Showing 1 words to 3000 words out of 23148 words

Chapter 1 - AUTAR HAJIYA COMPLETE Book Writing by Zeey Maman khady.txt

16 Dec 2024

1212

๏ปฟ[10/16, 7:54 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [29/07 3:49 am] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 1-5








_Amincin Allah ya tabbata ga duk wanda ze karanta wannan littafi nawa, duka da ma wanda besamu damar karantawaba_. ๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป


โœ๐Ÿฝ Kwance take kan d'an madai-daicin gadon mahaifiyarta, hannunta ri'ke da waya, kirar tecno Hยณ wani game take me matukar sanyata nishad'i, Ta tattara hankalinta duka ya koma kan wayar.


Muryar Hajiya ta tsinkayo tana kwalla mata kira, da sauri tasanya pause a game d'in domin zuwa kiran mahaifiyar ta.


"Hajiya gani, tafad'a bayan ta d'an rissina gabanta, Alamar girmamawa, matar da takira da Ahjiya ta d'ago ta kalleta, tace "ki shirya inaso in ayke ki yanzu, tace "ina? Tace "kije ki shirya mana koma inane ay zakiji.


'Daki tanufa ta cire kayan jikinta, tayi d'aurin kirji, sannan, tafito ta cika bokiti da ruwa ta nufi toilet.


Bayan ta she'ka wanka, tafito tanufi d'akin dai daya kasance nan ne na mahaifiyarta Wanda da Alama itama nan take, kwandon kayan shafarta ta d'auko ta ajiye gabanta, Wanda babu abinda babu aciki, tafara d'and'asa kwalliya, takai kimanin awa d'aya tana kwalliya, bayan tagama ne ta tashi' tanufi wadrope ta dauko wata green d'in atamfa, me zanen ganye golden, nd yellow, wacce akayima ado da yellow Codeless d'inkin zamani riga da zani pieces.


Bayan tasaka kayan, sun kuma kar6i jikinta, dan ba 'karamin kyau saukayimata ba, sun fiddo da duk wata kya'k'kyawar halitta da Allah yabata.


Fara ce, Amma ba irin tass d'innan ba, farinta dai-dai misali, tanada manyan idanu Wanda akoda yaushe idan ta kalleka, sai kayi tinanin kashe maka su takeyi, amma ba haka bane haka yanayin kallonta yake, ga dogon hanci Wanda ya 'kara fito da anaifin 'kyawunta, bakinta d'an karami, hakoranta farare tas, sai wushiryar data 'kara fito da kyawun su, gefen kumatunta ko magana take yana lotsawa, barantana kuma idan tayi dariya, wannan dimple ba karamin 'kara fiddo da 'kyawunta yake ba.


Bayan tagama shirinta tsaf, ta dauko hijab d'inta, kalar golden, ta Sanya tiare ta dauko ta feshe jikinta dashi, sannan ta d'auko plat shoes shima kalar golden, ta Sanya, tanada tsayi shiyasa bata damu da takalmi me tudu ba.


Fitowa tayi tsakar gida, inda mahaifiyarta ke jiranta, tace "gani Hajiya.


Hajiya tace "yauwa dama gidan Maman Ummi zakije, kicemata ya maganar adashi, yanaji shiru, ko har yanzu, ba'a gama had'a kud'in ba?.


Kuma kice ina gaisheta, sannan ta d'auko naira Hamsin tabata, Anshi ki hau napep, ta kar6a sannan tafice Daga gidan, Hajiya namata fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya.


Taje gidan ayken harta, Isar da sa'kon takuwa yi sa'a dan angama had'a kudin saboda haka aka bata, dama kwasar adashine na Hajiya.


Kasancewar hajiyar kud'in zuwa kawai tabata, can kuma gidan dataje, Mmn Ummi tabata, kud'in napep d'in Amma ta'ki kar6a, saboda haka a 'kafa ta tafi, tana tafiya tana zancen zuci, tayi matu'kar danasanin tahowa a 'kafa domin yanda ta lura da duk Inda ta gifta maza ke binta da ido.


Azuciyarta tace "Allah ya taimakeni hijab na Sanya, da nabani.










โœ๐ŸฝZee Elkasem
Mmn khady.
[29/07 4:33 am] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 6-10






โœ๐Ÿฝ Da sallama tashigo gidan, kitchen ta iske Hajiya, tana faman dafa masu abincin rana, Hajiya tafito Daga kitchen d'in tana mata sannu da dawowa.


Ta fiddo da kud'in ta mi'ka mata tace "gashi kuma Mmn Ummi tace tana gaisheki, kuma tace "dan Allah kiyi hakuri wallahi mutanen ne sai Ahankali,


Hajiya ta kar6i kud'in cikin farin ciki, ta kirga su dubu tamanin dai-dai, sannan ta kalli Autar Hajiya tace, "to Auta ga kud'in adashi sun samu yanzu ki gaya mani dami-dami kike bu'kata, kinga gobe idan nafita gurin ayki sai in sawo maki.


Autar Hajiya tayi murmushi, taji dad'i har cikin ranta, game da yanda iyayenta suke nuna tsantsar so da Kauna da kuma kulawa a gareta, dan ita iya saninta tinda ta taso gidan, bata ta6a neman wani Abu tarasa ba, duk da iyayenta ba masu kud'i bane Amma sunada rufin asiri, domin mahifinta yana ayki, mahifiyarta ma tana ayki.


Da misalin 'karfe hud'u na yamma, Hajiya suna zaune tsakar gida itada autarta suna shan iska, kasancewar yau Alhamis ba'a zuwa islamiyya.


wani yaro yayi sallama, bayan an amsa Mashi, ya gaida Hajiya, sannan yace "wai ance ana sallama da Zainab a waje, Hajiya tace je kace waye, yaron yaje ya tambayo sannan ya dawo yace, "wai yace ba'ko ne, dan Allah ta taimaka tafito, Hajiya tace jeka kace tana zuwa.


Tayi saurin tashi daga kwancen datake, tace dan Allah Hajiya kice baninan, ni wallahi banison wannan kiran, nifa ban ma San ko wayeba, Hajiya tace "to kifita mana sai kiga kowaye, haba zainabu na wulkanci bashida kyau, kifita ko gaisawa kuyi sai ki dawo ba sai kin dad'e ba.




Hijab dinta ta Zara, ta Sanya, wacce tsawonta ya kai mata iya gwiwa, sannan ta fita.


Jingine yake jikin motarsa, baki ne amma ba kirin ba, yanda 'kya'k'kyawar fuska, yanada saje Wanda ya'ara fito da kyawunsa, gajere ne dan baza'a ta6a sashi sahun masu tsayi ba, zai kai kimanin shekara talatin da takwas a duniya.


Tinda ta fito ya zuba mata, idanu yana kallonta, harta 'karaso, ta gaidashi, ya amsa cikin fara'a, Daga nan bata 'kara magana ba, sai shi yacigaba da magana.


"Wato Zainab, hausawa sunce maso tsuntsu shike binsa da jifa, a gaskiya tinda naganki naji kin kwanta min arai, kuma ba kome ya'kara karkatar da Hankalina garekiba illah kamun kanki, da kuma kaywun surar da Allah yayi maki, nidai tafe nake da 'ko'kon barata, idan kin Amice aurenki zanyi dan ba maganar wasa ta kawoni anan ba.


"Au sorry nacikaki da saurutu ban ko fad'a maki sunana ba, sunana "Adam kuma ni d'an nan cikin garin katsina ne, ina zaune a Unguwar Al'kali da iyalina, inada mata d'aya da yara ukku, da fatan zaki kar6i soyayya ta.


Kafin tayi wata magana ta hango babanta tafe kan mashin d'insa saboda haka bata tsaya bashi amsaba ta shige gida.


Nan Baban nata ya Tarar da Adam kofar gida, bayan sun gaisa, yayi Mashi yan tambayoyi.








Zee Elkaseem
Mmn khady.
[29/07 9:30 am] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 11-15






โœ๐Ÿฝ Koda ta shigo gidan d'aki ta wuce, ta d'auki wayarta tacigaba da danne-danne, azahiri idan ka ganta wayar take dannawa, Amma zuciyarta cunkushe take da tinani barkatai.


Itako a tsarinta babu Auren me mata, saboda ita mace ce me tsananin kishi, yaushe zata yarda ta auri namiji me aure, Amma wannan mutumin yama raina mata yawo, to wallahi, da matar shi hada 'ya'ya ukku kuma sannan yace yana so ya aureta, ya Allah tsareta da aurensa, wani irin mugun hauhinsa taji ya rufeta, itako da beda mata da zata iya daurewa ta Auresa, kidan saboda yanda babanta ya matsa akan yanaso tayi aure.


Da sallama mahaifin nata ya shigo, Hajiya dake zaune tsakar gida ce ta Amsa sallamar, sannan tayima me gidan nata sannu da zuwa, bayan ya amsa da "yauwa" d'akinsa ya wuce, Hajiya tanufi gurin ajiye ruwa tacika boket da ruwa takai toilet, sannan ta iske me gidan nata d'akinsa tace "Alhj ga ruwan wanka can na kai ma kewaye, yace "to bari inje inyi wankan, "Amma kafin in Shiga inaso in tabayeki, tace "to Alhj inaji, yace "Wannan yaron dana gani 'kofar gida yazo gurin Zainab tin yaushe yake zuwa, Hajiya tace "yau ne farkon zuwanshi, da Autar ma tace bazata fitaba dan bata sanshiba, nice nace tafita taji me ke tafe dashi,
Alhj yace "kin riga kinsan banison inga yarinya tana tsayawa da samari barkatai, saboda haka ki gaya ma ita Zainab d'in idan har tana son wannan yaron to tasanar dashi yaturo da magabatanshi, kafin yacigaba da zuwa gurinta.


Hajiya tayi murmushi tace, "Haba Alhj Daga zuwa d'aya sai ace yaturo kamar muna Neman maraba da d'iyar, ay dole dai su samu su fahimci juna kafin a kai ga maganar iyaye, yace " kidai gaya mata idan tana sonshi ya turo magabantashi, idan kuma bata sonshi kada in'kara ganinsa 'kofar gidannan, "kuma da kikace ba Neman maraba ake da itaba, so kike mu tasa ta gaba muyita kallonta, tinda tagama makaranata, kuma islamiyya sunyi sauka ai Alhamduliilah, Aure kawai yarage muyi mata hankalinmu ya kwanta, haka suka gama tattaunawa sannan ya fito yanufi kewaye, dan yin wanka, ita kuma tanufi d'aki inda Autar Hajiya take tana ta tinane-tinane kala-kala.


Da sallama ta shigo d'akin, ta isketa kwance, kamar me bacci, amma ba baccin takeba' tinani ne kala-kala acikin zuciyarta, nan Hajiya ta bayyana mata yanda sukayi da babanta, na maganr ba'kon datayi yau.


Cikin tsananin firgici, ta dafe 'kirji tace "wallahi Hajiya bani sonshi, ni banma sanshiba, yau ne fa kawai nafara ganinsa, "Dan Allah ki gaya ma baba abar wannna maganar, murya saukaji kamar Daga sama yana cewa, "ba saita gaya maniba inaji, waike zainabu yaushe zakiyi hankali, ki nutsu ki fitar da miji kiyi aure, yaufa shekara biyu kenan da gama makarantarki, Amma ko kad'an bakiso ayi maki maganar aure, to kisani bazan sanya maki ido ba kina zaune, muddin idan nagaji da zamanki zan za6a makin duk Wanda naga ya kwanta min arai.


Wasu hawaye masu zafi suka zubo, kan kumatunta, tace dan Allah Hajiya ki gayama baba wallahi banison miji me mata, wallahi zan iya auren Kowa amma banda me mata, Hajiya tacigaba da rarrashunta tana cewa, haba auta, saboda me bakison me mata, mace nawa ta Auri me mata ukku ma itace cikon ra hud'u kuma ta xauna lafiya.


Wani kululun ba'kin ciki taji ya tokare mata zuciya.


Azuciyarta tace _Ni in auri me mata ukku ay 'kila kafin a kaini zuciya ta buga namace saboda tsananin kishi_
_kome mata d'aya bazan iya aureba_


Wani sabon kuka ta faahe dashi.














Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:54 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [29/07 7:16 pm] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 16-20




โœ๐Ÿฝ washe gari haka Autar Hajiya ta tashi jikinta sukuku, a zuciyarta tana ma Adam Allah ya Isah, yanzu gashi sanadin zuwanshi, yajawo mata babanta ya tado da maganar tayi aure, Wanda a da ya lafa da maganar, kuma shi gashi yanada mata barantana ta auresa, itako yanda babanta ya matsa mata akan tafito da miji wallahi da Adam bayada mata data auresa, saboda Adam beda makusa, Amma kuma ya cuceta daya furta mata kalmar "So" Alhalin yanada mata, _Allah ya isah tsakanina da kai Adam_ ta Furta afili tare da zubar da wasu guntayen hawaye.


Ranar haka ta kasance ita d'aya cikin gida, tinani kala-kala ya addabi zuciyarta, kasancewar yau litinin Hajiya tana gurin ayki, tana aykine a general hospital katsina, yayinda babanta yake ayki, ma'aikatar agric, fannin dabbobi.


Da sallama wani yaro ya shigo, ta amsa masa sallamar, sannan yace auta ana sallama dake waje, tanajin haka bata tsaya tamabayar waye me sallamar ba tace kace ina zuwa, ko ba tamabaya tasan be wuce Adam, takoyi matu'kar farin cikin zuwansa dai-dai wannan lokacin, yanzu ko zata fita ta bige masa warning.


Hijab ta Sanya, sannan ta zari silifas d'inta na wanka tanufi kofar gida.


Shine kuwa, Wanda take tsammanin, jingene yake jikin motarsa, yauma yayi shiga ta musamman, yayi masifar kyau, cikin gadara da tsiwa ta isa gabanshi, yau ko gaisuwa be samu arzi'kinta ba, ta tsaya gabansa tare da d'aure fuska kamar bata ta6a dariya ba.


Cikin fara'a yake magana, "sannu da fitowa gimbiyar mata, ina fatan dai ban takura maki ba danazo dai-dai wannan lokacin, wallahi nakasa daurewa ne da rashin ganinki.......


Hannu ta d'aga mashi, tare da yimashi magana cikin d'aga murya, "dakata! Adam kake ko waye, inaso in gaya maka ka fita hanyata, dan wallahi tallahi kaji rantsuwar musulmi wacce daga ita babu wata, to ko duniya zata rage daga ni sai kai bazan aure kaba.


Cikin tsananin tashin hankali, da mamakin jin kalamanta, Wanda koda wasa beyi, tinanin jin wannan daga gareta ba, a yanda ya d'auketa yarinya, me hankali, da nutsuwa ga kuma uwa uba ilimi, na addini dana zamani.


Cikin sanyin jiki Adam yafara magana, yace "Zainab saboda me kika yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kaina,? Ko kinyi bincike ne kingano wani aybu da nike dashi?.


"Ko d'aya tafad'a, illah dalili d'aya shine bazan iya auren me mata ba, "idan kuwa ka nace akan saika aureni to wallahi saidai akai gawata gidanka, dan zan iya shan guba in kashe kaina, na tsani kishiya, hakan ne yasa duk Wanda ze zomin da maganar aure bamu dai-daitawa, saboda mafi yawancin masu zuwa Neman aurena masu auren sunfi samarin yawa.


Bata jira abinda ze fad'aba tashige gida,zuciyarta cunkushe da abubuwa da dama.


Wani kululun ba'kin ciki ya tsaya ma Adam azuciya, yama kasa matsawa daga Inda yake, yakai kimanin minti talatin tsaye a gurin sannan Daga bisani ya shiga motarsa ya tafi, jikinsa ba laka ko kad'an.


Tana shiga gida, ta wuce d'aki kan gado ta fad'a ta fashe da wani irin kukan takaici, kuka take baji ba gani.


Daga waje kuma anata sallama, amma batajiba, saboda kukan yinsa take tsakaninta da Allah.


Jitayi ba'ada niyyar amsa sallamar data dad'e tanayi, saboda haka kutsa kai tayi cikin d'akin, dan tanada tabbacin Hajiya bata nan.


Autar Hajiya datayi nisa cikin kuka, sai ji tayi an dafata, da sauri ta d'ago da manyan idanunta da suka canja zuwa ja saboda tsananin kuka, sadiyya tagani wacce batasan lokacin data shigo gidan ba.
Cikin tsananin damuwa sadiyya, ke magana, "kawata, meya faru? Naganki cikin wannna yanayin.


Bata tanka mataba, illah cigaba datayi da kukanta.








Zee Elkaseem
Mmn khady
[30/07 7:37 pm] .: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 21-25








โœ๐Ÿฝ Sai da tayi kuka me isarta sannan ta d'ago ta kalli sadiyya, wacce ta kasance 'kawa ce gareta, tin suna yara kuma bata da wata aminiya data wuce ta.
Nan tabata labarin duk abinda yafaru, tin zuwan Adam dakuma Abinda babanta ya fad'a na cewa idan bata fito da miji ba ze za6a mata duk wanda yaga yayi masa.


Sadiyya ta numfasa, sannan tace "wallahi Autar Hajiya kinada problem, ni narasa gane kanki, kwata-kwata tinda nake ban ta6a gani ko jin me irin wannan tsatstsauran ra'ayin ba irin naki, be kamata ace kin kartake akan ke bazaki auri me mata ba, ki duba kiga kwanaki yanda kukayi soyayya da Bashir kamar bazaku ta6a rabuwa ba, ba irin tsantsar soyayyar dabaki nuna masa ba, Amma lokaci d'aya kika bad'e ido toka kikace baki sonshi, dan kingano yata6a Aure kuma ya rabu da matar, wai kina gudun kada wata rana yace ze maida ita.


Auta ta numfasa sannan tayi wani guntun murmushi Wanda yafi kuka ciwo, tace "hum sadiyya bazaki ta6a ganewa ba wallahi duk lokacin da wani namiji yace yana sona daya furta min yanada aure jinake kamar in kashe kaina, dan na kwammace na mutu dana auri me mata.


Sadiyya tace "to Allah kyauta, Allah rage maki wannan zafin kishin naki, tace Ameen ni kaina ina yawan yin wannan addu'ar dan wallahi wani lokaci abin har tsoro yake bani.


"Wai ina khaleed ne? shiru naji kin daina zancensa, ko shima yanada matar ne?.


Auta tayi murmushi, wanda yasa har kumatunta suka lo6a, tace "Hmm khaleed mutanen Sudan, ay yana can karatu, kawai yasa gaba, ni inaga kila yanzu ya manta dani, shekara hud'u fa kenan rabon da muga juna, kuma tinda yatafi ko waya bamu ta6a yi dashi ba, Amma kuma ni nasan har in mutu bazan ta6a son wani d'a namiji kamar yanda nake sonshi ba.


Sadiyya tayi murmushi, tace tabbas kunyi tsantsar soyayya da khaleed, kuma bani tinanin shima ze iya mantawa dake, kuma naji ajikina khaleed shine mijin dazaki aura.


Wani farin ciki ya rufe Autar Hajiya, dan tinda take duniya bata ta6a son wani namiji ba, irin son datakema khaleed, Cikin jin dad'in maganar sadiyya tace "Allah ya tabbatar min da hakan, Allah sa khaleed yazama mallakina ni kad'ai batare daya had'ani da wata jaka ba.


Sadiyya tayi dariya, cikin tsokana tace au amaryar taki kike kira jaka, Auta ta kaimata duka cikin wasa tace "bani son iskanci, ki dainamin wannan wasan khaleed nawa ne ni d'aya Kedai kawai ki tayani addu'a Allah sa be manta daniba, sadiyya tace "to Allah sa be manta dakeba kuma Allah sa yana dawowa musha biki, su duka suka sa dariya, haka suka sha firarsu, sam Auta ta manta da wani ba'kin ciki datake tattare dashi, jitake kamr har khaleed d'inma yadawo an d'aura masu aure saboda tsabar farin ciki.


Sai gab da Hajiya zata dawo sannan sadiyya tayi haramar tafiya, Auta tayimata rakiya, tare dayimata Al'kawarin zuwa gidansu ranar Friday.










Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:54 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [31/07 10:47 am] ๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š


*AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š




ยฎNWA




๐Ÿ‘‡๐Ÿป
_ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜




_Page_ 26-30




*โ€ขBayan Wata biyuโ€ข*
Kwance take kan tabarma, tayi filo da cinyar Hajiya, yayinda ita kuma Hajiya ke tsefe mata manyan kitson dake kanta, cikin shagwa6a ta ri'ke hannun Hajiya tare da rintse ido Alamar tanajin zafi, tace "Hajiya dan Allah kiyi min Ahankali da zafi, Hajiya tace "to sarkin son jiki tsifar kan shine keda zafi, kitson da be wuce 'kwaya goma ba, cikin shagwa6a tace ni wallahi shiyasa ban fiye son kitson ba ma, dan dai kawai kina matsawa sai nayi.


Murmushi kawai Hajiya tayi "Uhm" sannan tacigaba da kwance mata kan, bayan ta 'karasa kwance mata kitsin, tasa masharci ta sharce ta shafe mata shi da mayuka masu kyau da dad'in 'kamshi, sannan ta hade mata shi guri day'a ta d'aure mata shi, yayi gwanin kyau ya zubo har kan kafad'unta, ga gashinta da tsantsi, ga tsananin ba'ki kamar na larabawa.


"Assalamu Alaikum, sallama yayi tare da shigowa cikin gidan.
saurayine, d'an kimanin shekara ishirin da tara a duniya, kya'ky'kyawa ne ajin farko, ba fari bane, Amma kuma baz'a kirasa ba'ki ba, choculate colour ne, me matsakaicin tsawo, jikinsa kuwa baza'a kirasa me 'kiba ba kuma ba za'a kirasa ramamme ba.


Hajiya ce tayi saurin tada, sadiya daga kan cinyarta, tace " a,a,a Bakin sudan ne, saukar yaushe, Auta najin haka tayi saurin kai dubanta ga Wanda aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login