Showing 18001 words to 21000 words out of 30185 words

Chapter 7 - AUREN TAGWAYE COMPLETE DOCUMENT Book .txt

Unknown   

29 Nov 2024

1270

na sawwa'kema na huta, wannan wane irin nacine kamar ni kad'aice mace a duniya kasakeni ka auro wata mana.


Wani gajeren murmushi jabeer yayi mai cike da takaici, "Hussaina bazan sakekiba, kuma badan ina son kyautata makiba kuma badan bazan iya rabuwar dakeba, bako d'aya kawai bazan iya sakinkiba dan saboda darajar mahaifinki, amma kisani duk abubuwan dakikemin watarana sai kinyi nadama....


Dariya tayi "Hmm nadama badai inyi nadamar rabuwa dakaiba sai dai inyi farinciki, saboda ko yanzu karabu dani inada masoyin daze aureni yari'keni da daraja da 'kima fiye da ri'kon da kakemin...
Saukar wani lagfyayyen mari taji a kumatunta shine yahanata cigaba da magana tare da dafe kuncinta wanda yakemata tsananin rad'ad'i.
"Ka mareni... Wlh bazan yardaba, kuma wlh sai kayi nadamar wannan marin dakayimin azzalumi kawai.
Ganin yayo kanta yasa ta ruga da gudu tashige bedroom tare dasa key ta jingena da 'kofar tana maida numfashi.
Cike da takaici da ba'kinciki jabeer yabar gidan,


** ** **


Hassanace zaune tare da Momy da Daddy bayan sungama cin abincin rana, daddy yatashi ze fita kenan Momy tayi magana "Alhj takira sunanshi, dakatawa yayi ya zuba mata idanu yana jiran jin abinda zatace, "nace wai yaushe Hassana zataje tagano gidan 'yar'uwarta yakamata ace kabarta taje yau kimanin sati biyu kenan dayin aurennan amma kahanani kahana yar'uwarta zuwa wannan wane irin abune, ta'karashe maganar cikin ladabi.


"Ba yanzuba, yafad'a tare da d'aure fuska, tun yaushe nake gayamaku lokacin zuwa gidan waccan yarinayar beyiba, idan lokaci yayi da kaina zan umarci da aje, daga yau kada wanda ya'kara tunkarata da wannan maganar idanba so kuke ranku ya6aceba, yana gama fad'a yasa kai yafice.


Yana fita Hassana tafashe da kuka tare da fad'awa jikin Momy "yanzu Momy me hakan ke nufi, daddy yana nufin yarabani da 'yar'uwatane ko miye.


Kiyi ha'kuri hassana ba hakan yana nufin anrabaki da ita bane akwai dalilin dayasa Daddynku yahana muje amma ki 'kara ha'kuri inshaAllah bada dad'ewaba ze barki kije, haka Momy tayita rarrashin Hassana tana kwantar mata da Hankali.


** ** **


Da misalin 'karfe Hud'u na yamma Hussainace Zaune tanacin abinci jalouf d'in taliya tadafa da busashshen kifi, gefe kuma ga lemu tanaci tana korawa tana gamawa nan tabar sauran abincin tare da cup d'in datasha lemun, ringing d'in wayarta taji dake ma'kale jikin soket tana charge da sauri tatashi dan ta d'auko wayar tayi kwallo da kwalin lemun data rage Wanda ko rufeshi batayiba, nan yafad'i ya zube kan carpet amma bata damuba saurin Isa tayi ta d'auko wayar ganin sunan Hafiz yasa tayi saurin danna OK tare da karawa a kunne.
"Hellow dear
"Haba babyna wannan wace irin rayuwace, Hafiz yafad'a cikin zafi-zafi.
Ace kullum muna tare a waya sai inkiraki yakai sau biyar arana amma kwata-kwata kin'ki kiyi dubarar dazamu had'u, gaskiya nalura kinfara son wannan mijin naki nike haukan banza, idan hakane kawai kifad'amin ni inha'kura.
Yayi 'kasa da murya kamar me shirin yin kuka "Amma idan kikamin haka kin yaudareni, tsakanina dake sai.... Be 'karasa maganarsaba ta tsinke wayar sakamakon jin Alamar shigowar mutum datayi,


Nan jikinta yafara kyarma dan ance marar gaskiya ko cikin ruwa yayi ji6i,


Sanye take cikin wani matsiyacin wando pencil, tare da wata d'amammiyar riga wacce ta sakko har gwiwa, kanta tayi rolling da wani shararan gyale Wanda behana ka hango gashin attach d'inda ke kanta, ga wasu muggan takalmi masu tsini dake 'kafarta. *Zuby kenan 'yar duniya Haya'kin taba*




Tsayawa tayi bakin 'kofar shigowa falon tana 'kara 'karema falon kallo, wani shu'umin murmushi tayi a zuciyarta tace "Allah kai damo ga harawa kobeciba yayi birgima, ma'ana idan nayi 'ko'karin raba jabeer da Hussaina koda be aureniba zanja ra'ayinshi ko zaman bariki muyi nikuma lokacin zan samu damar kwashe duk wani Abu daya mallaka in'kara gaba.














Love u all my Fan's πŸ‘―. Oya sagem πŸ‘―β€β™‚πŸŠπŸ»β€β™€
[11:07AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*






*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»






Page......................25


*Wannan shafin nakune masoyan wannan littafi*
*My Bestyn Nana, da kuma Ilham*
_nagode da kulawarku Allah bar zumunci_








"Welcome 'kawata ashe kece, Hussaina ta fafd'a tare da kamo hannunta ta Zaunar da ita kan kujera, Zuby tayi murmushi tace "wlh kuwa hanya ta biyo dani nace bara na le'ko mu gaisa,
"amma kin kyauta kuma naji dad'in zuwanki domin dama ina Neman shawararki dan kobakizoba dama zan kiraki a waya.


To ai gani nazo 'kawata miye matsalarki?
Shiru Hussaina tayi kafin ta numfasa, "Zuby kinsan dai irin son danikema Hafiz kuma nagayamaki muna waya dashi, to halin da'ake yanzu kullum idan mukayi waya sai yanunamin tsananin 6acin ransa akan na'ki yarda muhad'u, nikuma a gaskiya ina tsoron Daddy, kuma nasan jabeer baze barniba, kuma kinga nan gidan mijinane bekamata inkawoshi nan ba.


Murmushi zuby tayi a zuciyarta tace "Anzo wurin, da wannan damar zanyi amafani inraba Hussaina da jabeer,
"haba 'kawata wannan aiba matsala bace zuby tafad'a tana kallon Hussaina.
"Husaaina tace kamar ya ba matsalaba kinsan fa akwai igiyar auren wani akaina kuma nike tarayya da wani namiji ina 'ko'karin had'uwa dashi kuma kice ba matsala bace.


Matsowa zuby tayi gab da Hussaina tare da kanga bakinta dai-dai kunnenta ta rad'amata wani magana. _(wanda koni zee bansan me tafad'a mataba)_


Suduka suka kyal-kyale da dariya tare da tafawa, Hussaina tace "Kai amma wannan shawarar tayi 'kawata shiyasa koda yaushe nake alfahari dake, kinga idan nayi haka zanje gurin masoyina inyi ko kwana nawa nakeso batare da wata matsala ba.


Nan take ta d'auko wayarta takira Hafiz bugu d'aya yad'aga tun kafin yayi magana tarigashi "hellow my dear ka shirya tarbar babbar ba'kuwa gobe-gobe.
"Kai haba da gaske? Hafiz ya tambaya cike da farin ciki.
"Da gaske mana kuma idan nazo kwana biyu zanyima.
"Wow babyna amma naji dad'i kice intashi inyima gidana general cleaning saboda zuwanki,
Nan suka gama wayar zuby kuwa sai kallonta take tana wani shu'umin murmushi.
Kafin ta mi'ke "to 'kawata nizan wuce kome kenan zamuyi waya, "to shikenan sai munyi wayar ko, har kusan get Hussaina tayima zuby rakiya, sannan tadawo.


Hussaina na dawowa ta d'auki wayarta takira Hassana
"Hellow sister kina lafiya?
"Lafiya lao Husaina tafad'a, wai dan Allah sister yaushe zakizo gidana shikenan ace tunda aka kawoni keda Momy ba Wanda yazo.
"Hmm kedai bari sister wlh ko ranar nan saida mukayi maganar zuwana gidanki nida Momy wallahi bakiga fad'an da yayiba wai lokacin zuwa beyiba, idan lokacin yayi ze gayamin da kanshi.
"Hmm sister kema bakiyi niyyar zuwaba, kodayake nasanki da tsoro kamar farar kura, amma in bacin haka me zai hana idan kinfito islamiyya kitaho alabashi idan lokacin tashi yayi saiki koma.


"A'a sister nikam gaskiya bazan iyaba, kinsan halin dady muddin nayi haka yagane kinsan bazemin da sau'kiba,
"To shikenan sis yanzu nagane baki 'kaunata, amma danice ai duk yanda zanyi inzo gurinki zanyi tafad'a tare da fashewa da kuka.....
Hasaana Har cikin ranta taji tausayin 'yar'uwarta yakamata, "shikenan kibari zanyima Momy maganar idan ta amince inanan tafe goben,
"To shikenan nasan ma Momy bazata'ki amincewaba, Allah kaimu goben ina jiranki.


Suna gama wayar jabeer nashigowa, tana ganin shigowarsa tayimashi wani mugun kallo up and down tare da buga wani uban tsaki "mtswww badai Zuciya, tafad'a tare da shigewa bedroom, kallo jabeer ya "karema falon yanda yayi kace-kace can plate nan cup nan robar ruwa, can ledar biscuit can kwalin lemu, ga kuma inda lemu ya zube ba'ayi mopping ba, girgiza kai kawai yayi sannan yanufi d'aki sai gashi yadawo sanye da best da wando threequter, plate da cups yafara kaudawa yakai kitchen sannan yad'auko mopper ya goge lemun daya zube, cikin 'kan'kanin lokaci yagyara falon fess, sannan yashiga kitchen yadafama kansihi indomie dan yadawo da yunwa, cikin minti goma ya gama ya zauna falo yaci.












Love u all my Fan's πŸ‘― oya sagem πŸ‘―β€β™‚πŸ’ƒπŸ»
[11:07AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*






*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»






Page......................26






*gaisuwa gareku masoyan wannan littafi*
*Mmn Ummi*
*mummy Ramadan*
*Mmn Zee*
*Mom Afreem*
*Allah rayamaku yaranku yayima rayuwarsu Albarka, Nagode Allah bar Zumunci*






Washe gari tunda 'karfe biyu na rana Hussaina ke faman bugama Hassana waya dan ta tabbatar da zatazo d'in kokuwa bazatazoba,


Hassana na zaune kan kujera tana gyaran farce ta kalli Momy "Hmm kinga Hussaina ta isheni da waya A'kalla yau takirani yakai sau goma, wai dan Allah inzo gidanta kuma na gayamata daddy yahana yace lokaci beyiba amma ta nace da magiya, wai dan Allah in taimaka idan nafito islamiyya inje idan antaso sai indawo ai bazesan najeba shine nikuma nace gaskiya inajin tsoro amma bari in tambayeki idan kin amince sai inje.


Murmushi momy tayi "ba kome kije mana, amma kibari yanzu daddynku ze dawo, idan yadawo yaci abinci yafita, kekuma saiki shirya gurin 'karfe ukku saiki tafi, amma ki tabbatar da lokacin tashinku islamiyya yayi kidawo gida, "inshaAllah Momy aini kinsan banida matsala yanda nake tsoron Daddy inwuce mana ya 6allani cikin gidannan, murmushi Momy tayi "ah to nidai nagayamaki wlh.


Dai-dai lokacin kuwa daddy ya dawo Momy da Hassana sukayimashi sannu da zuwa, Momy ta kar6i jakar hannunshi suka wuce d'akinsa, bayan wani d'an lokqci suka fito tare daddy ya canja kaya da Alama wanka yayi, zama sukayi kan dining Hassana tayi serve d'insu bayan sun kammala cin abinci suka d'an ta6a fira, cikin firar tasune daddy ya kalli Hassana "watako kedai kin'ki fiddo miji kiyi aure ga 'yar'uwarki takusa wata d'aya a gidanta,


Momy ce tace "Alhj to a ina zata samu mijin kullum tana 'kunshe a cikin gida, bata fita ko nan da can, yaushe wani ze ganta yace yanaso, indai ba itama irin na 'yar'uwarta zakamata ba.


"No no Hassana bazan ta6a yimata abinda nayima Hussainaba, saboda nutsuwarsuma ba d'ayaba,
"To Allah dai yaza6a mata miji nagari, Momy tafad'a daddy ya amsa da "Ameen ya rabbi.
Sannan ya kalli Hassana "ki shirya yanzu idan zan fita in saukeki kigano 'yar'uwarki.


Wani irin tsalle tadaka cikin Farin ciki tanufi d'akinsu domin ta shirya.


A gaggauce tafad'a toilet ta she'ka wanka tana fitowa tashafa ainafin cream d'inta coa-coa butter sannan ta murza farar powder, man le6e kawai tashafa sannan tanufi wadrope ta d'au'ko wasu kaya riga da zani d'inkin simple ta Sanya, dan tasan daddynsu baya 'kaunar 6ingilallun kaya da matsatsen siket koda ta sanya zesa taciresu.
Wani madai-daicin hijab ta saka sannan tafito nan sukayima Momy sallama suka wuce, momy har cikin ranta taji dad'in zuwan Hassana gidan Hussaina da Amincewar Alhjn, dan ita dama tun abinda Hussaina tayi take tsoron bada izinin zuwa wani guri batare da saninsaba, duk da tasan Halin Hassana yasha ban-ban dana Hussaina.


Dai-dai 'kofar gidan jabeer daddy ya sauke Hassana sannan ya ciro dubu d'aya yabata "ga wannan kihau napep 'karfe shidda tayimaki gida, "to daddy nagode Allah kiyaye hanya,
Nocking d'in gidan tayi me gadi yataso yana tambayar waye tare da le'kowa ganin Hassana yasa yayi saurin bud'ewa tare da dur'kusawa ya gaisheta "Hajiya sannu da dawowa, wallahi banma kula da lokacin da kika fitaba, murmushi Hassana tayi dan tagane inda maganganun me gadin suka dosa a tunaninsa Hussainace, "Ba me gidan bace 'kanwartace tafad'a tana 'kara fad'ad'a fara'arta.
"To ikon Allah Amma kamarku tayi yawa gashi girmanku d'aya ba wanda ze iya ban-banceku, Allah me iko.....yafad'a yana ri'ke da baki.


Nan Hassana tawuceshi tabarshi cike da mamaki, yana wasi-wasi "Anya ba me gidan bace tafita, wata kila bataso asan tafita shiyasa tace ba itabace, amma in bacin haka ai kamar tayi yawa kome iri d'aya hatta da maganarsu ba ban-banci.
Wannan ai saiku rikita me gidan yakasa gane wacece tashi acikinku.
πŸ˜‚




Zaune Hussaina take kan d'aya daga kujerun falon hannunta ri'ke da remote tana kallon wata wa'kar turanci a tashar music plus, wasu had'ad'un Riga da wando na Pakistan ne jikinta tasa gyalen kayan tayi rolling, ga 'kamshin wani had'adden turare dake tashi jikinta, kafarta sanye da takalmi plate me masifar kyau, gefe kuma 'yar'karamar jakartace wacce tazuba kayanta kala biyu a ciki, jiran zuwan Hassana kawai takeyi tatafi gurin Rabin ranta Hafiz dan tun d'azu yake kiranta a waya gani yake kamar bazatazoba.


Agogon wayarta ta duba 'karfe bud'u dai-dai gashi har yanzu Hassna batazoba wani guntun tsaki taja tare da lalubo sunanta ta danna kira sai jiyo ringing d'in wayar tayi a dai-dai kofar shigowa da sauri takai dubanta gurin ido hud'u sukayi da Hassana batasan lokacin data buga wani irin tsalleba cike da farin ciki ta makaleta "oyoyo my sister.






*Tofah Readers me Hussaina ke shirin aikatawane, Me take nufi da son zuwan Hassana gidanta, wace shawarace Zuby tabata duk kubiyo Zee Elkaseem (Mmn khady) yar mutan KATAINAWA domin samun cikakkiyar amsa a cikin littafin AUREN TAGWAYE*










Love u all my Fan's πŸ’ƒπŸ» shoki πŸ’ƒπŸ» πŸŠπŸ»β€β™€πŸ‘ŒπŸ»
[11:08AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: πŸ‘­ *AUREN TAGWAYE* πŸ‘­
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•Έ
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*






*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* πŸ‘©πŸ»






Page......................27






Cike da farinciki suduka suka fad'a kan kujera, Hussaina ta kalli Hassana wlh sister na d'auka bazakizoba harna fara cire rai,


"Injiwaye inanan tafe ai,
"amma naji dad'in zuwanki wlh, dariya Hassana tayi "lallai sister aurennan ya kar6eki kinga kuwa yanda kikayi kyau kikayi wani fresh, kamar kinje wata 'kasar Honey moon, dariya Hussaina tayi tare da kaimata duka cikin wasa "kai sister bakida dama, nidai yanzu bari nafara kawomaki lemu kisha idan kuma kina bu'katar abinci ga kitchen nan zaki iya shiga ki girka dan kema gidankine, bata jira jin abinda zata fad'ba tanufi kitchen tabud'e fridge domin d'aukoma sister dinta lemun.


Bayan shigarta kitchen kuma idon Hassana ya sauka kan jakar dake gefen Hussaina ajiye, hannu tasa ta d'auko jakar tare da zuge zip d'in ganin kayan sawa cikin jakar dakuma yan abubuwan bukata yabata mamaki, bata kai ga rufe jakar ba Hussaina ta dawo d'akin d'auke da lemu da cup d'in glass a hannunta ta ajiye gaban Hassana.


Kallonta Hassana tayi sannan ta tambayeta "sister wannan kayanfa na waye? Matsowa Hussaina tayi ta kar6i jakar ta rufe ta ajiye gefe sannan ta zubo lemun a cup ta mi'kamata "kar6i sister kisha zanyimaki bayanin kona miye....


Ba musu Hassana ta kar6i lemun ta shanye sannan ta kalli Hussaina "uhum ina jinki.


Cikin muryar Neman Alfarma Hussaina tafara magana "dan Allah sis wani taimako nakeso kiyimin wanda duk duniya nasan ba wanda zeyiminshi sai ke.
Cike da mamaki Hassana ke kallonta "ina sauraronki sister wane taimakone wannan?

Matsowa Hussaina ta'karayi kusa da ita "ba wani abu bane me wuya inaso ki zauna a gidannan a matsayina.....


"What? Hassana tafad'a tare da mi'kewa tsaye "me kike cewa sister ban fahimci inda zancenki ya dosaba, kama hannunta Hussaina tayi tare da maidata kan kujera ta zaunar da ita "plz sister ki saurareni mana nasan zaki fahimci inda zancena ya dosa.
"Ina jinki Hassana tafad'a tare da bin yar'uwar tata da kallo.


Hussaina tacigaba da magana "kamar yanda nafad'a inaso ki zauna a gidannan a matsayin nice, ba dad'ewa zakiyiba kwana biyu kawai zakiyi, kuma ni zaki taimaka.


"Kamar ya in taimakeki wannan abinda baze ta6a yiyuwa bane yaushe za'ace wani yayima wani zaman aure, aurefa ba abin wasa bane.


"Hmm sister dan Allah ki taimakamin inshaAllah ba abinda ze faru kuma ba Wanda ze gane, sanin kankine babu Wanda ke bam-banceni dake, ko Momy da daddy suna ban-bancemune ta gurin halayyarmu amma bata kamaninmuba.


"Dakata sister duk ba wannan ba, shin idan na zauna gidannan amatsayinki kekuma ina zaki?
"Yauwa sister tambayar dayakamata kiyimin kenan.
"Wata 'kawatace zatayi aure shine ta gayyaceni to na tambayi jabeer ya Hanani kuma yace idan nasake tunkararsa da maganar ze gayama daddy, to nikuma yanda nike da 'kawar tawa yawuce ace ta gayyaceni bikinta banjeba,


"To shine kuma baki iya zuwa rana d'aya ki dawo?
"Baze yiwu inje rana d'ayaba saboda ba nan garin bane.
"Wane garine? Hasana ta tambaya.
"Yar Kaduna ce, kuma kinsan nisan katsina zuwa Kaduna, kuma daga can Abuja zamu kai amarya kinga dole inkwana biyu.


Tana kaiwa nan a zancenta wayarta tashiga ringing tana dubawa taga sunan Hafiz gabanta yayi mummunan fad'uwa da kamar bazata d'agaba ganin Hassana ta tsareta da ido yasa ta d'aga "Heelow dan Allah kiyi Ha'kuri bani nacemiki zanzoba to yanzu haka wayar damuke ina hanya. Bata jira me Hafiz ze fad'aba ta tsinke wayar.
"Kinganiko sister wallahi tund'azu takemin waya, Amaryar cefa.


Hassana cikin sanyin jiki tace "shikenan na amince zan Zauna amatsayinki "Amma ba nan gizo ke sa'kar ba ya zamuyi da daddy da Momy kinsan dole zasu nemeni......


Saurin katseta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login