Showing 18001 words to 21000 words out of 21076 words

Chapter 7 - RAINON YARO BOOK 1 FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO.txt

Amma ba taurarin take kalla ba – zuciyarta na karayin kuka cikin shiru.

“Daddy... me na yi maka? Me ya sa ka barni da wannan shiru da yake cin zuciyata kamar wuta?”



Kukan da take shanye ya hana ta magana, amma zuciyarta tana karanta kalmomi da MJ ya taɓa faɗa mata:

“I will always protect you.”


“I promise, Daddy.”



Tayi shiru, sai kuma ta ɗago kai kamar wacce ta yanke shawara.

“Na fara fahimtar wani abu. Kuma zan bi saƙon zuciyata, komai za ta fitar min da shi.”




---

A MASALLACIN FADAR SARKI...

Limamin masarauta yana cikin masallaci yana karanta ayoyi cikin nutsuwa. Sai ga shi ya ɗago kai da mamaki.

“La hawla...! Akwai sihiri da aka nannade da wuta da ƙiyayya. Ba MJ bane ainihin laifinsa. Wani abu ne yana sarrafa zuciyarsa.”



Ya tashi da sauri, ya nufi fadar Sarki.


---

A FADAR ZUWAIRA...

Zuwaira na zaune da mahaifiyarta a dakin su. Mahaifiyarta tana girgiza kai tana hurawa boka turaren sa da suka boye a cikin ƙamshi.

“Idan har MJ ya ci gaba da mantawa da ita, sannu a hankali, za mu zama dole ga rayuwarsa.”



Zuwaira ta ƙara kwafa da wulakanci:

“Ai yanzu ma ya daina kulata sosai. Shi fa ba yadda na ke so yake ba — amma tunda ya daina kula da waccan, zan sami damar shiga zuciyarsa.”



Mahaifiyar ta ce:

“Amma ki kiyaye... idan sihiri ya kama zuciya sosai, ba zai san me zai so ba, balle wacce zai aura. Sahi dai gashi kamar shara.”




---

MJ A DAKINSA...

A dakin MJ, yana zaune yana karanta littafi. Amma ba ya gane me ke ciki. Sai kawai ya mike, ya kalli madubi. A cikin madubi, sai kawai yaga fuskar Baby — amma fuskar ba ta murmushi ba ce, ba kuma ta dariya ba. Fuskar da ta cika da tambaya da raɗaɗin jin ƙiyayya daga masoyi.

MJ ya zabura — zuciyarsa ta yi wani irin bugawa.

“Me ya ke faruwa dani?”



Yayi wani numfashi mai nauyi. Ya zauna. Ya ɗauki wayarsa — sai ya duba hotonta da ya taɓa ɗauka ranar da ta samu kyautar karatu a makaranta.

“Na manta da ke... Amma kuma... me yasa zanji wannan ciwon yanzu?”




---

SAFIYAR RANAR ASABAR...

Baby na zaune a lambun makaranta. Fareeda, abokiyarta, ta zo kusa da ita da takarda a hannu.

“Na samo miki bayanin wata tsohuwa da ke cire asiri a wajen gari. Akwai labarin cewa tana iya tantance wanda aka tsare da sihiri. Idan baki so kowa ya je — mu je mu duba da dare.”



Baby ta girgiza kai. Cikin ranta ta furta:

“Daddy... ko da ba ka gane ni yanzu ba... zan nemi hanyar da zan dawo da kai.”

Afili Kuma tace "nagode sosai kawata da taimakon ki a kaina duk da cewar ban fadamiki abin dayake damuna ba, sai da kikai duk yadda Zaki kika nemo abin da ke damuna, daskiya ke kawar kirkice.


---Misalin ƙarfe 9:00 na safe
Fareeda da Baby suka tsinci kansu a cikin wani daji mai zurfi, inda bishiyoyi suka lullube sararin sama, kuma iska ke busa kamar tana ɗauke da sirri. A tsakiyar dajin, wata tsohuwa ke zaune, idonta biyu kamar gilashi — masu tsananin haske da fahimta.

Tsohuwar ta kalli Baby tun daga nesa, sannan cikin sauti mai tsawa ta ce:

“Kin zo da zuciya mai tsarki. Amma zuciyar wanda kike ƙauna an nannade ta da igiyar asiri.”



Ta miƙa hannunta, ta ɗora shi a kan ƙirjin Baby, sai ta ce cikin sanyin murya mai zurfi:

“Na fahimci wanda ya aikata wannan asirin. Ya samo asali ne daga cikin masarautar ku. Amma akwai mafita — sai dai farashi mai tsanani.”



Baby ta share hawaye, ta kalle ta da karfin zuciya:

“Duk abin da ake bukata zan yi. Daddy na ya fi kowa cancanta da a dawo da shi. Ko rayuwata ne za a nema — zan bayar. Indai game da shi ne, na riga na yarda da sadaukarwa!”



Tsohuwar ta gyara zama, sannan ta ce da ƙaramin murmushi:

“To ki sani… kafin zuciyarsa ta warke, dole sai naki ta sha wahala.”



Idanun Baby suka zaro, cike da mamaki:

“Me kike nufi da haka? Kina nufin sai na sha wahala kafin a karya shirin da ke jikinsa?”



Tsohuwar ta gyada kai a hankali:

“Tabbas. Baby, ke wata sirri ce wadda Ubangiji ya ɓoye. Babu wanda ya san hakikanin komai a kanki sai mahaifinki, mahaifiyarki… da kuma kishiyar mahaifiyarki. Ita ce silar da ya mai da ke marainiya, mai rayuwa ba tare da asali ba.”



Baby ta ja da baya, zuciyarta na bugawa:

“Ke… kina nufin kin san wani abu game da ni?”



Tsohuwar ta murmusa kaɗan, tace:

“Ba shi ne ya kawoki nan ba. Kin zo ne domin ceton ran mahaifinki.”



Baby ta sunkuyar da kai, jiki a sanyaye:

“Menene zan yi, wanda zai dawo da shi cikin hayyacinsa?”



Tsohuwar ta ce:

“Ina so ki zauna a nan — ki zauna da ni har abada. Ki zama ɗiyata. Na jima ina jiranki… ke ce cikon mafarkina.”.........





🕊️ RAINON YARO

Chapter 9



Baby ta tsorata, amma da ta tuna da MJ da yadda yake mata ƙauna da kulawa, sai ta ce a hankali:

“Indai hakan zai dawo da daddyna, na amince.”



Fareeda ta yi saurin janyo ta gefe, cikin tashin hankali:

“Baby, ba ki da hankali ne? Idan kika zauna anan, burinki fa? Karatunki fa? Rayuwarki fa? Kina so ki lalata komai? Idan MJ ya dawo lafiya kuma ya tarar baki kusa da shi — zai mutu da damuwa! Ki tuna da hakan!”



Baby ta numfasa, ta ce cikin murya mai sanyi:

“Fareeda, kin san cewa sarki ya ce ba zai taɓa aurar da ni ga daddy ba. Na san babu aure tsakanina da shi. Amma ni ‘yace a wajensa. Koda na rayu da daddy, dole wata rana za a tura ni ga wani. To me zai hana in sadaukar da kaina domin wanda ya fi kowa kaunata? Ka da ki manta Fareeda ,cina, suturata, kulawata, rainona, wankin Kashi, wankin futsari, shayarwata, karatuna,tarbiya ta,komai da kika gani atattare Dani daddyne ya minsu, kinsan mene kadai bai min ba haihuwata, da Kuma haluttata a doron duniya, bazan ma fadamiki wannan maganar ba tunda bani da tabbacin cewar bashi ya haifeni ba,tun da har yanzu na kasa sanin waceceni, Indai har iya zamane zan zauna da ita har abada' muddum zan ceto zuciyar daddy"



Tsohuwar ta tashi a hankali, ta nufo Baby da sandarta tana nazarin zuciyarta kamar tana karantawa daga takarda.

“Zuciyarki kamar ruwa ce mai tsarki — amma idan aka zuba ƙashi a ciki, sai ta zama baki. A yau za ki yanke hukunci tsakanin zuciyar ki da zuciyar wanda ke kiran ki Baby.”



Fareeda ta tsaya gaba da Baby tana girgiza kai, idonta cike da ƙwarin gwiwa:

“Wallahi idan kika zauna anan, Baby, na rasa ke. Ya Mujahid ya rasa ke. Kin san yadda zuciyarsa ke karaya ko da yana cikin jama’a. Kin san yadda yake zaune da mugun burin ganin ke kina dariya?”



Baby ta sunkuyar da kai, hawayenta suna zuba kamar ruwan sama. Tana jin duniyar na juyawa — tsakanin soyayya da sadaukarwa, tsakanin burin zuciya da ƙaddara.

Tsohuwar ta sake magana, cikin sautin da ya haɗa tausayi da rinjaye:

“Zaki iya dawowa, amma sai kin cika sharuɗɗa. Sharadi na farko: har sai ran mahaifinki ya dawo cikin nutsuwa, ke ba za ki sake masa dariya ba. Sharadi na biyu: kowanne mutum da kika ƙauna sai ya jarrabtu da rashin ki.”



“Wannan ba fushin Allah bane — wannan ne fansar ƙaunar ki da amincin ki.”



Baby ta ɗago da idanu masu haske amma cike da hawaye. Ta ce da Fareeda cikin murya mai sanyi:

“Na san zan iya rasa komai — amma idan daddy ya daina shan wahala, zan iya jurewa.”



Fareeda ta rungume Baby da karfi, tana hawaye:

“Sai ki dawo, please. Ki dawo da daddyn mu. Amma ba ki da damar ɓata rayuwarki wajen fansar kowa. Ke har yanzu kina da mafarki, kina da burin karatu... kina da zuciya da ba a gama gane ta ba.”



Tsohuwar ta gyara zama, ta ɗauko ƙaramar ƙoƙo daga gefe, ta miƙa wa Baby:

“Ki sha wannan ruwan ganyen rai-dore. Zai karɓi wani ɓangare na farin cikin ki. Amma zai ƙara wa zuciyar MJ haske.”



“Zan sha,” Baby ta ce, tana girgiza kai da murya mai ƙarfi. “Na amince da ƙaddarata.”



Ta ɗauki ƙoƙon — ta kai bakin ta — ta lumshe ido... ta sha.

A can masarauta, MJ wanda ke zaune cikin daki, sai ya ji zuciyarsa ta buga... kamar wani abu na tashi daga barci cikin jikinsa. Ya ɗaga kansa da sauri:

“Baby...?”




MJ ya farka da kyar, kamar wanda aka farkar daga mafarki mai nauyi. Yana zaune a kan gado, yana kallon hannunsa — ya tsinci kansa cikin wani irin nauyi da ba ya iya fassara.

“What’s happening to me... why do I feel like I forgot something important?”



Ya mike, ya nufi mirror, sai idonsa ya sauka kan takardar gaisuwar Baby da ta rubuta masa shekara guda da ta wuce a ranar da ya kai ta bikin makaranta.
Ya ɗauke ta, yana karanta rubutun da bai taɓa dubawa ba kwanan nan:

"To the best Daddy in the world. You didn’t just raise me, you rescued me. I will never stop learning, I will never stop dreaming — because you showed me how to live."
— Your Baby Girl, fateema



MJ ya runtse ido. Kamar zuciyarsa tana harbi da wani sauti... Sai kuma ya furta:

“fateema...”



Zuciyarsa ta buga. Idanunsa suka cika da ruwa. Sai ya ji wani abu ya shiga tunaninsa kamar sauti yana bayyana:

“Ba duk wanda ke kusa da kai ne ke tare da kai ba.”




---

A CAN BANGAREN BABY...

Baby ta farka daga barci da ciwon kai. Fareeda ta shigo da ruwa, ta durƙusa kusa da ita.

“Yau rana ce ta yanke hukunci, Baby. Tsohuwar nan ta aiko sako — cewa idan har aka karanta kalmar da ta ba mu gobe da dare a gaban MJ, zuciyarsa za ta yi yunkurin yaki da sihirin da ke cikin shi. Amma... zai iya mutuwa idan bai da ƙarfi.”



Baby ta ce cikin karfi, idonta cike da hawaye:

“If I have to lose him to free him, then let it be. Amma ba zan zauna in bar bokan nan su kasheshi da raye ba. , yanzu tsohuwa ta amince idan na tashi muje muyi aikin tare?”


Gydamata Kai fareeda tayi tace "eh tace dole sai dake bayan mun Kammala aikin sai in dawo dake batare da MJ ya ganki ba"

Kukane yakara taruwa a idon baby a hankula tace "daddy kamar wata zuciyace shi a gareni tsokace da Babu Wanda zai iya rabuwaw,Amma sai gashi yanzu suncu nasara akanmu ,burinsu ya cika fareeda sun rabani da daddy na" baby ta sake fashewa da kuka.



Daker farida ta lallasheta tace "kiyi hakuri kitashi bamu da lokaci "

--FADAR SARKI...

Zuwaira na zaune da mahaifiyarta a bayan wani ƙaton tagar fadar Sarki. Suna jin cewa MJ yana ta kai-kawo, yana tambayar mutane tambayoyi marasa dalili: “Ina Baby?” “Tana lafiya kuwa?” “Me nayi mata kwanan nan?”

Zuwaira ta fara zubar da gumi. Mahaifiyarta ta ce:

“Sihirin na fara yin rauni. Akwai wani abu da ke tayar da hankali a zuciyarsa.”



Zuwaira ta ce da tsawa:

“Ba zan bari ya dawo da ita ba! Ko da zan yi asiri na biyu — sai ya manta da ita har abada.”




---

*MJ*

Yana zaune cikin dakinsa, sai ya kira sunanta a hankali:

“Baby…”



Zuciyarsa ta cika da ɗoki. Wani hoto yana dawowa a zuciyarsa — hoton ranar da ta ce:

“I promise, Daddy.”



Sai MJ ya miƙe tsaye. Ya zaro jakarsa. Ya ce:

“I need to find her. Something’s wrong. I can’t breathe when I think of her face.”




---

DAREN DA AKA FARA KARANTA KALMAR TSOHUWA...

Baby da Fareeda sun zauna a wani ɓangare na masarauta — kusa da labulen da MJ zai wuce idan ya dawo daga wajen Sarki.

Kalmar nan ce a hannun Baby, sai ta kalli Fareeda, ta ce:

“Duk da tsoro na, na yarda — akwai zuciya a cikin zuciyarsa da ba bokan duniya zai iya rufewa ba.”



A daidai lokacin, MJ ya shigo falon. Idanunsa suka haɗu da na Baby.

Zuciyarsa ta harbi, gaban kansa ya ɓuga — kamar girgiza ya shigo kansa.

Baby ta miƙa hannu, ta karanta:

"Zuciyar da ka gina da ƙauna, za ta rushe sihiri da ƙiyayya..."



MJ ya dafe ƙirjinsa. Ya durƙusa.

“Why do I feel this pain... why do I feel like I lost someone?”



Baby ta matsa kusa da shi. Tana kuka, amma da murmushi a fuskarta.

“Because you did. But now, you’re finding her again.”



MJ ya kalli idonta. Na farko cikin tsawon lokaci, ya ce:

“baby....…”


Yana fadar haka ya yanke jiki ya fadi.



Zuciyarta ta karaya, ta furta cikin hawaye:

“Yes, Daddy. I’m still here.”


TA kifa kanta akan kirjinsa ta saki kuka, fareeda ganin baby tana shirin karya alkairin da tayiwa tsohuwa yasa ta mike daga Inda take da sauri tashiga zan hannun baby,

Baby tana kuka har damajina zuciyata na mata daci a haka tabar cikin dakin, suka bar MJ a kwance.


Tun da su baby suka fita daga masarautar baby ke juyawa Tana kuka tana tuna irin RAYUWAR da sukayi da Daddynta MJ sai gashi yau ranar daba ta taba tunanin zuwan taba tazo ,wai itace yau zata fara rayuwa da wata wadda ba MJ ba, a haka suna tafe Tana kuka har suka karasa jejin





Fareeda da Baby sun yi shiru yayin da suka isa bakin jeji. Kowane mataki da Baby ke ɗauka, kuka ke ƙara ƙarfafa a zuciyarta. Tana jin kamar ana yayyafa mata gishiri a buɗaɗɗen rauni. Kamar kowace ƙwaƙwalwa da ke da alaka da MJ, tana murkususu a cikin zuciyarta.

Suna karasawa bakin kujerar dutsen da suka saba zama, sai Fareeda ta tsaya. Ta juyo da ido cike da tausayawa da kuma damuwa, ta ce da Baby:

“Na san da wuya, amma lokaci ne ke kira. Dole na tafi.”




🕊️ RAINON YARO

Chapter 10




Baby ta rike hannunta da ƙarfi kamar ƙaramin yaro yana tsoron a bar shi cikin duhu. Hawaye na zuba kamar ruwan sama.

“Ki yi hakuri, Fareeda… Amma ki rike wannan sirrin. Kada ki faɗawa kowa inda nake. Ko daddy... har sai lokacin da lokaci ya ƙare.”



Fareeda ta ja numfashi, ta dafa kafaɗar Baby, ta ce:

“Zan yi miki alkawari — zan ɓoye wannan sirrin a cikin raina kamar yanda kike ɓoye ƙaunar MJ a zuciyarki.”



“Thank you… my sister.”



Suna kallon juna, sun fi magana da idanuwansu fiye da lafazi. Sai Fareeda ta juyo, ta fara tafiya da ƙafafuwa masu nauyi kamar tana barin ranta a baya.





Tana ficewa daga cikin dajin, iska mai sanyi ta fara busowa, tana ɗauke da ƙamshin wani sabon juyi a rayuwar Baby.

Baby ta tsaya — kanta ya zube kasa. Sai ta juyo da ƙyar, ta shiga cikin dajin inda tsohuwar ke zaune a tsakiyar sararin da fitilu masu asiri suka kewayeta.

Tsohuwar ta ɗaga kai tana kallon Baby kamar ta riga ta san zata dawo. Ta ce cikin murya mai kaifi:

“Yanzu ne gaskiya zata fara. Na gode da dawowarki, ‘yata.”



Baby ta durƙusa a gabanta, tana kuka. Amma a wannan karon, ba kukan rauni bane — kukan ƙarfin zuciya ne, da alkawarin da ta ɗaura a zuciyarta. Alkawarin ta bar ƙaunarta ta ƙone, don rayar da wanda ya koya mata ƙauna.


---To Kwana biyu kenan Baby na zaune a ƙasar tsohuwar. Gurinta na cikin jeji amma cike da tsabta da wani irin shiru mai ɗauke da natsuwa. Tsohuwar ba wai kawai mai ilimin asiri bace — amma wadda ta shafe shekaru tana tsare sirrin dangi da duniya bata san da su ba.

Kullum da safe, Baby na farka tana wanke fuska da ruwan itacen tsarki. Sai ta zauna a gaban wata madubi da baya nuna fuska sai ta gaskiyar zuciyarka. Idan ta yi ƙarya — madubin baya nuna komai. Idan zuciyarta ta cika da alhini — madubin yana zubar da hawaye maimakon ita.

Tsohuwar na koya mata magana da sararin zuciya — da karanta tunani — da gane zuciyar mutane ta duban idanunsu. Kowanne daren Jumma’a, Baby na zama a gaban wuta, tana karanta kalmomin da ke karya asiri da duhun zuciya. Amma duk da haka...

MJ ya tsaya mata a rai.

Daga nesa, idan ta zauna a ƙasan bishiya, sai ta rufe idonta, tana tunanin sa. Kamar yadda yake riketa a da, yana mata nasiha, yana yawo da ita makaranta.


👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑👑


A masarauta kuwa, MJ ya rikice. Koda ya farfaɗo daga faduwar da yayi, tunaninsa ya daina daidaituwa. Yana ganin hotonta a bango, yana jin sautin dariyarta a cikin iska. Ya tambayi Fareeda sau da yawa:

“Ina Baby? Me yasa take ɓoye min? Me nayi mata?”



Fareeda ta jure da ƙyar.ta ce masa itama bata San Inda baby take ba. Sai dai kullum da dare tana fuskantar kalmar alkawarin da ta ɗaura — ba zata tona sirrin Baby ba.

Sarki ma yana lura da MJ yana taɓarɓarewa. A wani zama na sirri ya ce masa:

“Ka rikice akan yarinyar da baka da hakki da ita. Na faɗa maka tun da farko — bazata taɓa zama taka ba.”



MJ ya miƙe, idonsa jajir:

“Ban nemi ta zama tawa ba. Ina neman ta samu lafiya. Ina neman ta dawo cikin duniyarta, ko da kuwa ba zata ƙara kiran sunana ba.”



Sarki ya kalli shi da mamaki. Bai taɓa jin MJ yayi magana da wannan zuciyar ba.

“Na rasa komai. Kuma yanzu, ko ganin fuskarta ba na i ya yi , Abba bakasan yadda nakeji ba, baby rayuwa tace Kuma duniya ta ,nashaku da baby tun tana tsumma haka nake goyata a bayana, idan tayi Kashi nawanke naciyar da ita da hannuna na raineta da zuciyata Abba , na kwana da ita na tashi da ita tsawan rayuwata ban taba iya minti 30 ban saka baby a ido na ba, ko makaranta taje saina bita, najure duk wata magana da akeyimin akanta, meyasa abba zakace baby batawa bace ? Shin ban cancanci nazama uba bane? Ko ban Kai nayi kukaba sabi da ita? Wallahi Abba hawayena bazai taba tsayawa ba Indai har ban saka baby a idona ba "?

MJ Yana gama fadar haka ya fice zuciyarsa na masa zafi da kuna.




---

A cikin daji...

Tsohuwar ta kira Baby da daddare. Wuta ta ƙone a tsakiyar gidan. Ta ɗora wata kwalba a gaban ta, ta ce:

“A yau za mu fara buɗe hanyar zuciyar MJ. Amma ki sani — da zarar mun fara, ba dawowa baya.”



Baby ta ce, murya a kasalance:

“Na shiga cikin duhu tun da na rasa shi. Bana jin tsoron komai — muddin zan dawo da shi cikin haske.”



Tsohuwar ta ɗan murmusa. Ta ɗaga kwalbar, ta ɗora a gaban Baby.

“Sha wannan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login