Showing 6001 words to 9000 words out of 23148 words

Chapter 3 - AUTAR HAJIYA COMPLETE Book Writing by Zeey Maman khady.txt

16 Dec 2024

1213

da gadon datake kwance, ya marairaice, cikin sigar rarrashi yake magana.


"Haba Zainab ki yarda dani, ki yarda da son danike maki, duk duniya ba macen danikeso kamar ke,....


A fusace ta d'ago ta kalleshi cikin tsiwa tace "Akwai khaleed, na tabbata kafi son Fadila a kaina, khaleed ka ha'inceni, ban ta6a tinanin ko a mafarki zakayi mani haka ba.


Ya salam...ki fahimceni Zainab, Fadila fa bani nace ina sontaba, had'in iyaye ne,kuma ke....


"Dakata khaleed, bakada kalaman dazasuyi tasiri akaina, ka adana kalamanka, wata kila suyima amfani nan gaba....


_(Hmm zainabu kenan halinki sai ke)_








*Zee Elkaseem*
*Mnn Khady*
[02/08 6:26 pm] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 56-60








โœ๐Ÿฝ Kwanan Autar Hajiya biyu aka sallamota daga asibiti, duk ta wani rame ta kod'e hancinnan ya'kara tsayi, ga wani haske data 'kara, idan ka ganta sai kayi tinanin tayi ciwon wata biyu ne, dan ba 'karamar rama tayiba, duk tsabar kishine kawai.


Ranar sukayi waya da 'kawarta sadiyya, tace dan Allah tazo yau tana son ganinta, sadiyya tace "lafiya dai? Auta tace "lafiya lao kizo mana akwai labari 'kawata wallahi ina cikin tsananin damuwa da ba'kin ciki, cikin rud'ewa sadiyya tace "Damuwa 'kawata?, wace irin damuwa kuma? Auta tace "kedai sai kinzo kome kenan kinji.




โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ข


Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa kalar sararin samaniya, wacce tasha d'inkin zamani, dinkin ya matu'kar kar6ar jikinta, dan ba karamin kyau yayi mataba, bata d'aura d'an kwaliba, sai wani karamin gyale me sharara ta yafa akanta, amma hakan baze hana ka hango madaidaicin gashinta ba Wanda yasha 'kuna, tayi parking dinsa tsakiyar kanta.


Wankan tarwad'a ce, amma dayake tana amfani da cream da lotion masu tsadar gaske masu matu'kar gyara fata,hakan ya 'kara fito da hasken fatarta, tanada idanu madai-daita, da dogon hanci, Wanda yayi dai-dai da matsakaicin bakinta, Wanda yasha romantic red colour,
kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da boko ya zauna jikinta, da kwalwarta, *Fadila kenan*.


Da sallama ta shiga falon da akayi Mashi masauki, tafiya take cikin yanga da karairaya,
Lokacin khaleed ya d'ago ya kalleta tare da amsa sallamarta,
Yanda take tafiya baya birgesa ko Alama, dan tanada 'yar'kiba shiyasa tafiyar bata mata kyau, ga Allah ya hore mata manyan nonuwa kamar me shayarwa.


Sannu da zuwa angona, tafad'a tare da zama kan kujerar dake kusa dashi, hannu tasa ta d'auki sauran lemun dayasha cikin cup d'in glass ta kur6a sannan ta ajiye, ta maida kallonta gareshi, tare da tambayarshi, "ya hidima? Yace "Alhamdulillah,
My dear lefe yayi kyau amma ka manta, da sarkar gold d'in dana fad'ama ba irin wacce ka sako bace, inaso dan Allah ko zaka musanyo mani ne?.......


"Ke Fadila, cikin d'aga murya yafad'a, idan bazaki iya amfani da abinda kika gani acikiba, to ba'ayimaki dole ba, nidai namaki iya 'kok'arina.........


Daga mashi hannu tayi, cikin d'aga murya take magana, "Dakata khaleed, bazakaje wata ta 6ata maka raiba kazo ka huce kaina, ko kana tinanin banida labarin abinda ke faruwa, tsakaninka da wannna yarinyar, Auta take ko miye.....


A fusace ya mike tsaye, yace ni zan wuce, ba wannan ya kawoniba, zowa nayi inji idan kina bu'katar wani abu, kuma naji bakida bu'katar kome sai anjima,


Ya fita Daga falon yanufi harabr gidan inda ya ajiye motarsa, yana niyyar Shiga yaga mamar Fadila, direba ya sauketa, ta dawo daga Unguwa, nan ya gaisheta, ta tambayeshi momynsa, yace tana lafiya, sannan ya shiga motarsa ya wuce.










Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [03/08 10:20 am] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 61-65




*_Bayan sati biyu_*โ€ข
โœ๐Ÿฝ Yau sauran sati d'aya bikin khaleed da Autar Hajiya da kuma Fadila, duka 6angarorin guda ukku shirye-shirye suke, ko'ina ka gani suna cikin farin ciki.


Amarya Fadila ansha gyara anyi fresh, dan tin ana saura sati biyu bikin take faman gyara kanta, duk wani Abu datasan yana da amfani a jikin mace tana amfani dashi, tin Daga kayan gyaran jiki zuwa kayan tsumi ba Wanda batayi.


6angaren Autar Hajiya kuwa kullum ba abinda take sai tinani, duk tabi ta rame ta kod'e tayi wani irin fari, idanunta sun kara fitowa, a haka dai aketa shirin biki, 6angaren Hajiya kuwa ba irin rarrashin da batayima Auta ba, haka babanta tin yana mata fad'a har ya dawo yana rarrashinta yana mata nasiha, da haka dai aka samu tad'an saki jikinta, aka cigaba da hidima.


A 6angaren khaleed kuwa shima hidima yake sosai shida abokaninsa, zuciyarshi fal da farin ciki, dan jiya yaje gurin Autar Hajiya ta saki jiki sunyi magana ta fahimta, wacce rabon daya samu haka tin ranar da tasan ze auri Fadila.








Ana saura kwana biyu d'aurin aure sadiyya tazo gidan su Auta, da sallama ta shigo, gidan cike yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, bayan ta gaisheda mutanen dake tsakar gidan, sannan ta wuce kitchen inda ta hango Hajiya tana faman had'a wasu kaya, tace "Hajiya ina wuni, Hajiya ta amsa da "lafiya lao sadiyya, ya mamarki, tace "lafiya lao tace a gaiaheki, kuma tace abaki hakuri bazata samu zuwa yau ba sai zuwa gobe, saboda tayi ba'ki, cikin fara'a Hajiya tace "ba kome wallahi Allah kaimu goben, sadiyya ta amsa da Ameen, sannan ta tambaya, "ina Autar take? Tana d'aki ki isa, tana ciki.


Kwance take kan godo ta juya fuskarta ta kalli bango, tayi lamo kamar me bacci, muryar sadiyya taji tana cewa "Amarya bakya laifi koda kin kashe d'an masu gida......


Auta tayi kamar bata jita ba, dan ko motsi batayiba, daga inda take kwance, sadiyya ta matso kusa da ita ta zauna gefen gadon, takara magana karo na biyu, "Amarya......., nan ma shiru Auta tayi mata, sadiyya ta'kara magana karo na ukku cikin jin haushi ta kaimata duka, tare da fad'in Auta banison rainin wayo, ya inata maki magana zaki wani sahareni......


Da sauri Auta ta tashi zaune tana Sosa inda sadiyya ta doketa, tana murmushi, tace "ina jinki wallahi, abinne naki yabani haushi da kika kirani amarya, aini nafi 'karfin amarya sai uwar gida, sadiyya tayi dariya tace to ai kinsan dai Fadila ta girmeki saboda haka itace babba, kuma itace uwar gida kekuma amarya, Auta tace "tab wallahi bazan yardaba, badai ance d'akin wacce yafara kwana ba itace uwar gida, to wallahi d'akina ze fara kwana.


Sadiyya ta kyalkyale da dariya, dan ita yanzu rigimar Auta dariya take bata,tace "to yanzu ba wannan ba kitashi muje gurin gyaran jiki, Auta tace "ke nifa na gayamaki ba wani gyaran da zanyi, a kaini haka yanda nake, wallahi sadiyya konayi niyyar yin wani Abu da natuna ba nikad'ai za'a kai gidan khaleed a matsayin matar saba sai inji duk na sire,


Sadiyya tayi murmushi, tace "Hmm auta kenan, to ay yanzu yakamata ki gyara, dan na tabbata ita waccan bazata zauna hakaba, kema dagewa zakiyi, ki gyara kanki yanda koda kin jera da waccan aga kamar sarauniya da baiwarta.


Suduka suka kwashe da dariya, haka sadiyya ta rarrashi 'kawarta harta yadda sukaje gurin saloon, Daga nan suka wuce gurin 'kunshi,


Basu dawo gida ba sai gab da magrib, suna dawowa, sadiyya tayo Alwala ta kabbara sallah, ita kuma sadiyya wanka tashiga, bayan tafito Daga wankan ta haye gado tayi kwanciyarta, kasancewar tana fashin sallah, bayan sadiyya ta idar da sallar ne suka cigaba, da tattauna yanda party da za'ayi gobe ze kasance, dan kuwa partyn Baki d'aya za'a yishi da fadila da Auta, kuma kowace da 'kawayenta.














Zee Elkaseem
Mmn khady
[03/08 11:57 am] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_*Page*_ 66-70






โœ๐Ÿฝwashe gari ana gobe d'aurin aure, yau ne aka shirya wani 'kawataccen party Wanda Za'ayi a liyafa parlance dake cikin garin katsina, duka a 6angarori guda ukku, kowane yana cikin shiri, khaleed da abokaninsa da 'yan'uwansa, Autar Hajiya ma da 'yan'uwanta da 'kawayenta, haka ma Fadila, tana cikin shiri itada 'kawayenta da 'yan'uwanta.


Da misalin karfe hud'u za'a fara aiwatar da partyn, sabida haka kafin lokacin Fadila ta gama shiryawa, wani tsadadden material ne red colour tasanya dinkin riga da siket, kayan sun matseta sosai, abinka game jiki, kirjinnan kamar ze fasa rigar, kanta kuma golden gwagwaro ta d'ora takalmanta masu masifar tsini, wanda suka taimaka gurin 'kara mata tsawo, suma golden colour, sai wata 'karamar jaka dake hannunta itama kalar golden, kallo d'aya zakama Fadila kasan amarya ce, fuskar nan tasha make-up, dan me kwalliya ta d'auko ta musamman ta gyara mata fuskarta, ta biyata kud'i me yawa.




A 6angaren Autar Hajiya kuwa zaune take itada 'kawayenta, anata labari anata shewa, ko kad'an Auta batada niyyar yin wanka barantana ta shirya, sadiyya ce ta duba agogon wayarta sannan ta kalli Auta tace, Auta kinsan kau 'karfe nawa yanzu? amma ko niyyar shiryawa bakiyiba, kafin tayi wata magana, taji 'karar wayarta, tana dubawa taga sunan Ahmad, wani abokin khaleed ne, hannu tasa ta d'auki wayar sannan ta dannan OK ta kara a kunne tare dayimashi sallama, a d'ayan 6angaren Ahmad yace Ku fito gamu kofar gida muna jiranku,
Tayi saurin tashi tsaye tare da dafe 'kirji tace kuna waje fa kace, yace "eh tace "gashi kuma bangama shiri ba, yace owk bari muje gidan su Fadila, idan kingama mundawo, bejira abunda zata fad'aba ya tsinke wayar.


Da sauri tashiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta d'auko wani lotion me dad'in 'kamshi ta shafe jikinta dashi, sadiyya ce ta 6ata lokaci gurin yima Auta make-up, tin nan Auta tafara yin kyau, fuskar nan kamar wata balarabiya, ga kunshinta Wanda yayi masifar kyau, manyan Flowers ne yayi bakikirin sai Jan ranin daya 'kara 'kawata kunshin.




Wani tsadadden farin Swiss less ne, Wanda yasha ado da flowers silver colour ta sanya dinkin doguwar riga, rigar ta kar6i jikinta dan ba 'karamin kyau tayimata ba, sannan ta sanya, takalmi silver colour, sai yar post d'in hannunta itama silver colour,kanta kuwa gwahgwaro me ta d'ora shima kalar silver, tayi masifar kyau, sannan ta d'auko turarurruka masu dadin 'kamshi ta feshe jikinta dasu.


Sadiyya ta kalleta tace Amarya kinsha 'kamshi, Auta ta harareta, cikin wasa tace "kin manta, sadiyya tayi dariya tace "oh sorry tuba nike Amarya uwar gida, Auta tayi dariya tace "ki karani kirani Uwar gidana
Kawai,
Sadiyya tace "to uwar gida sarautar gida, suduka suka kyalkyale da dariya.


Suna cikin wannan sukaji tsayuwar motoci, Ahmad, yakirasu yace su fito gasu a waje, nan aka fafa d'ibar 'kawayen amarya ana kaisu.
Daga karshe kuma aka d'auki Auta da wasu sauran 'kawayenta dasuka rage.














Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [03/08 9:43 pm] Zee Elkaseem: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




*_Page_* 71-75








โœ๐Ÿฝ Hall d'in cike yake ma'kil da 'yan'uwa da abokan arziki, tun daga kan 'yan'uwan khaleed da abokaninsa, har zuwa 'yan'uwan Autar Hajiya da kuma 'kawayen Fadila da kuma 'yan'uwanta, Kowa yayima kansa mazauni, ana jiran shigowar ango da Amarensa, Autar Hajiya da Fadila.


Bayan hall din yayi shiru, sakamakon Mr DJ daya fara magana cikin speaker's dinshi, Kowa ya maida hankali ga yanda yake jawabi.


Can na hango Ango khaleed da Amarensa sun jero, tsakiya suka sanyashi, Auta na gefen damarsa yayinda Fadila ke gefen hagu, suna tafiya ahankali cikin nutsuwa, kallo d'aya zakayima Auta ka fahimci tana cikin wani yanayi, dan yanda taga Fadila ta wani shishshigema khaleed ta kama hannunshi ta ri'ke abin ba 'karamin takaici yayi mata ba, tin nan tafara tinanin me zatayi ta ba'kantama fad'ila rai, kamar yanda ta ba'kanta mata.


Sun Isa high table inda nan ne yazama masaukin Ango da Amarenshi, tsayawa khaleed yayi yayima fad'ila nuni akan ta wuce tafara zama kujerar can, yayinda shi tashi kujerar take tsakiya,
Bayan Fadila ta wuce ta zauna kan kujerar ta, khaleed na niyyar zama kan tashi kujerar kawai sai ganin Auta yayi kan kujerar, yana shirin yimata magana ne yaji, ta kamo hannunsa, ta wani kashe Mashi manyan idanunta, tace "ka zauna mana my dear, tare da nuna mashi kujerar da itace zata kasance gurin zamanta,
ba yanda zeyi haka ya zauna, sai tsarin zaman ya canja, ya kasance Autar Hajiya itace tsakiya, yayinda Fadila ta koma gefe, cikin 'kawayenta.


Wani 'kululun ba'kin ciki ya tsayama Fadila a wuya, ta rin'ka cika tana batsewa, fuskar nan tata ba annuri ko kad'an duk 'ko'karin datayi na taga ta share da abin ta nuna be dameta ba kasawa tayi,


Itako Auta sai fara'a take, ta dan du'ko da Fuskarta saitin fuskar khaleed har sunaiya juyo numfashin junansu, Labari tari'ka bashi shikuma dama abinda, yake nema, sabkda haka ya biye mata, dan tin lokacin da Auta tasamu labarin ze auri Fadila maganr ta minti goma bata 'kara had'asuba, Shiyasa ya biye mata sukayita labari suna sakarma junansu wani 'kawataccen murmushi.


Can zuciya ta 'kule Fadila, batasan lokacin data tashi, cikin tsananin masifa, da bala'i ta fito daga ida take zaune, ta tsaya gaban tebur d'inda aka cika da kayan ciye-ciye da lemuka kala-kala, tasa hannu tafara watsi da kayan, 'karar fashewar kofunan glass d'in gurinne ya maido da hankalin duk illahirin mutanen dake gurin.


Cikin tsananin mamaki Auta ta nufi Fadila, wacce idanunta suka rufe saboda tsabar masifa, ta ri'ke hannunta tana fad'in "Haba Fadila lafiya, ya muna taron arziki zakizo ki 6ata mana, cikin tsananin fushi Fadila ta bankad'e Auta, abinka ga marar jiki ta tafi taga-taga zata fad'i dai-dai lokacin khaleed ya iso gurin yayi saurin tarbeta, ta kuwa fad'a jikinsa tana kukan shagwa6a, tana fad'in "my dear menayi mata zata tureni? 'Kara rungumeata yayi jikinsa yana rarrashinta, ita kuwa sai wani 'kara narkewa take.


A fusace Fadila ta nufi hanyar Barin hall din tana zubar da hawayen ba'kin ciki, Ahmad ne yabita yana cewa, "Fadila ki tsaya mana a gyara, ai bekamata kiyi hakaba, wallahi muna cikin maganar zamuyima khaleed magana agayara tsarin zaman kawai sai gani mukayi kin tashi kina wannan d'anyen ayki, cikin dusashshiyar murya tace "
Ahmad ka taimakeni ka maidani gida kada zuciyata ta buga bazan iya ba.


Bayanda Ahmad beyiba akan tayi ha'kuri ta koma ta 'kiya, dole tasa ya d'auketa a motarsa dan kada yabarta tatafi yanda ranta yake 6ace wani Abu yaje yafaru da ita a hanya.


Haka aka tashi partyn Kowa na jimamin abinda ya faru, wasu na ganin laifin Fadila, wash na ganin laifin khaleed,wad'anda kuma suka fahimci yanda abun yake laifin Autar Hajiya suke gani.










Mmn khady
[03/08 10:51 pm] Zee Elkaseem: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




*_Page_* 76-80








โœ๐Ÿฝ washe Gari da misalin karfe biyu na rana, dubban mutane suka sheda d'aurin Auren khaleed da Amarensa, Zainab _(AUTAR HAJIYA)_da Fadila.


Da misalin 'karfe hud'u na yamma aka fito da Auta dan kaita gidan mijinta, bayan an kaita d'akin mahifinta yayi mata nasiha me ratsa jiki, da kuma yimata nuni da tayi ha'kuri, dan duk Wanda yayi ha'kuri duniya baze ta6a ta6ewa ba.


Bayan an fito da ita daga d'akin mahaifinta aka wuce da ita d'akin Hajiya, itama Hajiya tayi mata nasiha me ratsa jiki, 'karfe hud'u da rabi aka fito da Auta aka sakata mota, ba abinda take sai kuka, da kyar aka rabata da hajiya,


A unguwar lay out dake cikin garin katsina, misalin 'karfe biyar suka isa gidan, can suka iske 'yan'uwan khaleed dana Fadila dan ita tin 'karfe hud'u aka kawota.


Bayan sallar magrib ne aka fara gabatar da walimar da 'yan'uwan khaleed suka shirya, wanda aka gayyato shahararriyar malama wacce zata gabatar da wa'azi kan zaman aure da kuma nasiha ga Amare, wato malama *AMINA ALIYU MOHM'D (BINTUSH~SHEIKH)*


Bayan malama ta bud'e taro da Addu'a, tayi wa'azi akan ha'kuri sanna tafara nasiha ga Amare kamar haka: "Alhamdulillahi Allah Kaine abin godiya, daka azurtamu da rai da lafiya, bayan wa'azi da nayi akan ha'kuri yanzu kuma inaso inyima Amare nasiha akan zaman Aure, Wanda shima dai ha'kurin akeyi, yaku wad'annan Amare ina ro'konku da kada kuyi kishi irinna jahilai, kada kuyi kishi irinna wad'anda basu san ciwon kansuba.


Kuyi kishi irinna matan Annabi Muhammad _(S.A.W.)_ Kada kuyi kishin da ze tada hankalin mijinku, kuyi kishi Wanda kullum burinku Ku kyautatama mijinku, kunsan shi rai yana son me kyauatata mashi, sannan daga 'karshe na horeku da tsafta, Ku zamto masu tsafta kada ku yarda mijinki yaga wata 'kazanta ajikinki ko ya sha'ki wani abu a jikinki sa6anin daddad'an kamshi.


Haka dai malama tayi nasiha me ratsa jiki, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a Kowa ya tafi gida, bayan an raba sadakar Qur'an Kowa izif sittin,
Ana Allah shima malama Albarka, Akan wannan wa'azi datayi.


Da misalin 'karfe takwas na dare, gida yarage daga Auta sai 'kawayenta guda biyu sadiyya da Zahra'u sune suka tsaya suka gyagayara mata kome suka share ko'ina suka kunna turaren wuta, ko'ina na sashen ya bige da 'kamshi sannan sukayi bankwana suka tafi.


Itama Fadila 'kawayenta ne suka tsaya sukayimata 'yan gyare-gyaren daya dace, sai misalin karfe tara da rabi suka bar gidan,


*TO FAH MASU KARATU GIDA YA RAGE DAGA AUTAR JAJIYA SAI FADILAโ€ข ๐Ÿค” SAI ALLAH YA KAIMU GOBE MUJI WACE IRIN WAINA ZASU TOYA*๐Ÿ˜‚










Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [04/08 8:00 am] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_*Page*_ 81-85










โœ๐ŸฝDa misalin karfe goma da minti arba'in da biyar basuji shigowar ango ba, dama kowace na d'akinta, kasancewar gidan irin plate house ne, farko idan ka shigo get d'in ka wuce harabar gidan akwai 'kofa waccce zata sadaka da general falo na gidan, cikin falonne 6arin dama d'akin Autar Hajiya yake, Wanda ya kasance cikinsa akwai falo d'aya sai bedroom guda biyu, a 6angaren hagu kuma d'akin fad'ila ne, itama kamar yanda na Auta yake, sai d'akin me gida khaleed da yake tsakiyar nasu d'akunan shikuma falo ne da bedroom d'aya, kowane da toilet cikin bedroom d'insa, daga side din kowace kuma kitchen d'inta yake.


Fadaila ce ta kalli agogon dake manne jikin bangon d'akinta, 'karfe sha d'aya saura minti biyar amma bataji shigowar ango ba, saboda haka toilet ta shiga ta she'ka wanka, bayan tafito ta d'auko wani tsadadden less ta sa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login