Showing 15001 words to 18000 words out of 21076 words

Chapter 6 - RAINON YARO BOOK 1 FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO.txt

da bai iya furta ba.


---

Can defe guda Kuma ...

Zuwaira ta kalli Baby tana dariya da Hafid, sai ta ce:

“Kalla yanda take dariya kamar budurwa da saurayi, gashi Ya Mujahid na kallon su shiru — yana mugun son yarinyar nan wallahi.”



Qawarta ta ce:
“Ba da ban ba, sai na zubar da mutuncinta a gaban dukan su…”


Zaro ido zuwaira tayi tace ",me rufamini asiri kekuwa mai yasa"

"Sabi da kowa sonta yake

---
**********************

MJ ya ce da ita a hanya:

“Kinji dadin picnic din?”



Baby ta ce da murmushi:

“Ina jin dadin duk inda kai kake.”



MJ ya kalle ta, yana jin yadda zuciyarsa ke ɗaure da zuciyar baby.

“Kada ki bari duk wanda ya ɗora miki tunani da ya zame miki nauyi. Karatu ki maida hankali… ki kare hankalinki,da mutunci ki Baby.”



Ta ce:

“To Daddy. Amma kai fa? Kana jin dadin ganin mutane suna tare dani?”



MJ ya yi shiru. Ya ce a ƙarshe:

“As long as you’re safe… I’m fine. Even if it hurts.” a haka har suka karasa cikin masarautar.




---

💞💞💞💞💞💞

Washegari, Sarki ya sake kira MJ. Ya ce masa:

“Abee, kana yin ƙoƙari. Amma wannan yarinya… ta fara girma. Kuma idan baka kula ba, mutane za su fara zargin ta, ko kuma kai.”


" Abba to meyasa zan a fara zarginmu?"

Sabida tayi girman da Yakamata ku rabu wanna kualwar da kake bata mijinta ne kadai ya kamata ya bata"

“A yanzu dai, ka ci gaba da nuna kulawa — amma ka fara janye kanka a hankali. Saboda zuciyar mace idan ta fara buɗe ido, zata fara kallo fiye da kallon uba kawai.”



MJ ya ce da siririyar murya:

“Abba… zuciyata na da amanar Baby fiye da nawa. Zan rene ta har sai ta fahimci duniya da kanta.”



Sarki ya ce:

“To ka cigaba da hakuri. Idan rana ta fito, kai za ka fi jin zafi fiye da kowa.”



To yauma kamar kullum a makaranta cikin rana mai ɗumi, makarantar Baby ta gudanar da inter-house sports competition. Akwai taron manyan mutane, iyaye da jami’an gwamnati. Baby na cikin ‘yan kwallon tseren mita 100, saboda ta kware wajen gudu — daidai da lafiyarta da horon MJ a gida.

Zuwaira da kawarta Ameenah, sun shigo makarantar cikin kaya masu ƙyalli, ba don su kalli gasar ba, sai don su jefa ruwan zafi a zuciyar Baby.

“Kalla ita can. Yarinyar nan da ko ba MJ ba da tuni bata wuce ragowarmu ba.”



Ameenah ta ce: “Mun shirya mata yau. Wallahi zamu nuna wa kowa cewa wannan ‘yar banzar da MJ ke raino — bata da mutunci.”




--*

Bayan an gama tsere, Baby ta samu nasara — ta lashe zinariya. Ana nan ana murna, sai wata karamar yarinya ta zo tana kuka. An tambaye ta me ya faru?

“Waccan yarinyar Baby ce ta sace wayata! Na ajiye ta a bag dinmu tana kusa... yanzu babu ita, babu waya!”



A hankali ake kara jefa zargi — wasu daliban da ke kishin Baby suka fara cewa “ai dama can tana jin kamar ita ce komai a makaranta, ta saba dauke dauke.”


---

MJ, wanda ke gefe da sauran masu kallo, ya ga yadda Baby ke rikicewa. Yana kallonta ta kururuta:

“Wallahi bani na dauka ba! Ban ma san da wayar ba…”



Zuwaira ta murɗa murmushi. Ta ce:

“Ehhh... yarinya mai gaskiya fa ba ta kuka. "





MJ ya shigo harabar gasar. Bai ce komai ba. Ya tsaya a gabansu, ya kama hannun Baby, wanda hawaye ke shirin gangarowa.

“Come with me.”



“Daddy... suna zargin—”



“I know. But your eyes are clean. That’s enough for me.”



Yana rike da hannunta suka bar wajen. Kowa ya zuba musu ido. Wasu suna mamaki, wasu suna harara, wasu kuwa suna jin haushi — amma MJ bai kalle su ba.


---

A GIDA…

Da dare, Baby na zaune kusa da MJ. Ya rike hannunta, yana goge mata hawaye da tawul.

“Idan duniya ta juya miki baya, ki kalli ni. I will always be your front.”



“But I don’t want to disgrace you, Daddy... suna cewa ni ban dace da kai ba…”



MJ ya dafa kanta, ya furta da nutsuwa:

“You don’t have to match me, Baby. You only have to match your truth. And I know your truth is pure.”



******
---

SARKI YAJI ABINDA YA FARU…

Da safe, MJ na shirin kai Baby makaranta, sai aka kira shi a fadar Sarki.

Sarki ya kalle shi da tsantsar basira:

“Abee... lokacin da yarinya ta fara fuskantar ƙiyayya, to zata fara girma da karfi. Amma ka san me ke cutar da mace da wuri? Idan ta dogara da soyayya kafin ta girma da zuciya.”



“Kayi hattara. Zuwaira da irinta... ba ƙiyayya suke ba — kishin rikonka suke.”



MJ ya ce:

“Zan kare Baby, ko da kuwa sai na hana zuciyata kwanciya. Tana min kamar wani bangare na rayuwa wanda babu wanda zai iya cike shi. Kayi hakuri Abba ammani bazan taba iya zuba ido ina kallon masu chutar da baby ban tsawatar musuba, da ace zuwaira zata Gane abin da zatai na sota, to ta kaunaci baby nikuma zan kaunace ta Amma bawai ta kulla mata sharriba" MJ Yana gama fadar haka ya bar cikin fadar gaba daya.

""""""""""""""""""🫂
Bayan dawowa daga makaranta, Baby ta zauna a gaban window tana kallon rana tana faduwa, tana rik'e da certificate ɗinta na zinariya, amma idanunta cike da tambayoyi da damuwa.

MJ ya zauna gefenta da cupcake a hannu, ya ce da dariya:

“You know what we do when the world frowns at us?”



Ta girgiza kai cikin rauni.

“We smile back. Amma ba dan muna jin dadi ba — sai don mu nuna musu we’re stronger than their hate.”



Baby ta kalle shi, sannan ta ce cikin hankali:

“Daddy… yaushe zan daina jin kamar bana cikin nasu? Kamar bana daga masarautar nan?”



MJ ya janye gashinta daga fuskarta, ya ce a hankali:

“Zaki daina, Baby. Lokacin da kike d'aukan kanki a matsayin tauraruwa, ba dutsen da zai iya hana ki haskaka.”

Gyda Kai kawai baby tayi hadi da rausayar da Kai ta Dora kanta a kan kafadar MJ Tana sauke ajiyar zuciya.


---***************

WATA SABUWA... MAHAIFIN ZUWAI RA YA DAWO MASAURAUTA DA ZAMA.

A lokacin da Baby ta fara samun karbuwa daga wasu malamai da manyan makaranta saboda kokarinta, sai mahaifin Zuwaira — Alhaji Faruq — ya shigo masarauta da korafi.

“Mai martaba Sarki, a yarda da za’a rika dora yarinya ba asalinta ba, bisa manyan mukamai a makaranta da masarauta? Wannan zai lalata tarbiyyar ‘ya’yanmu.”



Sarki Umar ya kalle shi, ya dan tsaya kafin ya ce:

“Ka tuna cewa ba jinin sarki ke sa mutum mutunci ba — halinsa da zuciyarsa ke gina shi.”



“Yarinyar da kake magana akai — Baby — na fi yarda da ita fiye da yawancin yaranmu da aka haifa da zinariya.”



Alhaji Faruq ya fita da jin haushi. Ya hadu da diyarsa Zuwaira a waje, ya ce:

“Idan baki hana wancan yarinyar nan taka kasa ba, to zan hana ki gado a gidana.”



Zuwaira ta dafe ƙirji da ɗan mugun murmushi.

“Don’t worry, Abba. She’ll taste salt without soup.”


Kai kawai abban ta ya daga ya ya juya ya tafi tabi bayansa da kallo.

---

Zuwaira da abokanta suka fara tsananta mugunta. Suna jefa Baby cikin gori a makaranta da gida. A wani lokaci har aka boye mata littafinta na jarabawa. Sai dai duk da haka, Baby ta ci gaba da samun matsayi na farko.

MJ na lura da komai. Wani dare ya kira Baby ya ce:

“Kinga... I won’t always be able to shield you. Amma zan koya miki yadda ake gina garkuwar zuciya. Ki tsaya da kafafunki, Baby. Don ba zaki iya gudu daga komai ba, watara na bazaki ganni ba dole ni ma zan mutu ,bazai zama kullum nine mai kareki ba.”



“I’ll try, Daddy. I’ll try…”




---

SHEKARUN GIRMA… KYAU NA BAYYANA

Baby ta ci gaba da girma. Yanzu tana da shekara goma sha bakwai 17 wayonta da kwarjinta na bayyana. Komai nata ya cika da ladabi da kamala. A makaranta, kowane yaro na kallonta fiye da sau biyu. Har wasu malamai sukan ce:

“Wannan yarinya, kamar Sarauniya ce da ba’a saka mata crown ba tukuna.”



Samari ‘yan masarauta, da yayansu masu kudi, sun fara aiko mata da notes da gifts, amma duk MJ yana karantawa kafin ta karanta.

Wani dare, MJ na goge mata kai yana mata kitso, sai ya hango wata love note daga ɗaya cikin yayansu Alhaji Faruq. Ya janye karyar murmushi, ya ce a hankali:

“Yanzu sun fara rubuta miki wasikun soyayya?”



“Na ce musu bana sha’awar soyayya. Ban san me soyayya take nufi ba. Ni dai ina da kai, kuma hakan ya ishe ni.”



MJ ya kalle ta. Idanunsa sun kada, amma da murmushin zuciya. Ya ce:

“That’s all I needed to hear tonight, Baby.”


🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺



A wani dare mai duhu da hazo, mahaifiyar Zuwaira — Hajiya Sa’adatu — ta ce da diyarta a sirrance:

“Zuwaira, idan da gaske kike son ki samu nasara, ki cire jin kai. Wannan yarinyar da kike bari tana daukar hankalin MJ? Kafin ki farka, zata dade a zuciyarsa fiye da rayuwar da kika yi tun kina cikina.”



Zuwaira ta dafe kirji. Zuciyarta cike da kishi da azaba. Ta ce:

“Mama, ban san lokacin da ya fara jin ta fiye da ni ba. Amma ina so na ga karshenta.”



Hajiya Sa’adatu ta saki murmushin mugunta.

“To sai mu kai sunansa da nata... gurin boka. Zamu juya duniya, zamu juya zuciyoyi idan kin amince.”



Murmushin mugunta zuwaira tayi tace" duk yadda kikace haka za ayi Momyna"
---


🕊️ RAINON YARO

Chapter 8










Washe gari da sassarfa suka shirya tsaba suka dauki hanyar zuwa wajen boka ,
a cikin wani daji mai duhun gaske — boka Malam Gado. Ya karɓi hoton MJ yana dariya cikin mugun sauti:

“Wannan saurayi, zuciyarsa cike take da tsarki da ƙauna. Amma zan shafa masa inuwa — yanda duk lokacin da yarinyar nan tazo kusa da shi, sai yaji haushi, kamar jini da toka.”



“Za ta shanye hawaye — ki shirya, domin daga yau, duniya za ta juyawa Baby baya.”



Malam Gado ya daga hayaki, ya fesa su akan hoton MJ da na Baby, sannan ya fadi wani zazzafan kalma:

“Zuciyarsa zata rufe... idonsa ba zai sake ganinta da ƙauna ba. Sai dai tsana. da baƙin ciki...”


Godiya sosai sukayiwa boka sanan suka aje tulinn kudin da sukazo da shi, sanan suka koma gida cike da tsantsar farinciki.

---

After two days 💍

Kwanaki biyu kacal bayan wannan dare, MJ ya dawo gida da fuskar da ba'a saba gani ba. Yana zaune a falo, Baby ta shigo da dariya a fuskarta tana dauke da wani zanen da ta yi a makaranta.

“Daddy, kaga na zana mu biyu... ka gani?”



MJ ya kalleta kamar wata ƙasa ce ke neman tsage masa fuska. Ya ce da ƙasƙanci:

“Na ce ki barni! Ki fita da wancan shashancin banzan naki!”



Baby ta tsaya cak, kamar wuta ta kone mata kafa. Hannunta na rawa, idanunta sun cika da mamaki.

“Daddy… me nayi maka?”



MJ ya miƙe da fushi, ya yi wurgi da zanen:

“Kin takurani! Kin dame ni! Ki fita ki barni!”



Baby ta fita daga falon tana kuka, zuciyarta na karaya, kanta na juyawa. Tun daga wannan rana, MJ ya daina mata kulawa. Ko kallonta baya yi. Kullum fuska tamkar yana kallon abinda yake ƙyama.


---****

A makaranta, ko da sauran yara suka fara ganin MJ yana guje mata, su ma suka fara tsanarta. Wasu sun fara mata dariya, wasu suna kiranta “marainiya mai bakin tabo.”

Har wasu malamai suka fara janye kulawarsu, suna nuna kyama da rashin yarda da ita. Duk da haka, Baby ta ci gaba da kokari.

Amma wata rana, bayan sun dawo daga makaranta, ta tsaya a bakin kofa, tana kallon MJ wanda ke zaune a falo ba tare da kallonta ba. Ta ce cikin muryar da ta ƙarye:

“Ka daina sona, Daddy?”



MJ bai ce komai ba. Ya cigaba da kallon TV, kamar bai ji komai ba.

Baby ta juya, tana tafiya cikin dare, hawayenta na gangarowa kamar ruwan sama, zuciyarta na faɗuwa, kamar bata san gaba ba.


---

" Wani mugun asiri na iya juyar da zuciya, amma soyayya ta gaskiya tana da darajar da ko bokaye ba za su iya murkushe ta ba Kai Anya asirine Kuwa" baby ta tambayi kanta har ta isa dakinta Daren dai yadda taga dare haka taga rana sabi da damuwa.



Baby ba ta da sauran kuzari. Duk safiyar da ta tashi, hawaye ne farkon kalmarta. Ba MJ ne ke tada ta zuwa makaranta ba. Ba MJ ne ke dakota ba. Ko lokacin da ta yi ciwon ciki a daren Juma'a, MJ ya zauna a dakin sa kamar ba komai ya faru ba.

Zuwaira kuwa sai shagwaba take a gaban MJ, tana kawo masa abinci, tana matsa masa kafafu, tana bin umarninsa da murmushi. Amma duk da haka, MJ bai taɓa nuna cewa yana sonta ba — sai dai a ce ya fi nuna mata kulawa fiye da yadda yake yi wa Baby yanzu.

Sai dai a fadar sarki, shiru ya mamaye zuciyoyi. Kowa yana mamakin sauyin MJ. Baby ta koma kamar ba a san da ita ba. Ko lokacin da sarki ya ganta zaune ita kaɗai a tsakar gida, yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, amma sai ya janye. Ba zai nuna goyon baya a fili ba, domin ya sa sharadi... Dan a tunaninsa MJ Yana nuna ko in kula akan babyne domin tasaba da rashinsa watarana.


---

A DARAREN JIYA.

MJ na zaune a farfajiyar gida, yana shan iska. Wata rana baby ta taho a hankali da takunta mai nutsuwa. Cikin riga da siket na makaranta, kanta cike da damuwa da tambayoyi. Ta tsaya gaban sa.

“Daddy…” ta ce cikin ƙasa da murya. “Ni nayi wani abu ne da ya ɓata maka rai?”



MJ ya ɗago kai, yana kallonta kamar ba ya ganinta yadda yake ganinta da. Akwai ƙara da sanyi a idonsa — kamar ba zai iya amsa ba. Ya buɗe baki da ƙyar:

“Kada ki kirani da Daddy. Ni ba mahaifinki bane.”



Wannan kalmar tamkar sara mata aka yi da wuƙa. Baby ta runtse idonta, ta ce:

“To... to meye ni a wajenka?”



MJ ya ce da ƙarfi:

“Ke? Ke ba komai ba ce! Kawai nauyi ne da aka dora min! Ammani ban saniki ba, Naga mahaifina Yana hadani dake ,kuma Yana tambayata ke bayan ni ban sanki ba, ki fita daga rayuwa ta". Ya daka mata tsawa hadi da tasowa kamai zai dake ta.



Ta juyo da gudu, ta nufi ɗaki, tana kuka kamar rai zai fita. Amma bayan ta shiga, ta rushe da kuka a kan gado, tana faɗin:

“Ba haka Daddy yake ba. Ba haka ba… Yana sona, wallahi yana sona. Me ya faru da zuciyar sa?”




---

ZUWAIRA

A gefe guda, Zuwaira tana kallon wannan fadowar, tana murmushi da girgiza kai:

“Na gaya miki ba’a karɓar zuciyar da ba taka ba. MJ zai kasance nawa — ko da da kisa ne.”



Mahaifiyarta kuma ta ce:

“Ki kwantar da hankali. Boka yace duk wata ƙauna da MJ ke ji mata yanzu wuta ce. Sai dai kallo — babu tausayawa, babu kulawa.”




---

A DARAREN KWANA GOMA BAYAN HAKA…

Baby ta soma sauya hali. Tana shiru fiye da da. Bata sake dariya kamar da ba. Wani dare ta samu wata ƙaramar takarda, ta fara rubutu da tawada mai ɗumi da hawaye:

“Dear Daddy... Na san wani abu ya faru. Ban san menene ba. Amma zan yi hakuri. Zan bar komai cikin hannun Allah. Zan girma. Zan koya. Zan jira — har ranar da za ka sake kirana ‘yar zuciyarka.”



Ta ɗora takardar cikin litattafinta. Sannan ta kwanta da hawaye a idanu, amma zuciya mai fata.


*Sarki Umar*


Sarki Umar na zaune cikin dakin karatunsa. Ya buɗe wani tsohon littafi da aka buga a kasar Andalus shekaru da yawa da suka wuce. Amma ba littafin bane a ransa — zuciyarsa na nan wajen MJ da Baby.

“Wannan yarinya… tana da wani irin haske. Amma yanzu ina ganin hasken yana dusashewa.”



Ya kalli hoton mahaifiyar MJ da ke manne a bango. Sai ya furta:

“Halinki ne ke jikin MJ. Amma ko zuciyarki za ta iya jimre da wannan azaba da Baby ke ciki? Kenason kina son baby to Amma meyasa ?.. sarki yayi shiru yanajin kodai yaje yasamu mahaifiyar MJ ya ji ko ita tasan mai ya faru a tsakanin MJ da baby har ya daina sauraronta.




---

*School*

A makaranta, Baby ta fara zama mai nisa da mutane. Duk da tana da ilimi, tana samun matsayi a ajinsu, amma sunan MJ na bibiyar ta — wasu suna cewa "Meye tsakani su da MJ?" Wasu suna cewa "Ai tana jin girman kai tunda MJ yana goyonta da can."

Sai wata sabuwar daliba, Fareeda, ta matso gareta:

“Kinyi kyau yau, Baby. Amma kin yi shiru sosai. Kin san me? Ina jin kamar akwai abu da ya dame ki.”



Baby ta ɗan murmusa, ta ce:

“Babu komai.”



Amma Fareeda ta tsura mata ido.

“ba Komai? To me ya sa idan MJ ya wuce kusa da ke, kina runtse ido kamar ki ɓalle da kuka?”



Baby ta yi shiru. Amma zuciyarta na faɗin: “Kin ce komai… Amma kin fara fahimta.”


---

A GEFE GUDA… BOKA NA RIKE DA HOTON MJ A DAKIN DUHU

Boka ya kalli MJ da ido irin na sihiri. Yana kara tsafi da gumaka da turare.

“Ka fara mantawa da ita gaba ɗaya. Za ka iya ganin ta ba tare da ka ji komai ba. Amma… akwai hadari.”



MJ ya ce da murya mai sanyi:

“Hadari?”



Boka ya ce:

“Idan zuciyarka ta taɓa tuna ta... asirin zai rushe. Kuma... kai zaka ji ciwo fiye da kowa.”



MJ ya kalli ƙasa. Sai kawai ya furta:

“Na rasa yadda nake ji yanzu. Komai ba shi da amfani. Kamar ni ba ni ba ne.”

Murmushin boka kawai yayi yace "ai Daman bakai bane daga haka ya kara matse hoton MJ hadi da cigaba da tsafetsafen sa.


---

A DAREN WATA LITININ…

Baby na dakin karatu tana ɗan rubutu da yatsanta a jikin takarda. Ta rubuta:

"Rai kamar ruwa. Kuma ni kamar jirgi ne cikin wannan ruwa. Amma daddy... kai hasken fitilar da ke kan ruwan ne. Ko da baka ganina a yanzu, ina can. Ina jiranka."



Sai ta lumshe ido. Ta janyo rigarta, ta kwanta, tana mai jin numfashinta kamar wani zazzafan yaki a zuciya.


---

A FADAR MASARAUTA...

Sarki ya kira limamin fadar asirce.

“Ina jin akwai wani abu mara kyau da ke faruwa a gidan nan. Wani abu da ya shafi MJ da Baby. Ka je ka nemo gaskiya — amma cikin sirri. Kada kowa ya sani.”



Limamin ya ce da tausayi:

“Zan bi komai da addu’a da bincike. Idan akwai sihiri, insha Allahu za mu bankado shi.”


🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺🥺


Baby na zaune a dakin ta, kanta a jingine jikin window, tana kallon sama mai taurari.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login