Showing 21001 words to 24000 words out of 30185 words

Chapter 8 - AUREN TAGWAYE COMPLETE DOCUMENT Book .txt

Unknown   

29 Nov 2024

1271

Hussaina tayi tare da dafa kafad'arta "indan wannan kada kidamu, ni zantafi da wayarki zan barmiki tawa koda su daddy sunkira nasan bayanin dazanyimasu.


"To shikenan Hassana tafad'a, kawai dai ta amince da bu'katar 'yar'uwar tata badan komeba sai dan taga yanda ta masifar shiga damuwa, amma can 'kar'kashin zuciyarta cike take da tsoro da fargabar abinda suke shirin aikatawa.


Nan Hussaina ta 'kar6i wayar Hassana ta kwafi Number Hafiz tasaka a wayar Hassana, wacce ke wayarta kuma tasata blacklist tare dayin delete d'in number daga wayarta sannan ta baiwa Hassana wayar.


Nan ta d'auki jakarta sukayi sallama da Hassana tatafi, tana fita takira Hafiz da number Hassana tafad'amashi tana hanya kuma idan ze kirata da wannan number ze kirata dan tabar waccan a gida.














Love u all my Fan's 💃🏻 shoki 🏊🏻‍♀😏
[11:08AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*






*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻






Page......................28






Gabanta yashiga dukan tara-tara a zuciyarta tarin'ka tunanin taya zatayi zaman aure da mijin 'yar'uwarta, bayan ba mutuwa tayiba, kuma ba rabuwa sukayba, lallai Hussaina tasakata matsala sai yanzu takejin dama bata amince da 'kudirintaba, amma yanzu aikin gama ya gama dole ta zauna tarufama 'yar'uwarta asiri har lokacin dazata dawo, da wannan tunanin taji ana kiraye-kurayen sallar magrib saboda haka da sauri tanufi bedroom tashiga toilet ta d'auro Al'wala ta kabbara sallah, bayan ta idar da sallar ta dawo falo tsayawa tayi tana tunanin yanda zata fara aiwatar da ayyukan gidan dan da Alama Hussaina duk yau bata gyara gidanba,


Sharar falon tafarayi, tare da yin mopping, sannan tasaka wani 'karamin towel me haske ta goge TV, center table, dakuma dining da sauran guraren da yakamata a goge, bayan ta kammala nan takoma bedroom, ta gayara tashare tare da canjama gadon bedsheet, lokaci guda gidan yayi fes kamar bashiba, freshner ta d'auko me dad'in 'kamshi ta feshe ko'ina hatta da toilet saida tagayara ta fesa freshener abin gwanin sha'awa gidan sai yakoma kamar wani Sabin kaya aka zuba saboda tunda yake Hussaina bata ta6a gyarashiba, kullum saidai ta 6ata.


Bayan ta kammala wannan kitchen tanufa nanma tsayawa tayi tana tunanin me zata dafa, dan tasan duk inda me gidan yake yana gab da dawowa duk da batasan lokacin dawowar tasaba, ta dad'e haka daga 'karshe ta yanke shawarar dafa abu mai sau'ki dan dare yafara gashi anata kiraye-kirayen sallar isha'i.


Jalouf d'in kus-kus ta dafa wanda yaji kayan lambu da kayan 'kamshi, sannan tayi amfani da tsoka nama zallah ta yankata 'kanana aciki yanda ze zamana duk lokacin da wanda zeci ya ebo yakai baki ze had'o da naman, dayake kus-kus ne cikin minti ashirin ta kammala dahuwar ta juye a flask, tare da had'a zo6o had'add'e shima sai 'kamahin flavour yake ta jera kan dining.


Bedroom takoma tafad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito bata wani 6ata lokaci gurin yin kwalliyaba lotion kawai ta murza tare da 'yar hoda sai man le6e, wadrope tanufa ta d'auko wani had'adden less d'inkin Riga da siket ta sanya, wow kayan kuwa sun masifar kar6ar jikinta kamar dama dan ita aka d'inkasu, duk wata sura ta jikinta ta bayyana.


Zama tayi falo tare da jawo wayar da Husaina ta barmata tashiga danne-danne, tana dubawa tashiga inbox bataga komeba, sannan tashiga chat nanma ba kome, dan Hussaina batabar komeba saida tayi delete, dan kada Hassana taga halin datake ciki.


** ** **




Daddy ne ke safa da marwa hannunshi ri'ke da waya yanata try number Hassana amma sai acemai switch off, abin na matukar bashi mamaki gashi kuma har 'karfe tara na 'ko'karinyi bata dawo gidaba, Momy kuwa hankalinta yayi 'kololuwar tashi "innalillahi Alhj yanzu ina yarinyar nan tashige, anya kuwa lafiya dan bata ta6a yimana hakaba,


Juyowa daddy yayi ya kalleta shima Hankalinsa a tashe, yace "ni kaina ina mamakin hakan dan Hassana yarinyace me matu'kar tsoro da kiyaye fushinmu amma yau ace tawuce ka'idar dana gindaya mata,


Momy wacce idanunta suka fara kawo kwallah tace bari inkira number Hussaina inji idan Hassana ta taho, wayarta ta d'auko ta lalubo sunan Hussaina tanata ringing ba'a d'agaba dan ganin sunan Momy a wayar ba 'karamin d'aga hankalin Hassana tayiba, dan tasan duk yanda akayi yanzu itada Daddy sunacan hankalinsu yatashi na rashin dawowarta gida, bata d'aga wayarba saida kiran Momy na hud'u yashigo sannan ta d'auka ta dannan OK tare da karawa a kunnenta saida ta dai-daita nutsuwarta sannan tace "Assalamu Alaikum.
A d'ayan 6angaren Momy cikin 6acin rai tace Hussaina kina ina inata kiran wayarki har kusan sau hud'u baki d'agaba.


Ba 'karamin fad'uwar gaba Hassana tayiba, tare da daburcewa dan gani take kamar Momy zata iya ganeta.
"Uhn ah am.... Dama bani kusa da wayar ne sai yanzu naji.
"To dama tambayarki zamuyi shin Hassana ta taho gida kuwa.?
"Eh tataho momy ai tun d'azu ta taho tace daddy yace kada ta wuce 'karfe shidda kuma biyar da rabi tabar gidannan.


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Momy tafad'a tare da fashewa da kuka, tama manta ko tsinke kiran batayiba, Hassana kuwa tsayawa tayi ri'ke da waya a kunnenta tana sauraren yanda Momy ke kuka tana gayama daddy cewa "tun 'karfe biyar da rabi Hassana tabaro gidan Hussaina.
"Subhannallah Daddy yafad'a tare da cewa Allah bayyana mamu ita a duk inda take.


Tsinke kiran Hassana tayi tare da sake kiran Momy, ringing d'aya ta d'auka, Nan Hassana ke tambayar "Momy wai meke faruwane, naji kinkira kintambayeni nabaki amsa kuma kinsa salati.
"Hussaina 'yar'uwarki Hassana har yanzu bata dawo gidaba kuma munkira wayarta switch off,


"Innalillahiwa'inna'ilaijirraji'un Hassana tafad'a tare da fashewa da kuka, kafin ta tsinke kiran.
A tunanin momy Hassana tana kukane saboda 6atan 'yar'uwarta.
Itako Hassana kukan nadama da ba'kin cikin halin dasuka jefa iyayensu takeyi, sai yanzu take datasanin yarda da kud'irin 'yar'uwarta.










Love u all my Fan's 💃🏻 shoki 🏊🏻‍♀. 🤒
[11:08AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*






*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻






Page......................29






Zaune take kan d'aya daga cikin kujerun dake zagaye da falon ta buga uban tagumi hannu bibbiyu, ba abinda take tunani sai halin da iyayenta suke ciki,


A zahiri tayi magana "nidai bari inkira Hussaina tadawo gidanta nikuma inkoma gida in fuskanci kowane irin hukunci daddy zeyimin koda kuwa zefi na Hussainar tsanani, dan bazan iya zama cikin tunani da fargaba ba.
Wayarta ta jawo talulobo sunanta ta danna kira amma kuma cikin rashin sa'a sai akacemata wayar akashe, "ya salam tafad'a tare da d'ora hannu bisa kai nashiga ukku, tafad'a tare da mi'kewa tsaye "kodai inyi tafiyata idan tadawo tamasu bayanin inda taje, "kai bazan iyayima sister hakaba, muddin nasan daddy yaji labarin tayi wannan tafiyar kasheta kad'ai ne bazeyiba....
Wayyo ni Hassana ansakani tsaka me yuwa tafad'a tare da komawa ta zauna kan kujera jiki duk ba lakka.


Horn d'in mota taji gabantane yayi wani mummunan fad'uwa da sauri tanufi window tad'ga labulen tare le'kawa, me gadi ta hango yana 'ko'karin bud'e get, bayan ya bud'e motar jabeer tashigo duk kan idon Hassana yayi parking sannan yafito hannunsa d'auke da jakarsa, da sauri takoma ta zauna sannan tayi 'ko'karin dai-daita nutsuwarta dukda mummunan fad'uwar gaban datakeyi.


Da sallama yashigo falon, Hassana na Zaune jikinta sai kyarma yake tana tunanin wace irin tarba zatayima mijin 'yar'uwar tata, da kyar tasamu ta dai-daita nutsuwarta tare da mi'kewa ta dur'kusa ta kar6i jakar hannunshi tana mashi sannu da Zuwa, jabeer kuwa tsananin mamakine ya lullu6eshi yayi tsaye inda yake yakasa motsawa yayinda itakuma Hassana ta dad'e da shigewa d'akinsa domin ajiyemar jakarsa.


Murmushi yayi a Zuciyarshi kuma yace "ikon Allah, yau kuma ni Hussaina kema wannan tarbar, bin ko'ina na falon yayi da kallo ya ganshi fes-fea ba kamar yanda yasaba ganinshiba kullum kace-kace, sannan tunda yashigo daddad'an 'kamshin girki dana freshner sun had'u sun dakar mai hanci, lumshe idonshi yayi tare dayin wani guntun murmushi sannan yanufi d'akin dai-dai Hassana itakuma zata fito daga d'akin kad'an yarage suyi karo da juna Hassanar tayi saurin ja da baya duk tawani daburce "um ga ruwan wanka can nahad'ama "To, kawai jabeer ya iya amsawa dashi tare da binta da kallon mamaki sannan ya wuce Zuwa toilet d'in, tana ganin shigarsa tayi saurin zuwa wadrope ta fiddo mashi 'kananan kaya marar nauyi tare da ajiyesu gefen gado sannan tafita zuwa falo.




: Yana fitowa daga wankan yayi tozali da kayan da Hassana ta ajiyemai murmushi yayi saida ya murza mai sannan ya d'auki kayan ya sanya tare da feshe jikinsa da daddad'an turarensa, sannan yafito zuwa falo, zaune take kan kujera da waya hannunta tund'azu number Husaaina kawai take try amma switch off, dan tunda jabeer yadawo hankalinta yayi matu'kar tashi jikinta keta kar-karwa tsoronta d'aya kada jabeer yagane ita ba matarshi bace.




Da sauri ta tashi tana mashi sannu da fitowa, tanufi dining ta zauna sannan ta kalleshi "bissmillah mana tafad'a tare da gyaramashi kujerar daze zauna, ba musu yazo ya zauna yana binta da kallon mamaki danshi har yanzu abubuwan dake faruwa ganinsu yake kamar a mafarki wai yau shine Hussaina ke tarairaya haka lallai da walaki amma koma miye ba yanzu yakamata in tambayetaba.


Yana cikin wannan tunanin harta zubamar abincin ta ajiye gabanshi sannan itama ta zuba nata, haka suka faraci dad'in abincin na ratsa jabeer har tsakiyar kanshi, a zuciyarshi yana cewa "yaushe rabon dayaci abinci me dad'in haka kullum yana hanyar zuwa restaurant,


Da misalin 'karfe tara da rabi na dare suna zaune falo kowanensu yayi ahiru wani Indian film suke kallo a tashar zee cinema, da Alama film d'in yayima Hassana kyau dan ta maida hankalinta kaf kan film din, yayinda jabeer bacci yacikamar ido, sai hamma yake d'aya bayan d'aya tasowa yayi daga kujerer dayake yazo inda Hussaina take zaune Yakama hannunta "Taso muje mu kwanta, wani mummunan fad'uwar gaba taji tayi saurin kwace hannunta Daga nashi tace kaje ina zuwa saina ida kallon wannan film d'in.


Juyawa yayi ya kalli TV cike da mamaki dan yasan Hussaina bata ta6a yimar musuba idan ya umarceta dasu kwanta, kuma da kallo be dametaba, da wannan tunanin ya wuce d'aki yayi kwanciyarsa kasancewar akwai gajiya jikinsa bacci yayi gaggawar d'aukarsa.
















Love u all my Fan's 💞💘💞💕💖😘
[11:08AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*






*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻






Page......................30






Husaaina kuwa bayan ta isa gidan Hafiz, cike da murna da jin dad'in zuwanta ya tarbeta, tana isa takira Zuby a waya, ringing d'aya zubyn ta d'auka dama jiran kiran takeyi.


"Hellow 'kawata Zuby tafad'a cike da 'kagara taji abinda Husaainar zata fad'a mata.
"Kawata naji dad'in shawarar da kikabani dan yanzu haka ina tare da mutumin,
Dariya zuby tayi a ranta tace "Zaki gane kurenki zaki gane da zuby kike magana.
Amma a zahiri sai tace "ai dama nagayamaki hakan kawai zakiyi kije inda ranki keso kiyi ko kwana nawa kikeso batare da wata matsala ba.
"Ai shiyasa nake masifar sonki 'kawata Hussaina tafad'a.
Zuby tace "ai nima banida kamarki shiyasa kullum nakeson ki kasance cikin farin ciki, da haka sukayi sallama, kowace ta ajiye wayar


Wata mahaukaciyar dariya zuby tayi tare da tafa hannu " yarinya kinshiga tarkona kad'an yarage in cimma manufata akanki,
Wata sabuwar dariya ta'kara kafin tasha mur kamar bata ta6a dariyaba "Hussaina ina me tabbatar maki yanda kika baro gidan jabeer kin barshi kenan Har abada.


Hussaina kuwa bayan sun gama waya da zuby toilet tashiga ta she'ka wanka, bayan tafito tabi jikinta da lafiyayyen lotion dinta tashafa kayan jikinta ta maida sannan tadawo falo ta zauna tana jiran shigowar Hafiz dan bayan sallar isha'i yafita yo masu take a way.


Be dawo gidanba sai 'karfe tara da rabi lokacin Hussaina nadai zaune kan kujera a falo sai hamma take jerawa d'aya bayan d'aya, ga yunwa na addabarta ga kuma wani irin bacci dake fizgarta


Da sauri Hafiz ya isa gareta tare da ajiye ledar dake hannunsa gabanta, "sorry babyna na dad'e ko? Ya tambaya yana kallonta yanda take lumshe idanu da Alamar jin bacci tattare da ita.


"Uhm, kawai tace tare da 'Kara gyara zamanta kan kujerar datake, "sorry sorry babyna tafad'a tare da nufar kitchen, bayan yan mintoci ya fito hannunsa d'auke da plate da cukulla da cup's, gabanta yazo ya ajiye sannan yazuba masu abincin, da sauri Hussaina ta fara ci saida taji tayi dam sannan ta kora da lemu, toilet tanufa ta wanke bakinta tadawo kan kujerar datake tad'an kishingid'a cikin mintina biyar bacci yayi awon gaba da ita.




Hafiz Kuwa bayan shima ya kammala cin abincin tattara plate d'in yayi da cup's ya mayar kitchen sannan ya wuce bedroom yafad'a toilet yashe'ka wanka yana futowa ya shafa cream wasu tare da feshe jikinsa da turare, jikinsa sanye yake da vest da shortnicar falo yanufa har yanzu Hussaina na kwance inda yabarta kan kujera sai sharar baccinta takeyi,


Tsayawa yayi kanta saida yakaremata kallo, take wata matsananciyar Sha'awarta ta d'arsu a zuciyarsa ahankali yakai hannunsa jikinta yafara shafata yana mata irin salon dayasaba tayar mata da hankali.


Can cikin bacci taji ana ta6ata saurin bud'e ido tayi tare da saukesu kan Hafiz dake aikamata sakon wani shu'umin murmushi, ture hannunshi tayi daga jikinta "miye haka kake shirin aikatawa kasanfa da da yanzu ba d'aya bane, yanda nasaki jiki dakai a da nabaka duk abinda kakeso yanzu baze yuyuba.


Hafiz yad'an 6ata rai "Haba babyna sabodame zaki hanamin kanki?
"Saboda kwakwkwaran dalili, Hussaina tabashi amsa.
"Inaga babu wani dalili dazesa ki hanamin wannan lallausan jikin naki me tarin ni'ima, a da kika amince dani baranrantana kuma yanzu da kome zamuyi baza'a ganeba kawai ki amincemin mu shana, yafad'a tare da jawota jikinsa ya matseta gam.












*sai kunyi ha'kuri da typing saboda 'yar matsalar da wayana ya samu koda aka gyara sai naji duk ta canjamin typing d'inma baya sauri*










Love u all my fan's 💃🏻 shoki 👄🍭
[11:08AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*






*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻






Page......................31








®TALANTED WRITER'S GROUP (T.W.G) 📝






Saurin tureshi tayi daga jikinta tare da mi'kewa tsaye cikin 6acin rai take magana "haba Hafiz wannan wace irin rayuwace, kabar ganin nakawo kaina gareka hakan ba yana nufin zan mallaka maka duk abinda kake bu'kataba daga gareni, akwai dalilin dayasa na amince da zuwa gidanka harna baro gidan aurena, duk wannan maganganun Hussaina tanayinsune cikin tsananin fushi da matsananancin 6acin rai.


Ran hafiz ya 6aci da jin maganganun Hussaina yayi niyyar gayamata magana kamar yanda gayamar amma sai wata zuciyar tace "fushi ba naka bane kabita a hankali har kasamu ha'karka ta cimma ruwa.


Cikin sanyin jiki hafiz ya dur'kusa gabanta shikenan babyna na ha'kura amma kitaso muje mu kwanta yafad'a tare da kama hannunta.


Fizge hannunta tayi daga rikon dayayimata tare da komawa kan kujera ta zauna tace "kaje kawai ni anan zan kwanta, tashi hafiz yayi yanufi bedroom jikinsa a sanyaye a zuciyarsa ba haka yasoba yaso ace ya kwashi gara ta hanyar kusantar Hussaina dan dama ya dad'e rabon dayayi mu'amula da wata mace tunda suka samu sa6ani da zuby kusan sati batazo gidanshiba wanda ada yasaba baya kwana biyu basu had'u suka she'ke ayarsuba.


Da haka ya haye gadonsa zuciyarsa fall da tunani "to miye amfanin zuwan wannan yarinyar guna tunda bazanji dad'i da itaba, amma bari inbarta inga iya gudun ruwanta zuwa gobe kuwa idan ta'ki amincewa zan danneta kota 'karfi, dan nariga na kwad'aitu da ni'imar jikinta da wannan tunanin bacci 6arawo yayi awon gaba dashi, yayinda Hussaina batayi wani baccin kirkiba sakamakon wani mummunan mafarki datayi da Hassana Hakan yasa ta yanke hukuncin komawa gida gobe dan ganin halin da 'yar'uwarta take ciki.


** **

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login