Showing 9001 words to 12000 words out of 21076 words
Chapter 4 - RAINON YARO BOOK 1 FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO.txt
tsaya cak.
Sarki:
“Baby — wannan yarinya da ka raina — daga yau zuwa gobe, za ta rayu a matsayin 'yar masarauta, 'yar ka, amma ba matar ka ba. Idan ta girma, ba za ku taɓa zama a matsayin miji da mata ba. Wannan ne sharadin da ke tsakaninka da gadonka.”
Zuciyar MJ ta buga! Ya dago kai da sauri kamar ba ya jin daidai. Wani sanyi ya shige shi, kamar ruwa mai sanyi ya zubo a kansa. Ya dubi Baby, tana bacci a bayansa — ba ta san da komai ba, amma rayuwarta na juyawa da wani hukunci.
MJ:
“Abba... amma…”
Sarki:
“Babu ‘amma’, abee. Wannan shine farashin matsayin da kake so. Idan ka yarda da amanar Baby — to ka yarda da ita a matsayin ‘yarka, ba wata ƙari.”
Akwai shiru mai nauyi da ya cika dakin. MJ ya runtse ido, ya saki numfashi, ya lumshe idanunsa, sannan a hankali — ya ce:
MJ:
“Na yarda. Na yarda da rainon Baby — komai farashinsa. Zan zauna da ita kamar ‘yata, zan tsare ta fiye da yadda na tsare zuciyata.”
“Zan so ta — ba don auren ta ba, sai don cewa ni nake da hakkin sanya mata dariya.”
Sarki ya ɗago sandarsa, ya danna ƙasa da ita.
“Da wannan, masarauta ta amince. Amma kada ka manta: ka ƙi auren duniya — ka zaɓi zuciyar jaririya. Ka zaɓi soyayya mai tsafta. Kada ka karya wannan alkawari.”
Hannu ya ɗaga, majalisar ta buga tambari.
MJ ya lumshe ido, Baby na bacci a bayansa — amma zuciyarsa ta sami kwanciya kamar an sauke tsauni.
To
Daren ranar ya kasance kamar bakan gizo — komai shiru, amma kowanne bango na masarauta yana ɗauke da tunani da ɓoyayyiyar magana.
MJ ya zauna a dakinsa, yana kallon Baby da ke kwance a kafadarsa. Hannunsa yana shafa bayanta a hankali, kamar yana ƙoƙarin tabbatar da cewa duniya ba za ta taɓa cutar da ita ba.
“How can I love you this much… and still have to pretend it’s just fatherly?”
“Yaya zan iya sonki haka, amma in ce wai da na raino ne?”
MJ ya furta cikin siririn murya.
Baby ta buɗe idonta, ta kalle shi da murmushin rashin sani. Ta sa hannunta ƙarama a fuskarsa — kamar ta san da rikicin da ke zuciyarsa.
---
Bayan kwana uku
MJ ya fara fita da Baby zuwa sashen sarauta, inda ake shirye-shiryen bikin cikar shekara da kafa da sabbin matasa da za a aurar da su ga ‘yan gidan masarauta. Zuwaira na daga ciki — ita da ‘yan uwanta biyu, Ameerah da Ramla.
Da zarar MJ ya shigo, da Baby goye a bayansa — dukan matan suka kafe shi da idanu.
Zuwaira:
“Kai, ni dai ban fahimce shi ba. Ya ɗaure kansa da ‘yar da ba a san asalinta ba. Yanzu duk wata kyakkyawar baiwar Allah ta zama ba ta da wurin shiga?”
Ramla:
“To ai idan baby ce matsalar, mu ma za mu iya rainon ta. Sai mu raba raino da soyayya.”
Ameerah:
“Shiru ku yi. MJ ba saurayi bane kamar sauran. Zuciyarsa ta fi soyayya — kuma irin zuciyar da ke iya ƙin buɗewa, ita ce mafi laushi idan ta buɗe.”
---.........
Wasu matan cikin masarauta sun fara nuna ƙiyayya da hassada a bayyane. A sashin da Baby ke yawan zuwa, sun fara watsa maganganu:
“Wannan yarinyar, ta fito daga ina ne? An ce ba a san iyayenta ba…”
“To ai duk mai kawo bakar rana cikin masarauta sai ta ɗauke haske!”
“Gashi ya Mujahid ya mayar da ita kamar sarauniya. Tana da karamin jiki, amma tana da babban zargi.”
---
MJ da mahaifiyarsa – Rasheeda
A wannan daren, MJ ya zauna a dakin mahaifiyarsa. Ita ce Rasheeda — ta fi kowa fahimtar zuciyarsa. Bayan ya bayyana mata komai, sai ta janyo shi kusa da ita, ta dafa kafaɗarsa.
Rasheeda:
“Kayi kamar mahaifinka. Amma kai ka fi shi — domin kai ba kawai ka tsaya tsayin daka ba ne. Kai ka yarda da rauni.”
“Baby zata girma. Zata ji. Zata gane. Kuma wata rana, zata tambaya — me yasa ba za ta iya zama matar wanda ya so ta tun tana jaririya ba?”
MJ ya ɗan sunkuyar da kai, yana kallon tabon zuciyarsa da ba a iya gani da ido.
MJ:
“Sai dai idan zuciyarta ta farka kafin nasan yadda zan ce mata 'no’.”
---
Mai Shigowa – Gari-gari
A sashin sarauta, wani bawan Allah ya shigo da saƙo daga wani ɗan sarki daga wata masarauta makwabta — ya nemi a aurar masa da Baby, domin yana da masaniyar cewa ba ‘ya ce ta jini ba.
MJ ya ji wannan labari a wajen falon sarauta.
Ya tsaya cak. Numfashinsa ya sarke. Zuciyarsa ta fara dukan da bai taɓa ji ba.
“She can’t belong to anyone else... even if she never belongs to me.”
Yarinyar har nawa take daza a fara zancen neman aurenta bayan ko jinin al,ada bata faraba "innalillahi wa inna ilaihirraju un MJ ya furta afili, hadi da kifa Kansa a bakin bed din.
Washegarin Asabar
Gari bai gama wayewa ba, MJ ya buɗe idonsa ya kalli Baby da ke kwance gefensa, tana bacci. Amma wannan baccin — ba irin na jiya bane. Sai da ya kalli fuskarta sau uku, sannan ya fahimci wani abu ya canza.
“She’s growing... And I can’t stop it.”
Ta girma... kuma ba zan iya dakatar da hakan ba.
Ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya.
A jikinsa yana jin zuciyarsa tana ce masa "kar ka manta da alkawarin ka".
Amma jikinsa na jin wani sanyi daban — kamar Baby ce ke ƙoƙarin faɗa masa "ka daina ɓoye gaskiya."
---
Ranar Lahadi
MJ ya shigo dakin Baby da kayan gyaran kai.
Ya zauna a bayanta yana yi mata kitso — da kansa.
Baby na zaune a ƙasa cikin doguwar riga, tana ɓoye fuskarta a hankali. Yau tana jin wani abu dabam... cikin jikinta na sauyawa.
Bata san dalili ba — amma zuciyarta kamar tana faɗa mata daddy ba kamar sauran ba ne.
Sai dai ta kasa fassara.
Baby (muryarta a kasalance):
“daddy… inaso ka sani, ban san iyayena ba… amma idan zan fassara ƙauna, to kaine na farko da na taɓa sani.”
MJ ya tsaya da hannunsa, ya rasa abin da zai ce. Ya dan sauke murya yana cewa:
“You don’t need to know where you’re from. Because I know where you’re going. And I’ll take you there.”
“Ba sai kin san inda kika fito ba. Ni nasan inda za mu je. Kuma zan kai ki da kaina.”
Baby ta lumshe ido, hawaye ya zubo. Amma ba na baƙin ciki ba ne — na jin ƙauna ce.
Kuma wannan hawaye ya tsaya ne a gefen kumburin idonta da ke nuna alamun ta fara jinin balaga.
---
Da daddare, MJ ya shigo da abinci, sai ya hangi rigar Baby a gefe, tana sanye da sabuwa.
Idonsa ya sauka kan jinin da ya ɓata rigar farko — ya tsaya cak.
Numfashinsa ya tsaya na biyu.
MJ (a ransa):
“The day I feared… has come.”
Ranar da na ke tsoro… ta iso.
Sai ya juya baya ya dafa bango.
Yana jin kamar yana kallon ƙaramar yarinya tana barin duniyar yara, tana ƙwanƙwasawa a ƙofar manya.
Ya dawo kusa da ita, ya zauna a gefenta, ya ce a hankali:
“Zaki iya tambayata komai. I’ll never judge you. Ever.”
“Koda tambayarki zata ɓata min rai, sai dai in amsa da ƙauna.”
Baby ta ɗago kai, hawaye a idonta:
“Yanzu na shiga duniya ne?”
MJ ya lumshe ido, ya dafa kafaɗarta:
“Duniya ta shige ki.”
---
Sashen Masarauta –
Wasu daga cikin matan sarauta sun fara jin tsoro — Baby na girma, MJ na kara nisa da su.
Suna jin wata rana zata jefa su cikin rana.
“Yanzu yarinyar nan ta balaga kenan? MJ fa zai iya aurenta nan gaba!”
“Ko da dokar Sarki tace a’a… idan MJ ya ce ‘eh’, wa zai ce a’a masa?”
“Yakamata mu yi wani abu kafin al’amari ya fita daga hannunmu.”
---MJ na zaune a gefen tagar ɗakinsa, yana kallon Baby da ke barci cikin natsuwa. Hasken rana yana daddafa fuskarta kamar Allah na shafa mata albarka da haske.
Ya dafa kansa a hankali, yana furta da zuciya:
"Allah Ka sani… ba wai ina sonta da wata manufa ba. Ina sonta ne kamar yadda zan so rainon da na shuka da hannuna — wanda na zuba jini da hawaye akai."
Ya mike, ya rufe labulen. Kamar yana ƙoƙarin rufe zuciyarsa ne.
---
A Dakin Mahaifiyar MJ –
Yau MJ ya kai Baby sashen mahaifiyarsa, momy domin ya tafi wani taron sarauta.
Momy ta zauna tana kallon Baby da dariya da ƙauna a idonta.
Momy (cikin murmushi):
"Wannan yarinya... tana da ƙwazo. Kuma tana da haiba. Kamar ita za ta cika wannan gidan da farin ciki da zaman lafiya."
Baby ta ɗago kai:
"Umma… daddy yana sona ne?"
Momy ta daka mata Kai da murmushi:
"Abee ya fi ƙaunarki fiye da yadda za ki fahimta. Amma ki sani… ƙaunar da ba ta da sharri ce za ta rike masarauta."
“Kada ki bar zuciyarki ta wuce inda hankalinki bai kai ba.”
Baby ta sunkuyar da kai, sai ta ce:
"Ina jin kamar ni ba kamar sauran yaran masarauta ba..."
Momy ta jawo ta jiki, ta ce:
"You don’t need to be like them. You are chosen differently."
“Ba sai kin zama kamar su ba. Allah ya zaɓe ki daban.”
---
MJ
Yana dawowa daga taro, MJ ya tarar da Baby na barci a ɗakin mahaifiyarsa.
Ya tsaya yana kallonta na wasu mintuna, sannan ya zauna yana shafa gashinta da hannunsa.
MJ (a ransa):
“You are still a child. I will guard that truth with my life.”
“Ke har yanzu yarinya ce. Zuciyata zata kare wannan gaskiya har abada.”
Ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya — irin wadda ke ɗauke da gagarumin alƙawari: ba soyayya, ba sha’awa — sai dai kariya da amana.
---
Rashin Jin Daɗi Daga Wasu Matan Masarauta
A bangaren matan masarauta, tsoro da kishi na ƙaruwa. Gani suke kamar MJ ya fi kowa kulawa da Baby.
“Ta ina MJ zai auri wata daga cikinmu, idan har zuciyarsa tana gefen yarinyar nan?”
“Yakamata mu nemi Sarki ya tsawatar masa. Wannan rainon ya fara zarce gona da iri.”
---
MJ & Sarki Umar
Sarki ya jawo MJ gefe, yana kallonsa da kulawa da nisa.
Sai ya ce:
"Ka tuna da sharadin da na baka, Abee Zaka iya kula da Baby har abada — amma ba za ta taba zama matar ka ba."
"Do you still stand by that promise?"
MJ ya daga kai da kwanciyar hankali:
"I still stand, Abba. I’m her guardian, not her groom."
"Ni mai kare ta ne — ba mai neman aurenta ba."
Sarki ya kalli idonsa da zurfi, kafin ya ce:
"If you can keep that boundary till the end, then maybe you’re stronger than I ever was."
“Idan har zaka iya kare wannan iyaka har ƙarshe, to ka fi ni ƙarfin zuciya. Huce ka tafi Abee Allah yayi Maka albarka "
°°°°°′°°°°°′°°°′°°°°°°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Wata rana da asuba, MJ ya tashi daga barci, ya juya ya kalli gefen gadon inda Baby ke kwance cikin rigarta ta riga da wando, tana barci cikin salama, hannunta na rataye a gefen pillow. Hasken fitilar bango na haskaka yatsunta kamar ana tsaga lu’ulu’u da rana.
Ya lumshe ido ya furta da zuciya:
“Yarinyar nan tana girma… kuma tare da kowanne girma, zuciyata tana ƙara tsorata.” yanzu baby baro dakin ki kikai kika dawo Nan, kash ni bansan yazan yiba yanzu fa TA girma Amma nakasa rabata da gangar jikina ,domin tasaba kwanciya a gefena tanajin dumina tamkar na uwa."
Ya mik’e, ya nufi toilet don wanka. Har ya fito ya shirya cikin farin shadda da hula mai launin sarauta. Daga nan ya kama gyaran gashinta — ya fara taje kanta da kulawa da lallashi. Duk sanda ya samu ƙulli, sai ya ja da sauƙi, yana cewa:
“Ki daina motsi mana Baby, ba so nake ki ji ciwo ba.”
Baby ta langwabar da kai a kafadarsa tana dariya.
"Kai ne daddy, ka fi ko wane gyaran kai da taushi.”
Ya murmusa, zuciyarsa na ɓoye wani abu mai nauyi — tsoron lokaci.
---
YAYIN DA BABY KE GIRMA...
Kwanaki sun ja. Watanni sun shude.
Baby ta fara nuna alamomin balaga. Jikinta na sauyawa da ƙanƙanin zane, murya na canjawa da laushi da tsawo. Amma abin da ya fi firgita MJ shine... tana fara ganin jini. Al’ada a Karo na biyu ta zo mata a rana da aka shirya babban liyafa a masarauta.
Tana cikin ɗaki ita kaɗai, tana kuka, tana cewa:
“Na ɓaci… daddy zai tsaneni.”
Amma kafin ta gama maganar, MJ ya shigo da kulawa, yana ɗauke da abin tsafta da gyaran kai da sabuwar rigar bacci.
Ya durƙusa gabanta, ya kama hannunta:
“Baby, wannan ba cuta bane. Wannan alama ce cewa kina girma. Kuma ba komai bane a ciki sai alfahari. You are becoming a woman, and that’s okay.”
Ya share hawayenta da tissue, sannan ya ce:
“Zan koya miki yadda za ki kula da kanki. Amma ki sani — ko kin zama budurwa, ko kina yarinya — ni har yanzu daddy ɗinki ne.”
Baby ta kalle shi da wani irin natsuwa da tsantsar amincewa. Sai ta jingina da kafadarsa ta ce:
“Na tsorata daddy… amma na fi tsoron rashin jin daɗinka.”
Ya shafa gashinta:
“Bana jin daɗin duniya, sai dai idan kina murmushi.”
---
🕊️ RAINON YARO
Chapter 6,
A gefe guda kuma, masarauta ta fara lura da girman Baby. Kallon da ake mata ya fara canjawa — daga na raino zuwa na tambaya da tsoro.
“Wannan yarinya tana girma da kyau. Idan MJ bai kange zuciyarsa ba, masarauta za ta shiga rikici.”
“Yakamata a maida Baby wani wuri kafin zuciyar MJ ta fita daga layin alkawari.”
Sarki Umar ya zauna da MJ a daren ranar, bayan sallar Isha’i.
Sarki:
“abee, ka lura cewa lokaci yana ƙara jefa zuciyarka cikin jaraba. Baby ba ƙarama ba ce yanzu. Har wani daga cikin masu sarauta yana cewa ka fi dacewa da ita fiye da sauran.”
MJ ya sunkuyar da kai, ya ce:
“Na san hakan. Amma har yanzu zuciyata bata saba da cutar da amana ba. I promised to protect her, not to touch her.”
Sarki ya dan lumshe ido:
**“Good. Amma idan zuciya ta fara jin wani abu, ka gaya min — kafin duniya ta gane kafin kai.”
"In sha allah ranka shi dade" daga haka ya mike ya bar gurin.
Masarautar tana da tsarin da ba kowanne zai iya jurewa ba. Duk inda Baby ta wuce, idan ba kallon mamaki ba, to kallon tsana ne ke binta. Amma duk da haka, MJ bai bar hakan ya tsorata shi ba — balle ya rage kulawar da yake mata.
Wata safiya kamar kowace, Baby na tsaye a bakin gado tana kokarin daura ɗamarar jakar makaranta, sai MJ ya shigo da murmushi.
"Let me help you with that, princess."
Ya durƙusa ya ɗaura mata ɗamarar, sannan ya gyara zip ɗin rigarta da hannunsa a hankali. Sai ya dafa kanta kamar yadda ake shafa albarka.
"You’ll do well today, I can feel it."
Baby ta gyara tsayuwarta, ta zuba masa ido, sai ta ce a hankali:
“Thank you… daddyna.”
Ya ɗan lumshe ido cikin jin daɗi. Wannan kalma "daddyna" ta fi masa komai. Kamar kalmar da ta tabbatar da alkawarin da ya ɗauka shekaru baya.
Yana kaita makaranta da kansa. Hatta idan yana gajiya, ko yana da taron masarauta, Baby na da fifiko. Suna zuwa tare, suna dawowa tare.
to bayan wani lokacin MJ ya je ya dakko baby daga makaranta ,suna dawowa yaga 'yan matan masarauta sun tsaya a kofar ɗakinsa — su Hajja Zuwaira, Hauwa’u da Salamatu. Suna kallon Baby da dariya mai ma’ana.
"Oho! Ga sarkin uwa da diyarshi sun dawo." "Ai kamar ita ce ‘yar ce da za a raina mu da ita nan gaba!"
Zuwaira ta ce da ihu kamar tana barkwanci amma Baby ta fahimta. Kamar yadda MJ ya fahimta. Amma MJ ya daure fuska.
“Zuwaira, if I ever hear that again, even jokingly — I’ll report you to Daddy.”
Zuwaira ta yi dariyar rainin hankali, amma ta ja jiki. MJ ya kama hannun Baby suka wuce ciki.
---
°°′°°°°°°°°°°°°°°
Washe gari Baby ta shigo ɗaki da kuka. MJ yana duba wasu takardu ne, ya juyo da sauri.
"What happened? Did someone hurt you?!"
Ta girgiza kai tana sharce hawayenta, ta ce:
"No… amma daddy jini Yana fito… daga… daga can…"
MJ ya dafe kansa. Yana matukar sanin wannan lokaci zai zo, amma bai shirya ba. Bai da wata mace kusa da su da zata koya mata ba. Yana tsaye cikin rudani,gashi Karo na uku kenan Yakasa fahimtar da ita tunda yanzu ita TA girma b yarinya bace, sai ya kira mahaifiyarsa.
---
Mahaifiyar MJ, Hajiya rasheeda, ta iso da sauri. Da zarar ta fahimta me ke faruwa, ta rungumi Baby da kulawa da tausayi.
"Kar ki ji komai yarinya… wannan alama ce kina girma. Zaki zama mace mai daraja."
Ta dubi MJ ta ce:
"Kai kuma, ka tsaya gefe. Wannan aikin mata ne."
MJ ya yi dariya da sauke ajiyar zuciya. ya ce “Alhamdulillah, an ceto ni.”
Daga wannan rana, Hajiya rasheeda ta fara ba Baby darasi kan yadda mace ke girma da tsafta. MJ kuwa ya rage shiga lamarin jikinta kai tsaye, amma soyayya da kulawarsa sai karuwa suke.
---
Kulawa Mai Narkar da Zuciya
Kullum MJ ke ɗakko ta daga makaranta da kansa. Idan yana da lokaci, yana jiran ta fito. Idan ba zai iya ba, sai ya aiko da wani amintaccen masarauta. Amma kullum da ta dawo, tana samunsa a gida da ruwa mai sanyi da ’ya’yan itatuwa. Yana karanta mata littafi, yana mata lacca akan karatu, rayuwa da juriya.
“Your mind is your sword, Baby. One day, the world will try to cut you — but your mind will protect you.”
---
*Bayan wasu kwanaki*
Wata rana da suka dawo daga makaranta, Baby ta buɗe jakarta tana neman wani takarda, sai MJ ya lura tana ta kai-da-kawo cikin ɗan rudani.
“Where’s your assignment?”
“It’s... it’s not here,” ta ce da murya mai rauni, “Salamatu ta cire min shi aji tana cewa 'ya'yan karuwa ba sa karatu.'”
MJ ya dafe kansa, zuciyarsa na tafarfasa. Bai yi magana ba sai da ya juyo gareta, ya zauna a gefenta, ya dafa kafaɗarta.
“You are not what they call you, Baby. And you will never be. Your name is dignity.”
Ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da tsawa. A cikin dare, MJ ya rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban makarantar da kwafin ta zuwa ga mahaifinsa, Sarki Umar. Washegari Salamatu ta samu kiran gaggawa daga gidan Sarki — kuma daga wannan rana, an dakatar da cin zarafin Baby a makarantar.
---
Duk da cewa Baby tana rayuwa cikin masarauta, tana ci da 'ya'yan sarki, tana saka irin tufafin ’yan masarauta — amma ba su taba yarda da ita a ransu cewar ita 'yar masarauta bace.
“Yarinya mai dogon buri,”
“Shi MJ ya raini kansa