Showing 1 words to 3000 words out of 19708 words
Chapter 1 - BAFULATANA Book Complete Hausa Novels BY ESHAAT.txt
๏ปฟCOMPILED BY
ESHAAT SMILER
HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE
?๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*BAFULATANA*
*_Written By Cibado๐_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 1*
Ina me farawa da sunan Allah subahanahu wa ti'allah Wanda shine zemin jagoranci rubuta wannan littafi nawa, INA me roqon Allah daya bani ikon gamawa lfy,,
Wannan lbariine da ya faru da gaske ba wai qagaggen labari bane, cikin ikon Allah zan fara kuma in gama da ikon sa.!
***
Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya CE wadda bazata wuce shekaru goma sha hudu ba she kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta be, cike da damuwa yarinyar ta daga manta ta kalli mahaifin NATA cika da kulawa tace wllh Baba nagaji kawai ka tafi idan na huta zan tawo cike da damuwa ta ware maganar
Cike da kulawa mahaifin nata me kallonta sannan yace to rabe, amma fa ki kula sosai a nitse ta amsa da to baba, yana kaiwa nan ya juya ya nufi hanyar gida, yana tafiya Rabe ta nufi wata bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta a nitse ta core takalmin robar dake wafarta tana cirewa ta shin gida, bata jima da kwantawa ba bacci ya dauke ta sabda gajiyar data yi mata yawa kallo daya Zak ayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da take
A hankali iska me dadi ta fara kadawa can kuma se aka fara iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar rabe daga bacci a hankali ta daga idonta zama aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci Yayi maganar aiko se shanun suka fara tafiya kamar yana tace musu suna cikin tafiya aka fara ruwa kamr wasa can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin qwarya aiko ruwan nan haka yayiwa Rave dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji 'yana magana lol
Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru a kan hanya aiko jikin ta yay jajir da jar qasa haka tai tayi har seda ruwan ya dauke sannan ta kama hanyar gida basu jima ba suka iso gida seda ta fara kai shanun cikin garken su sannan ta qarasa inda bukkokin su suke da gudun ta ta qarasa bakin qofar da zata sada ta da dakin matar babanta da sallama ta shiga tare da fadin inna na dawo cike da bacin rai tare da tarin tsana take kallonta, cike da masifa ta fara CE mata ki fita ki bani guri shegiyar yarinya me baqin jinin tsiya har yanzu kinqi auruwa sabida baqin jininki uwarki ma a tsiyace ta qare kuma kema a haka zaki qare muddin ina numfashi,
Tunda ta fara maganar Rabe me kallonta cike da rashin fahimta dan ita harga Allah bata fahimci abinda innah Laure take nufi ba Sam kullum tana gaya mata haka amma Sam abin baya damun ta amma kuma meyasa take yawan gaya mata haka? Kuma meyasa take yawan tunani akan magar innar a yan kawanakin nan?
Cike da mugunta inna Laure ta dauki kwanon dake gabanta ta jefi Rabe dashi a gishi aiko nan da nan mini ya fara fita a goshin ta a gigice ta juya ta nemi hangar fita daga bukkar dan Neman agaji sabida gigita da tsoron jini da Rabe keda shine yasa ta nufi hanyar garken shanunsu aiko se sukayi kacibus da mahaifin ta wato malam moddibo,
Cike da tashin hankali take firta innanillahi'wainnah'ilaihirraji'un
[8:47PM, 2/6/2018] โช+234 813 272 6929โฌ: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado๐_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 2*
Cike da tashin hankali ya nufeta tare da kama goshinta da sauri ya kama hannunta suka nufi dakinsa dan yasa mata maganin daze tsayar da zubar jinin, cikin ikon Allah kuwa jinin ya tsaya,, amma sedai goshin ya kumbura sosai kuma Yayi jajzir kasancewarta fara, a hankali ta shiga sauke numfashi sabida zafin da gurin ke mata cikin sanyi murya baba ya fara magana Lamar haka
Rabi'atu kiyi haquri da rayuwa kamar yanda nake gaya miki kullum kuma dik abin da ze dinga hadaki da Laure ki dinga kauce mashi sbda bata da burin daya wuce ta illatamin ke, kuma sanin kanki be bani da kowa yanzu seke tunda na rasa mahaifiyarki na rasa wani bangare na rayuwata shikuma dan uwana tuna kina jaririya aka nemashi aka rasa seda ga baya aka samu gawarsa a bakin hanya, run daga lokacin muka dena bin titi da dabbobin mu, tunda na rasa iyaye na ban qara samun farin ciki ba seda na auri mahaifiyarki, amma itama daga baya Allah ya karbe ta, ta rasu ta barmin ke tun kina shan nono a haka kina fara girma ina kula dake
Bayan rasuwar mahaifiyarki da shekara 2 malm iro yazomin da shawarar na qara aure sabida ki samu rayuwa me in ganci, cike da damuwa na kalleshi nace mai yanzu iro wace macce zan aura wadda zata Iya kulamin da Rabe??
Har ga Allah bana so ta rayu da ciwon maraici cike da kulawa malm iro ke kallon sa har ya gama mgana,,
Can kuma se Yayi murmushi yace zan baka qanwata Laure ka aura nasan zata riqeta da gaskia, badan zuciyata ta ameence ba na yarda nace zan aure ta
Da malam iro ya fahimci zuciyata bata gama amincewa da mganar auren ba se ya sake murmushi a karo na biyu yace indai ka amince ka aureta nikuma nayi maka alqawarin zan zama me koyar da ita ilimin addini cike murmushi ya qare maganar,
Batare da tinanin komai ba na amince zan auri Laure. Ashe abinda ban sani ba shine sanadin tarwatsewar rayuwar gidana da farin cikina na auto ba ya qare maganar tare da matsananci kuka๐ญ๐ญ
A nitse Rabe ta rarrafo kusa da mahaifin nata ta rugumeshi tana kuka tare da share mai hawaye da tafin hanunta seda moddibo Yayi kukan me isarsa sannan Yayi shiru, cike da kulawa yace kinci abinci ko? Da sauri ta daga masa kanta alamar ae kuma a zahirin gaskia bata ci ba the ae ne kawai dan hankali n mahaifin nata ya kwanta
Moddibo yay murmushi yace to maza tashi ki tafi daukar karatu maza jeki kuma banda tasayawa wasa kinji Allah ya albarkaci rayuwar ki Rabe na
Ta amsa da amin sannan ta tashi ta nufi makarantar allon malm iro inda take daukar karatu
Dik da cewa su fulanin daji ne amma hakan baya hanasu karatun addini dik cikin sa' oin Rabe babu wacce batayi aure ba se ita da ruqatu sune kawai suka rage a yaran da basuyi aure ba
Rabe kyakkyawar yarinya ce kallo daya zakai mata ka fahimci hakn tana da many an idanu tare da gashin gira me yawa hancinta dogo ne sosai kamar na mahaifin ta sannan ya a da dan fadi kadan labbanta ma daidaita ne kuma suna da dan tudu kadan tanada yalwataccen gashin kai ma'ana yana da tsayi sosai, Rabe doguwa ce amma ba sosai ba kallo daya zakayi mata ka fahimci tana da kyau da diri irin na fulanin asali, Rabe miskilace ta ajin qarshe magana ma ba damunta tayi ba balle ma tayi ta sedai hakan baya hanata Haida muta ne rabe yarinya be ma'abociya fara'a da son karatu hakan ne yasa malm iron ke qaunarta sosai
Sbda tana gane karatu sosai koda wasa bata sakewa samarin rugar tasu wannan ne yasa suke cewa tana da girman kai , amma a zahiri sam ba haka bane, a nitse ta qarasa makarantar ba Wanda yazo se ita kadai tan zuwa ta ajiye allon ta ta dauki tsintsiya ta share gurin sannan ta shimfida tabarman kabar tahau ta zauna ta fara bitan karatunta dan a ranar zata wanke allon ta
Tana cikin karatun ne ruqatu ta qara so da sallamar ta amma rabe bata tsayaba seda takai aya sannan ta daga kai da murmushi ta ansa mata sallamar
Ruqatu tayi dariya tace sannu sarkin hadda shine ko ki biyo min ko?? To ai gashi nazo nima kuma nasan dan ki rigani wanke allo ne yasa kika tawo kika barni ko to ai na gane wayon naki
(cikin harshen fulatanci suke maganar nayi haka be dan me karatu ya fahimci gundarin labarin sbda idan nayi ammafani da harshen fulatanci ba lallai wani ya fahimci abinda nake labarin yake nufi ba)
Rabe tayi dariya yace ruqatu kenan keada zakiyi aure kwanan nan ai kin ma kusa ki dena zuwa makarantar
Ruqatu ta hade rai tace to ai se munyi sauka zanyi kuma yau saura sati biyu mu sauke da ikon Allah murmushi Rabe tayi sannan tace to Allah ya nuns mana sati biyun
[8:47PM, 2/6/2018] โช+234 813 272 6929โฌ: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado๐_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page -3*
Da haka suka rufe hirar tasu saka makon qara so wan malm iro gurin cike da girmamawa suka gadashi ya amsa tare da sakin fuska yace dasu qawayen juna sukai murmushi suka sunkuyar dakai,,
Ruqatu aka fara biyawa kallonta sannan aka biyawa Rabe nata, suna kammalawa sukayi sallama da mlm suka kana hanyar gidajensu a hanyar komawar su ne sukai kacibus da Aliko Wanda ze auri ruqatu, cike da fara'a suka gaisa da Rabe ita kuwa ruqatu se boye fiska take a bayan Rabe wai ita kunya lol
Basu jima a tsaye ba Rabe tayimai sallama ta nufi gida cike da tinanin me zata tarar ta bata dawo gida ba se yamma liqis kasancewar suna da nisa da makarantar, cike da fargaba ta qarasa dakin da take kwana ta kwanta tare da sauke ajiyar zuciya,
A hankali ta firta alhamdulillah, dan har ga Allah batason haduwa da inna Laure dan tasan haduwarsu ba alkairi bane, tana cikin wannan tinanin ne taji kamar an taba mata qofa da sauri ta mike tsaye dan a tariga ta gama tsorata a, a zatonta innah Laure ce , da sallama ya shigo dakin tana ganinsa ta tafi da gudu ta rungume shi se kuma ta fashe da kuka sosai kukan ta ke taba zuciyarsa be hanata ba sda tayi me isarta sannan modibo ya share mata hawaye yace da ita kiyi haquri Rabe nasan tsoron Laure ne yake damun ki amma kiyi haquri wata rana se labari kinji ? Da sauri ta daga kanta alamar ae a hankali ya kama kafadunta ya zaunar da ita a bakin katifar ciyawar dake dakin yace daga yau nayi miki alqawarin bazaki sake kukan rashin uwa ba kinji ? Yana kaiwa nan a zancen sa yay hanyar fita da sauri ta dago tace baba kayin aure ko zan dena ganin innah Laure!
Cike da mamaki moddibo ya juyo yana kallon Rabe๐ณ aure kikace Rabe? Ba tare da tinanin komaiba ta daga kai alamar ae
Jikin sa a mace ya tako inda take ya dafata cike da kulawa yace dagaske kike kina son aure? Ba tare da fargaba ko shakkaba tace ae baba Ina so, harga Allah bata San me ake nufi da aure ba kawai ta fada ne dan ta samu sauqi a zuciyata
Mobabah yay murmushi yace shike nan zan kawo miki miji har gida kinji?
Da sauri ta washe baki cike da yarinta tace to babah yaushe zaka kawo shi?? Abin ma seya bawa moddibo dariya๐ itama murmushin tayi
A hankali ya kama kumatunta yace nan da 'yana kawanaki kadan zan kawo miki shi yana kaiwa nan yay hanyar fita ya tafi masallaci, itama tashi tayi taje tayi alwala tayi sallah sannan ta tashi ta nufi dakin babanta, tana shiga ta sameshi a zaune yana Hada magunguna, dayake yana bada magani irin na Gargajiya dik rugar su shi ake kira idan rashin lafiya ya samu wani cikin ikon Allah kuwa ana dacewa da maganin sa,
Da sallama ta shiga ta zauna,,,, tayi shiru bata ce komai ba ta hakan ne ya fahimci yunwa take ji be ce mata komaiba ya dakko kwanon dake gefansa ya mika mata da sauri ta karba furace da nono nana da nan ta kafa kai tafara sha yanda take shan furar ne abin ya bawa moddibo mamaki a nan zuciyar sa ta fara zargin anya kuwa Rabe taci abinci yau kuwa???
[8:48PM, 2/6/2018] โช+234 813 272 6929โฌ: ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ๐บ
*BAFULATANA*
_True life story_
*_Written By Cibado๐_*
_Dedicated to Khadeeja Candy_
*Page - 4*
Tabbas ze Iya daukar komai amma fa banda horon yunwa a fisace ya tashi ya nufi bukkar Laure ko sallama be mata ba ya hauta da bala'i kan cewa ze jure komai da zatai mai amma fa Sam be yarda da horon yunwa ba
Tunda ya fara masifar Laure ke kallonsa cike da mamaki sabida tunda take da moddibo be taba daga mata murya ba balle yay mata fada, Ashe haka moddibo yake?? Tabbas ta yarda ransa ya bacci sosai shiyasa bata CE masa komai ba tunda ya fara fadan, idan tace zatayi magana to tabbas komai ze Iya faruwa Wanda kuma ba lallai yay mata dadi ba
Yana gama zazzaga mata yay gaba ya barta da fargabar halinsa
Yana futa dakinsa ya nufa da sallama ya shiga dakin inda ya bar Rabe anan ya sameta da fara'arta tace sannu da zuwa yay mata murmushi ya shafa kanta, sun jima tana yi masa shirmen hira har ya gaji yace taje tayi bacci,, ayko fir taki tafiya wai seya rakata, haka kuwa akayi har dakin ta moddibo ya kaita seda ta fara bacci sannan ya tofa mata adduah sannan yay waje
Wshe gari da zanyi safiya Rabe ta fito cikin shirinta na tafiya kiwo, sanye take da kaya irin nasu na fulanin asali,qarta kuwa sanye take cikin wani rufaffen takalmi na roba,
Dakin moddibo ta nifa da sallama sannan ta shiga a zaune ta sameshi yana Karin kumallo, da fara'a ya dubi Rabe yace qara so kusa dani mana mamana? Cike da fara'a ta qarasa jikn Baban nata cike da soyayya ta fada jikin sa
Tare sukayi Karin kumallon dashi bayan sun gama ne suka fito tare a waje sukaci karo da Laure. Aiko seta hde rai kamar taga mutuwar ta
A dan tsorace rabe ta gaisheta, seda ta faki idon moddibo sannan ta wtsawa rabe wani kallo aiko da sauri Rabe ta koma bayan moddibo ta qanqameshi bece komai ba ya kama hannunta suka fice daga Gidan
Suna fita garke suka nufa dan su fita kiwo
A nitse ta kallo moddibo tace baba yau ni kadai zani kiwo na kaga se mu raba shanun biyu kai kayi hanyar gabas nikuma nabi yamma idan muka dawo se a ga nawaye sukafi qoshi ko?
Cike da kulawa yace mata to muje sena raba mana ko, da sauri take binsa cike da zumudi zata kiwo ita kadai
Basu dai lokaci ba ya raba shanun gida biyu ya Tisa nasa yay gaba itama tayi gaba seda yay mata kashedin ta kula da kanta sosai kuma kada tabi ta hanyar da bata da kyau ma'ana banda bin titi sbda ya tsani bin titi tunda ya rasa qaninsa zakariya๐ญ
Tafiya take cike da kwanciyar hankali daganin ta kasan tana cikin farin ciki da walwala haka sukaita yawo a cikin dajin seda suka dau lokaci me tsayi sannan Rabe ta lura lokacin zuwa makarantar ta Yayi
Dole ta kora shanun suka kama hanyar gida, koda ta dawo seta fahimci babanta be dawo ba, kuma kullum shine yake rigata dawowa daga kiwo to meyasa yau be dawo da wuri ba??
Bangaren moddibo kuwa yana hanyar dawo wansa daga kiwo ne se ya hangi kamar mutum a kwance da Yayi zaton ko hutawa yake amma dya qaraso seyaga sabanin tinanin sa
Yaro ne matashi sanye yake da wata tsaleliyar shadda light blue an masa dinkin jamfa kansa babu hula kansa wani qaton Sara ne hakama qirjin sa da kuma bayan sa
Jikinsa dik jini ne a jiki dik da saran dake jikin sa hakan baze hanaka fahimtar yana da kyau ba cikin sauri moddibo ya qarasa kusa dashi ya dago shi a nan ne ya fahimci yana numfashi, sabida tsabar riki cewa ma ya rasa ta India ze fara bashi taimako,, (likitan Gargajiya kenan lol)
Can dabara ta fado masa ayko da qar moddibo ya Iya dagashi ya Dora a bayan saniya daya ya daure shi a jikinta ta yanda baze fadi ba suka nufo hanyar gida
Sun jima sannan suka qara