Showing 1 words to 3000 words out of 21076 words

Chapter 1 - RAINON YARO BOOK 1 FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO.txt

🕊️ RAINON YARO

BOOK ONE
Chapter1


✍️ Hafsat Umar Dangoro (SAFHAT)


---

🌟 KASHI NA FARKO

“Rayuwa tana da sirri. Wasu ana haifarsu don su rayu, wasu kuma ana rayuwa da su.”




---

✨ MARUBUCIYA

SALWA
AFNAN
AMATULLAH
MARATUS SALIHA
BABBAR SAKAYYA
DEPRESSION
BABANA NE SILA
UMMU AMANIH
ZUCIYATA
BURINA MU, AZZALUMI
MECE RAYUWAR?
BA MAHAIFIYATA BACE
RAYUWAR KASKANCI
E.T.C


---

💎 JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION

(SADAUKARWA GA: MUJAHID)

To Mujahid, jarumi ne cikin duka, wanda da sunansa nake kiran karfi da kwarin gwiwa. Wannan littafin na musamman ne gare ka — kaine farko, kai ne gata. Allah ya kara maka haske da albarka a rayuwa. Ameen.


---

🕊 GODIYA

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah (ﷻ), Mahaliccin zuciya da fasaha. Mai bayar da iko da kaifin tunani. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (ﷺ), wanda shi ne ginshikin rahama a doron ƙasa.
Na gode wa masoyana, masu karatu, abokan shawara, da waɗanda suka bani goyon baya cikin shiru da addu’a. Ku ne hujja akan dalilin da yasa nake rubutu da bege. Ina alfahari da ku.


---

🎨 KIRKIRA

Littafin RAINON YARO ƙirƙirarren labari ne. Duk wani suna, masarauta, ko al’amari da ke cikin wannan littafi na soyayya, sirri, da gwagwarmayar zuciya — dukkansu ƙirƙira ne da nufin nishaɗi da ƙarfafa zuciya. Idan ya yi kama da rayuwarka, to ƙaddara ce ta labari, ba da gangan aka yi ba.


---

....._*🌒بسم الله الرحمن الرحيم🌒*_




Wata rana...



wata rana da ba zan taɓa mantawa ba. Rana ce da na buɗe ƙofar duniya da hannu guda, na tare bakin wahala da kafada ɗaya, kuma na rungumi jaririya — a lokacin da ban kai shekaru goma sha bakwai ba.

Sun ce namiji baya kuka. Amma jiya na kuka. Na yi kuka kamar yaro. Ko da yake... ni yaron ne.

Zaune nake a bakin bed din idanuwana a lumshe ,hannayena Kuwa gaba kidaya na Dora kan kunnena na rufe, alamar banason Jin karar da take tashi,gefe guda Kuma jaririne a lullube da zani sai faman ihu yake da alama yana bukatar mahaifiyar sa, tsaki naka na zaune a gefan gadon rai a bace,


Jikina Babu kwari nake taka kafata har na isah zuwa Inda jaririn yake, a hankali nasamu guri na zauna a gefan gadon hadi da Mika hannu na dauke ta, kekkewar yarinyar da a kalla bata huce shekara Daya a duniya ba ko wata 6 , abin mamaki ina daukar ta tayi shiru hadi da kama hannunsa ta ruke gam ,juyi nashiga Yi da hannuna alamar wasa can Kuma sai na ce "kash baby yanzu jibi fa kin hanani bacci ,ba kyjin tausayi na ne?" Nayi maganar kamar tababbe batare da sanin Wanda zai bashi amsa ba, mikewa na sakeyi da yarinyar a hannuna na dorata a kan kafadarta nashiga jijjigata alamar rarrashi, tun iana zagaye dakin iana Jin motsinta har bacci mai nauyi ya dauketa, Dan murmushi na saki hadi dacewa "yauwa nima kinga yanzu sai nasamu nayi bacci Kona awa 3 ne" na karasa maganar hadi da karasawa bakin bed din, sun kuyawa nayi a hankula na ajiye ta Sannan nima na kwanta a bayanta, bacci nakeson Yi Amma na kasa ,hakan yasa na Dan rankwafo na zubawa yarinyar ido iana kallonta, haka kurum na tsinci kaina da sakin murmushin na shafa kwantaccen kan yarinyar, a haka har bacci mai nauyi ya daukeni.




In the morning 🌄

Misalin karfe' 9 nasafe MJ ya bude ido, lokaci guda ya furgita ganin Wanda yake Kansa , a hankula ya furta "lafiya?" Namijin dake tsaye a gabansa sanye da uniform na bakaken kaya, Wanda a kalla ya bawa MJ kusan shekara 18 a duniya, saurin cewa yayi "Allah ya karamaka lafiya ranka shidade ganinai shiru baka fito ba ,har anzo daukarka Kuma yau idan ba mantawa nayi ba ina da exam" Mika MJ yayi hadi da cewa "uhm wallahi jiyane bansamu bacci ba shiyasa har nakai wannan lokacin ko sallar asba banyi ba ,jiya baby ta dameni da kuka, Allah yaso ma sai 12 Zamu shiga exam din" murmushi wannan mutumin yayi yasake cewa "Allah ya kara Maka lafiya ba daban kada kace nafiye shiga abin da Babu ruwana ba danace wani abu" " uhm inajin ka fadi komai ne" yayi maganar hadi da kafe shi da idanun sa "am nace ranka shi dade da zaka dauki shawarata danace ka Kai baby gidan marayu ko ka mai da ita sauba gidan sarauta, inaganin hakan sai yafi yaro da Kai baza ka iya RAINON BABY ba kaima yanzu baka huce a Raine kaba Sha..... " Saurin dakatar dashi MJ yayi hadi dacewa " Babu mai rabani da 'yata" abin da kawai yace kenan ya mike ya shiga bathroom, shikuwa wannan mutumin da kallo ya bishi, a cikin zuciyarsa Kuma yace "oh yau baga ikon Allah wai 'yarsa" daga haka ya fice daga part din gaba daya .



MJ Yana shiga alwala kawai ya dauro yazo ya gabatar da sallah, Sannan ya Yi addu,a sosai kana ya mike, bakin gadon ya karasa ya zauna ,Ananne ya tarar da baby ta farka, sai kalle kalle take, zuba mata ido yayi Yana kallonta itama shi take kallo, "good morning baby" abin da bakinsa kenan ya furta Sannan ya saka hannu ya dauketa , bathroom ya nufa da ita, rigarsa ya tattare ya daure a kugunsa Sannan ya saka hannu ya nade dogon hannunrigar, Sannan ya zame buri da wandon dake jikin ta, ta koma daga ita sai famfas ,zame famfas din yayi ashema har tayi Kashi, ya tsine fuska yayi hadi da sa hannu ya toshe hancinsa wai wari, Ashe bai sani ba ya lakuto Kashin aikuwa ya shafa a hancinsa, da sauri ya tsuguna ya ajiye baby acikin kwamin wankan, yashiga wanke fuskarsa ,a she abin da bai sani ba lokacin da ya ajiye baby a cikin kwamin wankan,ruwa ya taru,aikuwa baby duk ta duru ruwa acikin ta ,a razane ya dago yaganta bata ko motsi ,nan take MJ yasaki kuka ya dakkota, Kai tsaye waje ya nufa Yana fita, masu bashi tsaro sukayi sauri tararsa hadi da bude masa murfin motar, yashiga motar suka shiga ja ,Daya daga cikin sune yayi karfin halin cewa "yanka shidade ina muka nufa" Afusace mj yace "asbiti mana " daga haka MJ ya cigaba da kukansa Yana bubbuga bayan Baby Yana Kiran sunan ta "baby ! Baby!! Baby help me " har suka shigo harabar asbitin MJ bai daina kuka ba, suna tsayawa da motar ma,aikatan asbitin suka karaso sakamakon ganin lambar motar da sukayi ,MJ bai jira an bude masa kofar ba ya bude ya fito da sauri, ya Mika musu ita" da hanzari suka amsheta sukayi ciki da ita, shikuwa MJ tsaya wa yayi yashiga juyi a harabar gurin yakai ya komo yakai ya komo yama rasa mai yake masa, dadi.





Misalin karfe 12:30 yaji wayarsa na ruri, Yana dakko wayar a aljihu yaga Ashe lecturer dinsune, shaki yaja ya kashe wayar gaba daya Dan ma kada a damesa , can Kuma sai yaji karamar wayarsa na ruri itama ko kallonta bai ba balle ya dakko yaga ko waye, Daya daga cikin masu gadinsane ya kawo masa wayarsa yace "am ranka shi dade mai martaba Yana magana" da kamar bazai amshi wayar ba can Kuma sai ya karba ya kara a kunnensa, tun kafin yayi magana yaji muryar mai martaba Rai a bace yace "Abee meyake damunka ne? Kasan Kuwa yanzu karfe' nawa kana ina akace baka shiga exam ba" "am uhm am Abba ina asbiti" "asbiti Kuma Abee mai yakai ka asbiti lokacin jarabawa yayi wane abune haka har yafi exam dinka mahimmanci?" "Am am Abba Daman babyce bata da lafiya yanzu ma ko motsi batayi bansani ba ko tamutu ko Tana raye" MJ ya karasa maganar hadi da fashewa da kuka " innalillahi wa inna ilaihirraju un yanzu Abee har yanzu kana tare da wannan yarinyar,wai ni Dan ubanka ina kasamo 'yane?" Abba yayi maganar Rai a bace , batare da MJ yasake cewa komai ba ya katse wayar hadi da hullawa mutumin wayar sa Rai a bace tace "ko Abba na yasake kira kasake bani sai ranka ya baci wallahi Anakin aikin ka" daga haka MJ ya karasa bakin dakin da aka shiga da baby.





Na tsugunna a gefen gadon wata tsohuwa domin tai Maka mata , sai ga yarinya — ba girma ne da ita ba, amma kuka nata ya fi ƙarfin zuciyata. Kuka mai sanyi, mai buƙatar kulawa. Kuka da ya fashe min zuciya fiye da buƙatar abinci.

> “Kai ne mahaifinta?”
Tambayar da ta katse min tunani, daga bakin wata matar asibiti da ke kallona kamar ba dan adam ba ne.
Ban ce komai ba. Sai dai na lumshe ido... na ɗago jaririyar, na manna bakinta a kirjina kamar za ta shanye zuciyata.
Ni ne mahaifinta. Ko ba na da ƙarfi, ina da ƙauna.


Abin da na fadawa ma,aikaciyar asbitin kenan,

Mutane za su ce, Ina mahaifiyarta? Ina danginta? Ina kake so ka kai wannan rainon?

Zan ce musu:

“Na rasa iyayena tun ina ƙarami. Amma bana fatan ita ta rasa ni.”



Sunanta Fatima Amma ni ina ce mata baby. Sunana MUJAHID Amma anfi Sanina da MJ . Littafin nan ba wai labari bane kawai — ba soyayya kawai ba — ba tausayi kawai ba... Kai dai karanta ki ji.





*Sauba*


"Wai yau ni Abee yake kashewa waya?" Sarauniya abida wadda ke gefansa ce TA danyi murmushi tace "ranka shi dade ai ba a banza ba ,tun farko Saida nace kada a tura Danan karatu wata kasar kaki saurarata sabi da kafin kaunar uwarsa a kaina ,ai ga irinta Nan yaro tun Yana Dan shekara 15 har da 'ya andaiji kunya wallahi" "ya Isa haka abida Indai har bazaki fadi alkairi akan Dana ba to ki saurara Kuma insha Allah abin da kike fada akansa bazai zama gaskiya ba" kwafa mai martaba kawai yayi ya mike hadi da cewa "sarauniyar agadas ina miki izini akan ki biyoni muje misra yanzunan" Babu musu ammi ta mike hadi da yin dakinta. sarauniya abuda kallon mai marta ba tayi tace" ranka shidade nikuma Dan bani na haifi MUJAHID ba shine baza a Dani ba kenan" shiru mai martaba yayi can Kuma sai yace "tashi ki shirya mutafi ,amma da sharadi bana son fitina nafada miki" itama mikewa tayi tashiga daki, shikuwa. Mai martaba sarkin garin sauba ci gaba yayi da juyi a a tirakarsa yakai ya dawo ya Kai ya dawo hakadai ya dingayi Yana cigaba da sunbatun sa....






"Yaron nan ba zai iya ba."
"Waye shi da zai raini yarinya?"
"Ko shi ne ya yi mawa wata ciki har aka haifi baby?"
"Wannan jariri ba nasa bane — to ba nashi ba ne... Nawane kenan?"




*MJ*

Maganganun mutane sun fi ƙonani fiye da rana. Amma wallahi ban damu ba. Saboda kowanne kalmarsu na sa ni ƙara matse Fatima a kirjina.

Na tsinci kaina ina kallon fuskarta mai ɗauke da dumin sabuwar haihuwa. Wannan jaririya... wannan ƙaramin numfashi da ke motsa hannuwanta a wuyana... ita ce burina.
Ba saboda na haifeta ba. Sai dai saboda... ni na zabi rainonta.

“, ka tuna kai yaro ne,”
cewar Malam Lawal, Daya daga cikin masu gadina.
“, babu tsari, babu uwa, babu uba… yanzu kai kuma kana tare da jaririya?”



Tsaki nayi cikin facin Rai n
girgiza kai ina kallon jaririya a hannuna, kamar ƙaya ce da zan nutse da ita.




Lokaci guda Mujahid yashiga tunani a zuciyar sa kamar wani mai yin mafarki

Wata rana na yi mafarki. Na ga Fatima ta girma, tana dariya, tana cewa:

“Na gode, dady Na gode da ka zamo mahaifina ba don jini ba — sai don ƙauna.”



Na farka da hawaye a idona. Sai na kalli ta — tana bacci, hannunta a hannuna.
Na furta da ƙasa da murya:

“Wallahi sai na ba ki rayuwa... ko da ni zan rasa tawa.”



Ban an kara ba naji muryar malan lawal Yana cemin ranka shidade Zamu iya tafiya gida tunda baby tasamu tafiya?" Batare da nace masa komai ba na mike muka bar harabar asbitin zuwa parking space, mota na shiga idona kur akan baby kamar Wanda za a rabani da ita haka nake kallon kekkewar fuskar ta. A haka har muka karasa gida.


**********""

Na sake mafarkin nan yau.
A cikin mafarkin, na tsinci kaina ina dariya — ba dariyar wauta ba, sai dai irin wadda ke zo ne idan mutum ya ga abin da yake ƙauna cikin aminci.
Wata ƙaramar yarinya ce, mai idanu kamar tabon ruwa, tana ta gudu da ƙafa ba safar kafa ba, tana cewa:

"Dady! Dadyna! Ka kama ni, ka kama ni!"



Ta durfafi ƙirjina kamar bazata, na ɗauketa, na juyo da ita sama. Sai dariyarta ta cika sararin mafarki — dariya mai dumi, mai tsarki.

A wannan mafarkin na ji kalma guda da ba zan taɓa mantawa ba.

“Na gode da ka bani duniya... ko da ba kai ka kawo ni ba.”



Na farka da hawaye a cikin dare. Na juyo a gadon katifa mai kyau wadda mahaifina sarkin garin sauba yasa aka kirkira domin ni kadai, sai ga Baby — tana barci, tana nannade a bargon mara nauyi.

Na matso kusa da ita. Na sanya hannuna a gefen fuskarta. Na daɗe ina kallonta kamar na rasa nutsuwa.

“Shin ke ce? Ke kika zo cikin mafarkina?”



Amma shiru.
Ko mafarki ne kawai?
Ko kuwa zuciyata ce ta fara saka min hoton da ba na kallon sa da ido?

**

Mutane da yawa suna kallona da tambaya a idonsu.

> “mj wace ce wannan?”
“Yarinyarka ce?”
“Ka samu ciki da mace?”
“Ko dai shirme kake yi?”



Amma ba zan ce komai ba. Domin bana da amsar da za ta gamsar da su. Sai dai ina da zuciya da ba ta bar ni na kawar da ita ba — Baby.


*******


Wata rana wata mata ta tsaya a kofar shagon sayar da burodi, ta kalle ni da Baby a bayana.

> Sai ta ce,
“Wannan dai ƙaddara ce... ba ’ya ce kawai ba. Wannan zata saka ka zama mutum.”



Na kalle ta, amma sai ta wuce kafin in tambaya. Kamar mafarki — kamar kalmarta ta zo daga wata duniya.

**

Na ci gaba da rike Baby, fiye da yadda ake rike rai.
Wani lokaci ina tambayar zuciyata:


🕊️ RAINON YARO

Chapter 2






“Shin me ke tsakanina da ke, Baby? Me ya haɗa rayuwarmu?”


Tambayar da nakeyi wa kaina akullum.



A kullum da safe, kafin rana ta huda samaniya, na saba kallon fuskar Baby. Kafin na yi addu'a, sai na kalli idanunta — ko da tana barci, kamar tana jin zuciyata.

Kullum ina cewa da kaina:
“Ina tsoron in rasa ki, fiye da yadda nake tsoron rasa kaina.”


After two year

*****

Yau na yanke shawara: zan nemi aiki — ko da kuwa aikin gadin tsafta ne a makaranta, ko share titi. Ban danmu da cewar ni Dan sarki bane. Domin Baby tana buƙatar madara, da rigar sanyi, da bandir na diapers. Tun da dai mahaifina sarkin sauba ya ce Indai har zan cigaba da rayuwa da baby babuni Babu shi, Dan haka dole nanemi kudi da karfina domin na ciyar da baby da gumina.




*******Na shirya tsaf
Na shiga unguwar Attarin Bab Zuweila, cikin ƙanƙanin lokaci na sami masu tambaya:

“Kai, wannan yarinyar taka ce?”
“Ina uwar ta?”
“Ko tsintarta Kai a hanya?”



Kullum tambaya ce, ba amsa. Domin babu amsar da ta dace da sirrin da zuciyata ke ɓoye.



A haka dai ina tafe da baby a bayana har yamma tayi ban samu aikin Yi ba, Babu yadda na iya haka na koma gida jikina duk ya mutu Babu kwari, Ananne nasamu mahaifiyata da abbana sun zo har sunayi wa masu gadina fada akan meyasa zasu na barina ina fita, basu an karaba suka ganni na shigo a gajiye duk na gala baita GA baby a kwance a bayana. Baki mahaifina ya saka yace "innalillahi wa inna ilaihirraju un Abee !! Batare da nace musu komai ba na shige falon, biyoni sukayi a baya abbana ya dakamin tsawa Yana cewa:



“abee,” ya faɗa da ƙwaryar murya mai izza, “ka zo nan.”



Mujahid ya janye Baby daga bayansa cikin nutsuwa, ya gyara mata hijabi, sannan ya ce mata:

“Tafi ɗaki, Baby. Zan zo nan da mintuna kaɗan.”



Ta jinjina kai da ƙaramin murmushi, ta tafi tana jinginar da ƙafarta kamar mara nauyi.

**

Sarki ya yi masa kallon da ya saba yi masa tun yana yaro – kallo mai cike da ƙauna, amma kuma ƙa’ida.

Na yi shiru tsawon lokaci, saboda ina son na ba ka damar fahimtar rayuwa, tsawan shekara biyu kana tare da wannan yarinyar. Amma yanzu dole na tambaya.”



Mujahid ya lumshe ido.

“Ina ka samo wannan yarinyar?”



Ya yi shiru.

“Ba ‘yar gidanmu bace. Ba a ɗaukota daga danginmu ba. Kuma ka fara ɗaukarta kamar ‘yar jini.”



Mujahid ya haɗe hannuwansa a ƙirjinsa, yana kallon ƙasa.

“Ta rasa gida, abbana.”



“Toh akwai orphanage a gari. Akwai gidajen ‘yan uwa. Me yasa ita ce ke ɗaukar hankalinka fiye da sauran?”



Shiru ya sake dawowa. Sai daga baya Mujahid ya ce da ɗan murya:

“Saboda idan Baby ta kalle ni, ina jin kamar ni ne abin da ta rage dashi. Kuma ita ce ma kawai take tunasar da ni da zuciya.”



Sarki ya ɗan daga gira. Idonsa ya rikice kaɗan.

“Kana ɓoye min wani abu ne? Ko kuwa ita ce…”



Mujahid ya ɗago, cikin sauri:

“abba, wallahi ba zan ɓoye maka gaskiya ba, amma yanzu... yanzu ba lokacin bayani bane. Ina roƙonka ka barni in ci gaba da rainonta.”



Sarki ya danyi murmushi mai raɗaɗi.

“Toh, ka sani, ranar da gaskiya ta bayyana, zata zo da ƙarfi fiye da kowane jiki. Kuma ni, a matsayin sarki, ba zan yarda da kowanne abu da zai ɓata sunan gidan sarauta ba.”


Batare da MJ yace komai ba ya mike yace "burina shine na kula da baby Dan Allah ka taimaka kada ka rabani da ruhin da baisan komai ba sai maraici" Yana gama fadar haka ya bar dakin, zuciyarsa kamar ta nitse da nauyi. Yana da burin kare Baby, yana da sirrin da zai iya tarwatsa komai, kuma yana cikin dangi da ba su yarda da “mara jini” a matsayin “ɗa” ba.

MJ Yana shiga daki ya zauna a gefan bed yayi shiru, sai Jin baby yayi ajikinsa Tana murmushi Tana masa gwaranci.


A hankula ya dago jajayen idanunsa ya soma magana cikin nutsuwa Yana cewa:

“Baby, ke ce ruwan da nake ɗora wa a zuciyata. Amma ruwan nan, idan ya zubo a fili… zai iya ƙone ni gaba ɗaya.”


Daga haka ya janyo ta jikinsa hadi da lumshe ido .


Su Abba Kuwa jiki Babu kwari suka fita daga gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login