana iya fita kai tunda ba daureka nayi ba dan iska kawai, dariya faisal yayi kaima ka kusa zama dan iskan ai tunda kakusa sanin hanyar da baka sani ba, tsaki tafida yayi yasake xukar tabar ya busar da hayakin ai wannan hanyar ko zan santa ba yanzu ba, kai dan iska ne sau nawa zaka santa? Inji faisal murmushi tafida yayi kaine dan iska amma ni banida hadi da kowacce mace,yanzu ai zakayi hadin da ita faisal yafada yana dariya, hira suka cigaba dayi har karfe dayan dare sannan suka kwanta bacci amma shi tafida bacci gagarar idonsa yayi shima faisal din baiyi dayawa ba yatashi. Kamar yadda yasaba fita yauma haka ya shirya ya dakin inno ya gaisheta dakyar ta amsa fuskarta babu walwala, fitowa yayi ya shiga dakin mai martaba shima hakan take, dakin momcy ya shiga itace ta karbeshi da fara'a ga kayan karyawa ta shirya masa sai data kara yi masa nasiha sannan yatashi yatafi. Yana zuwa asibitin su ya zauna jugum yana nazari wai shi mai martaba zai yiwa auren dole, bayan auren dolen ma marar lafiyace yarinyar, kai ai auren nan bazai dadeba yafada yana bude laptop dinsa.
[10:30AM, 11/13/2015] Ummi A'isha: ALHERI DANKO NE!
1⃣8⃣
Na UMMI A'ISHA
Laptop dinsa yabude yashiga email dinsa anan yaci karo da wani sako daga kungiyar litocin mata ta duniya ta shirya musu wani course har na tsawon wata 5 kuma har dashi aciki zasu gudanar da course din ababban birnin kasar India wato Mumbai dadi yadanji domin dama garin yayi masa zafi da azamarsa yatashi yanufi maternity domin duba halin da suke ciki. Tunda yadawo daga office yakule adaki shi kadai yafara cike ciken takardun tafiya