Showing 3001 words to 6000 words out of 23148 words

Chapter 2 - AUTAR HAJIYA COMPLETE Book Writing by Zeey Maman khady.txt

16 Dec 2024

1215

kira ba'kon Sudan, wani mummunan fad'uwar gaba taji, dan ba Kowa bane tagani sai masoyinta khaleed, Wanda bata ta6a jin son wani namiji aduniya ba kamar shi.


Cikin fara'a yace "Yau sati biyu kenan da dawowar mu, Hajiya tace " sannu da zuwa, shigo mana, a falo akayimasa masauki, sannan suka gaisa da Hajiya, nan take tambayarsa, ya momynsa, yace "tana lafiya tace tana gaishe Ku, tace "ina amsawa, ya karatu kuma, yace "karatu angama, yanzu kuma sai maganar ayki, tace "Allah taimaka, yace "Ameen, tace kuma yanzu Baban naka yafita da kun gaisa, yace ay mun gaisa dashi jiya, tace kaga kuwa be fad'a mamu dawowar kaba, yace "Eyyah ina tinanin mantawa yayi.


Auta kuwa tun bayan shigowar khaleed, tanufi d'aki ta gyara fuskarta, sannan ta yafa wani karamin gyale ta rufe gashinta, sannan ta nufi pridge ta dauko ruwa pure water da holandia fresh milk, ta d'auko d'an karamin cup na glass ta d'ora kan wani madaidaicin tire ta nufi falo, ta ajiye gabansa, Hajiya tafita waje, tacigaba da yan hidindimunta.


Auta kuwa guri ta samu ta zauna, kan kujerar, dake facing d'insa, sannan ta gaidashi, ya tsareta da ido, a zuciyarsa yace _wai Autar hajiya ce takoma haka lallai yanzu nakara tabbatar da gangancin danayi na amincewa da auran fadila_ "sannu da zuwa, tafad'a cikin zazza'kar muryarta, me kama da ta yara, yace "yauwa sannu na sameku lafiya, tace "lafiya lau, tasowa tayi tazo gabansa, ta zuba Mashi, fresh milk a cup ta mi'ka mashi, ya kar6a ya kur6a sannan ya ajiye, kallonta yaci gaba dayi yanda Kasan yau yafara ganinta.


Ita kuwa wani sabon sonshi, taji ya 'kara mamaye zuciyarta, a ranta cewa tace _Allah sa yanda nakejinka a zuciyata kaima haka kakejina_.












Zee Elkaseem
Mmn khady
[31/07 11:49 am] 😘: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊


*AUTAR HAJIYA* 💃🏻


🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊




®NWA




👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘




_Page_ 31-35


Saida yagama 'kare mata kallo a zuciyarshi yana cewa _Allah ka mallakamin zainab Amatsayin uwar 'ya'yana, tabbas nayi gangancin Amincewa da Auren fadila,Amma ba kome tinda itama inasonta zan had'a dukansu in auresu_


Ita kuwa auta duk ta tsargu da yanda ya tsareta da ido, gashi ya'ki magana, sun kai kimanin minti goma a haka, sannan yace " Autar Hajiya, kece kika koma haka? Cikin jin kunyar tambayar dayayi mata tayi murmushi kawai, dan batada Amsar dazata bashi, illah tsananin sonshi da 'kaunarshi dake d'awainiya da zuciyarta.


Jin dayayi batada niyyar magana, yasashi tasowa daga inda yake zaune, ya dawo kusa da ita, ya zauna kan hannun kujerar datake zaune akai, kasancewar kujerar ta zaman mutum d'aya ce.


Wani irin kallo yayi mata, Wanda yasata jin wani yarrr ajikinta, lokaci guda kuma ya kashe mata ido, yace "ya maganar soyayyarmu tananan kokuwa bayan tafiyata kin samu wani?, cike da jin kunya, da kuma jin dad'in zancen daya fito daga bakinsa, itama ta watsa mashi wani kallo, wanda lokaci guda yaji jikinsa yayi sanyi, tace "ai kaine yakamata inyima wannan tambayar, domin tinda katafi ko a waya ka nemeni baka ta6a ba, kaga kuwa kaine zance kasamu wata.


Yayi wani 'kyayataccen murmushi, yace "Zainab bazan ta6a had'a soyayyarki da wata mace ba, ina sonki ina 'kaunarki, kuma burina Aurenki, kawai yanzu ki amice in sanar da baba,saboda na matsu na ganki gidana a matsayin matata, ke kinga yanda kika koma kuwa, ai gaskiya nataki sa'a dana iskeki, wani be min shigar sauri ba.


Tinda yafara magana Auta jinsa kawai take, a zuciyarta kuwa cewa take _"Khaleed nafika son kasancewa matarka dan a duniya banida wanda nakeso nake 'kauna kamar kai_


Khaleed yace "kinyi shiru Kodai akwai Wanda kukayi al'kawarin aure ne? Tayi murmushi, wanda har saida kumatunta suka lo6a, tace "babu wani bayan kai, kuma na Amince da ka sanar iyaye su shiga maganar, sai
Kuma fatan Allah shige mana gaba, yace "Ameen, Amma nayi matu'kar farin ciki, gaskiya auta ina sonki, so irin Wanda be musaltuwa, wani sanyi taji ya mamaye zuciyarta, tare da jin wani irin shau'ki a cikin ranta.


Haka suka kwashe kusan awa biyu suna Fira, kafin Daga bisani yayi haramar tafiya, har Bakin mota tayi masa rakiya, bayan sunyi sallama da Hajiya,


Wata leda ya Ciro Daga motar ya mi'ka mata, "ga tsarabarki, ta kar6a cikin jin kunya tare dayimasa godiya, Tananan saida yashiga mota yatafi, harya 6ace tana d'aga mashi hannu sannan takoma gida, cikin farin ciki ta tarar da Hajiya zaune falo ta mi'ka mata ledar.


Hajiya ta amsa tare da tambayarta "na miye? Auta tace "tasaraba ce khaleed ya kawomin, nan suka zazzage kayan suna cikin dubawa me gidan ya shigo, falon yanufa kai tsaye dayake ya jiyo maganarsu a can.


Hajiya tayi mashi sannu, itama auta cikin girmamawa tace "Baba sannu da zuwa, yace "yauwa zainabu, sannan ya kalli kayan dake gaban Hajiya yace "wannan kayan fa, tace "khaleed ne yazo yanzu be dad'e da tafiya ba, yakawoma auta tsaraba.


Kayan cosmetics ne masu tsadar gaske, sai takalma kala biyu, suma tsadadadu, sai swiss less guda, sai atamfa super aura, sai turaruruka designer's, masu dad'in kamshi.














Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊


*AUTAR HAJIYA* 💃🏻


🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊




®NWA




👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘




_Page_ 36-40




*Bayan wata d'aya*


Soyayya tayi nisa tsakanin khaleed da Autar Hajiya, dan yanzu yanda takejin khaleed a zuciyarta, bazata iya rabuwa dashiba, kome rintsi kome wuya, bata had'a sonshi dana Kowa ba, shima haka yake mata wani matsanancin so.


Yanzu dai iyaye sun san da maganar soyayyar khaleed da Zainab, dan har anyi maganar aurensu, ansaka ranar auren nan da wata ukku.


Ranar da auta tasan an saka ranar aurenta da khaleed, ranar jitayi kamar anyimata busahara da gidan Aljanna, saboda tsabar farin ciki , shima 6angaren khaleed d'in haka, dan tinda yake beta6a had'a son auta dana wata mace ba, ko fadila yana sonta ne kawai saboda wasu dalilai amma ko kad'an bazaya iya had'a son da yake mata ba da Wanda yakema auta.


***** ****** ******


"Wai ni khaleed bangane me kake nufiba, Cikin gadara da nuna isa take maganar "kana nufin ka raina za6in danayima a matsayina na mahaifiyarka ban isa dakai ba, sai kawai inji labarin wai ansaka ranar aurenka da Autar Hajiya, dan Baku d'aukeni a Bakin kome ba kaida mahaifinka, kun maidani shashasha, to wallahi baka isaba, wato ka za6i 'yar'uwarka shikuma mahaifin naka dan yaga d'iyar d'an uwansa ce shine ya Amince hadda sa ranar aure ba tare da saninaba, sai bayan anyi anyi kome angama ranar aure kawai ake jira tazo sannan aka sanar dani.


Tinda matar tafara magana khaleed be ce uffan ba sai da tayi shiru sannan yafara magana cikin nutsuwa, da Alamar rarrashi, yace "kiyi ha'kuri Momy nasan idan na tinkareki bazaki yarda da maganar aurena da Zainab ba, shiyasa na ro'ki daddy akan kada ya sanar dake har sai an tsaida ranar, amma dan Allah Momy kiyi hakuri, badan banison Fadila nayi haka ba, kawai manufata shine bayan na auri Zainab da kamar shekara ita kuma sai in aureta daga baya.


Wani irin salati ta kwad'a Wanda yasa 'yan'cikin sa juyawa, sannan tafara magana cikin masifa, Wato khaleed ni zaka cima mutunci ka nuna dangin ubanka sunfi dangina daraja a gareka, to wallahi ban Amince da wannan manufar takaba, sai dai kafara auren fadila sannan daga baya ka auri Autar, dan bazan hanaka aurensuba, dan su duka 'yan'uwanka ne, kuma Addini be hanaka auren Mace biyu ba ko ukku, kai harma hud'u, Amma kasani Fadila, itace ta farko idan kuma ka'ki za6ina to wallahi sai dai kafasa aurensu su duka.


Khaleed rasa yanda zeyi yayi, dan yasan halin mahaifiyarsa sarai, zata iya wargaje maganar aurensa da Auta, wacce kuma itace macen daya fara so a duniya kuma har yakoma ga mahaliccinsa baze so wata mace kamar yanda yake sonta ba.


Cikin tsoron halin mahaifiyarsa, yace "na Amince momy zanyi yanda kikace, zan fara auren Fadila Daga baya sai in auri Zainab d'in.


Bata san lokacin da ta saki wani murmushi ba tace "yauwa to ko kaifa, murmushi yayi na k'arfin Hali dan gabaki d'aya ji yake Momy tagama takura rayuwarsa.


Amma dan Allah Momy ina Neman wata alfarma, tace "ina jinka
Yace dan Allah Momy idan antashi sa bikina da Fadila, asa wata d'aya saboda baniso a canja lokacin da aka sa bikina da Auta, cikin nuna rashin damuwa tace "wannan kuma matsalar kace, idan ma sati d'aya kace a sanya iyayenta shirye suke,kamar yanda kake shirye.


A ranar Momyn khaleed ta sanar da daddynsa, yanda sukayi da khaleed, be musa mataba, ya Amince da duka bayanin datayi mashi.


Anje Neman auren Fadila, wacce ta kasanece 'ya ce ga 'Kanwar Momyn khaleed, Fadila kwarkwararrar 'yar duniyace, wacce boko yagama zaunawa jikinta, da kwalwarta, wayayyace ajin farko, zata kai shekara ishirin da biyar a duniya.


Cikin sati d'aya aka gama magar auren khaleed dafadila, ansaka ranar biki wata d'aya da sati biyu.












_To fah jama'a kunsan dai ba abinda Auta Hajiya tatsana kamar namiji me mata kuma gashi sahibinta wanda tafi 'kauna zaya fara auren wata kafin ita tab, 🤔 lallai akwai bada'kala_


*kudai kubiyo Zee Mmn khdy dan jin yanda zata kasnce*


08166169254






Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [01/08 7:32 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊


*AUTAR HAJIYA* 💃🏻


🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊




®NWA




👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘




_Page_ 41-45




*Bayan sati Biyu*




✍🏽 "Auta,....... Hajiya ce ta kwala mata kira tana daga kitchen, da sauri ta iso tace "gani, Hajiya ta mi'ka mata wani d'an karamin bokiti, "anshi ebo min ruwa nan in tsame d'an wakennan, sauri nake fita zanyi, da sauri Auta ta kar6a ta ebo ruwan takawo ta ajiye sannan ta d'auko kujera irin ta zaman tsakar gida ta zauna tace "Hajiya ina zaki ne?, Hajiya tayi murmushi tace kai lefe zamu koh, Auta ta kalleta cikin rashin Sani tace waye zeyi aure? Hajiya tace to waye zeyi aure kuwa in banda yayanki, Amma ay nasan dai ya sanar dake, Auta tace "Hmm Hajiya nifa ban gane wane yayana kike nufiba tukun,
_kwata-kwata Auta bata kawo khaleed aranta ba dan tasan ita kadaice za6insa kuma be had'a sonta dana kowaba_


Hajiya tace "yayanki khaleed mana, kina nufin be sanar dake nan da sati biyu za'a d'aura auren sa ba,


Jitayi kanta na juyawa, zuciyarta tayi mata nauyi, idanunta sun daina ganin haske, kanta yayi wani irin sarawa, lokacin kuma ta nemi numfaahinta ta rasa, Hajiya na daga kitchen kawai sai gani tayi Auta tafad'i kasa ba Alamar numfashi tattare da ita, da sauri tanufi inda ta fad'i tana furta Kalmar *Innalillahi,wa'inna,ilahirrajiun*
A d'imauce take gigizata tana kiran *Zainab*....... amma ko Alamun motsi batayi, cikin tsananin rud'ewa ta dauko waya takira me gidanta, ta sanar dashi Auta ce ba lafiya, gata kwance ko motsi batayi,


Cikin tsananin rud'ewa suka nufo gidan shida daddyn khaleed, dan lokacin da Hajiya tayi waya ta gaya Mashi suna tare.


Kusan minti sha biyar sannan suka iso, har yanzu Auta na kwance ba Alamun rai tattare da ita, Hajiya na tallabe da ita tana faman zubar da hawaye, batare da 6ata lokaci ba aka sakata mota sai asibiti, suna zuwa aka wuce Emergency da ita, kahleed shine likitan daya kar6e ta tare da taimakon wasu abokan aykinsa suke kokarin ceto rayuwarata,


Kusan minti talatin Amma Auta bata farfad'o ba, hankalin iyayenta yayi masifar tashi, ba kamar Hajiya wacce saboda tsananin kuka idanunta sun kumbura sunyi jawur, kallo d'aya zakayimata ka gane tsantsar tashin hankali tattare da ita.


An akai kimanin awa daya, sannan Auta ta farfad'o Amma duk da haka bata san inda kanta yakeba, haka aka fito da ita Daga Emergency, aka maidata wani d'akin, tare da sanar da iyayenta inshaAllah kome normal data farka, babu wani ciwo dake tartare da ita sumar datayima yanada Ala'ka da wani Abu daya d'aga mata hankali, amma muddin aka kiyaye zata cigaba da samun sau'ki, khaleed ne kema Hajiya wannna bayanin, dakuma daddynsa da Baban Auta Wanda su duka shi suke sauraro.










Zee Elkaseem
Mmn khady
[01/08 8:36 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊


*AUTAR HAJIYA* 💃🏻


🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊




®NWA




👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘




_Page_ 46-50






✍🏽 Hajiya zaune gaban gadon da Auta ke kwance, ta zuba mata idanu tana kallon yanda take maida numfashi, ahankli tafara motsawa alamar farkawa daga baccin datakeyi, Ahankali ta bud'e idanunta ta 'karema d'akin kallo ta tabbatar da asibiti take, sannan Ahankali ta ri'ka tino maganar da Hajiya ta gaya mata, wasu zafafan hawaye suka zubo ta gefen idonta, A zuciyarta tana cewa.


_shikenan rayuwata batada wani amfani wanda nikeso yaci amanata ya cuci rayuwata bayan yariga yasan ba wanda nakeso kamarsa, bazan iya mallakama wani namiji kainaba bayan shi, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta_


Da sauri Hajiya ta matso kusa da ita tana yimata sannu, "auta kiyi hakuri ki d'auki 'kaddara, kisani duk me rai ba Wanda kaddara bata fad'amawa, kuma ki d'auki wannan Amatsayin jarabawa ce daga nahaliccinki, kawai sai kiyi fatan cinye wannan jarabawar.


Cikin disashshiyar murya, auta tace "Amma Hajiya khaleed ya cuceni yaci Amanata yagama da rayuwata, Allah ya Isah tsakanina dashi.


Ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi, ta sauko daga kan gadon datake ta dur'kusa gaban mahaifiyarta, tace "Hajiya dan Allah ki gaya ma Baba bazanyi aureba har Abada, na hakura da aure, dan Allah Hajiya kada Ku 'kara tinkarata da maganar aure.


Kama hannunta Hajiya tayi ta mi'kar da ita tsaye, ta maidata kan gadon ta zaunar da ita, sannan tafara mata magana cikin sigar kwantar da hankali, tace
"Auta wannan maganar dakikeyi bame yiyuwa bace, ke kanki kinsan halin mahaifinki sarai ba saina sake maimaita makiba, kin San dai baze samaki ido ki zauna ba aure ba, kuma khaleed ba cewa yayi yafasa aurenkiba, maganar aurenki dashi tananan ba Abinda ya canja, ita wannan wacce ze aura d'iyar kanwar momynsa ce, kuma tin yana sudan mahaifiyar ita yarinyar tabashi ita, saboda haka inaso ki nutsu ki kwantar da hankalinki, kisani aurenki da khaleed ba fashi, idan kuma zaki tinkari mahaifinki da wannan maganar to kisani nidai ba ruwana.


A hankali aka turo kyauren d'akin, suduka suka maida hankalinsu gurin dan ganin me shigowa, khaleed ne yashigo da sallamarsa, sanye yake cikin milk d'in shadda wacce tasha ayki da zare copee, sai wani daddad'an 'kamshi ke tashi daga jikinsa, lokaci guda kamshin turarensa ya bige d'akin, kallo d'aya auta tayi mashi taji wani masifaffen sonshi ya'kara shiga zuciyarta, lokaci guda kuma ta tuno da cin Amanar dayayi mata, batasan lokacin data tashi Daga kan gadon datakeba taje ta cakumeshi, ta fashe da wani irin kuka, tace "Khaleed ka cuceni kaci amanata, Allah ya isah tsakanina dakai, kuma ka Sani bazan aurekaba koda Kaine auntan maza a duniya.


Da hanzari Hajiya ta mi'ke tana 'ko'karin 6an6are hannun Auta Daga jikin khaleed, amma hakan ya gagara dan Auta ba karamin ri'ko tayi Mashi ba, cikin 6acin rai Hajiya ke magana, "ki sakeshi nace auta, saima ta'kara rikeshi tana mashi wani matsiyacin kallo Wanda shi kanshi yakasa gane kona miye.


Ji kake tasss, Hajiya ta d'auke Auta da mari, hakan kuma yayi dai-dai da shigowar daddyn khaleed, da kuma babab ita Autar, cikin 6acin rai Hajiya take magana, "waike Auta wace irin shashashar yarinya ce da ina maki magana amma kin raina maganata, cikin sanyin jiki Auta ta saki khaleed tafad'a kan gado ta fashe da kuka,


Ko kad'an khakeed beji dad'in marin da Hajiya tayima Auta ba, dan dama yasan duk ranar dataji labarin aurensa zatayi abinda ma yafi wannna dan yanda take gaya mashi batason kishiya, ta tsani kishiya.








Zee Elkasee
Mmn Khady
[10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [02/08 5:24 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊


*AUTAR HAJIYA* 💃🏻


🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊




®NWA




👇🏻
_ZEE MMN KHADY_ 😘




_Page_ 51-55









✍🏽 "wannan zancen banza ne zancen Wofi, abinda baze ta6a yiyuwa bane,
Wato Zainabu kinaso ki maidamu 'kananan mutane ko? ko kinaso ki haramta abinda Allah ya hallata, duk namiji Allah ya halatta mashi Auren mace daga d'aya har zuwa hud'u, saboda haka ke baki isa ki haramta Abinda Allah ya halatta ba.


Mahaifin Auta ne keta faman fad'a tinda suka shigo asibitin shida mahaifin khaleed, Hajiya tabasu labarin abinda ya faru tsakanin Auta da khaleed.


Cigaba yayi da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,
Auta kuma banda aikin kuka ba abinda takeyi, kwance take kan gadon asibitin ta juya fuskarta dan bazata iya had'a ido da khaleed ba, dan ita kanta sai daga baya tayi danasanin abinda tayi mashi, cikin zuciyarta kuwa cewa take.


_Allah kasa kada Abinda na aikata yazama silar fasa Aurena da khaleed inason khaleed son da bazan ta6ayima wani namij iirinsaba_....


Wani sabon kuka ta fashe dashi lokacin data tsinkayo muryar daddyn khaleed yana cewa, "A'a Alhj baza'ayi hakaba kada fa atakurama yarinya, yakamata atambayeta aji ra'ayinta, tinda ada lokacin data Amince da aurensa ba'ayi da ita ze fara auren wata kafin itaba....


"Haba Alhj ka daina wannan mqganar" Baban Auta yafada' "yaushe zamu zauna yarinya 'karama kamar Zainab tana juyamu, "to kisani cewa aurenki da khaleed ba fashi, ke barima kiji in sanar dake, an sassauto da lokacin bikin yadawo lokaci daya da wanda za'a d'aura mashi nan da sati ukku, inshaAllah lokaci guda za'a kaima khaleed mata biyu, Alabashi kinga idan aka kaiki saiki kashe kanki saboda tsabar kishi, shashasha kawai wacce bata San ciwon kanta ba.


Cikin fushi yafita daga d'akin, daddyn khaleed yabi bayansa, Hajiya ma binsu tayi,
Harabar asibitin suka tsaya daddyn khaleed yana cigaba da ba d'an'uwansa hakuri " yana cew "Kabi kome a sannu Zainab d'in duka nawa take dazaka ri'ka yimata fad'a kamar kanayi da wata babbar mace, duka bana fa take cika shekara sha takwas, kaga kuwa akwai 'kuruciya tattare da ita.


Hajiya dake tsaye tana saurarensu, tace " haba Alhj ai halin Zainab dole sai da haka, idan ba'a tsawata mata haka zata ri'ka mana yawo da hankali, ni kaina naji dad'in haka, kuma 'kara da aka sassauto da bikin ayi a huta.


Daddy khaleed yace "Allah sa haka shine mafi Alkhairi, suduka suka Amsa da "Ameen.


Cikin d'akin kuwa khaleed na ganin fitar iayensu yafara rarrashin auta, yana nuna mata irin sonda yakemata,
Amma ko kallo be ishetaba,


Ahankali ya matso ya dur'kusa kusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login