Showing 9001 words to 12000 words out of 19708 words
Chapter 4 - BAFULATANA Book Complete Hausa Novels BY ESHAAT.txt
damuwarta akan ya sanar da ita meyake damunsa
Fir yaqi gaya mata hakan ne ya qara tayar mata da hankali
Kafin tace wani yabu yace mata gobe kisa ahmad ya kaiki air pot ki taho Nigeria be jira cewarta ba ya kashe wayar
Hakan ba qaramin tayarwa da Mamie hankali Yayi ba se kuma ta fashe da kukan da bata San dalilinsa ba ta jima tanayi har seda kanta ya fara ciwo sannan ta haqura tayi shiru
Ban garen dady kuwa tunda ya kashe wayr umma take kallonsa cike da son qarin bayani akan wayar daya gama, dataga bashi da niyar tanka mata setace alhaji wacece wannan kuma??
Be ko kalleta ba yace matata dake qasar India itace
Dik da cewa ta girgiza Bata nuns masa komaiba
Seda ta dan jima sannan ta tashi ta fice daga falon ta nufi dakinta,
Tana shiga ta fara zarya a dakin data ga zaryar ba fishsheta zatayi ba ai seta nufi dakin Momy sbda tashin hankali ko sallama batayiwa Momy ba ta fada mata daki
A tsorace Momy ta dago tana kallonta tace haba dan Allah wllh kin tsorata no bata kulata ba ta kalli su fadeelah da suke zaune a bakin gado tace ke Ku tafi falo zamuyi magana
Ba musu fadilah ta dauki laptop dinta da wayar ta sannan ta fice daga dakin
Tun shigowar umma Momy take kallonta baki a sake tace ke wai meya faru ne?
Umma bata boyewa Momy komaiba akan yanda sukayi da Dady,
Tashin hankalin da Momy ta shiga yafi Wanda Ummah ta shiga, cike da masifa Momy tace tabdi lallai ma mutuminnan ya raina mana hankali wllh be isa ba, mu ze mayar 'yan iska ?
Ashe dama gunta yakai wancen gantalallen? Wato mun gama dashi shine ze kawo mana wata tsinanniyar ko? To wllh be isa ba bari ma naje falon nasa na sameshi wllh Yayi kadan yace zega bayan mu, fuuuuu tayi hanyar fita dagudu umma ta rugota tace ashe baki da hankali ?
Yanzu idan kikaje masa a haka kina ta jaraba ai seya zargemu akan hallaka masa dansa
Kinga kawai mujira muga zuwanta idan ta ishemu base mu kashe shegiya ba?
Da fara'a Momy tace yauwa 'yar gari dadina dake a kwai tunani. Suka tafa sannan suka cigaba da qulequllensu
Allah ya kyauta
Ni wacece da za'a sani a gaba ?? Har wacece cibado a cikin marubuta?
Wllh ni ba kowa bace illa me koyan rubutu har yanzu ban qware ba! Zefi a gareku kudena wahalar da kanku a kaina sbda in yar koyo CE, kuma daga yau ni cibado na dena rubuta sannan lbri dan haka Ku kwantar da hankalinku
No cibado ban Iya tashin hankali ba ๐
[8:52PM, 2/6/2018] โช+234 813 272 6929โฌ: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado๐_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page -1 2*
Sun Dade suna qulle qullensu sannan umma ta nufi dakinta zuciyar ta fal farin ciki
Tunda Rabe taji batun tafiyar muzaffar hakan ba qaramin daga mata hankali yayi ba, amma sedai ba yadda ta Iya dama tasan dik daran dadewa dolene wannan ranar zata zo
Shiyasa bata son sabawa da mutane daga qarshe suzo su barta,
Muzaffar na fitowa daga daki hanyar garke ya nufa sabda yasan nan ne gurin zaman Rabe bata da wani gurin zuwa se nan,
Yana qrasawa kuwa ya hangeta a zaune tayi shiru da alama tinanin wani abun takeyi,
A hankali ya fara tafiya sadaf sadaf sbda baya so ta ganshi ayko yayi sa'a bata ganshiba har ya qaraso daf da ita hannunsa ya daga ya tafa aiko seta zabura zata gudu, da sauri ya ruqo hannunta yace ke tsaya matsoraciya kawai ya qarashe mganar yana dariya
Kamar zatayi kuka tace yaya zafar meyasa kake son tsorata mutum?
Cike da kulawa yake kallonta sannan yace ke kadai nake iyayiwa haka sabida ke din qanwata ce kuma inaji dake Rabi'atu ya qarasa maganar tare da Jan kumatunta.
Tunda ya fara magana Rabe take kallonsa kawai seta fashe da kuka, nan da nan hankalin muzaffar ya tashi cike da tashin hankali yake tambayar ta meke damunta!
Da kyar ta Iya bude baki tace yaya zafar idan ka tafi Dawa zan dinga hira ? Kuma Dawa zan dinga zuwa kiwoo? Ta qarasa maganar tana kuka me cin rai๐ญ
Tunda ta fara maganar yake kallonta dan haka sosai ya tausaya mata be Iya CE mata komai ba ya jawota ya hadeta da qirjinsa yana rarrashinta , ta Dade tana kukan sannan tayi shiru,
A hankali ya zaunar da ita sannan ya fiskanceta yace, Rabbi'atu har ga Allah nima zanyi kewarki bama ke kadai ba Harda baba, amma zanyi miki wani alqawari amma se kin min alqawarin bazakiyi kuka ba gobe idan zan tafi,
A nitse ta dago jajayen idonta da suka fara kumbura tace uhmm ni se kace zaka zauna tare dani anan shine bazanyi kuka ba, cike da quruciya tayi maganar
Abin yaso ya bawa muzaffar dariya amma kuma seya dake yace haba qanwata idan kika CE haka to ni kuma babana fa?
Kinga ai ze damu tunda besan inda nake ba ko?
Da sauri tace to ba se shima yazo nan mu zauna tare ba?
Sosai muzaffar yayi dariya har yana tafa hannu
Sannan yace ai bazeyu muzo gidanku mu zauna ba sabda muna da yawa sosai, dasauri tace aini kai kadai nake so mu zauna tare dakai๐
Sosai maganar ta ke taba zuciyar muzaffar
Kamar daga sama tace nasan idan ka tafi Gidan Ku mantawa zakayi dani!
Da sauri ya kalleta sannan yace wllh bazan manta dake ba qanwat..... Bata bari ya qarasa abinda zece ba tace to kamin alqawarin komai daran dadewa zaka dawo gareni yaya zafar!
Muzaffar yace ki yarda dani mana!
Da sauri tace bazan yarda da kaiba har seka min alqawarin zaka dawo gareni wata ranah!
Batare da tinanin komaiba yace nayi miki alqawarin zan dawo gareki qanwata
Sosai abin yay mata dadi dan haka tayi dariya sosai sannan suka kama hanyar gda.
Suna tafe suna hira Har suka qaraso gida, suna shiga da Laure suka fara arba aiko da sauri Rabe tayi bayan muzaffar, beyi mamaki ba sabda yasan tana bala'in jin tsoronta, cike da girmamawa ya gaida ta a daqile ta amsa be damu da hakan ba ya wuce daki abinsa yana tafiya Rabe na take masa baya seda yaje daf da qofar sannan ya tsaya yace INA kuma zaki?
Ba tace masa komai ba ta nuna masa dakin bece komaiba ya shiga ita kuma tabi bayan sa
Ina miqa gaisuwata me tarin yawa a gareki aunty Qween ๐
Bazan mata da cikakkiyar masoyita ba (Sadiya na Abbah )๐๐
[8:52PM, 2/6/2018] โช+234 813 272 6929โฌ: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado๐_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 13*
Yana shiga ya nemi guri ya zauna itama zaman tayi tunda ta zauna take kallon sa tun be lura ba har ya ya fahimci irin kallon da take masa, amma seya share sabda yasan indai ya kalleta dena kallon sa zatayi, shi kuma haka kawai yaji baya so ta dena kallonsa haka kawai yaji yana son hakan,
Ta jima tana kallon sa sannan ya dago ya kalleta se kuma ya kashe mata ido daya ๐คช
Da sauri tayi qasa da idanunta sbda wani irin kwarjini da yay mata bugu da qarima ga kashe mata idon dayayi
Abine ya bashi dariya yace qanwata ta kaina wllh bana so ki dinga damuwa nace miki idan na tafi zan dawo wani lokacin kodan sabida ke๐
Ya qarasa maganar tare da nuna ta da hannunsa,
Sosai maganar tayi mata dadi dan haka ta saki murmushin daya qara baiyana kyawunta sannan tace na yarda dakai yaya zafar! Nasan bazaka manta dani ba kuma nima bazan manta dakai ba zafar,
Da sauri ya kalleta yace amma meyasa kike kirana da zafar ?
Murmushi tayi sannan tace sbda bazan Iya fadar sunanqanwata, sbda akwai wahalar fada,
Tunda ta fara magana yake kallon ta sannan yace oho shiyasa kike cemin zafar? Ta daga kanta alamar ae, dariya yayi sannan yace hakan dakike cemin ma yana min dadi qanwata,
A nitse ta kalleshi tace yaya zafar idan ka tafi zanyi kewarka sosai bazan gaji da gayama cewar na saba dakai ba , ni kaina bansan dalilin daya sa nake jin zafin tafiyarka a raina ba yaya zafar!
Sosai yake kallon ta tunda ta fara magana sannan yace ni kaina INA jinki a raina Rabi'atu! Ta yanda har nake jin bana so na tafi na barki! Har ga Allah naji jini na ya hadu dake, bama Iya nanan abin ya tsayaba shiyasa ma nake kiranki da qanwata ,
Bayan Mamie na da dadyna ban saba da kowa ba se ke! Dan haka kina da matsayi a zuciyata dama rayuwata gaba daya!
Yanda ta nutsu tana sauraransa seka rantse tana fahimtar abinda yake fada , ta Dade tana juya abin a ranta kafin ta jefa masa wata magana wadda seda yayi mamakinta , CE masa tayi yaya zafar dama ana Iya bawa mutum matsayi a zuciya?๐ณ
Da sauri ya kauda tinanin ta daga maganar yace mata a'a ba'ayi, suna cikin maganar Laure ta bankade qofar dakin tace to tsinanniya fito nan kiyi min aiki
Kin shige daki da namiji kina lalata dan rashin kunya se liqe masa kike yi se kace ba BAFULATANA ba !
Karuwar banza karuwan wofi, sosai abin yayiwa muzaffar zafi a rai amma seya danne zuciyar sa, Rabe ko banda kuka ba abinda takeyi, a hankali ya matasa kusa da ita yana rarrashinta. Laure kuwa seda ta gama tijarar ta sannan ta fice ta bar musu dakin!
Sosai abin ya batawa muzaffar rai dan haka ya kasa cewa komai, cikin tatatausan lafazi yace tashi kije kiyi shirin kiwo mutafi
Tana jinsa amma setayi kamar bataji me yace ba ta cigaba da kukanta, sosai kukanta yake taba zuciyarsa dan haka seyaci gaba da rarrashinta daqar ya samu tayi shiru,
Suna cikin haka ne moddibo yay sallama a qofar dakin sannan ya shigo beyi mamakin ganin su tare ba sabda hakan ba sabon Abu bane
Da gudu Rabe ta mike ta nufi Baban nata ta rungumeshi se kuma ta sake fashewa da kuka cike da damuwa moddibo ya dagota yana kallon fiskarta yace meya faru kuma ?
Bata CE komaiba sabda kukan daya ci qarfin ta da qar ta Iya nunawa moddibo muzaffar da hannunta tace baba yaya zafar ne wai zetafi Gidan su ya barmu, ta qarashe mganar tare da cigaba da kukanta,
Murmushi moddibo yayi sannan ya dafa Kafadunta yace haba mamana , meyasa zakiyi haka?
Kadafa ki manta ke qanwarsa CE dole wata rana ze sake zuwa dan ya ganki dan haka ki dena kuka kinji mamana?
Da sauri ta daga kanta alamar ta yarda da batun Baban nata, dan hka ta share hawayenta sannan ta koma kusa da muzaffar tace yaya baba yace zaka dawo wata rana dan haka bazan sake kuka ba sbda babana baya min qarya komai ya fadamin gaskia nake daukar sa, tunda ta fara maganar muzaffar yake kallonta sosai yake nazarin yarinyar gata qarama amma tana da kaifin tunani wannan idan ta kai shekara 20 yazata kasance?
Lallai Rabi'atu tana da wayo kuma yana jinjina irin soyayyah dake tsakanin ta da mahaifin ta,
Murmushi yayi mata tare da Jan hancinta da hannunsa dikansu dariya sukayi sannan suka yiwa moddibo se sun dawo sannan suka wuce kiwo ita da yayan nata.
Gasar India
Tunda momie ta ji batun Dady na ta zo Nigeria hkan ne ya tabbatar mata tabbas akwai matsala, to meyasa Dady ze mata haka? Bayan yasan bata son zuwa Nigeria, sbda wani dalili nata!
To meye wannan dalilin na Mamie da ze hanata zuwa qasarta na haihuwa?????
Jikinta ba qwari ta mike ta shiga hada kayan da zata tafi dasu, dik wasu mahimman takardu na Dady seda ta hada su guri daya a cikin wata qaramar a kwati sannan ta kulle, dik wasu kayan da zata buqata seda ta dauka sbda ta qudurtawa kanta cewar bazata sake dawowa qasar India ba, wannan Karon yaki zatayi da wa'yanda suka rushe mata farin cikin ta na rayuwa!
Nigeria
Bangaren Dady kuwa daqar ya mike ya nufi toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin wata farar shadda me ratsin blue ammata din kin irin na dattijawa ba laifi kayan sun masa kyau dik da ramar dake jikinsa kana kallon sa zaka fahimci baya cikin kwanciyar hankali, yaa fito cikin shirin fita Momy ya samu a zaune a falo se su fadilah da zahra'au, se kuma ameerah da Fa'iza dake ta fada akan rumot , fitowar Dady CE ta katse ameera da fa'iza sukavar fadan da sukayi sbda sunsan Dady ba wasa a lamarinsa !
Dady ya kalli fa'iza dake cika tana batsewa yace dan ubanki baki da kunya ko? Zakici qaniyanki,
Daga haka yayi waje abinsa be sake cewa kowa komai ba , yana fita ya bude mota ya shiga bashir driver yaja motar suka dauki hanyar Gidan shugaban 'yan sanda wato haruna musa majia.
To se ince a suka lafiya dady๐
Bani da ta cewa sedai ince Allah ya shiga tasakanina daku!
Bani da qarfin da zan Iya kare kaina daga sharrin makiyana !
A cikin Ku babu Wanda ya halicceni balle kuma yayimin wani Abu !
Niba kowa bacce balle kusa ni a gaba .
Fatan alkhairi shine fatan cibado ga kowa, ciki kuwa Harda Ku masu yimin barazana๐๐
[8:52PM, 2/6/2018] โช+234 813 272 6929โฌ: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado๐_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 14*
Suna isa qofar Gidan aka bude musu gate suka shige kasancewar sunsan Dady sosai
Parking space suka nufa suka ajiye motar sannan ya ta sarwa qofar da zata sadashi da falon da sp majiya yake saukar bakinsa na musamman
Yana shiga ya samu guri ya zauna sannan ya dauki wayar sa ya danna number sp majiya ya sanar dashi cewar ya qaraso,
Bugu daya ya dauka ya fada masa ya qaraso sannan ya ajiye wayar ya zubawa TV idanu,
Ba jimawa aka cikawa Dady gabansa da kayan motsa baki kala kala, kodaya Dady be taba ba sabda shi yanzu ma ko wani irin abinci ya kalla Sam baya bashi shi'awar sa, dan haka kallo daya yayiwa abincin ya dauke kansa,
A hankali sp majiya ya qaraso falon tare da sallamar sa, har ya qaraso falon Dady be San ya shigo ba har seda ya tabashi sannan ya dawo daga duniyar tinanin kudan jininsa,
A dan daburce Dady yace barka da fitowa,
Sp yayi murmushi yace haba alhji abdul dubi fa yanda ka damu kanka da tunani wllh Harka rame kayi baki kamar ba kaiba, kayi haquri ka yarda da qaddarar da Allah ya aiko maka kaifa musulmi ne , insha Allah zamu samo inda muzaffar yake da izinin Allah, tunda sp ya fara magana Dady ke kallon sa sannan yace naji abinda kace sp kuma na gamsu da bayanan ka zanyi qoqarin cire ragewa kaina tinanin kamar yadda ka shawrce ni ngde Allah ya bar zumunci,
Sp yayi murmushi yace ba komai, kada ka damu,
Kuma insha Allah zamu zage dantse wajan gano inda danmu yake da ikon Allah.
Sosai Dady yaji dadin maganganun majiya dan har ya samu nutsuwa a zuciyar sa kuma yadan sake sunyi hira kadan,
Sannan sukayi sallama da juna cikin aminci har bakin mota sp majiya ya rako dady , ya shiga mota suna masu dagawa junansu hannu,
Dady be koma gda ba se 6:00pm koda ya dawo be tsaya ko INA ba se dakinsa alwala yayi ya sake fita be dawo ba se da yayi sallar magrib
RUGAR HARDO
tunda su muzaffar suka tafi kiwo bashi da aikin daya wuce kallon Rabe dik inda tabi idanunsa na kanta,
A hankali ta bude baki tace yaya zafar meyasa kake yawan kallona?
Murmushi yayi sannan yace sabda zanyi missing naki!
Sosai take kallon sa sannan tace me Kalmar take nufi?
A taqaice yace zanyi kewarki to.
Dariya tayi sosai irin wadda bata tabayi ba a gabansa a Iya zaman da yayi dasu, daqar ta saita kanta ta dena dariyar,
Tunda ta fara yake kallonta kamar wanda zeyi kuka yace, meyasa ki dariya haka?
Murmushi tayi tace abinda ka fada ne yasani dariya senaji Kalmar taban dariya,
Hade rai yayi yace to kada ki sake min irin wannan dariyar bana so, kinji yanda kika tsorata ni?
Sunkuyar dakai tayi sannan ta riqe kunnuwanta dika biyun kamar yanda yakeyi mata idan ya bata mata rai, kamar zatayi kuka ta tsuguna qasa tace kayi haquri yaya zafar badan qara ba,
Dariya ta bashi sosai dan haka yay murmushi tare da Jan kumatunta yace shikenan na haqura amma kadan.
Dariya sukayi dukansu, sannan suka kamo hanyar gida dabda magariba suka dawo,
Tunda suka dawo Rabe bata qara bari sun hadu da zafar ba, a cewarta wai bata so taga tafiyar yayan nata !
Daki ta nifa tayi sallah tayi addu'ointa ta shafa, amma kuma bata tashi daga gurin ba,
Bangaren muzaffar kuwa tunda suka shigo