Showing 9001 words to 12000 words out of 30185 words
"zanfad'a.... Zanfad'a wlh.
"Oya ina saurarenki d'ansandan yafad'a tare da tsareta da manyan idanunsa masu ban tsoro.
"Ni Yar gidan Alhj Mansir company ce.
"What? 'Dan sandan yafad'a tare da mi'kewa tsaye.
"Karya kike yafad'a tare da nunata da yatsa, duk fad'in garinnan waye besan Alhj Mansir kamfaniba, mutumin kirki me halayya ta kwarai ace ke yarsace kina wannan munanan halaye.
Kuma ba wannan ba iya saninmu Alh Mansir bayada wasu 'ya'ya sai yara biyu yan tagwaye.
"Yan la6ai wlh nice ai mune yan tagwayen Nice Hussainar dan Allah Ku taimakeni Ku maidani gidanmu.
"Sajen Habu, dan sandan yakwalama wani daga cikin yansandan kira.
Da sauri d'ansandan ya iso gabanshi ya 'kame tare da saramashi.
"Maza a fiddo mota yanzu zamuje gidan Alh Mansir kamfani "yes sir yafad'a saida ya'kara saramashi kafin yafita zuwa ma'ajiyar motocin.
Dare ya tsala misalin 'karfe biyu na dare motar yan'sandan tayi parking bakin get din gidansu Hussaina, nocking sukayi lokacin mal bala yana kwance cikin d'an karamin d'akinsa yafito da sandarsa a hannu yana tamabayar "waye? Hussainace tayi magana "nice mal bala, "kece wah? Ya tambaya.
"Nice Hussaina.
"Husssaina da wannan daren subhanallah bud'e 'kofar yayi ahankali yana le'kowa yayi ido hud'u da ita da 'yansanda biyu tare da ita.
Da Sauri Hussaina tashiga gidan 'yansandan suka take mata baya, a harabar gidan suka tsaya "kishiga kiyimana magana da mahaifin naki.
Bata ko sauraresuba tayi cikin gidan da gudu,
Lokacin Daddy,Momy da Hussaina suna Zaune a falo, Momy sai Addu'a take Allah maidomata da 'ya lafiya a Zuciyarta tana cewa "danasan haka zata kasance daban amince da fitartaba.
Hassana kuwa kuka kawai takeyi, yayinda dady Zuciyarsa tagama 'konewa jiyake inama yaga Hussaina yanzu Allah kad'ai yasan irin dukan dazeyimata.
Begama wannan tunaninba yaga anturo 'kofar falon, mikewa yayi da sauri dan ganin me shigo masu gida da wannan tsohon daren, ido Hudu sukayi da Hussaina saurin isa yayi Inda take a zuciye ya dun'kule hannu yakaimata wani mugun naushi sannan yasa 'kafa ya hard'ota.
Fad'uwa tayi 'kasa tana maida numfashi sama-sama ko kukanma yakasa zuwamata saboda tsananin azabar datake ciki.
Dukda haka Daddy beyi 'kasa a gwiwaba gurin ciro cherger wata fitila dake jikin soket yarin'ka tsulamata, sai lokacin tasamu damar fasa ihu tare da d'aukewar numfashinta ta sulale 'kasa sumammiya.
Ganin tafad'i yasa Momy 'karasowa gurin tana kuka "innalillahi Alhj miye haka kake shirin kasheta, kabari mana kaji ta bakinta, "Bazanbariba da bata fitaba da hakan be faruba, kuma ko mutuwa tayi bani nadamar kasheta saboda da inyi mugun gani 'kara narasata baki d'aya.
Hassana kuwa ganin 'yar'uwarta kwance ba Alamar rai tattare da ita yasata rud'ewa tafito zuwa harabar gidan dagudu tana kuka, ganinta yasa 'yansanda sukayi saurin tarbarta a tunaninsu Hussainace saida suka kula da kayan jikin wannan basubane jikin wacce suka kawo yanzu "ke lafiya suka shiga tambayarta, a gigice take nunamasu cikin gidan tana cewa "daddy yakasheta, ya kashemin 'yar'uwa.
"What suka fad'a tare da abkawa cikin gidan baki d'ayansu..
Love u all my Fan's ππ» shoki ππ»
[11:05AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: π *AUREN TAGWAYE* π
πΈπΈπΈπΈπΈ
πΈπΈπΈπΈ
πΈπΈπΈ
πΈπΈ
πΈ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member's group of* *Ciwon ya mace* π©π»
Page-------------------------14
A gigice Momy tabi Hassana da kallo tare da 'yan'sandan dake tare da ita.
"Hassana Kina Haukane, mahaifin naki kika kirama 'yan sandan.
Cikin muryar kuka Hassana tace "Wlh momy bani nakirasuba ina fita nagansu a harabar gidannan.
Kallonsu daddy yayi a gadarance yace "waya kawoku gidana, kuma da izinin wah kuka shigo har nan? Yafad'a yana nuna inda suke tsai-tsaye.
"Babban cikinsune yayi magana "Sunana inspeter Sabi'u wale, mune wad'anda suka kawo wannan yarinyar gidannan bayan mun tsinceta cikin halin maye, bayan ta dawo hayyacinta mukayimata 'yan tambayoyi shine tasanar damu kaine mahaifinta shine muka kawota, muna tsaye a haraba munajiran tayimana magana dakai shine mukaga wannna tafito tana fad'in a taimaketa ankashemata 'yar'uwa shine dalilin dayasa muka shigo domin gudanar da aikinmu kamar yanda doka ta tanada.
"Owj naji duka bayaninku nagode, inaso kutafi kawai ni zan iya solving kowace matsala tagidana batare da wani yasamin hannuba nagode da taimakon dakukayima 'yata.
"Muma mungode Alhj Amma dan Allah ari'ka kai zuciya nesa, saboda gudun danasani....
Sai a hanzarta a kaita asibiti suka fad'a suna kallon Hussaina dake kwance bako motsi.
Bayan fitar 'yansandan momy ta kalle daddy Wanda yaketa mazurai da Alama har 'yanzu zuciyarsa bata gama hucewaba,
Hussaina kuwa har 'yanzu tana kwance batasan inda kanta yakeba, momyce tamatso inda take ta tallabo kanta ganin ba alamar rai tattare da ita yasata fashewa da kuka, "Dan Allah Ahj mukaita asibiti kada tamutu.....
"Tamutun mana, yafad'a cikin d'aga murya.
Sannan yayi 'kasa da muryarshi yana cewa "ba inda zan kaita na kwammace inrasata baki d'aya da mugun halin datake Neman jefa kanta.
Tajamani abin fad'i a gari, yana gama fad'in haka yashige d'akinshi ya maido 'kofa yarufe.
Cikin kuka Momy ta kalli Hassana tace kawomani ruwa.
Da sauri Hassana ta d'ebo ruwa cikin cup takawo, amsa Momy tayi tashiga kwarama Hussaina a jiki amma ko motsi batayiba saida ta zubamata a fuska sannan tayi firgigi ta tashi ta 'kan'kame Momy tana fad'in dan Allah kibashi ha'kuri wlh bazan 'karaba.
"Ke Hussaina kitsaya mana, ki nutsu nace ba daddynku bane nice Momy
'Kara 'kan'kameta tayi tana fad'in "wayyo Momy wlh bazan 'karaba kigayamashi na tuba.
"Cikin tsawa Momy tace "dallah ni sakeni tare da tureta daga jikinta, kinsan kina tsoro kikaje yawon har kika kai wannan lokacin baki dawoba, itama tana gama fad'in haka tayi tafiyarta d'akinta tabar Hussaina nan tana kuka itada Hassana.
Hassanace tamatso kusada ita takama Hannunta ta mi'kar da ita tsaye suka nufi d'akinsu.
Koda suka shiga d"akin zaune sukayi jugum-jugum suduka suna sharar kwallah.
Ita Hassana tana kukan halinda 'yansandan nan suka fad'i sunkama Hussaina na maye.
Itakuma Hussaina tana kukan yaudara da Hafiz yayimata har yayi nasarar rabata da budurcinta.
Wasu sabbin hawaye suka zubo a kuncinta.
Hassana ta kalleta tare dasa hannunta ta sharemata hawaye
"Dan Allah 'yar'uwata naro'keki ki gayamin gaskiyar inda kikaje har kikakai wannan lokacin baki dawo gidaba, kuma da gaskene abinda 'yansandan nan suka fad'i na kamaki dasukayi cikin halin maye?
Tana gama fad'in haka ta tsareta da idanu tana jiran jin amsar dazatabata "Hmm ko d'aya Hassana wlh bansha komeba, kuma ni ba inda naje nasan dai naje asibiti kamar yanda na tambayi momy zanje kuma ta amincemin, ana gaf da magariba nabaro asibitin ina tsaye inajiran abin hawa wani me mota yatsaya gabana yaro'keni da inshiga yaragemin hanya nikuma ganin ina sauri yasa na Amince nashiga motar to shinefa daganan ban 'kara sanin abinda yafaruba saida na tsinci kaina yashe a titi, wannan shine gaskiyar abinda yafaru.
Hassana najin haka ta 'kara fashewa da kuka tare da rungume 'yar'uwarta tana fad'in "sister Allah yasa da rabon sauran shan ruwanki a duniya, ya Allah na godema daka kwatomin 'yar'uwata daga hannun muyagun mutane.
Hussaina kuwa dad'i taji har cikin ranta dan ganin Hassana ta yarda da 'karyar data tsaramata, a zuciyartama cewa tayi aiko gobe idan daddy da Momy sun tuhumeni abinda zan fad'amasu kenan, da haka suka kwanta bacci yayi awon gaba dasu kowace da tunani barkatai a zuciyarta.
*Washe Gari.*
Koda suka tashi bayan sunyi duk abinda yadace na gyaran gida, komawa sukayi d'aki sukayi wanka wasu dogayen riguna suka sanya masu kyan gaske tare da 'yan 'kananan hijab.
Lokacin Momy tagama had'a break fast zuna zaune kan dining tana zubama daddy kasancewar tara hartayi yana sauri yafita office saboda yanada ayyuka da dama a can.
Jerawa sukayi gwanin ban sha'awa suka nufi inda iyayen nasu suke sannan suka zazzuna bayan sun gaishe da iyayen nasu.
Hussaina sai sunne kai takeyi alamar rashin gaskiya.
Bayan sunkammala breakfast ne daddy ya kalli Hussaina tare da d'dd'aure fuska kamar beta6a dariyaba yace "inaso kigayamin gidan ubanwa kikaje jiya.
"Uh...im asibiti naje ganin mamar 'kawata.
"Da izinin wah kika fita?
Kallon Momy tayi suna had'a ido Momy ta watsamata wata muguwar harara, ba shiri ta saddar da kanta 'kasa, tayi shiru.
Dadyne yacigaba da magana "koma waye ya d'aure maki gindi a gidannan kike Neman lalacewa tonidai ba agabana ba, kuma yau basai gobeba zan d'auki mataki kanki dan bazan zauna ina kallonki kijamin surutu a gariba, yana gama fad'in haka ya d'auki jakarsa yafice daga gidan ranshi a matu'kar 6ace.
Love u all my Fan's ππ» shoki ππ»
[11:05AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: π *AUREN TAGWAYE* π
πΈπΈπΈπΈπΈ
πΈπΈπΈπΈ
πΈπΈπΈ
πΈπΈ
πΈ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* π©π»
Page......................15
Daddy ne Zaune office d'insa yahad'a hannu bibbiyu ya buga tagumi ba abinda yake tunani sai irin rayuwar da Hussaina take neman jefa kanta,
Mi'kewa yayi tsaye ya maida hannuwansa duka biyu baya tare da fara zagaya office d'in yafara zancen zuci "yanzu wane mataki yakamata in d'auka dan ganin nayima tufakar hanci bata war-wareba, yau kimanin shekara ishirin ina tarbiyantar da yarannan amma lokaci d'aya suna nema su bijiremin, komawa yayi kan kujera ya zauna tare da maida kanshi sama ba abinda yake tunani sai abinda 'yan sandan dasuka kawo Hussaina gida suka fad'i na cewa sun kamata cikin Halin maye, wato rayuwar dazata jefa kanta kenan, wadda daga haka mutum ze iya aikata kome hatta da kisan kai mashayi na iya aikatawa batare da shakka ko shayin irin hukuncin daze biyo bayaba.
"Assalamu Alikum, da sallama jabeer yashigo office d'in hannunsa d'auke da wasu files-files, jin shiru ba'a amsa sallamar ba yasa ya'kara yin wani sallamar karo na biyu, nanma shiru daddy be amsaba dan yayi nisa cikin tunanin dayake, guri jabeer yasamu ya zauna tare da ajiye files-files d'in kan tebur d'indake gabanshi da d'an 'karfi yanda daddy zeji karar ajiyewar. Hakan kuwa ya maidoshi daga dogon tunanin dayake ya d'ago da kanshi ya kalli jabeer "Ah jabeer badai har kagamaba, "eh nagama gashinan saura wad'annan files d'inne sunada 'yar matsala akwai takardun da babu aciki, yafad'a yana ware wasu files guda biyu gefe.
"Owk to ba Matsala idan na duba zanyima magana sai a gyara, "to kawai yafad'a tare da mi'kewa ze fita daga office d'in harya kai bakin 'kofa daddy yayi kiransa "jabeer, cikin girmamawa jabeer ya amsa tare da dawowa ya zauna,
Saida daddy yayi shiru na kimanin minti biyu kafin ya sauke ajiyar zuciya "Jabeer dama inason magana dakai "to Alhj Allah sa dai lafiya,
"Eh to lafiya lao, kan maganar Aurenka da Hussaina kanasonta kuwa har yanzu?
Cike da jin kunyar tambayar da daddy yayimasa ya amsa da "eh.
"To bakada matsala inaso da anjima bayan sallar azahar kataho da magabatanka da shedu koda basu wuce mutum gomaba, nima zan sananar da 'yan'uwana za'a d'aura aurenku kaida ita, bani bukatar kome naka sadaki kawai zaka taho dashi naira dubu hamsin,
Kada kayi mamaki kan wannan abin dana aiwatar akwai dalilin yin hakan Wanda nasan koda kaji dalilin na tabbata bazaka'ki jininaba,
Jabeer dai shiru yayi yana sauraron Alhj cike da mamaki a zuciyarshi yana cewa "wannan shine ikon Allah me tsaida wando koba zariya, kome wannnagaggawar take nufi Allahu wa'alamu.
Haka ya kauda kowane tunani cikin zuciayrshi yayima daddy godiya sannan yakoma office d'inshi.
Koda ya koma tunanin dai yahanashi sukuni saboda haka rufe nashi office d'in yayi Yakama hanyar gida.
*Waye Jabeer*
Jabeer Suleman shine asalin sunanshi Haifaffen garin katsina, Alh sule tankuri shine mahaifinsa sai mahaifiyarsa Hajiya sa'ada sunada rufin asiri Bakin gwargwado amma ba'a kiransu masu arziki, su biyu iyayensu suka haifa dagashi sai 'kanwarsa Nusaiba wacce akwai tazara sosai tsakaninsu dan ahalin yanzu nusaiba bata wuce shekara sha shidda zuwa sha bakwaiba yayinda jabeer yakeda talatin da d'aya.
Tun yana d'an shekara sha bakwai mahaifinsu yarasu lokacin mahaifiyarsu na d'auke da 'karamin cikin nusaiba bayan rasuwar mahaifinsu da wata bakwai ta haifi nusaiba, haka sukacigaba da rayuwa yau da dad'i gobe babu, yayinda mahaifiyarsu ta tsaya tsayin daka dan ganin jabeer yayi karatu, da kyar da sud'in goshi sukasamu ya kammala karatunshi a F.C.Ekatsina kasancewarshi hazi'ki yasa yasamu sakamako me kyau amma dukda haka samun aiki yayi wahala kusan shekara biyu yana neman aiki besamuba, kwatsam rannan yaji ana Neman ma'aikata a Company Alhj mansir badan yasa ran zesamuba yaje yayi interview cikin ikon Allah kuwa saiga sunanshi cikin wad'anda aka d'auka aiki, sunyi matu'kar farinciki shida mahaifiyarshi da 'kanwarshi, ranar dazefara zuwa aiki mahaifiyarshi tayimashi nasiha me ratsa jiki akan ri'kon amana da gaskiya, sannan tabishi da addu'ar samun s'a.
Bayan wata shidda dafara aikinsa Alhj mansir yalura da Halin gaskiya da ri'kon amana na jabeer hakan yasa yajawoshi jiki tare da 'karamashi matsayi a office d'in Wanda a halin yanzu shine mataimakin manager company.
*Masu yimin magana ta prvt najina dasukayi shiru kwana biyu Dan Allah kuyi hakuri na rashin ganin reply d'ina naga sa'konku saidai be karantuwa kasancewar nasake download whatapp ne nagode da kulawarku.*
Love u all my Fan's ππ» shoki ππ»ββ
[11:06AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: π *AUREN TAGWAYE* π
πΈπΈπΈπΈπΈ
πΈπΈπΈπΈ
πΈπΈπΈ
πΈπΈ
πΈ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* π©π»
Page......................16
Saboda haka cike da tunani barkatai jabeer ya isa gidansu, 'kanwarsa Nusaiba yafara gani zaune falo tana kallon wani Indian film me suna salam namaste, da sauri ta tarbeshi tanamashi sannu da zuwa, bayan ya amsa d'akinsa yanufa ya ajiye jakarsa sannan ya dawo falon, har yanzu dai nusaibar ce ita kadai a falo tambayarta yayi "ina mama?
"Tana bedroom,
"Owk kawai yafad'a tare da nufar 'kofar dazata sadashi da d'akin kwanan mahaifiyar tashi, da sallama yashiga d'akin zaune ya isketa gefen gado hannunta ri'ke da waya da Alama waya tagama, kallonshi tayi bayan yasamu guri ya zauna kan bedsite "a'a jabeer yanaganka kadawo tun yanzu ko mantuwa kayine?
"A'a mama ba mantuwa nayiba wani babban Al'amari ya maidoni Wanda ni kaina ya d'auremin kai,
"Wannan wane Al'amarine tafad'a tare da maida duka hankalinta gareshi,
"Watako yanzu danaje office shine Alhj yakirani yake cemin inje insanarda magabatana kuma inbada kud'in sadaki naira dubu hamsin yau ze d'aura aurenmu da Hussaina.
"Alhamdulillahi mama tafad'a tare da d'aga hannuwanta sama tana godema Allah, kai Amma naji dad'i wannan abu ai abun farincikine dama kullum Addu'ata be wuce inga aurenkaba, Allah sanya Alkhairi yabaku zaman lafiya.
"To amma mama kina ganin babu wata matsala, "wace matsala haba jabeer me kanema karasa inaji kadade da kammala gidanka, kuma Hallacin da Alhj mansir kamfani yayimana ai kobakada kome yace ka auri d'iyarsa ka aureta kazubama sarautar Allah ido dan nasan baze barka hakaba,
"To mama Allah dai yasa haka shine mafi alkahiri,
"Ameen haka nikeso naji kana fad'i.
Daga nan yafita zuwa d'akinshi ya canja kaya sannan yakoma yayima mamarsa sallama tare da sanar da ita zeje ya d'auko mutum ukku dangin babanshi sannan mutum ukku a dangingin ita mamar tashi, fatan Alkhairi tayimashi sannan yafita.
β±. *Misalin 'karfe 3:00pm*
Aka taru a masaalacin dake 'kofar gidan Alhj mansir mutane 'kalilan suka sheda d'aurin auren Jabeer Suleiman tankuri da Amaryarsa Hussaina Mansir kamfani, bisa sadaki dubu hamsin.
Bayan ankammala Alhj mansir yasa aka gabatarma duk mutanen dasuka halarci d'aurin auren abun lasawa take away akayima akaiyma kowane suka wuce suna sanya Albarka.
Bayan ankammala wannan daddy yashiga gida da sallama, su duka falo ya taraddasu zaune Momy ce ta amsa sallamar, Hassana tace "daddy sanu da dawowa "yauwa ya amsa,
Hussaina kuwa daddy nashigowa jikinta yafara kyarma dan wani masifaffen tsoronshi takeyi, cikin muryar tsoro tace "d...dad...daddy sannu da zuwa.
Wani matsiaycin kallo ya watsamata sannan yawuce d'akinsa batare daya amsa sannu d'inda tayimashiba.
Can bayan kimanin minti baiyar yafito ya kalli Hussaina "ki shirya yanzu inaso zan fita dake kuma minti talatin nabaki, kinajina "inaji daddy tafad'a tare da mi'kewa tanufi d'akinsu jiki na kyarma.
Daddy kuwa fita yayi harabar gidan, waya yakira jabeer "ya masu aikinnan sun kammala kuwa,? Ya tambaya
cikin ladabi jabeer yake magana "Eh Alh sunyi kusan minti sha biyar ma da gamawa.
"Sun had'a kome dai yanda yakamata ko?
"Eh sun had'a kome 2 bedroom ne da falo 2 sai kitchen ba abinda ba'a zubaba na bu'kata.
"Owk to anjima ka shiryar tarbar Amaryarka,
Kasa magana jabeer yayi saboda kunyar Alhj yakeji sosai.
"Basu dad'e da kammala wayaba wata had'addiyar mota tayi parking 'kofar gidan sannan wasu maza suka ri'ka jido akwatina suna shigowa dasu saida suka shiga da guda goma manya- manya, sannan sukayima jabeer bayani Alhj mansir yace akawo kayan amaryane.
Mamakine yahana jabeer magana danshi harga Allah yayi niyyar had'a wannan kayan Amma Alhj yahashi had'a kome.
Love u all my Fan's ππ» shoki ππ»ββ
[11:06AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: π *AUREN TAGWAYE* π
πΈπΈπΈπΈπΈ
πΈπΈπΈπΈ