Showing 12001 words to 15000 words out of 19708 words

Chapter 5 - BAFULATANA Book Complete Hausa Novels BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

1646

yayi sallah amma bega shigo war Rabe ba se abin ya fara damunsa, har akayi ishsha beganta ba se abin ya fara daga masa hankali,
Daqar ya Iya bude baki ya cewa moddibo dake ta faman dura madara ajarka yace, baba!
Ya a nitse moddibo ya dago yace yaro ya akayi ?
A daburce yace dama,,, dam,,,,, Rabe se kuma yayi shiru.
Murmushi moddibo yayi yace yaro INA zaton ko tayi bacci ne,
Kayi qoqari ka kwanta sbda gobe asibanci zamuyi ,
Bashi da yanda zeyi haka ya kwanta amma fir bacci ya gagari idanunsa ,
A hankali ya firta meke faruwa dani ne??


Bangaren Rabe kuwa baccinta take hankalin ta kwance babu abinda ya dameta ,


Qasar India


Mamie tana idar da sallar asuba bata tsaya ko INA ba se airports dan cika umarnin mijin nata duka 5:30am suka daga zuwa Nigeria, tun da ta hau jirgi gabanta ke faduwa komeyasa????


Ban garan su muzaffar kuwa tunda gari ya waye suka gabatar da sallar asuba suka fara shiri ba yanda beyiba dan su hadu da rabe
Amma fir taqi da abin ya isheta ma seta bar Gidan tayi tafiyarta gidansu danejo qawarta,


Ba yadda ya Iya haka suka tafi ya naji yana gani suka shiga wata a mortar shanu suka kama hanyar garin kano garin alfarma!
Dik wannan uban sammakon da sukayi basu suka isa kano ba se qarfe 4:00pm
Wanda yayi dai dai da saukar mamie a qasarta ta haihuwa!
Cike da kulawa moddibo ya kalli muzaffar yace yaro zaka gane gida ko?
Muzaffar yayi murmushi yace zan gane,
Adaidaita sahu suka tare sannan muzaffar yace malam nasarawa g.r.a zaka kaimu ,
A take me napep yace musu dubu daya !
Bece komaiba suka shiga suka tasarwa nasarawa g.r.a


Mamie na sauka daga jirgi bata wani jima ba driver yazo ya dauke ta tana cikin motar gabanta yay mummunar faduwa!
Da sauri ta firta innanillahi wa'inna ilai hirraji'un.


Qofar wani gida na alfarma muzaffar ya nunawa me napep din tare da bashi izinin shiga horn me napep din yayi amma shiru ba'a bude gate din ba ,
Muzaffar ne ya zuro qafarsa da nufin ya suka , amma se moddibo yayi carap ya riqeshi yace yaro Sam be kamata ka shiga kanka tsaye ba, dolene ka badda kamannin ka,
Cike da rashin fahimta yace ban gane ba!
Murmushi moddibo yayi ya fito da wani rawani ya CE bani kanka, ba musu ya miko masa kan NASA ya shiga Nada masa,
Watabara'kallahu'ahsanulkhaliqin,
Abinda moddibo ya Iya fada kenan sbda wani azababben kyau da rawanin yayi wa muzaffar
Gashi sanye da kayan Fulani seya koma kamar wani balarabe!
Horn suka sake yi a karo na uku sannan me gadin ya bude yana ganin baquwar fuska ai seya dakatar dasu yace daga malamai daga INA?
Moddibo ne ya bashi amsa yace daqa rugar hardo!
Ba musu me gadi ya bude musu qofar suka shige sbda kwarjinin da moddibo yayi masa
Sauka sukayi shi kuma me napep suka bashi hagginsa Harda qari, mebawa fulawa ruwa suka samu su kace dan Allah ya sanarwa da alhaji abdul yana da baqi daga rugar hardo, cike da girmamawa ya amsa tare da kaisu falon saukar baqi






Se ince fatan alkhairi mlm moddibo๐Ÿ‘
[8:53PM, 2/6/2018] โ€ช+234 813 272 6929โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*BAFULATANA*
_True life story_


*_Written By Cibado๐Ÿ˜˜_*


_Dedicated to Khadeeja Candy_


*Page - 15*


Sun jima suna zaune, sannan aka kawo musu abin motsa baki.


Lokacin da aka sanar da Dady zuwansu moddibo yayi mamaki sosai sbda shi bema taba jin sunan garin ba, amma dayake mutum ne shi me jama'a da kuma son mutane shiyasa be wani yi mamakin zuwan su ba, tashi yayi ya nufi falon sa na da yake saukar baqin sa,
Da sallama ya shiga falon, ya nemi guri ya zauna sannan suka gaisa da moddibo.
Kwata kwata be lura da wanda ke zaune a qasa ba,
Sosai Dady ya sakarwa moddibo fuska, a nitse moddibo ya fara magana tare da yiwa Allah godia yace da fari alhaji ka godewa Allah bisa ni'imar da Allah yayi maka a wannan rana!
Cike da rashin fahimta Dady yace ban fahimceka ba dan uwa?
Murmushi moddibo yayi sannan yayi masa nuni da muzaffar dake zaune da uban rawani a kansa gaba daya ya badda kama
Sosai Dady yake kallon dan nasa cike da so da qauna, da sauri ya nufi inda muzaffar yake da nufin ya rungume shi, haka shima muzaffar din beyi qasa a gwiwaba ya nufi mahaifin nasa suka rungume juna suna masu zubar da hawaye๐Ÿ˜ญ
Sosai suka bawa moddibo tausayi, sun jima suna rungume da juna sannan Dady ya cire jikinsa daga na muzaffar ya zubawa fukar dan nasa ido sosai rama ta baiyana a jikinsa sedai kuma beyi duhu ba haskensa yana nan yanda yake!
Se kuma alamar ciwon dake gefan kansa na dama Wanda be gama bacewa gaba daya ba.
Cike da damuwa Dady yake tambayar dan nasa meya faru dashi? Kuma ina ya shiga har tsawon wannan lokacin?
Muzaffar yayi shiru kamar bazece komai ba, seda ya dan nisa sannan ya gayawa Dady komai sedai be gaya masa da sa hannun su Ummah da Momy ba akan abinda ya faru dashi ba!
Har abinda ado yayi masa be gayawa Dady ba, kawai CE masa yayi 'yan fashi ne suka farauci rayuwarsu kuma sukayi yunqurin kashe shi, badan wannan bawan Allahn ba da tini na rasa rayuwata, ya qarasa maganar tare da zubda hawaye!
Da sauri Dady ya qaraso kusa da qafafuwan moddibo ya rige yana fadin ngde, Allah ya saka maka da alkhairi, haqiqa banida abinda zan biyaka dashi a wannan duniyar sedai kawai ince Allah ya biyaka da Gidan aljannah๐Ÿ‘
Ya qarasa maganar tareda hawaye!
Murmushin qarfin hali moddibo yayi sannan yace haba alhaji dan Allah ka dena godemin sbda ni nayiwa yaro taimako ne don Allah ba dan kayi min godiya ba, dan haka ka bari godiyar ta isa haka, sedai kawai abinda zancema shine kayi a hankali sbda maqiyanka Dana danka suna tare dakai kuma sune sukafi kowa kusanci dakai!
Cike da rashin fahimta Dady yake kallon moddibo, kai moddibo ya daga masa alamar ae,
Kiran sallar da aka fara kira ne ya katse Dady daga tambayar da yaso yayiwa moddibo,
Tashi sukayi suka nufi masallaci dan su gabatar da sallar magrib,
Bayan sun idar ne suka nufi qofar da zata sadasu da Fallon,
Horn akayi daga bakin gate hakan ne yaja hankalin Dady da muzaffar, shiko moddibo shigewarsa yayi ya samu guri ya zauna, sannan ya fara nazari akan maganar da muzaffar ya gayawa mahaifin sa, to meyasa be gayawa mahaifin sa gaskia ba??
Lallai muzaffar yaro ne me sanin ya kamata kuma me gudin masifa.
Sbda gudin ta da fitina yayiwa mahaifin sa qarya dan ya fanshi kishiyoyin mahifiyarsa!
Gaskia samun irin sa se'an tona a irin wannan zamanin, haka kawai seyaji yaron ya qara shiga ransa.


Wata baqar Toyota benza ce ta sako kai cikin Gidan ko ba'a fada ba Dady yasan Mamie ce parking space suka nufa sukayi parking tana fitowa daga motar Dady ya yiwa muzaffar nuni daya shiga falon tun kafin ta ganshi,, haka kuwa akayi
Da sauri Dady ya nufi inda Mamie ke tsaye da murmushi a kwance a fiskarsa yace sannu da zuwa Uwar gida ran gida,
Murmushi Mamie tayi ba tace komaiba ta nufi bangaranta visa ga mamkinta ba ta ga qura ko daya ba harta isa falon ta ko INA tas tas ba datti daret bedroom dinta tanufa, tana shiga toilets ta shiga bisa ga mamakinta dik abinda take Amfani dasu tin daga sabulun Wanka har zuwa MacLean komai a kawai a ciki kuma dika sababbi, haka ma su towels,
Murmushi tayi sannan tace abou muzaffar kenan har yanzu kana nan yanda kake baka canza ba!


Dady ne yasa masu aiki suka shigarwa da Momy kayanta bangaren ta sannan ya nufi falon da moddibo ke zaune shida muzaffar,
Dady ne ya yiwa muzaffar izinin yakai moddibo bangaren saukar baqi dan yaje yayi Wanka ya huta
Haka kuwa akayi suna fita Dady ya nufi bangaren sa dan ya samu yayi Wanka zuciyar sa cike da farin ciki Mara musaltuwa,
Suna isa ban garen baki ya nunawa moddibo ko INA sannan suka zauna , a nan ne moddibo yake tambayar muzaffar meyasa baze tafi bangaren sa ba?
A taqaice yace Dady ne yace na zauna a nan har seya nemeni!




















Lallai akwai magana a qasa se ince Allah ya huta gajia Mamie๐Ÿ‘
[8:54PM, 2/6/2018] โ€ช+234 813 272 6929โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*BAFULATANA*
_True life story_


*_Written By Cibado๐Ÿ˜˜_*


_Dedicated to Khadeeja Candy_


*Page - 16*




Seda ta yi Wanka sannan ta gabatar da sallar dake kanta, ta jima tana adduo'inta sannan ta shafa,
Bangaren Dady kuwa yana shiga cikin gda dakinsa ya wuce seda Yayi Wanka ya kimtsa, sannan ya gabatar da sallar ishsha'insa, sannan ya nufi falon su momy,
Yana shiga falon ya same su dukansu akan dining sunacin abinci suda yaransu, kallo daya zakayiwa Dady ka fahimci yana cikin farin ciki, dan haka umma cike da gulma tace alhji da dikkan alamu kana cikin farin ciki, kodai an sake samun riba a company n ka na takalma ne?
Cike da masifa Momy ta fara magana tace riba? Ba wata riba da aka samu, wannan farin cikin da yake ba komai bane dalili ila zuwan matar sa, kuma wllh ka sani tunda ka jajibota cikin mu to wllh kayi bankwana da kwanciyar hankali, tana gama magana ta mike da nufin ta wuce dakinta,
Tsawa Dady ya daka mata wadda seda hanjin cikin ta ya kada yace ke kishiga hankalinki niba sa'anki bane da zaki sani a gaba kina yimin ihu, ko ba komai ni mijin ki ne kuma uban 'ya'yanki ko banci darajar kowa ba naci darajar 'ya'yana yana gamawa ya juya da nufin yabar falon, se kuma ya dawo yace idan sun gama suzo falon sa yana son magana dasu a bangaren da aka fat din Mamie kuma su zo da yaransu gaba daya sbda a kwai Abu me mahimmanci,
Yana kaiwa nan Yayi waje abinsa ban garen Mamie ya nufa da sallamar sa ba kowa a falon se qamshi dake tashi a falon sosai yake kallon falon Yayi matiqar kyau kamar yanda yake buqata, hanyar da zata sa dashi da dakin Mamie ya nufa tin kafin yakai ga dakin qamshin turarenta ya baqunci hancin dady, murmushi Yayi a zuciyarsa yace salma kenan kedai Allah Yayi miki son qamshi
Yana shi shiga ya sameta tana daura dan kwali a kanta sallamar ta amsa sannan tayi murmushi tace sannu abban muzaffar na sameku lfya ?
Dariya Yayi sannan yace Uwar gida ran gida lfy. Qalau mun godewa Allah ya gajiyar hanya?
Murmushi tayi sannan tace gajiya kam akwai ta Baban muzaffar.
Shiru suka dan yi na wani dan lokaci sannan Dady yace idan kinci kin gama shiryawa akwai maganar da zamu dan tattauna daku, gabanta ne ya fadi! da sauri ta furta innanillahi'wa'innah ilaihirraji'un, da Sauri Dady ya matsa kusa da ita ya dafata yana tambayarta meya faru?
Kuka ta saki sekace wata qaramar yarinya, beyi yunqurin hanata ba, seda tayi me isarta sannan tayi shiru,
A hankali ta fara magana ban San meyake damuna ba Sam! Koda yaushe a ' se in dinga jin gabana yana yawan faduwa, musamman ma yau ,
Lamarin nifa ya fara bani tsoro wllh, kodai wani abin ne ze faru dani? Ta qarashe maganar tana zubar da hawaye,
A nitse Dady ya fara magana yace haba salmah, har zuwa wani lokaci zaki kai kina wannan kukan?
Yakamata kisani cewa ko wani mutum da zanan qaddarar sa, kuma ko wani mutum da irin tasa qaddarar, don Allah kiyi haquri ki dena zubar da hawaye haka, insha Allah zamu samu cikar burinki da izinin Allah wata rana zamu hadu da su!
Cikin kuka Mamie ta fara magana tabbas nayi kuskure a rayuwata Abdul, gashi hakan yajamin rashin kwanciyar hankali da nutsuwa,
Kuka sosai takeyi, har ga Allah ya tausaya mata dan haka yayta rarrashinta har ya samu tayi shiru,


Kicin ta nufa ta sa ruwan zafi ta hada tie sannan ta fito ta zauna a kan dining ta fara sha, tana cikin sha ameerah da zahra suka shigo falon da sallamar su cike da kulawa Mamie ta amsa sallamar tare da sakin fuska sosai baki ameerah ta saki tana kallon Mamie, zahra kuwa hankalinta yana kan Falon musamman yanda taga komai sabo ne bugu da qari ma gurin Yayi matiqar haduwa, a hankali ta furta waw gaskia falon nan ya hadu,
Ta juya da nufin ta tabo ameerah ai se sukai ido biyu da Mamie, air se itama ta tsaya tana kallon Mamie n, murmushi Mamie tayi sannan tace Ku shigo Ku zauna mana sekace baqi? Maza Ku shigo mana
Jiki a sanyaye suka shigo falon suka zauna ameerah CE ta fara gaida Mamie sannan zahra ma ta gaisheta, sosai Mamie ta sakar masu fuska suka dinga hira, a nan ne ameerah tacewa Mamie aunty gaskia ke kaykkyawa ce, daria Mamie tayi sosai dan har ga Allah ameerah ta bata daria,
A hankali Mamie ta sunkuyo taja hancin ameerah tace kema ai kyakkyawa ce,
Darirya ameerah tayi sannan tace aunty ni suna na ameerah wannan kuma zahra,
Murmushi Mamie tayi sannan tace ba suna na aunty ba Mamie zakice kinji?
Dariya zahra tayi sannan tace ke in banda baki da hankali Waya fada miki ana cewa babba kamar wannan aunty ? Ta qarasa maganar tareda nuna Mamie da hannunta, baki ameerah ta murgudawa zahra sannan tace an fada din ta qarasa maganar cike da tashin kunya,
Tunda ameerah ta fara zuba rashin kunyarta Mamie ke kallon ta, bata CE komaiba sema ja baya datayi daga kusa da ita ta koma kan daya daga cikin kujerun falon, sun jima a dan zaune sannan Mamie ta koma daki dan ta dakko wayarta a hanya suka hadu da Dady yana shirin fitowa falon shima, murmushi yayiwa Mamie sannan ya wuce ta gefanta ya nufi falon, yna shiga ya zauna a kan kujerar dake daukar mutum biyu, yana zama zahra ta sauka qasa tare da yiwa mahaifin nata barka da fitowa,
Sosai Dady yaji dadin abinda zahra ta yi shiyasa yake sonta sbda baba daya yaransa idan ka cire muzaffar a kyawawan halaye to se zahra ameerah kuwa yana zaune da alama ma bata da niyar sauka daga kan kujerar.
Tsawa Dady ya dakawa ameerah da sauri ameerah ta sauka qasa sannan ta fashe da kuka sbda tsoratar da tayi,


Ummah CE ta fara shigowa sannan Momy ta biyo bayanta se kuma fadilah dake bayan Momy n, Ummah CE tayi qarfin halin yin sallama,
Kallo daya Dady Yayi musu sannan ya dauke kai, a daqile ya amsa sallamar, sosai suke kallon falon sbda yanda ya hadu, koda wasa basu taba shigowa falon ba se yau, cike da masifa Momy ta fara magana tacewa Ummah kin gani ko? Ai dama na fadamiki gashi nan ai kin gani wllh dama na san tsugune bata qare ba, mun gudu ne bamu tsira ba da sauri Ummah ta dannewa Momy baki, tace haba zuwaira me kikeyi haka sekace wata qaramar yarinya?
[8:54PM, 2/6/2018] โ€ช+234 813 272 6929โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*BAFULATANA*
_True life story_


*_Written By Cibado๐Ÿ˜˜_*


_Dedicated to Khadeeja Candy_


*Page - 17*




Gaskia zuwaira baki kyauta ba, kuma gaskia ya kamata ki bawa alhaji haquri yanzunnan, ta qarashe maganar tare da kanne mata ido daya.
Nan da nan Momy ta fahimci manufarta dan haka ta sunkuya ta bawa Dady haquri,
Be ko kalleta ba ya juyar da kansa yace mata ya wuce,
Guri suka samu suka zauna, sun dan jima a zaune sannan umma tace alhaji ka kira mu amma har yanzu baka CE komai ba,
Shigowar Mamie ce ta sa umma hadiye maganar ta, da sallama Mamie ta qaraso falon kusa da zahra ta zauna , da murmushi a fuskarta tace sannan ku ya gda ?
Ummace tayi carab tace lfy qalau ya hanya? Ta qarasa maganar tana hararar Mamie,
Da kulawa Mamie ta amsa mata tare da jefa mata tambayar ta same su lfy.
A taqaice suka bata amsar lfy,
Dady yana zaune a inda yke wayarsa ya dauka a gefen kujerar daya ke zaune , ya kira wayar telho din dake dakin saukar baqinsa bugu daya muzaffar ya amsa, a taqaice Dady yace kazo falon Mamien ka Ina son Zama daku gaba daya,
Be ce komaiba ya ajiye wayar
Moddibo dake zaune kan sallayar da suka idar da sallah, bece masa komai ba se kallon sa kawai daya ke yi, jiki ba qwari muzaffar ya qaraso kusa da moddibo yace , baba wllh har ga Allah ina jin tsoron muta nan nan!
Cike da rashin fahimta moddibo yace yaro ban fahimci maganar ka ba, tsoron me kake ji?
Muzaffar yace baba INA magana ne a kan mutanen Gidan nan, ina jin tsoron kada su sake shirya min wani mugun abin!
Murmushi moddibo Yayi sannan yace yaro kaifa namiji ne dan haka ka daure ka zama jarumi, kuma ka dage da addu'a haqiqa babu abinda yafi qarfin Allah dan haka kada ka bari tsoronsu ya samu gurbi a cikin zuciyar ka, kaji yaro? Maza kaje kiran mahaifinka, Sam kada ka nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login