Showing 12001 words to 15000 words out of 23148 words

Chapter 5 - AUTAR HAJIYA COMPLETE Book Writing by Zeey Maman khady.txt

16 Dec 2024

1214

da yanda koda yaushe khaleed ke yabon girkin Auta, amma ita idan girkintane yanaci yana 6ata rai kamar mecin magani, amma ita bata ganin laifin kowa sai na momynta dan itace bata koya mata girkiba, gashi Auta har magana take gayamata a kaikaice, wai makarantar Hajiya ta koyi girki," Hmm tayi kwafa sannan ta wuce d'akinta.




Da misalin 'karfe daya da rabi na rana Auta tagama had'a kome ta jera kan dining, 'kamshin girkinta yagama buge ko'ina na gidan kamar yanda ta saba.


Dambun shinkafa ne tayi me rai da lafiya, Wanda yaji kayan lambu, Kara's da kabeji da sauransu, ga kamshin kori, nama ta yanka gutsi-gutsi ta zuba gurin yin dambun ta yanda zeyi wuya mutum yayi cokali guda batare daya ci da naman ba, gefe Kuma zo6o ne tahad'a Wanda shima yayi dadi sosai yaji flavor me 'kamshin Abarba yayi sanyi dan jug d'in har ra6a yake.




Bayan ta kammala wannan d'akinta tanufa ta she'ka wanka, bayan tagama gyara ko'ina na gidan da kuma kitchen d'inta, ta turare gidan da turaren wuta, abin dai gwanin birgewa.


```{ ๐Ÿ˜„kaini su Auta an iya kwanare da sa kishiya taji haushi}```


Da karfe biyu khaleed ya dawo gidan, bayan Auta tarakashi d'akinsa yayi wanka, ya canja kaya, wata 'karamar riga ce yasanya sai wando three quarter, sannan suka hallara su duka kan dining, Auta cike da nishad'i da jin dad'i ta zuba ma kowa a plate tare da sanya cokali, sannan ta tsiyayama kowa zo6o a cup d'in glass ta ajiye gabanshi, sannan itama ta zauna, khaleed cike dajin dad'i ya d'ebi abincin yakai bakinsa, tare da lumshe ido.


```Yasalam ya furta tare da saurin furzar da abincin dake bakinsa```


Lokacin itama Fadila ta kai abincin bakinta dan jin meke faruwa, da sauri ta zuddo abincin tare da saurin d'aukar ruwa tasha, dan kuwa wani irin mugun gishiri ne yayi yawa cikin abincin, dan komin dauriyar mutum baze iya cin saba.


Cikin tsananin rud'ewa Auta ta ebi abincin taci dan taji meye yasa khaleed zubar da abincin data 6ata lokaci gurin girka Mashi dan ya yaba, wani irin zau taji abakinta *Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* tashiga furtawa, aranta tace yaushe nayi wannan aikin haka, yaushe na zabga gishiri cikin abincina har ya wuce misali.


Khaleed kuwa kasa magana yayi, dan yasan ko be fad'aba suduka sun san kome kenan, baya bu'katar a can-cana maganar.


Kitchen d'in Auta yanufa ya d'ebo cake cikin plate dan kuwa yunwar jinta yake sosai, dan har gidan abokinsa Ahmad yaje akayimasa tayin abinci ya'ki ci dan yasan Auta zata yimashi special coaking ๐Ÿ˜œ.


Zama yayi ya fara cin cake d'in sannan ya d'auko zo6on da Auta ta zuba mashi a cup yakai bakinsa, da sauri ya cire cup d'in daga bakinshi dan jin wani sabon d'and'ano a zo6on wanda beyi tinanin jinsa acikiba, lokaci guda ya maida kallonshi ga Auta wanda mamaki yahanata motsawa daga inda take,
Khaleed yagama 'kulewa da Al'amarin Auta, saboda haka batare dayace kome ba yatashi ya wuce d'akinsa,
Cikin tsananin mamaki Auta ta d'auki cup d'in ta kur6i zo6on gishiri taji zau Wanda har ya zarce za'kin sugar, kalmar *innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* kawai take furtawa,
Binshi tayi d'akinsa kwance ta iskeshi kan gado ranshi yayi matu'kar 6aci, nan tashiga rarraahinshi tana bashi ha'kuri tare da nuna mashi wallahi batada masaniya akan wannan gishirin da yayi yawa cikin abinci barantana kuma cikin zo6o.


Fadila kuwa koda taga shigewarsu d'aki wata irin shu'umar dariya tayi tace ~```Hmm Auta dani kike magana```~










Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [06/08 10:33 pm] .: [06/08 9:42 pm] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




*_Page_* 101-105










โœ๐Ÿฝ A firgice Fadila ta farka daga baccin datakeyi da niyyar zuwa falo dan kada khaleed ya dawo ya wuce d'akin Auta bata saniba.


Innalillahiwa'ainna,ilaihirraji'un tafad'a tare da saurin le'kewa ta windon d'akinta dan tabbatar ma idonta abinda ta gani gaskiya ne,
Hasken ranar daya haske idonta shine ya tabbatar mata da cewa tabbas ba mafarki takeba, safiya tayi, da sauri ta fita zuwa d'akin khaleed dan taga nan ya kwana ko kuwa, tana zuwa ta tura 'kofar d'akin tashiga taga ba kowa aciki, kuma babu Alamar mutum ya kwana aciki.


Take wani irin kishi ya turni'keta, "shikenan abinda ta kwana ukku tahana idonta bacci sabodashi yariga ya afku, jitayi 'kafafunta sun kasa d'aukarta, batasan lokacin data sulale 'kasan d'akinba kan tiles tayi zaman dirshan tana zubar da wasu zafafan hawaye, a zuciyarta take cewa:


*_(Shikenan khaleed ka cuceni ka gama sanyawa yarinyar nan ta rainani, shikenan khaleed ka fito fili ka nuna kafi son Auta a kaina, )_*


Shiru tayi na kimanin minti goma tana tunani, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta, zuwa can sai tayi wani shu'umin murmushi, tace




*~Hmm Auta idan Kin san wata baki san wata ba "Hmm dani kike magana~*


: Tashi tayi daga zaman takaicin datake, tanufi d'akinta tafad'a toilet tayi wanka sannan ta d'auro Alwala ta kabbara sallah lokacin har karfe bakwai da minti sha shidda na safiya, bayan ta idar da sallar ta wuce gaban dressing mirror ta 6ata lokaci gurin gyara fuskarta, sannan ta sharce gashinta wanda koda yaushe yake a 'kone, ta d'aure shi tsakiyar kai, bayan tagama wannan wadrop tanufa wasu Riga da siket na atamfa ta d'auko d'inkin zamani ta sanya ajikinta, kayan sun matu'kar zama ajikinta, dan ba 'karamin kyau sukayimata ba, sannan ta d'auko manyan turarrukanta masu dad'in 'kamshi ta feshi jikinta dasu, bayan humra data rin'ka mungulawa ajikinta.

Lokaci guda kuwa 'kamshinta ya mamaye dakin,
Tana cikin d'aura d'an kwali ne khaleed yashigo d'akin da sallama, sanye yake cikin farar shadda d'inkin zamani, bayan ta amsa sallamar ta juyo ta kalleshi, tayi mashi wani tattausan murmushi tace "Barka da fitowa my man, wani irin dad'i yaji ya ratsashi har cikin zuciyarsa, dan yayi tunanin Fadila zata tada hankalinta ne idan gari ya waye ta tabbatar da d'akin Auta ya kwana, shima wani murmushi ya sakar mata, har cikin ranshi yaji dad'in yanda ta tarbeshi, ga kwalliyarta ta masifar yimata kyau, lokaci guda yaji ta matu'kar burgeshi, take kuma yaji wani sabon sonta ya shiga zuciyarshi.


Ahankali ya 'karaso inda take yayi mata wata kya'ky'kyawar runguma, sannan yabata kiss a kumatu yace "Gud morning my special wife, har cikin ranta taji dad'in kalamansa, itama ta mayar masa da nata sakon kiss d'in a lips, tace "morning my man.


Auta kuwa koda ta tashi kitchen tafad'a dan had'a musu break fast,
Cikin k'ank'anin lokaci tagama had'a kome na break ta jera kan dining table, sannan takoma d'akinta ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta tsaya gaban dressing mirror tayi simple make-up sannan ta nufi Wadrope ta d'auko wasu English wear riga da siket, siket d'in farine har 'kasa, amma ya kameta daga sama, sannan k'asan ya bada fad'i, jikinsa akwai kwaliyya flowers da copee zare, sai rigar copee colour, tasha ado da duwatsu daga gabanta, rigar batada hannu, sai wani siriri kamar na bes, bayan tasanya kayan sun matu'kar yimata kyau, wani 'karamin farin gyale ta d'auko tayi rolling din kanta, sai ta ida fitowa balarabiya sak.














Zee Elkaseem
Mmn khady
[06/08 11:42 pm] .: [06/08 11:10 pm] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




*_Page_* 106-110












โœ๐Ÿฝ Zaune suke kan dining suna break, kowanensu ci yake yana jin dad'in abin, dan kuwa Auta ba daga baya ba gurin iya girki, ita kanta Fadila ta jinjina ma Auta a zuciyarta, dan ko a hotel abinci baze wuce wannan dad'i ba.


Bayan sun gama ne khaleed yafara magana "Amma gaskiya naji dad'in yanda kuka dawo yanzu, kungane wannan rigimar ba abinyi bace, saboda haka inaso inyi amfani da wannan dama inyimaku nasiha akan dan Allah ku had'e kawunanku ku zauna lafiya, ba cuta ba cutarwa, domin zamanku lafiya shine kwanciyar hankalina.


Sannan ya kalli Fadila, yace "kinga Fadila jiya na kwana d'akin Auta, to gobema zan kwana d'akinta kinga kwana biyu kenan, daga lokacin kuma zan dawo d'akinki inyi kwana biyu.


Suduka sunyi shiru suna saurarensa, kowace da abinda take kitsawa a ranta.


Auta tace "to wane lokaci kake ganin ya dace ari'ka kar6ar aykin? Khleed yace "Ku yakamata ku fidda, sai lokacin Fadila tayi magana tace kamar da 'karfe biyar da rabi na yamma, ta kallesu tace hakan yayi koh,? Khaleed yace "yayi.


Haka dai suka d'an ta6a fira, wacce yawancinta tsakanin khaleed ne da Fadila, dan Auta ita haushi ke hanata magana, dan ita kome Fadila zatayi bala'in haushi yake bata, wani irin mugun kishin khaleed ne ke kamata duk lokacin dataga yana kula Fadila.


A haka aka cikama Auta kwananta d'aya batare da wani tashin hankali ba, dan Fadila ta hakura, kuma kullum girkin Autar takeci, dan kuwa tare suke cin abinci su duka,
โ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ขโ€ข


Yau yakama ranar da Fadila ta kar6i kwana, saboda haka itace tayi masu abincin dare,
Ta had'a kome ta jera kan dining, da misalin 'karfe takwas na dare suka zauna cin abinci, Fadilar da kanta ta zuba ma Auta bayan ta zuba ma khaleed ta tura mashi gabanshi.

Auta cike da jin haushi ta debi abincin takai bakinta, bata San lokacin da tasaki wani tattausan murmushi ba dan jin testing d'in abincin, a zuciyarta tace
" ~_Salmanu!...... kada inga salame idan haka take_~"
Dan jin abincin tayi ba wani testing ko kad'an, aiko take wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta, data tuno cikin kwana biyunan yanda khaleed ke buga santi idan yana cin abincinta, koda yaushe yana yaba mata kan iya girki.


Khaleed kuwa koda ya d'ebi cokali d'aya yakai bakinsa, yaji abin ba'a magana, daurewa yayi ya had'iye na bakinsa, haka dai ya daure yaci gaba da ci, itama Auta dataga haka saita ri'ka tutturawa tanaci tana jin dad'i aranta, ita kanta Fadilar daurewa kawai take tanaci dan tasan ba yanda za'ayi tayi girki kuma ta'ki ci' sai afara zargin kota tasarma rashin gaskiyane, amma ko ita kanta tasan abincin beyi dad'iba, saboda haka ta dage tayita d'ibar girki.


Bayan sun kammala sun d'an ta6a fira har kusan 'karfe sha d'aya da rabi Auta nata jan khaleed da surutu dan kada su tafi su kwanta, shikuwa ya biye mata dan bemasan lokaci yayi nisa haka ba.


Saida Fadila tagaji, ga bacci tanaji, tanata hamma sannan ta kalli khaleed tace "my man bacci nakeji kazo muje kaga dare yayi har sha d'aya, sai lokacin ya duba agogon wayarsa yaga k'arfe sha d'aya da minti arba'in da tara, saboda haka khaleed yatashi sukayima Auta sallama suka wuce d'aki.


Itama nata d'akin tanufa, ta cire kayan jikinta ta sanya wata doguwar riga ta bacci ta haye gado da niyyar yin bacci, amma ina kasawa tayi lokacin data tuno yanzufa khaleed yana d'akin wata ba itaba, kuma ze nuna mata soyayya irin yanda ya nuna mata.


Zunbur tayi ta tashi kamar wacce aka tsikara, takama zagayen d'akin zuciyarta nata tafarfasa, falo ta dawo ta zauna ta sa hunnu biyu ta buga uban tagumi, zuwa can taga zaman beyi ta tashi ta dinga safa da marwa tsakanin falo da d'akinta, daga 'karshe da takaicin ya ciyota batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba, tafad'a kan gado tacigba dayi, har misalin 'karfe ukku da rabi na dare Auta na aykin kuka, daga 'karshe dai bacci 6arawo yayi awon gaba da ita.










Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [10/08 11:29 pm] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜






```Page```121-125












โœ๐Ÿฝ Haka Auta tacika kwanakinta biyu kullum zata tsaya ta kwantar da hankalinta ta tsara girki tun kafin ta kai kan dining saita d'and'ana taji testing d'insa saita tabbatar da lafiya lao sannan take ajiyewa, amma abin mamaki sai sun zauna cin abincin suji gishiri za'ka'ka, Abin yana matukar damun Auta amma ba yanda zatayi, dan batada hujjar kare kanta akan cewa ba ita ta zuba gishiri haka ba,
ba abinda ya kara d'aure mata kai sai lokacin da tayi girki ranar ko gishiri bata zuba ba dan gudun kada yayi yawa, amma babban abin mamaki shine suna fara ci sukaji gishiri zau' abin ba dad'in ji.




****************************
Fadila ce cikin shigar 'kananan kaya riga da wando sun matseta sosai, wasu had'ad'un kuloli ne take d'aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, gefe kuma lemun ```5alive``` ne sai ruwan swan, abin gwanin ban sha'awa.


Da misalin 'karfe biyu da rabi khaleed ya dawo gida, Fadila ta tarbeshi cike da murna, Auta kuwa tana zaune gefe, cikin sanyin jiki tace "Sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ya wuce d'akinsa,
Dan yanzu Auta tariga tagama sure mashi, kwata-kwata tagama 6ata ranshi, ace kullum mutum baze iya tsayawa yayi Abu cikin tsariba, sai ace yau ayi girki acika gishiri, kuma gobe ma haka za'ayishi,
babban abin takaici sai kaji gishiri cikin zo6o ko kunun aya, wnnan ay rainin wayo ne.


Wani 'karamin tsaki yaja "mtsw, sannan ya wuce d'akinsa, Fadila ta bishi tana wani karairaya, koda takai bakin 'kofar d'akin saita juyo ta kalli Auta dake zaune kan kujera abin duniya duk ya dameta, tayi wani shu'umin murmushi sannan tashige d'akin tare da canja salon tafiya tana wani juya mazaunai.


Fadilar ce ta taimaka mashi ya cire kayan jikinsa yayi wanka, da kanta taje cikin kayanshi ta dauko mashi kaya marassa nauyi ya Sanya, sannan suka fito falo, dining suka sauna dan cin abinci Auta kuwa ba'kin ciki ya gama cika mata zuciya, bayan shigewarsu d'akinta tanufa tafad'a kan gado ta rushe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan tafad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta shafe jikinta da cream me dadin kamshi da gyara jiki sannan ta shafa powder ta dauko man le6e ta shafa,
wadrope tanufa ta d'auko wata doguwar riga ba'ka me adon fararen duwatsu daga gabanta ta Sanya, sannan tasa d'an 'karamin gyalen rigar ta rufe kanta dashi, lokaci guda ta fito balarabiya Sak, dan ba 'karamin kyau Auta tayiba.


Kan dining ta iske Fadila da khaleed suna jiran fitowarta, guri ta samu ta zauna duk da zuciyarta na cunkushe da ba'kin ciki da kuma jin haushin Fadila amma ko kad'an bata yadda khaleed da fadilar suka fahimci halin datake ciki ba.
Bayan Fadila ta zuba abincin ta ajiyema Kowa nashi gabanshi, jalouf d'in taliyace wacce taji kifi, cike da fargaba Auta ta ebi taliyar takai bakinta, ```Ya salam```...... Auta ta fad'a tare dayin hanyar toilet da gudu ta rina'ka kwara amai, saida ta amayo duk abinda ke cikinta, khaleed kuwa binta yayi daga baya yana mata sannu, bayan ta gama ta wanke bakinta khaleed yakamo hannunta suka dawo falon, kan kujera ya zaunar da ita yanamata sannu, ita kuma sai wani langwa6ewa take, tana lumshe ido, Fadila ta kalleta cike da jin haushi, amma sai ta daure dan bataso a d'ago da ita, tace "sannu dama bakida lafiya ne? Auta tace lafiyata lau, kifin da akasa agirki ne 'karninsa yayi yawa shine ya tayarmin da zuciya,
Fadila ta ta6e baki ta samu gu ta zauna, a zuciyarta tana cewa


```lallaima yarinyar nan nizakima duniyanci kice wai bakison kifi sau nawa ke kikeyin girki da kifin akwai dai inda kika dosa```.


Auta kuwa 'kara narkewa take tana wani shagwa6ewa, 'karshe ta kwanta kan kujerar datake tayi filo da cinyar khaleed,
Shikuwa sai wani rarrashinta yake yana tarairayarta, "sorry my dear ki daure kici abincin bekamata dan kinyi amai ki zauna da yunwa ba.
Cikin shagwa6a Auta tace " nidai banison wannan ka siyomin wani, tunda yanzu ba time d'in da zan girka wani, yace "fad'i mi kikeso in sayo maki, cikin shgwa6a tace ka siyomin kome kaga ze Sani farin ciki, yace "kada ki damu my only ina zuwa, makullin motarshi ya d'auka yafita, be kobi takan Fadila ba wacce tacika tayi fam saboda takaici.












Zee Elkaseem
Mmn khady
[11/08 11:44 am] .: [11/08 10:19 am] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




```Page``` 126-130








*_BAYAN KWANA BIYU_*
โœ๐Ÿฝ Auta ana kitchen anata faman girki, yau tasha Alwashin tsayawa tsayin daka tayima mijinta abinci wanda ze faranta ranshi, wanda zesa ya manta duk wani 6acin rai na baya, kuma ya dawo da tsananin so da 'kauna da kulawar dayake mata.


Sakwara tayi niyyar dafa mashi da miyar agushi, saboda haka doyarta me kyau ta fere ta d'ora kan wuta, sannan ta dora miya kan wani stove kusa da doyar, bayan ta kammala sakwarar ta maida hankalinta kaf gurin miyar, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala miyar ta juye kome cikin wasu kuloli masu Khan gaske, fridge tanufa da niyyar ta d'auko abarba domin yau *(pineapple juice)*lemun abaraba tayi niyyar had'a musu, tana bud'e pridge din kuwa cikin rashin sa'a saitaga ashe batada sauran abarba, sai lokacin ta tuna aahe fa ta kare tin bayan kwana biyu datayi lemun da ita.


'Dakinta tanufa ta dauko karamar hijab ta sanya sannan tanufi harabar gidan da niyyar taba me gadi ya siyo mata Abarba,
Zaune ta iskeshi kan benci yana ri'ke da yar rediyonshi yana sauraren labaran duniya, cike da ladabi ta gaidashi sannan ta bashi sa'kon ba musu ya kar6a yafita ya siyo mata, dayake kusa da su akwai wurin da ake saida kayan fruit.


Data tashi dawowa sai bata biyo ta babbar kofar falon ba, ta baya ta biyo hanyar da zata sadata da kitchen d'inta kai tsaye,
tazo dai-dai window kitchen dinta kamar ance tayi duba gurin,
Wani irin mummunan fad'uwar gaba taji dan ganin abinda ke faruwa a kitchen d'inta.
Fadila tagani da kullin gishiri cikin leda ta bud'e had'ad'd'iyar miyar agushinta wacce keta zuba 'kamshi ga nama zud'u-zud'u aciki tsoka zallah tayi amfani da ita gurin yin miyar.


Aiko da sauri Auta takoma baya ta la6e dan taga ikon Allah,
Gani tayi Fadila tasa cokali ta ebo gishiri ta zuba cikin miyar ta 'karo wani cike da cokali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login