Showing 27001 words to 30000 words out of 30185 words
wayam bako cokali gurin barantana yasa ran abinci, cike da mamaki yashiga kitchen nanma ganinsa yayi tas ko ina a share a goge ba alamar andafa wani abinci cikinsa, cike da mamaki yadawo falon sannan yanufi d'akin Hussaina nocking yayi ahankali duk da yasan ba bud'ewa zatayiba, hannu yasa yad'an murd'a handle d'in 'kofar da mamaki kawai sai gani yayi kyauren ya bud'e, ahankali yashiga d'akin yari'ka dubawa inda ze ganta can idanunsa sukayimai tozali da ita tana kwance kan gado ta kudundune a bargo tanata makyarkyata kamar wacce aka she'kama ruwan 'kan'kara, duk zafin da akeyi a garin.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un jabeer yafad'a tare da nufar inda take kwance, zama yayi gefen gadon tare da bud'e bargon yana kallonta sannan yakai hannunsa kan wuyanta, jin wani irin zafi yayi rau ajikin nata, "subhanallah zazza6i Kike amma baki gayaminba sai ki zauna da ciwo ajiki, kitashi mutafi asibi,
: Bejira mezata fad'aba yanufi wadrope ya d'aukomata hijab, da kanshi ya taimaka mata ta sanya hijab d'in sannan suka nufi mota da sauri jabeer yabud'emata gaban mota ba musu ta zauna sannan ya zagaya yashigaazaunin driver suka d'au hanyar asibiti.
Bakin wani private Hospital suka tsaya me suna *Allah Bamu Lafiya* dake cikin garin katsina jabeer da kanshi ya taimakama Hassana tafito daga motar suka nufi cikin asibiti, suna zuwa kai tsaye aka bud'emata file sannan aka turasu gurin likita, bayan yan tambayoyi da likitan yayima Hassana itakuma tayimai bayanin duk abinda takeji, nan take likitan ya danna wata 'yar karaurawa saiga wata nurse tashigo, ta rissina gaban likitan cikin ladabi, ya nunamata Hassana "kije da ita kiyimata wannan gwaje-gwajen yafad'a yana mi'kamata wata takarda, "owk sir tafad'a tare da amsar takardar sannan takama hannun Hasaana suka nufi lab, nan aka ebi jini sannan tanunamata toilet tabata wani d'an konkoni na roba ta umarceta datayo fitsari anan, haka Hassana tayo fitsarin takawo sannan takoma kan wani benci Wanda masu jira ke zama ta kwanta ta kudundune cikin hijab d'inta dan har yanzu wani irin sanyi takeji,
Kusan minti talatin suna jiran result ganin yanda mutane ke 'kara yawa yasa jabeer matsawa kusa da Hassana yace "ko muje inkaiki gidanmu tunda kusane ni sai indawo injira sakamakon dakuma magungunan daza'a rubuta.
'Daga mashi kai kawai tayi, alamar hakan yayimata dan dama ita tamatsu dasubar wannan asibitin ganin yanda mutane suketa zuwa gashi gurin zama ma yana neman gagarar wasu itakuma ga wani irin sanyi datakeji.
Da taimalonshi suka isa gurin mota, bud'emata yayi tafara shiga sannan shima yashiga yatshi motar suka tafi, kasancewar ba nisa tsakanin asibitin da gidansu jabeer ba'a d'au wani lokaciba suka iso, bakin 'kofar gidan sukayi parking sannan suka fito, suka nufi cikin gidan Ahankali Hassana take tafiya tana biye da jebeer, yanayi yana waigenta har suka isa cikin gidan suka kwad'a sallama Umman jabeer daga d'aki ta amsa, dai-dai lokacin 'kanwarsa nusaiba tafito daga wanka ta kai dubanta garesu cike da fara'a "Lah Yaya jabeer ashe tare kuke da aunty Hussaina, jin an ambaci Hussaina yasa Umma Fitowa daga d'aki tana masu sannu da zuwa, takai dubanta ga jabeer baka cemin tare kuke.
"Eh wlh mama daga asibiti muke shine nace bari inkawota nan tad'an huta kafin agama gwaje-gwajen daza'ayi.
"Subhanallah, Umma tafad'a meyasameta? Ta tambaya tana 'karema Hassana kallo wacce ta saddar da kanta ta'ki bari su had'a ido da Umma, amma hakan behana Umma tagano wani Abu tattare da itaba, murmushi tayi me d'auke da farin ciki, sannan takama Hannun Hassana suka nufi d'aki tanata jera mata sannu.
Love u all my Fan's 👄🍉
[11:10AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻
Page......................41
® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(RWG)_ 📝
Jabeer ne zaune gaban likita, saida likitan yayi wasu 'yan rubuce-rubuce sannan yafad'a mashi ainafin abinda ke damun Hassana, sannan yabasu shawarar hanyoyin daza'abi domin kare lafiyarta,
Nan jabeer yayi godiya sannan ya sayi magungunan da'aka rubuta ya wuce gida.
Da sallama yashigo gidan, zaune ya iske Hassana da kwano a gabanta d'an wake ne Mamanshi tayimata shine takeci dan ba 'karamin dad'i yayimataba, dai-dai lokacin nusaiba tafito daga d'aki cikin kayan islamiyya kalar ruwan 'kasa, cikin ladabi ta isa kusa dashi "yaya harka dawo? "Eh nadawo nusaiba ina mama take ? "Tashiga nan makwabta zata kar6oma Aunty Hussaina kunun aya, tunda kashigo ni bari na wuce islamiyya dama nafara latti baniso inbar aunty ita kad'ai shiyasa nad'an jinkirta.
"To shikenan maza kitafi ga wannan kihau napep dan kiyi saurin zuwa yafad'a yana mi'komata d'ari biyu hannu biyu tasa ta kar6a sannan tayi godiya tawuce.
Kujera jabeer yajawo ya zauna gaban Hassana suna fuskantar juna "sannu ya jikin naki,? "Da sauki, tafad'a tana cire Hannunta daga kwanon d'anwaken, buta ta d'auka tanufi bakin maguji domin wanke hannunta, jabeer yabita da kallo har cikin ranshi yake matu'kar tausayamata ganin yanda tarame sai wani uban fari datakara.
Umma ce tashigo da sallama, dai-dai lokacin Hassana tagama wanke Hannunta zata mi'ke Umma tayi saurin kamata ta mi'ke tana ri'ke da ita har kan tabarma datake ta zaunar da ita, tana jeramata sannu a zuciyarta kuma fall da farin ciki ganin takusa samun jika.
Dai-dai lokacin kuma aka kira sallar la'asar saboda haka jabeer besamu damar yin wata magana da maman tashiba yad'auki buta yayi Al'wala ya wuce masallaci.
** ** **
Zaune yake gurin wani sha'katawa, gurin ya 'kawatu da itatuwa da flower's masu kyan gani da dad'in 'kamshi, mutane ne kala-kala a gurin wasu mata da mijine da yayansu, wasu kuma saurayi da budurwa, kowa harkar gabanshi yakeyi babu Wanda yadamu da wani, shikam yakasa zaune yakasa tsaye kad'an-kad'an yaduba agogon hannunsa, dan 'karfe hud'u sukayi da ita zatazo nan suhad'u amma gashi har hud'u da rabi kome kama da ita be ganiba.
Wayarshi ya d'auko yayi 'yan danne-danne sannan yakara a kunne, wani abin takaicin cemasa akayi switch off, wani mugun takaici ya lullu6eshi jiyayi kamar ya kwala wayar da 'kasa dan haushi.
Dai-dai lokacin me napep ya sauketa, sanye take da ba'kin wando pencil da jar riga iyakar cinya, wacce ta d'ameta tafiddo duk wata sura da Allah yayimata, sai wani yala-yalan gyale kalar ba'ki datayi rolling dashi kafarta jan takalmine mai matu'kar tsini, hannunta ri'ke da waya 'kirar iPhone 7 yayinda d'ayan hannun take ri'ke da poss kalar ja, duk illahirin gurin ya buge da 'kamshin tsadadden turarenta, wani 'katon ba'kin glass ne rufe da kwayar idanunta wanda ake kira no respect, cikin takunta na yanga da 'kasaita ta iso inda yake lokacin yayi zurfi cikin tunanin rashin zuwanta besan ta iso gurinba saida taja kujera ta zauna 'kamshin turarenta ya daki hancinta sannan ya maida dubansa gareta.
"Haba zuby saboda me zaki shanyani anan aka gayaki banida aikin yine tun d'azu nake kiran wayarki gaba d'aya a kashe, cikin tsananin 6acin rai da d'aga murya yake mata magana.
Tashi tayi tsaye tare da d'age bakin glass d'inda ya rufe kwayar idanunta ta d'aga mai hannu "dakata Hafiz karfa kace zaka d'agamin murya, kasani da da yanzu ba d'aya bane, sabodame zakari'kamin shouting a kunne banison hayaniya
Hafiz sakin baki yayi yana kallon zuby yanda take gayamashi magana son ranta, wanda a da koda kud'i aka sakata bazata iya gayamai hakaba.
A zuciyarshi yace lallai dole inyi maganinki zuby, amma a zahiri sai yayi murmushi "sorry abin bekai hakaba yanzu dai zauna muyi magana ta fahimta
Komawa tayi ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya kan d'aya tana taunar cingam irinnan gogaggin yan duniya.
"Kingane zuby abinda yasa nakiraki nace muhad'u anan kinga yanzu rabona dake kusan wata biyu kenan kuma kinriga kin sabamin da lallausan jikinki, kin shagwa6ani da shan daddad'ar zumarki 'kauracewarki gareni ba 'karamin cutar dani yakeba yakamata mukoma yanda muke da.
Murmushi zuby tayi me d'auke da rainin wayo, "Hmm Hafiz aini yanzu na wuce ajinka, dan yanzu gaf nake danayi aure, kuma wanda zan aura yafika kyau kud'i wayewa, kai yafika kome wlh.
"Amma waye wannan wanda ze aureki shin besan Halinkiba, ze kwasarma kanshi bala'i "besaniba kuma baze ta6a saniba dan iya sanin da yayimin mutunniyar kirki yasanni kuma ahaka zan bayyanamai soyayyata kuma inada tabbacin ze aureni.
"Kada kaji inata baka labari ban gayama ko wayeba, ba Kowa bane face *JABEER* mijin 'kawata Hussaina wacce tarigamu gidan gaakiya.
Tana gama fad'amai tasa hannu ta d'auki wayarta da poss d'inta dake ajiye kan table d'in tare da gyara zaman glass dinta a fuska tace kaga tafiyata sai anjima ko...
Tafiya take tana karairaya Hafiz kuwa bin bayanta yayi da kallo yanda take juya mazannai, wani miyau ya had'e 'kutt sannan ya kwalamata kira "Zuby....... A yangance tajuyo ta kalleshi tana wani shu'umin murmushi, hannu yasa Aljihu ya ciro wata agogo ya d'aga mata zaki iya sheda wannan agogon da kuma ranar da kika yaddata.
Wani mummunan fad'uwar gaba taji lokacin data tuno da ranar data kashe Hussaina bayan ta dawo gida tanemi agogon tarasa.
Love u all my Fan's 👄🍒
[11:11AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻
Page......................42
® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝
Dawowa tayi ahankali jikinta yayi sanyi, "Hafiz ina kasamu agogona?
"Murmushi Hafiz yayi me cike da samun nasara "Zuby kenan idan ke sammako kikayi wani a hanya ya kwana, kince zaki auri jabeer ko, saboda kinaso zaki aureshi shine kika raba matarshi da duniya, kina tunanin bansan ke kika kashe Hussainaba.
Kyarma Zuby tafara 'kirjinta na dukan tara-tara ta kalli jabeer, sannan ta dake ta nuna ba Alamar tsoro tattare da ita tace "of course, bazan tsaya jayayya dakaiba Nina kashe Hussaina kuma bazan ta6a danasaniba saboda Hussaina tashiga gonatane ta hanyar rabani dakai, Wanda a lokacin banida wanda nakeso bayanka.
Amma yanzu na canja akalata zuwa ga jabeer kuma nasha Al'washin saina aureshi.
Murmushi Hafiz yayi tare da mi'kewa tsaye yayi taku ahankali yazagayo bayan kujerar datake zaune yadafa bayan kujerar sannan yadu'ko saitin kanta yace
"Karya kike Zuby nasan har yanzu kina sona, kuma inada tabbacin babu wani namiji daze maye gurbina a zuciyarki.
Kawai shawarar dazan baki shine :nasan ke mayyar kud'ice kuma nasan badan kome kikeson jabeer ba sai dan kud'insa.
Idan kinajin shawara me zai hana mu had'a kai inrufa maki asiri idan kin auri jabeer shima ki aikashi inda kika aika matarshi ki kwashe mana dukiyarsa muyi aure mucigaba da jin dad'inmu. Yana gama fad'in haka yadawo kan kujera ya zauna yana fuskantarta.
Wani shu'umin murmushi tayi tacigaba da taunar cingam d'inta sannan tayima Hafiz wani sakaran kallo "baka isaba Hafiz bakuma zeta6a yiyuba kura da shan bugu gardi da kwace kud'i.
Ai dukiyar jabeer tawace ni kad'ai tafad'a tana nuna kanta,
Murmushi Hafiz yayi sannan ya d'auki wayarshi yayi yan danne-danne saiga duk magan-ganun da zuby tayi ashe yayi recording _Of course bazan tsaya ina jayayya dakaiba nina kashe Hussaina kuma bazan ta6a danasaniba, saboda tashiga gonata_ latsa wayar yayi ya kashe sannan ya maida Aljihu, zaki iya fansar kanki da shawarar danabaki idan kuma kinyi gardama zan mi'ka wannan recording d'in ga hukuma.
Take zuby takashi ta duri ruwa ta dad'e da sanin shu'mancin Hafiz tsaf ze kaita a hukuma kuma ya wanke kansa. "Kada ka damu na amince da shawararka amma dan Allah ka goge wannan rocording d'in, tafad'a tana kyarma kamar wacce akayima wanka da ruwan 'kan-'kara.
"Zan goge kada kidamu fatana kawai mucigaba da harka kamar yanda muka saba.
"Indan wannan ne kada kadamu muje koh.
Owk muje kawai yafad'a, mota suka nufa gidan gaba Hafiz yabud'ema zuby tashiga sannan ya zagaya mazaunin driver suka d'au hanya.
Gidan Hafiz suka sauka ranar sun she'ke ayarsu suduka sun nunama juna sunyi missing d'in junansu.
** ** **
Sai bayan sallar isha'i jabeer yadawo lokacin ya iske Hasaana tagama sallah mama ta zubo mata tuwon masara da miyar ku6ewa ga manshanu, nan Mama ta kalleshi "zakaci tuwon ne azuboma "Eh mama ai kinsan tuwo mutuminane, mama da kanta tashiga kitchen ta zuboma jabeer tuwon
Bayan sun kammala ne sukayi haramar tafiya gida, mama ta kalli jabeer "shin ka kar6o sakamakon kuwa a asibitin naji har zaku tafi bakayiman bayanin komeba
"Eh mama na kar6o wallahi ba wani abu bane ke damunta (Malaria) zazza6in cizon sauro, amma ga magun-guna na siyo likitan yace inshaAllah indai tanasha zata samu sauki.
Fara'ar mama tad'an ragu dan ita a tunanunta cikine da Hassana, amma saitaji sa6anin haka "to Allah sauwa'ke Allah maidaku gida lafiya, nan sukayi bankwana suka d'au hanyar gida.
Suna isa sukayi horn megadi yabud'emasu get jabeer nayin parking Hassana tafito da sauri tanufi d'akinta tarufe da key kamar yanda tasaba tayi kwanciyarta, tunanin Hussaina yafad'o mata a rai batasan lokacin data fashe da kukaba,
Shikenan ni yanzu haka zancigaba da zama, gidan yar'uwata ba gidan mijinaba. Ya Allah ka kawomin mafita ina cikin tsaka me wuya.
Love u all my Fan's 👄🍇
[11:12AM, 2/11/2017] Zee Mmn Kd: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member's group of Ciwon "ya mace* 👩🏻
Page......................43
® _TALENTED WRITER'S GROUP_ _(TWG)_ 📝
*wannan shafin nakine my lovely jikalle ta Halimatu Shu'aibu, momynki na mi'ko gaisuwa gareki sweet dougher d'inta Allah bar zumunci*
Washe gari da misalin 'karfe goma na safe jabeer ne zaune office d'insa da wasu fayiloli yanata faman wasu rubuce-rubuce, nocking d'in 'kofar akayi ahankali, d'agowa yayi ya kalli 'kofar sannan ya maida hankalinsa ga aikinsa, kara nocking akayi karo na biyu, aje biron hannunsa yayi sannan yabada izinin shigowa.
Da sallama tashigo office d'in sanye take da riga da siket na less, wad'anda suka kame mata jiki, sai wani madaidaicin gyale data yafa har saman kai dan kan nata bako d'an kwali, 'kafarta sanye cikin plate shoe,
Kallonta jabeer yayi daga sama har 'kasa yace "zuby kece tafe da wannan lokacin,
"Nice tafad'a tana murmushi.
"Bissmillah zauna mana yafad'a yana nunamata kujera.
Ba musu ta zauna tana wani sakar mashi wani shu'umin murmushi, bayan sun gaisa tace "dama zowa nayi inyima gaisuwa dan lokacin da'akayi rasuwar bani gari, gaskiya munyi babban rashi tafad'a tana matsar kwallan munafinci, Hussaina 'kawatace banida tamkarta nayi babban rashi.
A mamakance jabeer yake kallonta, kindai manta Ai Hassanace tamutu ba Hussaina ba.
Wani mummunan fad'uwar gaba zuby tayi lokacin data tuno da shawarar databa Hussaina na cewa Hassana ta zauna maimakinta.
Inkau hakane ba shakka Hassana bata gayama jabeer ba itabace Hussaina idan kuwa hakane akwai aiki babba agabanta.
Jabeer ya kalleta "naji kinyi shiru me kike tunani, firgigi tayi kamar wacce tafarka daga bacci, ah bakome, nizan wuce Allah bada ha'kuri. "Ameen kawai jabeer yace sannan yacigaba da aikinsa.
Jiki ba lakka Tabar office d'in, daga nan gida kawai tawuce zuciyarta cike da tunani barkatai.
Zuby a d'akinta sai safa da marwa takeyi, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta "tabbas Hafiz shine babban matsalata idanko hakane dole in d'au mataki kanshi.
Wani mugun murmushi tayi lokacin wanda koni zee bansan ma'anar yinsaba.
Wayarta ta d'auko ta danno sunan Hafiz bugu d'aya ya d'auka "hellow zuby na yadai, akwai labari ne?
"Sosaima kuwa akwai labari me dad'in sauraro, inaso muhad'u a park dinda muka saba had'uwa.
"Owk ba damuwa kamar 'karfe nawa?
"Yanzu-yanzu kome kakeyi ka ajiye kataho dan abari ya huce shike kawo rabon wani.
"Owk ganinan zuwa.
Saurin fad'awa wanka zuby tayi ta she'ka wanka, tana fitowa batare da 6ata lokaciba lotion kawai ta murzama jikinta sannan tasaka irin 'kananun kayan data saba sakawa, tana fitowa bakin titi ta tsaida me napep tagayamai inda ze kaita, cikin mintinan dabasu wuce talatinba ta iso gurin ta sallami me napep, wayarta ta fiddo da niyyar takira Hafiz ta tambayeshi ya isone hangoshi tayi jingine jikin motarsa yana sakar mata murmushi, itama murmushin tayi sannan tanufi gurin wasu kujeru kai tsaye ta zauna, shima Hafiz nan yadawo ya zauna kusa da ita a 'kagare dayaji labarin datazo mai dashi.
Kusan minti biyar da zamansu zuby batayi maganaba, a 'kagauce Hafiz ya kalleta inajinki zuby, na bud'e kunne ina sauraron jin daddad'an labari kinyimin shiru.
Kallonshi tayi daga sama har 'kasa "owk kada ka damu nad'an gajine inaso in huta tukun, bari naje can na kar6o mana drink's mud'ansha konaji sanyi-sanyi,
"A'a kibari in anso mana Hafiz yafad'a yana mi'kewa tsaye,
"A'a kabarshi kawai zan amso saurin yin gaba tayi dan kada Hafiz d'in yacemata a'a.
Haka ta isa gurin siyar da drink's kwalbar lacasera biyu ta kar6o