Showing 3001 words to 6000 words out of 21076 words

Chapter 2 - RAINON YARO BOOK 1 FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO.txt

suka hau mota, zuwa airport.




In the night 🌉

A wani dare, ina zaune a gefen Baby tana bacci, sai na ji kamar zuciyata na cika da tambayoyi.

Shin me ke faruwa da ni?
Shin ina rike wani abu da ba nawa ba?
Shin mafarkin da na gani yana nufin wani abu ne?
Shin Baby ba yarinyata bace?
Ko kuwa ita ce, kuma kawai duniya na kokarin kwace min ita?



Na kalli hannunta — ƙarami, mai dumi, da ɗan zafi kadan.
Sai na ruƙe shi da lafazin da ya fito daga ranta — ko da bata furta ba:

“Ka rike ni, dadyna… ni zan tsaya da kai.”


Sai na furta:
“Ko wacece ke — ’yata ce a zuciyata. Kuma idan duniya na so ko ba ta so, wannan ba zai canza ba.”


Sake rungumota yayi Yana cewa "yanzu kenan yazanyi ni yarone meyasa har yanzu matarnan bazata dawo ba, ai ba haka mukayi da itaba , meyasa zataminn haka har iyayena su soma zargina akan ko nayiwa wata cikine?"


Kara gyra kwanciya ta nayi Ina kallonta tana barci, hannunta na kan kirjinta, tana numfashi a hankali kamar furucin wardi. Baby ta yi sanyi, amma zuciyarta bata daina zafi a raina ba.

Kullum idan na kalle ta, nakan manta ni saurayi ne da burin kammala makaranta, neman rayuwa, da mafarkar nasara.

Yanzu mafarkina shi ne ta buɗe idonta, ta ganni — ta gane ni.


A haka bacci mai nauyi ya daukeni.


***********†***********

In the morning..... Misalin karfe' 9 na safe

Yau zan kai ta wajen wata mata mai suna Maman Gambo, wata tsohuwa ce da ake kira da yar gani da faɗi. Duk da ban yarda da dukkan maganganun mutane ba, amma zuciyata ta tura ni.

Na zauna a gabanta, Baby na hannuna. Tsohuwar ta ɗauki lokaci tana kallona. Sai ta ce da kakkausar murya:

“Wannan yarinyar ba ta zo maka ba don ka cika rayuwarka — ta zo ne domin ta fara taka.”



Na girgiza kai.

“Ban gane ba…”



Ta ce:

“Zaka gane. Amma kada ka yi saurin tambaya. Sirrin da bai kai lokacin bayyanarsa ba — idan ya fito, sai ya tarwatsa gaskiya, kuma kadaina tunanin cewar bazaka zauna da ita a masarautr kuba, zaka zauna da ita acan Amma masifar da kake cikin ayanzu na tuhumar da mutane suke Maka ayanzu tafi Maka sauki ,akan wadda zaka tarar a masarautar sauba.”





Lokaci guda jikina yayi sanyi batare da nasake cemata komai ba na mike na saka baby a bayana ,sanan na dakko zanin danake goyata a gefe na daureta kam, kamar mace ,Na tafi da wannan magana a zuciyata, cikin dare mai duhu da rana mai zafi.
Ina zaune a ƙarƙashin bishiyar mangwaro, Baby na barci, sai wata mace ta zo ta tsaya a kaina da kallo mai zurfi.

“Wannan yarinyar ba taka bace.”
“Ina kika san haka?”mj ya tambayeta cike da mamaki.
“Idan kai ne mahaifinta, da ba za ka kalli idonta da wannan tsoron ba.”
“Ko kuma ni uba ne da zuciya…” na amsa a raina, ban faɗa ba a fini.



Ta juya ta tafi, amma kalmarta ta barni da tambaya gaba daya so suke su haukatani ,nakasa Gane shin aljana nake rainon ko mutum, meyasa nake yawan mafarki ,meyasa nake ganin kamar aljanu na bibiyata?"


Ganin Babu Wanda zai bani amsa yasa na mike na koma cikin gida ,baby na sauke a kan kujera na dakko mata Madara na Mika mata, ita Kuwa sai murmushi take baiwar Allah tana kallonsa kamar mai shirin fadamin wani bu, bance mata komai ba na mike nashiga daki, jakata na dakko na fito da wani book na felli faifa guda Daya ,sanan na dauki biro na dawo na zauna kusa da baby na soma rubuta wasiƙa — ba don wani ba, sai don Baby.
Wasiƙar da za ta karanta wata rana idan ta girma. Ko kuwa… idan ta gano wacece ita.

“Baby,
Ba na da tabbacin daga ina kika fito,
Amma na tabbata cewa kin fito daga inda Allah ke ajiye zuciya,
Domin tun lokacin da kika zo, ban sake sanin kaina ba —
sai dai sanin ke, ina ji ajikina ke kyau ta ce daga Allah ,Kuma nayi alkawarin cewa koda zan karar da numfashi nazan raineki da soyayyata, .” daga haka ya rufe' takardar ya ajiye gefe guda, sun kuyawa yayi kamar mai yin rarafe baby ta hau yashiga jankafa Yana mata doki, suna wasa ita Kuwa sai dariya takeyi.



**

Washegari na koma makaranta, sai malamai suka ce:
“Kai ne saurayin da ke zuwa da jaririya a hannunsa?”
“Yanzu kana rainon yaro?!”
“Ka ajiye rayuwarka don wata yar tsana?”



Nai murmushi. Sai kawai na ce a raina:
“Eh, don wata yar tsana ce — amma ita ce ta sake sosa ni, ta gyara ni, ta sake gina ni.”



Na san ba kowa zai fahimce ni ba. Amma ba don su nake rayuwa ba — don Baby nake ƙoƙari.

“Wata rana, sai ku gane cewa akwai nauyin da ba’a iya shi da jiki — sai da zuciya.”


Daya daga cikin malaman nawane ya dakamin tsawa "ya Isa Mujahid kada kaga Kai Dan sarkine kanemi ka fada mana duk abin da yazo bakinka ,ka kula mu malamanka ne Kuma iyayenka,

Wannan yarinyar da kake raino masiface a gareka, ta hanaka komai karatu kadaina kacan rayuwarka zuwa kamar ta mace kullum Kai da goyo abaya ,Anya kana cikin hayyacinka Kuwa, haka jiya kayi asarar exam kawai sabi da wannan abar....


Saurin katseshi MJ yayi dacewa Indai ina raye komaine zai iya aikatawa akan baby" daga haka ya fice daga office din.

Kai tsaye ban koma cikin class ba ,na dawo gida, ina dawowa na shirya ma,aikatana suka rakani kasuwa domin yin siyya,sosai nasha wahala lokacin da na Isa kasuwa, ganin yadda kowa ke kallona da mamaki yadda naci damara da zanyi da baby a goye a bayana masu gadina Kuwa, kowanne zuciyarsa cike take da bakincikin yadda nake zubar da ajina a ko ina, a haka dai har na Kammala siyayyata Babu abin da ya dameni ,muka taho



Muna dawo daga kasuwa da Baby — na siya mata wasu riguna 'yan rago da turare mai kamshi. Sai dai abinda na fi saya yau, shi ne abin da ba a sayarwa — hasashen cewa lokaci yana kokarin bayyana sirri.
Yau babyna ta soma zuwa makaranta kullum ni nake kaita na dawo da ita sabi da na kaitane akwai don ta huta itama badan karatu ba, tun da dai shekarunta basu Kai ta soma zuwa school, nakai ta makaranta domin Nima nagaji da zancen da ake akaina ,ko ina kashiga sai kaji ana gulmata.


To yau ma kamar kullum bayan baby ta dawo daga makaranta
A ɗaki, ina wanke rigunanta sai na ji kamar wani abu ya fito daga gefen jakar da ta zo da ita. Wani ƙaramin envelope ne, fari fat-fari, an nade shi sosai. Ya shige cikin ramin zipp ɗin da har yanzu ban taba buɗewa ba.

Na buɗe a hankali. Hannuna na rawa. Zuciyata na bugawa kamar karar ƙaho.

A ciki, akwai hoto — hoto na mace da Baby tana jaririya sosai a cikinta. A bayan hoton, an rubuta da ink mai launin shuɗi:

"Idan wannan ya kai hannunka, to nasan kai ne — wanda zai iya riketa har zuwa ƙarshen gaskiya."
"Ka riƙeta — har zuwa inda zata gane kanta."



Na shaƙi hoton. Na ji kamar numfashina ya canza. Na kalli Baby, tana barci… amma kamar tana motsa bakin ta cikin mafarki.

Na ce a hankali:

“Wacece ke a gaske, Baby…?”
“Shin ni Allah ne ya ɗora wa amanarki — ko kuwa duniya ta jefa ki a raina don wata ƙaddara?”
“Shin ina wannan matar ta shiga ta ajiye ki — ko kuwa rayuwa ce ta ƙwace ki daga hannunta ,mai take nufi tana nufin naci gaba da rukon ki, mai na iya mai zan miki ,ko ta manta da cewar ni yarone mai kananun shekaru?"


🕊️ RAINON YARO

Chapter 3


**

Tun daga wannan rana, nake ganin mafarki iri ɗaya.

Ina zaune da Baby a bakin rijiya.
Wata mata ce ke tsaye a bayanmu tana kuka, tana cewa:
“Mujahid… ka riketa kafin su dawo.”
“Kar ka faɗa wa kowa komai. Komai.”
“Idan ka faɗa — zata ɓace da sirrinta, sanan zasu kasheta da ranta,domin basa da Imani..”



**

Ina farkawa da zufa. Sai na duba inda Baby take — tana nan, amma kamar numfashinta na haɗa da wani sirri. Sai nakan furta a hankali:
“Wannan ba kawai raino ba ne — wannan alƙawari ne.”
“Ni zan kareki — ko da kuwa ba zan taɓa gane wacece ke ba.”



Hannu nasaka na jayo baby jikina Sannan na kara kanka meta da karfina ,hadi da lumshe ido ina tunanin abin da zaije ya dawo.


"Lokaci yayi nakusan Kammala karatuna yanzu yazanyi kenan ,ta ina zan fuskanci su Abba da maganar su barni na zauna da baby a masarautar mu"


MJ yasake lumshe ido hadi da sa hannu yashiga shafa kwantaccen sumar kan baby.


Ina jin dumin jikinta kamar wuta a cikin sanyi. Duk lokacin da na lumshe ido, numfashinta yana shigowa cikin zuciyata kamar kalmar da ba a taɓa faɗa ba amma na fi kowa fahimta.

“Baby... ke kadai ce da kika yarda da ni a lokacin da duniya ta kalli rainona a matsayin laifi.”



Na lumshe idona sosai — sosai har sai da hawaye suka latsa gefen kuncina. Ba kuka bane na karaya, a’a. Wannan hawaye ne na soyayya, hawaye ne na alƙawari da niyyar kare rayuwa.

Na zura hannuna cikin mayafin da na lullubeta , na shafa gashinta mai laushi. Ina nishi kamar wani ƙaramin jariri da bai san ko ina bane, amma ya yarda da numfashin mahaifinsa a matsayin amana.

“Zan kasance wurinki, Baby... ko da kuwa na rasa komai.”


👑👑👑👑👑👑
Lokaci ya tafi. Kwanaki sun zame min kamar watanni. Karatuna ya kusa ƙarewa, amma kuma zuciyata tana ɗaure da wata tambaya da babu wanda zai iya amsawa sai Abba.

Ta yaya zan je gaban Abba in ce masa 'ka barni na kula da yaron da na haifa tun kafin a bani damar aure'?

Sassanyar iska ta daki labulen dakin. Sai da ya girgiza, ya shafe fuskata da danshi. Sai na yi dariya — irin dariyar da yake da kyau amma kuma cike da ɗaci. Baby ta motsa a jikina, sai na kara matseta, na dan busa mata iska a kai kamar zan kore mata duk damuwa.

“dady... ka tashi kai min labari?

Yaji muryar baby tana magana cikin gwaranci.



Ban san yaushe ba, amma na soma jin wani zafi a kirji — zafin soyayya ce. Irin wacce zata sa ka fuskanci duniya baki ɗaya domin mutum guda. Wata zuciya ce ke furta min cewa:

“Ka je gaban Abba. Ka zauna. Ka ce masa ka fi kowa sanin darajar wannan yarinyar.”



Sai na furta a hankali:

“Zan tsaya tsayin daka. Domin wannan ba raino bane kawai... wannan kalma ce: Zan zama uba kafin a bani damar zama miji.”



Wannan shi ne karfina. Wannan shine mafarkina.

Ina so a karanta labarin RAINON YARO a ce:

“Wannan ba littafi bane — zuciya ce da take rubuta kanta da hawaye.”


****************




---Washegari da safe, MJ ya farka da kukan baby yana ƙara sama da ƙasa. Kamar wata ƙarar ƙararrawa ce da take faɗakar da zuciyarsa cewa lokaci na tafiya, kuma ba za a iya tsaya masa ba.
Ya ɗago da gajiya, cikin wani irin yanayi na tunani ya rungume baby kam a kirjinsa yana shafa bayanta a hankali kamar yana mata sannu da safe da ƙauna.

"Shhh... Daddy's here. No one will ever hurt you. Not while I still breathe."



Sai MJ ya nufi gaban madubi. Idanunsa jajaye, alamun rashin barci da damuwa. Ya dafa kan madubin da hannunsa guda, ɗayan hannun na goye da baby. Ya kalli kansa, ya furta:

"What kind of father am I if I let fear make my decisions?"
“Ni zan iya tsayawa in fuskanci masarauta saboda yarinyar da na haifa. Sai me?”


Dawowa yayi bakin gadon ya zauna Sannan ya sakko da baby daga bayan sa yace:

“Ni ba wai na yanke shawarar zama uba bane. Allah ne ya bani wannan damar. Kuma bazan tsaya gefe ba in zuba ido.”



“Sometimes, love is louder than bloodline. Kuma wuta ta ƙauna ce kadai ke iya kone dambar masarauta.”



Cikin zuciyarsa:
Yasan cewa a yau ne zai fuskanci Abba. A yau ne zai ce:

“Ku bani damar zama da baby da na raina — ko da kuwa hakan zai sa ku kore ni daga gado, daga masarauta, daga tarihi.”



Sai MJ ya ɗauki baby ya ɗago ta sama, tana dariya mai cike da hawaye:

"You are not a mistake, my daughter. You're the reason I'm brave."
“Ke ce ƙarfin zuciyata, baby... Ke ce RAINON YARINYAR DA YARO KAMATA YAKE RAINA..”



[Yau – 8:00am | Gaban Gidan mj]

Hasken safe ya ratsa tagar dakin MJ. Iskar safe tana busawa cikin sanyi da nishadi. MJ ya fito cikin farin kaya masu tsafta, kansa a lulluɓe da hula mai launin zinariya. A bayansa, Baby ta kwanta a cikin baby carrier, tana baccinta da kyakkyawar fuskarta da kwalliyar fuska irin ta su MJ.
sannu a hanakli
Ya sauka daga step ɗin gida, ya zuba ido sama, ya furta:

“Bismillah. Wannan ba tafiya ce kawai ba. Wannan dawowa ce. Dawowa cikin tarihin da zan gina da hannu na.”



9:35am | Filin saukar jirgin saman masarauta

Jirgin su MJ ya sauka cikin sanyi da sheƙin sarauta. Masu gadin masarauta suka nufi inda aka bude kofa suka matsa gefe cikin girmamawa.

Da MJ ya sauka, kaya masu sauƙi ne a jikinsa amma kamanninsa sun kai da nisa – kyan fuska, nutsuwa da nutsuwar zuciya. A bayansa, Baby na kwance, har yanzu cikin bacci. Sai murmushi kawai ke sauka a fuskarta kamar tana mafarkin amininta MJ.

A cikin masarauta kuwa...

Da MJ ya taka ƙasa, kowa ya tsaya kallonsa. Masu gadi, bayin fada, hatta manyan dattawan fadar suka kalli goyon a bayansa da mamaki.

“Subhanallah, wannan ne ɗan Sarki da yake shan wahala da ɗiya?”
“Goyo fa! Cikin masarauta?”
“Innalillahi... Irin wannan tausayi ne sai mutumin Allah!”



Matan sarki suka fito da alkyabba da mayafi, kowacce da kallon mamaki da kishi a idonta.

Matar Sarki gimbiya zubaida ta harare shi, amma daga bisani sai ta ce:

“Toh haka za a bar wani namiji ya shigo da jaririya kamar wata matar shi? To wallahi bazan ta sabuba"






Sittatu, wata matashiya da aka tanada domin auren MJ nan gaba, ta buɗe baki da kishi:

“ya Mujahid da kuka ce zai zama sarkinmu bayan karatunsa, ashe tun yanzu yana da amarya da baby? Wallahi ba zan iya ba Kuma bazan yarda ba.”



Zuwaira,wadda duk cikin su tafisu hatsari da masifa ta ce cikin sassauƙan murya:

“Amma ku duba yadda yake goyo kamar uwa. Haka kawai zuciyata ke kiransa da mijina.to wallahi ko wace ta mallaki abin da ba nataba sainayi ajalinta "zuwaira ta fada Rai a bace.



MJ kuwa yana tafiya cikin nutsuwa, bai duba hagu ba ko dama. Baby na cigaba da baccinta, idonta a lumshe, kamar tana karatun zuciyar MJ ne.

Sarki ya kalli MJ daga nesa, ya furta a ransa:

“Wannan yaron ba karamin sauyi yayi ba. Ya dawo mana da zuciyar jagora. In har zai iya kare jaririya, zai iya kare masarauta, bana ce muddum zai zauna da wannan jaririyar sai dai ya zaba komu ko ita ba, to mai yakawosa? Saiki ya furta a zuciyarsa Rai a bace.



A hankula MJ ke takowa zuwa gaban abba. Zaune suke a babban falon masarauta. Gidan ya cika da shiru mai nauyi, irin wanda yake kashe kuzari. Kowane bango yana da tarihin sarauta, kowace kujera na da nauyin da ake so a ɗora wa kai. MJ yana tsaye, yana fuskantar mahaifinsa — Sarki UMAR, wanda ke zaune cikin cikakken kaya na sarauta, hannunsa a jingine bisa sandar mulki.

Idanun MJ sun cika da natsuwa amma cikin zurfin shawara. Ya durƙusa, ya gaishe, sannan ya ce:

"Abba, yau ban zo matsayin ɗa na sarki ba. Na zo matsayin uba. Wani uba da yake neman hakki."



Abba ya kalle shi ba tare da motsi ba, sai kuma ya girgiza kai kaɗan.

"Ka san cewa duk wanda ke cikin gidan sarauta, ba shi da ‘hakkin kansa’ gaba ɗaya. Hakkin masarauta yafi nashi."



MJ ya haɗiye yawu. Ya haɗa hannayensa, ya matse su kamar yana da abin da zai fashe dashi idan bai furta ba:

"Na ɗauki yarinyar nan da hannuna. Na raine ta cikin dare da rana, hawaye da dariya. Ba raino kawai bane, Abba. Wannan amanar zuciyata ce. Kuma ko duniya zata ce ba nawa bane, na riga na ce — NA SA ta A ZUCIYA."



Abba ya ɗan ƙara ƙarfafa muryarsa:

"Wai kai ka manta da dokar masarauta? Duk wani ɗa da ba'a haifeshi da sunanmu ba, ba zai shiga cikin gado ba. Ba za a karɓe shi cikin zuriyya ba!"



MJ ya ɗaga kansa, cikin nutsuwa amma da ƙarfin zuciya:

"To idan haka ne, na fi son in rasa gado, amma in samu zuciya. Baby tana da ni. Kuma hakan ya isheni fiye da komai."

🕊️ RAINON YARO

Chapter 4



Sarki ya zuba masa ido... har ya sauke ajiyar zuciya. Kamar zuciyarsa na faɗuwa da sautin gaskiya da tausayi daga bakin MJ. Sai ya ce:

"Kayi kama da mahaifinka fiye da yadda ka sani. Ni ma na yi haka da mahaifina saboda mahaifiyarka..."
"...amma ka sani, Abee,zuciyar sarki tana da wuta da ruwa. Kuma kai kake da zabi wanne ka zuba.”



MJ ya durƙusa, idanuwansa sun kada, amma ba ya kuka. Sai ya ce a hankali:

"I will choose love, Abba. Even if it burns me."
“Zan zabi ƙauna, ko da kuwa wuta za ta ƙone ni.”



Abba ya ɗago sandar mulki, ya ɗan doka ƙasa da ita a hankali. Sannan ya ce:

"Ka tashi, abee. Ka cigaba da rainon yarinyar ka. Amma ka sani, daga yau kai ubanta ne a rubuce da Kuma fili da boye. Idan ka fadi — masarauta ce ta fadi. Idan ka yi nasara — to zuriyarka zata cigaba."



MJ ya miƙe, ya lumshe ido — da yarda, da godiya, da kwanciyar zuciya.


--MJ ya miƙe a hankali, kamar an ɗebo nauyin duniya daga kafaɗunsa. Ya juya, sai idanunsa suka sauka kan wata ƙaramar yarinya wacce take zaune a gefe, tana wasa da sandar tambarin sarauta da MJ ya bari lokacin da ya shiga.

Baby.
Jininta. Numfashinta. Hankalinta da zuciyarsa tamkar an daure su da igiyar rayuwa guda.

Ya taka zuwa gareta, ya tsuguna yana fuskantarta. Sai ya sanya hannunsa a kumatunta, yana murza fuskarta da murmushi mai nauyin albarka.
“Let’s go home, Baby. Home is where love raised us.”



Baby ta kalleshi, ta ɗaga hannayenta biyu kamar tana neman tsira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login