Showing 15001 words to 18000 words out of 23148 words
Chapter 6 - AUTAR HAJIYA COMPLETE Book Writing by Zeey Maman khady.txt
ta juye, saida ta zuba cokali biyar ciakakke sannan tasa cokali ta motse,
Ta kulle ledar gishirinta ta kakka6e hannunta tayi saurin barin kitchen d'in.
Cike da mamaki Auta ta shigo kitchen d'in, ta bud'e miyar tasa cokali ta motsa lokacin gishirin yagama narkewa cikin miyar, saboda haka zubar da miyar tayi ta ta d'ora wata cikin 'kan'kanin lokaci tagama had'a wata sabuwar miyar ta gama kome ta had'a lemun abarba, tasaka pridge sannan ta gyara ko'ina na kitchen d'in,
'Daki ta wuce ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito simple kwalliya tayi sannan ta d'auko riga da siket na atamafa ta sanya ta dauko turare ta feshe jikinta dashi, tafito falo sai 'kamshi take bugawa, sannan ta d'auki makullin kitchen d'inta tafita zuwa kitchen d'in, dan tin lokacin dataga abinda Fadila tayimata data gama girkin ta kulle kitchen d'in ta tafi da makullin d'akinta.
Bayan tagama jera kome kan dining, lokacinne kuma khaleed yashigo gidan, cikin murna dajin dad'i Auta ta tarbeshi tayi Mashi sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ta kar6i jakar hannunsa tayi gaba zuwa d'akinsa shikuma yabi bayanta, bayan ya rage kayan jikinsa suka fito zuwa falo
Sun zauna kan dining Auta ta zuba ma Kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda 'kamshin girkin ya mamaye falon,
Fadila tasa hannu ta d'ebi loma guda zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalli khaleed tace "my man , ya juyo ya kalleta, tace "nifa wallahi fargabar saka abincinnan nake a bakina, saboda kasan gishiri yana iya yima mutum lahani, kasan fa da mutum ya d'ibgama cikinsa gishiri 'kara yaci ba dad'i.
Auta tayi murmushi tace "Fadila kici mana kiji, idan kikaji gishirin yayi yawa ai baza'ayi maki dole akan sai kinci ba, sannan ta kalli khaleed tace "my dear kaci abincinnan hankalinka kwance, nayima Alkawarin daga yanzu kagama jin wani aybu cikin abincina, wancan lokacinma matsala ce aka samu amma yanzu kome yakoma normal inshaAllah.
Khaleed bece kome ba, sai dai ya ebi abincin ya kai bakinshi cike da fargabar irin testing d'in dazeji,
Cike da mamaki khakeed ya ida saka abincin bakinsa, dan wani irin dad'i yaji yartsa kwanyarsa.
Besan lokacin daya sakarma Auta wani tattausan murmushiba, yace *Weldon* my wife, amma nayi matu'kar farin ciki dajin wannan gyara naki, gaskiya yau kin matu'kar faranta raina Allah maki Albarka ya saka miki da Aljannah, cike da jin dad'in yabata da kuma addu'ar da mijinta yayimata, tayi dariya har dimple d'inta ya lo6a tace Ameen mijina, Allah kara dan'kon soyayya tsakaninmu, yace "Ameen my wife.
Cike da mamaki Fadila ta kai abincin bakinta, take dad'in abincin ya ratsa mata kwanya, batasan lokacin data cigaba da cin abincinba, dan dama su duka akwai tsohuwar yunwa tattare dasu dan tin lokacin da Fadila tafara 6ata ma Auta abinci da gishiri suka daina cin abinci su 'koshi,
Domin dai ita Fadila kotayi ba sosai suke iya Ciba, saboda ba dad'in yau bare na gobe
Ranar dai haka suka ci abinci cike da farin ciki da annushuwa,
Sa6anin Fadila wacce ba'kin ciki yagama cika zuciyarta.
```Auta dai tagano Fadila ce me 6ata mata abinci, amma kuma bata tanka mataba kuma bata nuna 6acin ranta ba```
*_Kome take nufi da hakan kubiyo zee mman khady dan jin yanda za'a kwashe tsakanin Auta da Fadila_*
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [12/08 3:00 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*AUTAR HAJIYA* 💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘
```Page``` 131-135
✍🏽 "Haba 'kawata aini wallahi bayi fushi dake, ace tunda aka kawoni gidannan sai yau kika tuna dani,
Sadiya tace "Ayimin afuwa wallahi kinsan hidimomi idan sukayima mutum yawa sai ahankali, Auta ta harareta cikin wasa tace "kinjiki ko, ke har wata hidima ke gareki kamar wata me iyali, Sadiya tace "ay iyalin ake niyyar yi shiyasa hidimomin suka fara tun yanzu,
"Hakane fa yau saura 3 week's koh? Sadiya tace "au tambayata ma kike, duka yaushe mukayi waya dake na gaya maki.
Haka sukacigaba da firar yaushe gamo, nan Auta ke tamabyar ta "waini ina uwar gidanki? Tunda nazo ban gantaba, "Auta ta harereta tare da kaimata duka cikin wasa tace "Uwar gida fa kikace, kodai amarya' ay nice uwar gidan kamar yanda nad'au Alwashi, nan auta tabata labarin yanda sukayi ranar da aka kawosu da kuma kwanakin da suka kwashe suna kwanan zaune.
Sadiya tayi dariya sosai sannan ta kalli Auta tace "kai Auta bakida dama gsky rigimarki tafiki 'karfi, khaleed d'in kuka samu shiyasa kuke yanda kukaga dama, idan nice shi wallahi sai in za6i d'akin danikeso kawai inyi kwanciyata kuma dole wacce ban za6a ba ta hakura.
Auta tayi dariya tace" Ay koda hakan yayi nasan d'akina ze za6a dan na dad'e da fahimtar irin tsananin son da khaleed kemani, shiyasa bani yarda inyi abinda zai 6ata ransa,
Sadiya tace Yauwa 'kawata haka yakamata kiri'kayimasa shine zesa ya'kara jin sonki da 'kaunarki, kuma kada ki yadda koda wasa kiyi fad'a da abiyar zamanki wanda ze d'aga hankalinsa randa duk haka ta kasance sai son dayake maki ya ragu a cikin zuciyarsa.
Auta tace "ina ay bazan yarda haka ta faru ba, dan nayi al'kawarin babu ranar daza'ayi kace-nace dani a gidannan, amma kuma naga take-rakenta tana Neman ta ragemun son da mijina yakemin ta haryar 6atamin duk wani Abu dana girka dan na faranta ransa.
Nan Auta ta kwashe labarin yanda Fadila tari'ka zabga mata gishiri cikin abinci, Wanda sanadin haka khaleed yafara juya mata baya,
Sadiya tace "tab ammafa yarinyar nan makira ce, wato ita nata ba dad'i shine ta 6ata maki,
tsabar ba'kin ciki kawai, amma kin kyauta da kika kyaleta, kawai ki ri'ka kaffa-kaffa da duk wani Abu wanda kikasan zata iya 6ata maki.
"Tab wallahi bazan 'kyaletaba, Auta ta fad'a cikin d'aga murya, Sadiya tayi saurin sa hannunta ta rufema Auta baki, tare da cewa "ki rufamin asiri kada kiyi wani Abu ace nice nazo na sakaki, kuma kinsan fa yanzu haka tana jinmu,
Sai lokacin Auta tayi 'kasa da murya tace "wallahi bazan 'kayletaba dole sai na rama abinda tayimin, sadiya tashiga bata hakuri akan ta hakura ta 'kyaleta ai dai tasan tafita, Auta tace "Hmm Sadiya inaga kin fara manta ni, sadiya tayi murmushi tace "ina zan manta da rigimarki Auta, amma ai yanzu yakamta ki rage wasu abubuwan saboda yanzu gidan aure kike ba gidan iyayenki ba.
Auta tasan halin Sadiya idan ta biyemata tsaf zata sage mata gwuyawu taji bazata iya aiwatar da kome akan ramuwar abinda Fadila tayimata ba,
Yawarta ta d'auka dake ajiye kan bedsite ta duba, sannan ta kalli Sadiya tace "kinga rana tayi har karfe sha d'aya da yan mitoci, bari nashiga kitchen na samo maki abinda zakici, nasan bazaki iya cin abincin waccan matar ba,
Sadiya tayi murmushi tace "wallahi da kin barshima dan tafiya zanyi yanzu, Auta tace wallahi bazaki tafiba sai kinci abinci, kinsan me zan dafa maki, bata jira abinda zata fad'a ba tace taliya da manja da yaji zan dafa, nasan ke mayyar tace, suduka suka sa dariya.
Tare suka shiga kitchen d'in, cikin minti talatin suka gama girka taliyar suka zuba a flate, sauka zabgo uban yaji, amma duk da haka saida Auta ta taho da wani Yajin cikin wani 'karamin vowel wai zata 'kara gabanta.
Sai gurin karfe sha biyu da rabi Sadiya tayi haramar tafiya gida, tare suka fito daga d'akin a babban falo suka had'e da Fadila ta fito daga d'akinta zata shiga kitchen, nan suka gaisa da Sadiya kowanensu ba yabo ba fallasa, sannan suka wuce, har kusan get Auta ta rakata sukayi bankwana, tare da mi'ka mata wata yar 'karamar leda wacce ta had'amata kayan make-up aciki.
Auta na komawa d'akinta, toilet ta fad'a ta she'ka wanka, bayan tafito ta zauna gaban mirror ta d'and'asa kwalliya, sannan ta d'auko wasu 'kananan kaya riga da wando ta sanya,
Rigar ta d'an sauko dan ta rufe mata rabin cinyarta, amma ta matseta sosai, sai wando pencil, sannan ta dauko wani karamin gyale tayi rolling, lokaci guda ta tashi daga jinsin Hausa zuwa na larabawa, dan idan ba magana tayiba sai kace bata ta6a jin yaren hausa ba.
Fadila kuwa itama lokacin tagama tsara kome na abinci kan dining, sannan takoma d'aki ta she'ka wanka shigar doguwar riga tayi ta atamfa, itama tayi kyau gwargwadon nata.
Da misalin 'karfe biyu da minti arba'in khaleed yadawo gidan, suduka falo ya iskesu, sukayi mashi sannu da zuwa, hankalinshi duka nakan Auta, kallonta kawai yake yanajin wani feeling tattare dashi,
Saida Fadila ta lura da irin kallon dayakema Auta sannan tayi dabarar zuwa kusa dashi tace, "muje ka watsa ruwa ko, ga kuma abinci yana jiranka.
Beyi mata musu ba suka wuce d'akinsa, amma cikin ransa jiyake inama Auta ce suke tare da ba abinda ze hana su kashe arna kafin su futo.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[12/08 4:14 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*AUTAR HAJIYA* 💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘
```Page``` 136-140
✍🏽 Zaune suke kan dining sunyi shirin cin abinci, kamar yanda suka saba duk wacce ke girki ita ke zuba ma kowa ta ajiye masa gabansa, yauma Fadila ce ta zuba masu ta ajiye masu, lokaci guda Auta ta ebi abincin takai bakinta,
Dadai lokacin shima khaleed ya ebo abincin yakai bakinsa,
Wani irin zafi yaji ya ziyarci 'kwalwarsa, ya mamaye duk illahirin Kansa, har cikin kunnuwansa yakejin bala'in yajin da aka zambad'a cikin abincin,
Wani mugun attaruhu aka zabga irin me yajin nan,
Kalmar innalillahi kawai yashiga furtawa, dan shi mutum ne wanda be shiri da yaji ko kad'an,
Robar ruwan dake gabanshi yayi saurin jawowa, ya tsiyaya ruwan cikin cup ya shanye, ya kara cika cup d'in ya shanye ko zeji sau'kin rad'ad'in yajin dayakeji amma abanza dan ko alamar zebar jin zafin beyiba.
Dai-dai lokacin kuma yaji Auta ta fashe da wani irin kuka, yanda kasan wata 'karamar yarinya ta tashi tsaye, duk ta wani gigice tanata yarfa hannu, ta bud'e baki tana sha'kar iska tana fad'in yaji, lokaci guda fuskarta tayi jawur, abinka ga farar mace, ga hawaye share-share.
```{Niko zee da nike tsaye ina kallon ikon Allah ri'ke baki nayi ina mamakin Auta dake kukan yaji, kamar ba ita bace tagama cin abinci da 'kawarta suka zabga yaji amma ita saida ta 'kara kan wanda suka zuba}```
Khaleed kuwa koda yaga yanda Auta ta fita hayyacinta, tanata kuka saboda yaji, besan sanda yayi saurin zuwa inda takeba ya rungumota jikinsa, ya nufi kujera three saater da ita ya zauna ya d'orata kan cinyarsa, yana rarrashinta kamar wata 'karamar yarinya, ruwa ya d'auko ya zuba cikin cup yabata ta shanye amma yana cire cup d'in daga bakinta saita fashe da wani sabon kuka,
Lokaci guda khaleed ya rud'e yarsa yanda zeyima Auta taji sau'kin yajin.
Bakinsa ya d'ora kan nata tare da tura harshensa cikin bakinta yashiga tsotsar bakin nata kamar yasamu wani sweet 🍬, wai a dole ze tsotse mata yajin,
Dama abinda auta ke nema, itama tacigaba da kissing d'insa tana 'kara shigewa jikinsa, lokaci guda khaleed ya susuce ya manta da maganar wani yaji dayakeji, yacigaba da aika mata da sa'konni masu wuyar fassarawa, ita kuma sai wani 'kara shigewa take jikinsa tana shagwa6ewa,
Abu yayi nisa hannuwan khaleed kan 'kirjin Auta yanata wasa da dukiyar fulaninta, itako batayi 'ko'karin hanashiba saima 'kara mi'ka mashi kanta datayi.
Wani irin kukan ba'kin ciki Fadeela ta fashe dashi, dan duk abinda sukeyi gabanta sukeyi, kallonsu kawai take takasa magana saura kad'an zuciyarta ta buga, wannan kukan dayazo mata shine samun sau'kin takaici da ba'ki cikin da Auta ta 'kunzuga mata.
Da sauri ta tashi tanufi d'akinta, minti biyar batayiba da Shiga, sai gata ta fito, sanye da gyale, da takalmi a 'kafarta, sai yar poss a hannunta,
Sai lokacin ta iske khaleed ya sake Auta, amma suna zaune kusa da juna kowanensu yana cike da sha'awar d'an'uwasa saboda wasanni da sukayi, abin ba'a cewa kome 🙈.
Bata ko kallesuba tanufi 'kofar fita daga falon, fuuu kamar zata tashi sama, khaleed ne yayi saurin tashi yabi bayanta yana tambayarta "Fadila ina zaki?
Bata ko saurareshiba tayi gaba abinta.
Tana fita get d'in gidan takoyi sa'a wani me napep ya ajiye wata mata wani gida kusa dasu, nan tafad'a mashi inda ze kaita, tashiga.
Khaleed na fitowa napep d'in na barin 'kofar gidan, "ya salamm ya furta, can kuma sai yayi wani guntun tsaki yace
```"kinyi laifi kuma kifi wanda kikayiyamawa zuciya```
Gida ya koma ya iske Auta zaune inda yabarta, nan take tambayarsa, "Lafiya kuwa saboda me Fadila ta tafi, be bata amsa ba sai rungumota dayayi jikinsa yafara shafata ta ko'ina, Auta batayi 'ko'karin hanashiba saida taga yana neman wuce gona da iri, sannan tayi saurin tureshi, ta tashi zaune, nan khaleed ya marairaice mata yayi kalar ban tausayi yace (please Auta help me) ki taimakeni nariga na shiga wani yanayi, cike da tsoro Auta ta kalleshi taga yanda idanunshi suka kad'a sukayi ja,
Lokaci guda ta langa6e tana bashi ha'kuri "kayi ha'kuri my dear kaga ba aykina bane, yanzu idan nabaka kaina mun shiga ha'k'kin Fadila, kayi hakuri kada kasa kanka cikin maza masu rashin Adalci tsakanin matayensu.
Haka Auta ta rarrasheshi har ya hakura, nan ya wuce dakinsa, ya shiga toilet yasake watsa ruwa sannan ya dawo yabi lafiyar gado.
Itako Auta yana shiga d'akinsa, itama nata d'akin tanufa tana ahiga ta she'ke da dariya tace
~_(Fadila dani kike magana)_~
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [13/08 7:03 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*AUTAR HAJIYA* 💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘
```Page``` 141-145
✍🏽 Da sallama Fadila ta shiga gidan, falo ta tarar da momynta tana zaune hannunta rike da (newspaper) jarida tana dubawa,
Cikin fara'a ta kalli Fadila ta amsa mata sallama, dai-dai lokacin Fadila ta tsinci kanta da tinanin yanzu idan momynta ta tambayeta meya kawota me zatace,
Muryar momynta ta katse mata tinanin datake,
"Ina me gidan naki na ganki ke kad'ai? Fadila tayi saurin dawowa daga tinanin datake ta kalli momynta tayi murmushi, dan bataso ta gane tana tattare da wata damuwa, tace "shine ya saukeni yana sauri ne yanada meeting a office d'insu shine ya wuce, yace idan yadawo d'aukata ze shigo, Momy tace "owk"
Sukayi shiru na 'yan wasu mintittika, Fadila kuwa tunani tashiga yi, a zuciyarta tana cewa:
*_Yanzu wannan 'karyar danayi idan khaleed ya'ki biyoni ya zanyi, kokuma idan yazo yace bada izininshi na fito ba , Allah dai yasa ya rufa min asiri_*
"Fadila lafiya naga kinyi shiru kamar kina tunanin wani abu, kodai akwai abinda ke damunki ne?
Da sauri Fadila ta washe ta tashi tana murmushi tace "lah ba kome Momy, tanufi hanyar kitchen tana fad'in me kuka dafa wlh yunwa nakeji,
Bata jira amsar Momy ba tashige kitchen tazubo tuwon shinkafa da miyar d'anyar ku6ewa, sannan ta d'auko lemu a pridge ta dawo falo ta zauna tafara ci, Momy kuwa kallonta kawai take azuciyarta tace *Anya Fadila*
"Fadila yanaga kinatacin abinci haka kamar wacce ta kwana bataciba?
Fadila tayi saurin kai dubanta ga momynta tace " banci abinciba na fito saboda ina d'okin ganinki Momy, tafad'a tana murmushi,
Itama Momyn murmushin kawai tayimata tacigaba da duba jaridar dake hannunta.
Har misalin 'karfe shidda da rabi na yamma khaleed bezo d'aukar fadila ba, momy ta kalleta tace "khaleed shuru kodai ya manta dake ne,
Fadila taji gabanta yafad'i tace "a'a Momy yana zuwa, inaga har yanzu begama abinda yake bane.
Fadila tashiga damuwa hankalinta yafara tashi ganin har angama sallar magrib amma khaleed bezo d'aukar taba, gashi bataso dadynta ya tarar da ita kuma tasan ana gama sallar isha'i ze dawon gidan.
Karar tsayuwar motarahi ce ta dawo da ita daga dogon tinanin datakeyi,
Da sallama ya shigo gidan, Momy ta amsa tare da yimashi sannu da zuwa, falo akayimashi masauki, bayan sun gaisa ya kalli fadila wacce dama on ready tagama shirin tafiya zuwanshi kawai take jira, yace "ki taso muje ko kinga dare yafara,
Wani sanyi fadila taji cikin zuciyarta, da khaleed be fad'i dalilin tahowarta ba.
Haka suka bar gidan, Fadila, nata godema Allah daya rufa mata asiri, dan yau da Momy tasan da yanda ta taho gida da ranta idan yayi dubu sai ya 6aci.
Haka suka shiga mota suka d'au hanya, tinda suka fara tafiya ba Wanda yacema d'an uwansa kome har suka isa gida.
Koda fadila tafito daga motar kasa shiga tayi gidan saida tajira khaleed sannan suka shiga tare,
Falo suka iske Auta zaune kan kujera, sanye take da wata riga me hannun bes da wani d'an 'karamin siket iya gwiwa, hannunta ri'ke da remote tana canja tasha zuwa *ZEE CINEMA* dayake ita meson kallon Indian film ce, kanta babu ko d'an kwali gashin nan ya zubo 'kan kafad'unta, cike da murna ta taso ta rugume khaleed, "sannu da zuwa mijina, murmushi yayi tare da bata kiss a kumatu yace "yauwa matata.
Fadila kuwa tana tsaye tana kallon ikon Allah, sai lokacin Auta ta kalleta tace "Andawo lafiya,
Bata amsa mataba illah wata uwar harara data buga mata sannan taja dogon tsaki "mtswwwww ta wuce d'akinta.
Khaleed ma d'akinsa ya wuce,
Auta kuwa dariya tayi, dan ganin tagama 'kule fadila, ta koma ta zauna taci gaba da kallonta, canja tasha tayi zuwa *STmusic* aiko ta iske an sanyo wa'kar *justing viiver* cikin wa'karshi me taken _(Love me love, kiss me kiss me)_ dama tana masifar son wa'kar duk ta iya ta, saboda haka taciga da bi, tana 'yar rawa daga inda take zaune.
Lokacin Fadila tafito daga d'akinta tanufi kitchen, ta kai dubanta ga Auta wacce tayi kamar batasan da mutum a falon ba, wani 'kululun ba'kin ciki ya tsaya mata tayi tsaki Mtsww "Aykin banza tafad'a sannan tawuce kitchen din.
Zee Elkaseem
Mmn Khady
[13/08 8:10 am] .: [13/08 7:40 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
*AUTAR HAJIYA* 💃🏻
🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
®NWA
👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘
```Page``` 146-150
✍🏽 Washe gari, Fadila tagama had'a musu break fast, kunun gyada ne ta she'ka musu, yayi gwanin kyau, dan ta masifar iya kunun gyad'a dan duk cikin abinda take girkawa a gidan shi kad'ai ne takeyi susha cikin kwanciyar hankali, kuma wani lokaci har khaleed ya yaba.
Yauma shine ta