Showing 15001 words to 18000 words out of 19708 words
Chapter 6 - BAFULATANA Book Complete Hausa Novels BY ESHAAT.txt
rauninka a gaban maqiyanka,
Muzaffar yayi sannan Ya nufi qofar fita daga Falon,
Site din Mamie ya nufa , da sallama ya shiga Fallon da uban rawani kamar wani ba Sarake, tunda ya shiga falon muta nan dakin suke kallon sa dik da cewa basu gane shi ba , ciki kuwa harda Mamie, murmushi Dady Yayi sannan ya miqa hannayensa alamar yazo gare shi , da sauri muzaffar ya nufi mahaifin nasa ya suka sake rungumar juna , umma CE tayi qarfin halin cewa wai alhaji waye wannan din da kashigo dashi cikin gida har falo?
Ga kuma uban rawani kamar wani bafade!
Momyce ta qara da cewa inda duniyar nan ba gaskia ka jajibo mana shi baka tsoron yazo ya cutar damu a gaba?
Itadai Mamie bata CE komaiba sema kallon su da take, ta Kali wannan ta kalli wannan,
Murmushi Dady Yayi sannan ya kalli Momy yace kin taba ganin inda da ya cutar da ubansa?
A taqaice tace yo alhaji nawa akayi?
A hasale yace idan kuwa kika ga da ya cutar da ubansa to wllh wannan dan ba dan halak bane,
Ynan gama bata amsa yace zoka zauna Dana ,
Umma CE tace danka kuma alhaji ?
Kodai batan muzaffar yasa kanka ya fara kwancewa ne?
Ya zaka samo wani bafulatanin daji da uban rawani kace danka ne shi?
Da sauri Momy tace yauwa gaya masa dai maman zahra,
Murmushi Dady Yayi Wanda yake dauke da manufofi masu yawa, sannan yace, babu tabin hankali balle a samu matsalar qwaqwalwa!
A yau da yamma cin nan lbri mafi dadi a duniya ya sameni,
Ba wani lbri bane illa labrin baiyanar gudan jini na wato Dana namiji tilo wato muzaffar!
Gaban Ummah da Momy ne Yayi mummunan faduwa, nan da nan gumi ya fara karyo musu dik da sanyin Ac dake dakin hakan be hanasu fitar da zufa ba,
Kallo daya zaka yi musu ka fahimci suna cikin wani yanayi!
Momy CE tayi qarfin halin cewa to alhaji INA muzaffar din yake yanzu?
Bece mata komaiba se nuna mata shi da Yayi da yatsansa,
Cike da rashin fahimta Mamie tace abban muzaffar nifa ban fahimce Ku ba wai don Allah meyake faruwa ne??
Sam Dady be boyewa Mamie komaiba tun dga batan shi muzaffar din har zuwa yanzu da Allah ya baiyana shi, da sauri Mamie miqe daga inda take ta saukko qasa Inda muzaffar ke zaune, ta Dora tafikan hannayenta a kan fiskarsa tana me zubar da hawaye tana kallonsa cike da tsantsar so da qauna tace, haqiqa INA matiqar qaunarka Dana kuma dik duniyar nan dik Wanda ze soka wllh a bayana yake muzaffar!
Dama abinda ya faru dakai kenan yasa kwana kin baya nake ji a jikina wani Abu ya faru da gudan jini na?
Ashe shiyasa na rasa kwanciyar hankali? Ta qarasa maganar cikin kika me matiqar ban tausayi!
Daqar ta tsagaita kukanta sannan tace INA matiqar sonka dana, idan wani abin ya sameka wllh har abada zanyi Dana sani!
Cike da makirci umma tace ke kinga fa bawaifa fin mu sonsa kikayi ba! Kin wani sashi a gaba se kuka kikewa muta ne, kafin kisanshi fa mumuka sanshi, tunda mu muka fara auren ubansa kafin ke,
Da sauri Momy tace gaya mata dai zata yiwa mutane kini bibi wai ita matar uba,
Mamie batace komaiba se kika da take, muzaffar ma kukan yake yana me mamakin irin qaunar da Mamie take masa !
Tabbas koda mahaifiyarsa CE irin son da zatai masa kenan,
Hawayen fiskarta ya fara goge mata da hannayensa,
Dik wannan abin Dady yana kallon su sannan yace dikkan Ku Ku dakata sbda wannan abin ba shine mafita ba, yau kowa zeji abinda na Dade ina boyewa a gare Ku
Wata qila ya bku mamaki amma kuma Sam ba abin mamki bane
A cikin masu mama kin nasan harda kai muzaffar!
[8:55PM, 2/6/2018] ‪+234 813 272 6929‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 18*
Cike da rashin fahimta muzaffar ke kallon mahaifin nasa sedai bece komaiba,
Dady Yayi ajiyar zuciya sannan ya ci gaba da magana kamar haka
Haqiqa na boye muku wani al'amari a Iya zama na daku, ya nuna umma da Momy
Sannan ya cigaba da magana,
Na gwada Ku a baya ta hanyar kawo muku Dana muzaffar tin yana shekara daya a duniya na raboshi da mahaifiyar sa na kawo muku shi,
Sbda na gwada tsoron Allah n Ku da kuma tausayin Ku,
Amma se kuka kasa riqeshi da gaskia, kuka dnga cutar da shi, abinda Baku sani ba shine mahaifiyar muzaffar tananan a Raye bata mutu ba,
Cike da tashin hankali gami da fir gita muzaffar yake kallon mahaifin nasa yace, Dady kana nufin kace min mahaifiyata tana nan da rai bata mutu ba?
Amma Dady meyasa ka rabani da mahaifiyata?
Meyasa ka zabi na rayu da wasu sabanin mahaifiyata?
Meyasa kace min mahaifiyata ta rasu? Pls Dady ka cireni a cikin rudanin Dana ke ciki don Allah
Da rarrafe ya matsa gurin Mamie ya riqe hannayenta yace Mamiena don Allah ki cewa Dady ya kaini gurin mahaifiyata na ganta koda so daya ne don Allah Mamie!
Ya qarasa maganar yana kuka sosai kamar wani qaramin yaro,
Da qyar Mamie ta saita kanta sannan tace ka kwantar da hankalin ka yarona baka da wata Uwar da ta wuce ni kaji ? Nice mahaifiyarka ba wata ba,
Momy CE tace haba malama kinga ki dakata ki barmu da almarar data muke ciki, ya za'ai kizo kisamu a gaba kina yimana kukan kirsa da makirci,
Ki rufe mana baki muji qarshen zance,
Ummah tace muma fa muna son yaron nan kawai dai tsautsayine da kishi yasa muka kasa riqeshi tun farko, shiyasa ma ya kawo miki shi amma bawai finmu sonsa kikayi ba
Kuka sosai muzaffar yake yi, dadyne ya katse su ta hanyar ce gaya musu cewar Mamie itace mahaifiyar muzaffar, kuma itace matar daya fara aure a rayuwar sa, dan haka itace Uwar gidansa kuma mahaifiya ga muzaffar!
Dikkansu seda suka girgiza musamman ma momy, sbda tashin hankalin da momy ta shiga numfashinta har sama ya fara yi,
Umma ce tayi qarfin halin zaunar da momy,
Sun jima suna alhini
Mamie qara rungume dannata tayi cike da soda qauna,
Seda suka dauki lokaci me tsayi babu Wanda yace komai ,
Fadilah CE tace momy tashi mu tafi sbda ki samu nutsuwa,
Ba musu momy ta tashi dan dama hanya take nema
Suna shirin fita umma ma ta bisu,
Suna fita ameerah tace zahra zo mutafi muma, harara zahra ta zab gawa ameerah tace ba inda zani kawai kiyi tafiyarki,
Tashi ameerah tayi tabar falon kamar zata tashi sama,
A hankali zahra ta sakko qasa daidai inda qafafun Dady suke tace Dady don Allah kayi haquri da halayen da iyayen mu suke Nuna maka nasani dole wata rana zasuyi nadama,
Tana gama magana da Dady ta juya ga muzaffar tace yaya, haqiqa ina me jajanta ma abinda ya faru dakai ina me yi maka addu'ar alkhairi a koda yaushe sbda kai dan uwa na ne kuma guda daya tilo, nasani wata rana dole Kaine zaka zama uba a garemu gaba daya,
Nasani bamuyi sa'ar iyaye ba, amma don Allah INA me roqa masu afuwa akan abinda suka aikata maka kana yaro don Allah yaya muzaffar kayi musu afuwa, tana maganar ne tana hawaye,
A hankali ta daga jajayen idanunta ta kalli Mamie tace , haqiqa ke uwa CE wadda ta cancanta a yaba mata tunda har kika Iya sadaukar da danki guda daya tilo dan farin cikin mijinki, wllh dik inda uwa ta gari Takai kinkai Mamie, dama kece kika haife ni wllh danayi alfahari dake,
Tana kaiwa nan ta miqe ta fice daga fallon tana me zubar da hawaye
A wannan rana muzaffar kwanan farin ciki Yayi, hakama Mamie da Dady
Su umma da momy kuwa kamar su mutu din bakin ciki
RUGAR HARDO
Tunda muzaffar ya tafi komai ya dena yiwa rabe dadi
Gashi yau kwanan sa daya da tafiya amma har ta rame sbda kuka , bugu da qari ga kuma azabar da Laure take gana mata, abin gwanin ban tausayi,
Tashi tayi daga dakin ta fita chan gurin garken shanunsu Inda suke zama ita da muzaffar, dutsen daya ke zama a kai ta Dora hannunta akai seta sake fashewa da matsanancin kuka me cin rai
Cikin kuka take fadin ya Allah Kaine ka bani farin ciki a lokacin da bani tsammani ba!
Ya Allah ina ina roqonka da sunayenka kyawawa, ya Allah ka cika rayuwata da farin ciki me dorewa, ya Allah ka bani ikon jure ko wacce irin jarrabawa!
Tanayi tana kuka sosai abin qwanin ban tausayi,,,,,,
[8:55PM, 2/6/2018] ‪+234 813 272 6929‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 19*
Hka tayita rusar kukanta babu me rarrashinta, sda rana ta bude sosai sannan ta Tisa dabbobin suka tafi kiwo, haka ta dinga tafiya jiki ba qwari, inda suke zama da muzaffar idan sun gaji ko kuma zasuyi sallah, a nan ta zauna ta sake yin shiru, nan da nan ta tafi duniyar tinanin yayan nata!
A ranar dai haka ta wuni sukuku da ita
Momy ce tsaye a cikin dakinta tana ta safa da marwa da Waya a hannunta, falo naga ta nufa fiskarta a daure fadilah ta samu a zaune bata ko kalleta ba tace tashi kije ki kiramin Umman zahra, bata jira cewarta ba ta koma dakin ta
Ba'a dau lokaci me tsayi ba sega umma ta shigo dakin , Sosai take kallon Momy sannan tace nariga na fahimci me kike son gaya min tin daga qwayar idanun ki, yanzu meye mafita ? Tambayar da Momy ta jefawa umma kenan,
Bata CE mata komai ba ila daga wayar hannunta da tayi da alama wani take son kira,
Ba'a dau lokaci ba ta fara magana cikin isa da nuna gadara tace ado haka mukayi dakai?
Nawa muka baka a kan ka kashe mana wannan dan iskan?
Da kasan ba zaka iyaba kuka karbar mana kudi?
Cike da mamaki ado yace haba hajjaju, ai tin tini aka gama wannan aikin dan sda na tabbatar baya numfashi sannan na qyaleshi!
Kema kinsan Baku taba bani aiki na kuskureba,
Momy CE ta fisge wayar daga hannun umma ta kara a kunnenta cike da masifa tace har kana da bakin da zakace baka kuskure a aikin ka?
Kai daqiqin inane da zaka yarda shi a Inda mutane suke shige da fice?
To gashi yanzu ka jiqa mana aiki yaron ya dawo gida da ransa da kuma lafyar sa, kuma kasan dole 'yansanda zasu karbi bayanai daga bakinsa , dan hka seka zauna cikin shiri, at any time zasu Iya zuwa kamaka!
Ta qarasa maganar cike da masifa gamida tarin bacin rai
Umma CE tayi saurin karbar wayar tace ado kana jina?
Cike da tsoro yace ae Hajia inajinki
Maza- maza ka shirya kabar garinnan kayi nesa da kano Sam karka dawo semun nemeka, da sauri yace to Hajia, sda ta dan nisa tace masa amma dai a kwai kudi a hannunka ko?
A'a yace mata nan da nan tace yaushe na saka maka million daya a account dinka da zaka cemin ba kudi?
A daqile yace sorry Hajia na shiga rudani ne, bata sake cewa komaiba ta katse wayar sannan ta bude wayar ta cire sim din ta karya sbda gudun seta kwana!
A hankali umma ta dafa kafadar Momy tace haba zuwaira kada ki bada mata mana, ai yanzu damace tazo mana,
Cike da rashin fahimta Momy tace kamar ya ?
Murmushi tayi irin nasu na 'yan duniya sannan tace shishigewa waccan matsiyaciyar zamuyi, idan ta saki jiki damu se mu aika shegiya garin da ba'a dawowa! Koya kika CE?
Dariyar jin dadi Momy tayi sannan tace wllh kamar kinsan abinda ke raina,, suka sake kwashewa da dariya suka tafa(haqiqa kishi da rashin tsoron Allah yana kai mata dayawa ga halaka, mugun nufi bashida wata fa'ida illa yakai mutum ga na dama! Dan Allah mata mu gyara zukatan mu, kishi halitta ne kuma kowace mace tana dashi a tare da ita muddin tana da lfy, amma idan kika bishi ta hanyar daya dace wllh zaki zauna da kowa lfy, wannan abin nasu Momy Harda son zuciya gamida tarin rashin tsoron Allah, ya ubangiji Allah kasa mufi qarfin zukatan mu)
Moddibo ne zaune qasan kafet yana daure boronsa da alama shirin tafiya gda yake muzaffar ne ya shigo dakin da murmushi a kan fiskarsa yace baba,,,, se kuma yayi shiru, da sauri ya qaraso inda moddibo yake cike da damuwa yace baba badai har ka fara shiriba tin yau?
Murmushi moddibo yayi irin na dattijawan qwarai yace to yaro me kuma zan tsaya jira?
Tunda Allah ya amince mana min samu nasarar kawoka Gavan Iya yenka ai kuma nima sena fara shirin komawa gida kodan sbda Rabe na!
Nasan yanzu tana nan cikin kewata , ban taba tafiya me Nisan haka na barta a gda ba, a Iya zaman ta dani ban taba tafiyar da takaini ga kwana ba sbda tinanin halinda zata shiga idan bana nan,
Dan haka Gobe da ikon Allah zan kama hanyar gda ,ya warashe maganar da murmushi a fiskarsa
Shiru muzaffar yayi na dan lokaci tabbas yana mamakin shaquwa irinta moddibo da diyarsa, yanzu idan tayi aure ya zeyi?
Kafadarsa moddibo ya dafa yace yaro naga daga jiya zuwa yau kanata farin ciki,
Murmushi muzaffar yayi sannan ya labirtawa moddibo komai, sosai moddibo yayi farin ciki gamida yiwa muzaffar nasihu masu shiga jiki sosai,
Jikin muzaffar haka yayi sanyi sbda nasihun da moddibo yayi masa, a ransa seyaji dama moddibo ya zauna tare dashi haka kawai dattijon ya gama shiga ransa,
Jiki ba qwari muzaffar ya miqe sbda jin kiran sallar ishsha'i, be cewa moddibo komaiba, ya nufi hanyar fita
Murmushi moddibo ya kuma yi sbda ya fahimci muzaffar fishi yayi sbda yace ze tafi gobe
Miqewa yayi shima suka nufi masallaci, daidai lokacin da Mamie ta loqo ta window falon ta bayan su ta hanga sannan ta koma taci gaba da jera abinci akan dining,
Koda aka idar muzaffar ya Dade yana addu'oinsa sannan suka shafa suka fito gaba daya,
Dai dai lokacin da Dady ma ya fito tare suka jera suna tafe suna hira anan muzaffar ke shaidawa Dady tafiyar moddibo, sosai Dady ma yaji ba dadi sbda yanda ya saba dashi a kwana daya kamar sun shekara da sanin juna, moddibo akwai sauri saboda mutane, gashi da haquri da sanin ya kamata shiyasa yake da dadin mu'amala,
Indai ya zauna dakai koda na wuni daya ne to Seka qaunace shi. Sbda dattijon a kwai shiga rai
Suna shiga Dady yacewa moddibo tunda gobe ze tafi don Allah yazo suje bangarensa suci abinci tare amma fir moddibo yaqi amincewa , haka Dady ya haqura badan yaso ba yayiwa moddibo seda safe sannan ya wuce bangaren Mamie,
Ban garen da aka sauki moddibo suka muzaffar yana biye dashi a baya har suka isa a falo suka zauna, muzaffar ne ya fita dan dakko musu abinci a bangaren Mamiensa , be jima ba ya dawo dauke da manyan food flasks guda biyu se zahra dake bayan sa hannunta dauke da flat da spoons ajiyewa tayi sannan ta koma ta daukko wani flat dauke da kosilo Wanda yaji qwai da bama ansa wata fara leda an rufe farantin da ita ta yanda kana Iya ganin abinda ke cikin flat din da sallama ta shigo ta ajiye sannan ta gaida moddibo cike da girmamawa, da kulawa ya amsa mata tareda sakin fuska, an an yake tambayar ta sunan ta murmushi tayi sannan tace zahra,
Murmushi moddibo yayi sannan yace Ashe mata nane da kanta, dukansu suka sa dariya sannan ta miqe tayi musu saida safe ta wuce bangaren su
[8:55PM, 2/6/2018] ‪+234 813 272 6929‬: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado😘_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 20*
Zaune suke kan dining suna cin abinci, Dady yake sanar da Mamie tafiyar moddibo da safe idan Allah ya kaimu, gaban Mamie ne yay mugun faduwa sbda sunan da taji mijinta ya ambata , take yanayinta ya sauya,
A hankali tace daga zuwansa har ze koma se kace ana korar sa?
Murmushi Dady yayi sannan yace wllh nima haka nace dashi amma fir yaqi yarda ya qara kwana ki,
Dik wannan hiran da suke itada Dady qarfin hali kawai take tinda taji sunan moddibo, sunan da bazata taba mantawa dashi ba a rayuwata
Dady ne ya katseta ta hanyar sanar da ita yayi kewarta,
Murmushi Mamie tayi sannan tace abban muzaffar kenan sekace wasu yara?
Dariya yayi sannan yace mata au yara ne kawai suke soyayyah?
Bata CE masa komaiba dan ta fahimci Neman magana kawai yakeyi,
A hankali ta ajiye cokalin dake hannunta ta miqe a taqaice tace seda safe,
Sam beyi qoqarin hanata tafiya ba sbda ya fahimci yana yinta ya canza tunda ya ambaci sunan moddibo.
Abinda ya qara daure masa kai shine meyasa bata son taji wani me suna irin hka?
A hankali ya rintse idanunsa, sbda baya son abinda ze batawa matar tasa rai, a daddafe ya kammala cin abinci, ya miqe ya nufi bedroom din shima, a zaune ya sameta da alama daga toilet ta fito, kana kallon ta zakasan tayi kuka, bece mata komai ba ya shiga toilet yayi brush sannan yayi wanka