Showing 162001 words to 165000 words out of 193749 words

Chapter 55 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

1683

tana tamke fuskarta, a nutse ta dafa )?irjinshi duk da yana sanye da kayan bacci masu laushi na kamfanin Adida ??aya hannunta kuma ta shiga shafo fuskarshi cike da tsantsar kulawa tace "Ayyah! Me ya samu jarumina haka? Nake ganin damuwa a tattare dashi."

Waina idanunshi yayi sai kuma ya kalleta, a hankali ya rumgumota jikinshi ya matseta a sanyaye yana sauke numfashi yace "Ahhhhhhh! Matarmu, mulki...nauyinsa ya min girma sosai..."

Sai kuma ya ??ago ya tallabo fuskarta yace "Zo muje ki tayani bacci, na gaji sosai."

Cike da kulawa ta sake shafo kumatunshi tace "Sannu bawan Allah, Allah ya tayaka ri)?o, in sha Allah za ka cinye wannan jarabawar."

?auke hannayenta tayi ta juya da niyyar zuwa drowerta dan ??auko kayan baccinta sai kuma ya ri)?o hannunta, kallonshi tayi da jiran )?arin bayani, hakan yasa shi nuna mata )?allayen nan da idanu sannan yace" Na me ye? Ban sanki da barin datti a wuri ba."

Murmushi ta saki tace" Oh! &?allaye ne kawai."

Da alamar tuhuma yace" Me kike yi da su?"

Marairaicewa tayi tana kallonshi tace" Har yanzu baka san wacecr matarka ba, ba dan an hanani cimmasa ba, da yanzu ni ??in nan babbar ma??inkiya ce, sai dai..."

Yawu ta ha??e sai kuma tayi murmushi tace" Ban samu cimma burina ba, hakan yasa ya mutu sannan ya gudu ya barni."

Jaye hannunta tayi daya ri)?e tace" Bari na canza kaya."

Da kallo ya bita har ta )?arasa ta shiga ciro kayan da za ta saka, yana tsaye yana kallonta yana jin kamar ya rageta ta wani fannin, dan gaskiya lokacin nan da suka ??auka bayan ?ban uwanta bai san komai game da rayuwarta ta baya ba, kuma laifinshi ne dan shi ne bai tambayeta ba, ita kuma ya gama gane miskila ce akan abinda ba'a nemeta da shi ba ko kuma akan abinda ba ta ba wa mahimmanci ba.

Har ta shirya suka tafi ?angaren nashi baya da walwala dan kunya ce ma yake jin tana son kamashi da ya kasa mata tambayar ko da bani labarinki ne, hakan yasa daren yau ya tafi baya da annashuwa dan kwan yayi da tunanin *wacece matarsa*?

*Tsaf*! Ta shigo ??akin ri)?e da kofin shayin har turiri yake ta )?araso gabanshi, a ladabce ta mi)?a mishi ya kar?a yace "Nagode matanmu."

Murmushi tayi ta zauna gefenshi tana kallon alkyabbar jikinta tace "Me yasa ka za?amin wannan kayan? Kamar wacce za ta je gaishe da wani..."

Idanun da ya watso mata yasa ta ha??e maganar shi kuma yace "Wani wa?"

?war )?aramar harara ta watsa mishi tace "Kishi wai? To ni kamar wani shugaban )?asa nake nufi."

A nutse yasa yatsunshi biyu ya mintsineta a damtse hakan yasa ta zabura tace "Aouchh! Abdul mugu..."

&?yal)?yalewa yayi da dariya ya kai kofin daidai bakinshi ya sur?a ka??an sannan ya kalleta yace "Ke ce muguwa, saboda kin saba min da komai naki yanzu, a yadda nake ji ba lallai na iya rayuwa idan babu ke ba."

Gyara zamanta tayi sosai tana rauda kanta tace "Sona kake wai?"

Da sauri ya girgiza kai yace "Um-um! Sha)?uwa ce kawai."

Kallon wutsiyar idanu ta masa tace "Shiyas afa nima bana sonka, dan gaskiya ba zan so wanda baya so na ba."

Fuska a game idanu a kakkafe kan fuskarta ya tsura mata su tare da janye kofin daga bakinshi gaba??aya yace "Kenan ba ki ta?a jin sona ba?"

Ba alamar damuwa a tare da ita tace "E, kamar yadda kai ma baka ji a kaina."

Juyar da kanshi yayi ya aje kofin )?afa ya mi)?e tsaye sannan ya kamo hannayenta ta mi)?e tsaye yana kallon idanunta yace "Ajiye maganata gefe, da gaske ba kya sona?"

Saida ta ??aga kafa??unta sannan tace "E, haka nake ji."

Da mamakin daya kusan halakashi ya wara idanunshi ya nuna kanshi yace "Haka ma kike ji ne? Akan nawa?"

Zuba masa idanu tayi a sanyaye tace "To kai ma ka ce baka sona k..."

Sakin hannayenta yayi a tsawace sosai yace "Ni ban fa??a miki haka ba malama, ni ina s..."

Sai kuma yayi tsit! Tamkar an ma)?ureshi ya rarraba idanu tsakanin fuskarta da jikinta, ja baya yayi yana fa??in "Hakane, hakane nima ba sonki nake ba."

Harara ta galla masa sama da )?asa tace "Hmmm! Kar ka so nin mana, dama ni na san ba kyakyawa bace kuma ba wayayya ba, amma ka sani ni ba shashasha bace..."

Saida ta matsa daf da shi ta ??ora yatsarta kan )?irjinshi tace "Ina da hankali ai, ba za ka rainamin wayo ba Abdul."

Hanyar ??akin ta tunkara zata fice sai kuma ta juyo ta kalleshi tace "Na fa??a kar ka so nin, nima bana sonka."

Kama )?ofar tayi ta bu??e tana daf da fita Abdus-samad da gaba??aya lamarinta ya mishi na kama da masu son kasheshi ya zuba mata idanu kawai yayi sauri ??aga bakinshi da )?yar yace "Ki jirani, zamu je gidanku ne."

Da sauri ta dakata tare da juyowa ta kalleshi, ranar farko da ya bata izinin zuwa gidan sumbatar da ta mishi ta fi ashirin a fuska kawai, ya ??auka zai ga wannan farin cikin ne da irin kalmar da ta fa??a masa a ranar cewa " *Ka fi kowa sarkina, ina alfahari da kai.*" Amma yanzu sai ta yatsina fuska kawai ta juya ta ficewarta ta barshi tamkar wani gaula.

Mantawa yayi da shayin da sauri ya nufo gadon dan ??aukar hularshi da rawani da kuma sandar nan, saida ya bigi kofin ya zubar mishi a )?afa ya ji zafi sannan ya ankara da me ya yi, ba ma wannan ne ya ??aga mishi hankali ba kamar )?aramar ihun da yayi ya yarfe hannu wanda shi yasa tashin hankalin da yarinyar can ta kunna masa ne ya sa shi feso abun a suffar ihu. Ca??!

Da sauri ya ??ora hular a kanshi haka ma rawanin ya laulayashi dai ne amma shi kanshi yasna baiyi ba, saidai bai da lokacin tsayawa gyarawa, ita yake so ya bi ya ri)?e damtsenta da kyau ya zazzare mata idanu dan kar ta sake kwatanta masa haukan nan irin na yay, haka kawai ta ??aga masa hankali, akan me? Sai ka ce wata mai son ??aukar fansa. Da ??an sauri ya fita a ??akin sai dai kuma saurin nashi ya ragu ne lokacin da ya ganta zaune a kan ??aya daga cikin kujerun royal ??in dake falon ta wani ??ora )?afa ??aya kan ??aya sai cika take tana batsewa.

A hankali ya shiga takawa saidai hata takalmin dake )?afarshi )?afa ciki sauti suke bayarwa wani )?was )?was! Fuskarta da yake kallo ya ji tana razanashi haka kawai kamar ya ga dodonniya, sai ya ji zafin da ya fito da shi dan ya mata kashedi idan ma ta kama ya gaura mata mari dan gaskiya ta dagula masa lissafi sai ya ji duk ya ?ace, neman duburburcewa yake tun bai isa gareta ba.

Gabanta ya tsaya )?i)?am yace "Shine kika ya?amin magana kuma kika baroni?"

A hankali ta ??ago kanta ta zuba masa idanunta farare, sai kuma ta ??auke kanta tana ??aga gira sama irin "Ohon maka."

Da wani sabon ?acin ran ya nunota da yatsa yace "Ke! Ke tsaya ki saurareni, kinga bana son irin haka, ban kulaki ba ki daina sakani a uku haka kawai, kuma kinga idan dai ba tsoro ba ki maim..."

Irin kallon nan na gani kasheni ta watso masa, sai kuma tayi raurau da idanunta ta marairaice a sanyaye tace "Na maimaita? Marina za ka yi idan na maimaita? Saboda kawai ka tsaneni sai ka tsareni kana min ihu a kai..."

Kamar an jonata kuma sai ta zabura ta mi)?e ta dafe )?ugu tana kallonshi sama da )?asa fuskarta a ha??e zuciyarta na tafasa saboda cewa da ya yi baya sonta, ita yanzu a ganinta ai ta zama jini da tsokarshi, amma shine zai ce baya sonta sai sha)?uwa kawai, lallai ma! Haushinshi take ji sosai akan wannan maganar.

Hawayen da suka cika mata idanu lokaci ??aya ta ha??e tare da cewa "Wallahi ba dan kana sarki ba ko, da wani ne daban ko? Ji nake da na kabta mishi mari, amma ba komai akwai Allah."

Bu??e baki yayi irin zai yi magana, sai kuma mamaki ya hanashi fa??in komai ya sake gyara tsayuwa ya kalleta, )?an)?ance idanu yayi ya sake kallonta da kyau, to shi dai bai san ya zaiyi da ita ba, ya cakumeta da kokawa ne? Ko gidan horo zai sa a )?argame mishi ita a bisa wannan zunubi da take aikatawa? Shi ma ba dan yana sarki kar a ce bashi da adalci ba, wannan abubuwa da take masa tana hassalashi ai )?ararta zaiyi wajen babban al)?ali.

Da ta ga bai ce mata )?ala ba kuma so take ya kulata ko ta feso abinda ke ranta, sai kawai ta zura hannayenta biyu ta warware masa rawanin dake kanshi wanda ta ga ya ??aura ba daidai ba, fuskarta a ha??e sosai amma kuma tana gyara masa na??in rawanin, tsatsareta yayi da idanu sai kawai ya saki murmushi yace "Kin san dan ke ce shiyasa na )?yaleki ko?"

Ba tare data kalleshi ba da muryarta dake nuna a hassale take tace "Ni ma dan kana kai ??in ne."

Matse baki yayi ya )?ara gyara tsayuwarsa yace "Hummmm!"

Ba ta kalleshi ba tace "Kai ma hmmm ??in."

Sai kuma ta koma gunguni tana fa??in "Tunda ka san kaine mijin, me ye ma na kulaki? Dan in fa??i wani abu a ce ?bar wuta ce ni, wallahi dan kana sarki ba zan bari ka tauyeni ba, haka kawai."

Gama fa??arta da daidai gama ??aura masa na??in kawai ta kama hanyar fita tana fa??in "Muje."

Da kallo ya bi bayanta yadda yau ake tafiyar ba ma ??an legezen ???i (elegance) nan in ji yan boko sai kawai ya girgiza kai yace "Lallai, za ki san ko ni waye."

Sanin yanzu fa dogarai zasu mata caa idan ta fita suna gaisheta dan a tunaninsu shine yasa saurin ri)?e alkyabbar da kyau ya ??aga sandar gaba??aya ya zuba a guje ya tare gabanta suna kallon kallo, da sandar ya nunota yace "Kinga dakata, idan fa??an kike ji ki bari har mu dawo, wallahi kar ki sa na tauye ha)?)?in al'ummata saboda rikicinki."

Jinjina kai yayi ya gyara jikinshi da saita nutsuwarshi sannan ya jawo hular alkyabbarta ya rufe masa fuska kafin ya ri)?o hannunta ya bu??e )?ofar suka fita a nutse.


Suna fitowa kowa ya shiga haramar kula da abinda ke wuyanshi, dogarai biyu ne suka shiga gabansu sai hu??u dake bayansu suna ta faman zabga musu kirari na takawarsu lafiya, dreban dake cikin mota zaune yana ganinsu ya fito yana rusunawa shima, ??aga daga cikin dogarin ne ya bu??e musu )?ofa, cikin nutsuwa ba tare da ya saki hannunta ba ya mata alamar ta fara shiga, a sanyaye ta ??aga )?afarta ta shiga kafin ya bi bayanta ya zauna aka rufo musu )?ofar.

Dreban ne ya shiga lokacin da Saleema ta jaye hannunta daga cikin nashi, hakan yasa shi kallonta har zaiyi magana sai kuma dreban ya shigo, matsawa yayi sosai kusanta cikin ra??a yace "Har yanzu hushi kike dani?"

Sadda kanta tayi tare da ??an karkato da kanta kusan na shi kan ita ma da sigar ra??a tace "Yaushe ma muka fara fa??an da har kake tunanin ya isa a ce mun gama?"

"Da saura kenan?" Ya fa??a yana le)?a fuskarta, ??aga masa gira tayi sai kuma ta kanne masa ido ??aya, hakan yasa shi sake ra??a mata "Kina irin haka sai ki sa sarkinki ya kauce hanya a gaban masu girmamashi."

?auke kanta kawai tayi tana kallon gilmawar doguwar da??a????ar katangar gidan, shiru motar ta ??auka babu sautin komai duk da su hu??u ne a motar, dan bayan ita da shi da dreba akwai ??an-baka dake tare da dreba a gaba, motar dake gabansu ma irin wacce suke ciki ce Prado sai dai fara, amma ita ma kamar wacce suke ciki ce daga bayanta wajen rubuta lamba sai motar ke ??auke da rubutun sunan *sultan de Maradi* sai ??an hoton tutar Niger daga gefe ka??an.

Numfashi ta sauke a nutse tare da ??an waigowa ta kalleshi, yadda ta ga motocin nasu suna ??aukar hankalin mutane ba wai dan kyawunsu ko tsadarsu ba sai dan shaida wa??anda ke cikin motocin, yau ita ma ta kasance ??aya daga cikin mata masu wani matsayi da iko a garin nan ko ma ta ce a )?asar, lokaci )?an)?ani da ya wuce a sake take tana rayuwar ta kamar kowa, yau gashi idan tana tafiya harda jami'an tsaro a bayan motar da take ciki guda biyu baya ga dogarawa.

Zafin da ta ji kan kumatunta ta tabbatar da hawaye ne take, hakan yasa ta a hankali ta sakala hannunta ga nashi hannun ta ??ora kanta a kafa??arshi ta ??an ja majina, a nutse ya le)?a fuskarta ganin hwaye sun sauke mata yayi saurin ??agota yana tallabo fuskarta cike da tsantsar kulawa yace "Matanmu, me ye faru? Fa??an namu ya kai hakane?"

Da sauri ta girgiza kai a sanyaye tace "A'a, ba shi bane."

"To me ye?" Ya fa??a yana sake tsareta da idanu, )?ara jan majina tayi dan hancinta ke neman ??umewa sannan tace "Falalar ubangijina nake tunawa, yadda ya min *BAIWA* sai na ke jin tamkar ni ka??ai ce a fa??in duniyar, shiyasa na yi nasarar wawushe komai."

Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jawota ya ??ora kanta a )?irjinshi yana ??an shafawa a nutse yace "Shiii! Ki godewa Allah."

Jinjina kai tayi a zuciyarta ta furta "Alhamdulillah." Haka suka ci gaba da tafiya ba da gaggawa ba har suka isa )?ofar gidan, motar dake gaba mai gadin ya le)?a suka ??an yi magana jim ka??an ya shiga ciki ya wangale musu )?ofar ya koma gefe yana kallon wucewar motocin guda uku, a farfajiyar sukayi fakin inda duk suka fiffito suka taru a daidai motarsu sai wata hadima dake tare da jakadiyar Saleema a motar dake bayansu ta yi azamar nufa cikin gidan dan sanar da su shigowar mai martaba da iyalinshi.

Kallonshi Saleema tayi tana jin kamar ta cijesu, to ita a ganinta gidansu ne sai an mata iso za ta shigo? Takurar banza kawai! Saida hadimar ta fito ??anbaka ya kama hannun motar ya bu??e yana fa??in "Takawarka lafiya mai mara??awa, giwa kake mai takon )?asaita, zaki a dawa ma sarki kake, Allah ya taimaki mai taimakon talakawa."

A hankali ya fita a motar inda Saleema ta fita ta ??aya )?ofar da jakadiyar ta bu??e mata, a nutse suka tako har suka sake ha??ewa kafin su ci gaba da takawa a hankali har suka haye ?bar matakalar suka isa daf da )?ofar shiga falon. Jakadiyarta tare da hadimar ce suka fara shigewa gaba sannan ??anbaka dake ri)?e da bulala ya shiga dan dolenshi ne ya tabbatar da zaman sarkinshi lafiya.

Safiya da fitowarta kenan bayan komawa da tayi ta ??auko hijabi sanda aka sanar da zasu shigo tsayawa tayi tana kallon ??anbaka dake gyara kujerar da kusan ita ce ta farko a layin kujerun sannan ya koma da sauri yana fa??in "Allah ya )?ara maka lafiya da nisan, bismillah zaku iya shigowa."

Saleema ta fara shigewa kafin ya biyo bayanta, a tare suka yi sallama a cikin tausasan muryoyinsu musamman ma Abdus-samad da kamar baiyi ba. Alhaji Yusuf da ke tsaye tun ??azu yana mamakin wannan zuwa na safe haka da sauri ya matso yana amsa sallamar da yi musu barka da zuwa.

Carpet ??in dake gabansu wanda )?aramin teburin ke gabansu yasa Saleema cire takalminta da basu da tudu sosai, a nutse cike da kamala da girmamasu da son nuna musu shi ma ??ane garesu ya sunkuya yana )?o)?arin kwance zariyar ba)?a)?en takalminshi, da sauri Alhaji Yusuf yace "Ranka shi da??e ka barsu ba komai, ba sai ka cire ba ai bismillah ka zauna."

Kanshi kawai ya ??ago a hankali ya kalleshi ya girgiza kai sannan ya kwance duka ma??aurin ya mi)?e tsaye, cikin nutsuwa yasa ??aya )?afar ya ??an take ??aya takalmen sannan yasa )?afar dake sanye da safa fara tas tamkar shaddar dake jikinshi ya cire ??ayan sannan ya )?arasa ya zauna.

A hankali Safiya ta )?araso cike da dattako kusa da Saleema, shirin zubewa tayi )?asa kamar yadda ta ga hadimar nan da jakadiya sun yi, hakan yasa Saleema yin zunbur ta ri)?o kafa??unta ta furta "Subhanallah Mama!"

Mi)?ar da ita tayi sannan ta zaunar da ita suka zauna tare tana sake ri)?o hannayenta, Alhaji Yusuf ma kusan Safiyar ya zauna hakan yasa shi da Saleema suka sakata tsakiya yana maida hankalinshi kan mai martaba yace "Ranka shi da??e..."

Kallon ?angaren da yayi inda suke yasa bai )?arasa fa??a ba saboda umarnin da ya ga yayi ma jakadiyar da hannu, rusunawa sukayi suka amsa tare da mi)?ewa suna fadin sun barshi lafiya a fito lafiya.

Fitarsu a ??akin daidai da fitowar Ardiya tare da Hadeeya cikin shirinsu na tafiya gidan Saleema, wanda Ardiyar ce ta matsa sai dai su je tare da ita, kan wanda idanunsu suka sauka yasa kwarjini da tsananin haibarsa da shigarsa ta kamala data ?oye fuskarsa yasa Ardiya kallon inda mijin na ta yake sai dai dake hankalinshi baya kanta yasa ta )?arasowa tana mai ci gaba da kallonshi sosai.

Saida ta zo kusanshi ne ya ??aga kai ya kalleta cikin ra??a yace "Zauna mana, mai martaba ne fa mijin Hajiata."

Wara idanu tayi ta sake kallon inda yake sai dai idanun da suka kusa ha??awa da Abdus-samad yasa ta saurin sadda kanta ta zauna kusa da Alhaji Yusuf din tana )?a)?aro murmushin da ita dai bata shirya masa ba tace" Barka da zuwa... *ranka shi da??e*."

Hadeeya ma dake kallo tana mamakin yaushe suka shigo )?arasowa tayi da wayarta a hannu da niyyar zama kusa da Ardiya akan kujerar, a nutse yasa hannunshi ya jaye glass din daya rufe mishi idanu duk da fari )?ar ne, tamkar damisa haka Hadeeya ta ga ya watso mata wani kallo da bata ta?a sanin cewa akwai kallon da zai sa ka shiga hankali ba sai yau, da kallon nan da ya mata sai ta ji kamar za ta iya cewa ta fahimci me yake nufi, sai kuma ta sulale )?asa tana sadda kanta ita ma tace "Allah ya taimaki yalla?ai."

?auke idanu yayi daga kanta yana hango tsantsar raini a tare da yarinyar da kuma al'ajabi a idanun matar da ta fito yanzu, sai kuma dattako daga matar da ya samu tsaye tun shigowarsa. Yana jin su lallai suma iyalinshi ne, kamar yadda ta shiga rayuwarsa haka shima yake buri a yanzun, dan haka ma ya ri)?e glas ??in da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login