Showing 18001 words to 21000 words out of 21010 words

Chapter 7 - MAI SAKO Garin Neman Gira Book Complete Document by Billy Galadanci .txt

09 Dec 2024

1072

bi bayanta har zuwa wani babban parlour dake da dining anan ta zauna shima ya zaune matar jiya ta kira ta zuba musu abinci tana kallon matar ta ce, ki zauna muci abinci mana." Matar da ta saba da kirki hajiyarsu taja kujeea ta zauna tana murmushi ta zubawa kanta, Anty ta ce "Saif wannan mai aikin gidance sunanta Munira, Munira kinga wani ƙanina daga Zaria sunansa Saif." Munira cikeda girmamawa ta kuma gayar dashi ya amsa fuskarsa a sake ganin tare da me aiki ma take cin abinci ya sanya Saif ya saki jikinsa yaci abincin sosai bayan sun kammala Munira ta kwashe kayan, Hajiya Nasare ta ce "Saifullah ya kukayi da Mama." Yana ɗan murmushi ya ce "Anty ta yi addu'a kawai, maganar zama anan ɗinma tace in zauna dama ɗaki ɗaya ne gidan so ni ina kwanan zaure ne ko kuma in kwana ɗakin samarin layinmu." Murmushi ta yi


"Alhamdulillah haka ake so ubangiji Allah ya sa alkhairi ne sgaremu baki ɗaya, amma don Allah ka rike amanar fukiyar mutane Saif kaga nima sure nike a gidan duk da ina da aikina amma wannan dukiyar dai ba tawa bace Kam." Cikin ladabi ya ce "In Shaa Allah" Bayan dan wani lokaci ya mata sallama akan gobe zai tattaro ya dawo.


**************
Bayan kwana uku.*


Yau ma dai Meenal na maƙale a ɗakin Bashir duk yanda ya korata ƙin zuwa ta yi shikuwa harga Allah sam bayaso take shige masa a jikin nan, kuma da farko tsoronsa yaga tanayi yanzu kuwa yaga ta rage wannan tsoron ba hanyar be bi da ita ba amma taƙi tashi daga bisani akan 3str dake ɗakin ta kwanta tana kallonsa da murmushi


"Yaa Bash saboda gadonka kake korana ko don't worry i will just sleep here." Be iya yace mata komai ba sai kallonta ya ke har sanda bacci ya fara ɗaukarta, sai da baccinta ya yi nisa sannan a hankali ya sakko daga kan gadon carefully ya buɗe ƙofar not to wake her up ya fice daga ɗakin baya ya rufe mata duvet a jikinta.


Da asuba Mami ta sakko ta bishi da kallon mamaki, tashinsa ta yi akan yaje ya yi sallah at the same time tana tambayarsa me ya ke a parlour?" Be bata amsaba ya wuce ɗakinsa ya tarar Meenal ta fito daga toilet da alwalarta anan ɗakin tayi sallah sannan ta fito bayan ya wuce masallaci ta shiga ɗakinta. A daren ranar Zuhair ya iso Abuja anan suka zauna hirar duniya Meenal kuwa tana can maƙale da shi kamar zata cinyeshi tsabar shagwaɓa. Daga bisnai sai watsewa akayi aka barsu shi da ita akan saman cinyarshi bacci ya kwashe ta, Bashir ya fito daga ɗakinsa yana kallon Zuhair ya ce "Wai Zuhair haka Meenal ke zuba taɓara yarinyarar nan so biyu tana kwana a ɗakina, gaba ɗaya na fahimci bata samun kwaɓa a wurinku kai kaga ranar farko yanda ta maƙalƙaleni kamar wata jinjira? Shiyasa jiya data kwana a ɗakin ni a parlour na kwano wai tukunna tsaya kaima tana maka haka." Murmushi Zuhair ya yi kafin ya ce


"Bash ai kasan Meenal tun tana ƙarama a wurina take kwana kuma kasan son jikine da ita kamar mage, ni kaina yanxu abin yana damuna banaso tana xuwa ɗakina kwana amma duk randa takejin haukan ko yays zan mata ssi ta kwana." Bash da tunda ya fara magana yake kallonsa ya sauke wata iriyar ajiyar zuciya kafin a hankali ya ce,


"Zuhair ka mata faɗa ta daina, nan ɗinma da ta ke xuwamun halama kasheni take so ta yi? Gwara ma kai ai kasan ƙanwar jininka ce ni wallahi ranar data kwanamun na farka tun 4 har asuba ban koma bacci ba kaga idan wani dabanne fa? Shin kowane brother a wurinta brother ne? Beside ta girmi wannan shashancin don ko yanzu aka aurar da ita zata haihu." Zuhair ya ɗanyi murmushi kafin a hankali ya ce "Bashir you are also her brother talk some sense in to her brain, ni idan na koreta wani zubin kuka take kwana yi." A nutse Bashir ya ce "Zan mata magana gobe gaskiya saboda tsaro." Shiru sukayi kafin daga bisani Xuhair ya soma ƙoƙarin tashin Meenal, zsune ta miƙe tana mutsitsike idonta kafin a hankali ta ce "Yaa Zuhair muje ka kwana a ɗakina kaji." Yana kallonta ya ce "A'a Meenal ba za'ayi haka ba ɗakin Bashir nanne ɗakin samari kije ɗakin su Intee mana." Bata fuska ta yi kamar zatayi kuka


"Ai yaya su basa sona fa, tunda nazo idan bq Yaa Bashir ba bamai kulani kamar sunga kashi." Dariya kawai Zuhair ya yi ya ce "Laifin kine bakya sakin jikinki da mutane sam na rasa meyasa." Miƙewa ta yi kawai ta nufi hanyar ɗakinta saboda bacci sosai takeji.


*****************
Babban compound ne mai ɗauke da flat huɗu sunyi kyau sosai har ba'a magaba, gaba ɗaya gidan kacokam na ma'aikatan gwamnati matasan masu kuɗi a aljihunsu, dukkansu aikine ya kawo su da iyalansu a garin Abuja kuma duk compound ɗin suna mutunta juna matan sun ɗauki junansu kamar wasu aminan juna saɓanin mazan da iyakarsu da juna gaisuwa saboda duk ayyukan su yasha kansu. Yau ma kamar kullum duk matan compound ɗin suna zaune a farfajiyar gidan a ƙasan parking lot da ke cikin gidan wanda dama kowane gida a gefensa akwai parking lot da zai ɗauki motoci guda biyu to a kowane lokaci akwai mijin ɗaya da baya shigowa sai after magrib to kuwa kullum anan suke zaune suna taɗin duniya. Mijin ɗaya daga cikin su aka wangale gate ya shigo dukkansu idon su ƙyam akan motar kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kansa ya isa yay parking sannann calmly ya sakko daga cikin motar lokaci guda ilahirin compound ɗin ya haɗe da ƙamshinsa, Salima lumshe ido ta yi ta bude sannan ta kalli Yusra ta ce "Your boo is back yana baɗemu da ƙamshi as always." Dariya Yusrah ta yi irin an yabi mijinta ɗinnan yafi na kowa ƙamshi kafin ta ce "Yea That's My Boo for you." Kowa ya ɗan dara Arwa na kallon Yusrah ta ce "To ki tashi mana." Taɓe baki ta yi sannan ta ce


"Saboda ga ubana ya dawo ko? Ai yaji dashi kawia sai duka mazan gidan sun hallaro ma tashi a tare." Shewa sukayi dukkansu shikuwa batare da ya koda kalli inda suke ba duk da yake dama dai yanada nisa da su ya nufi cikin gidansa kai tsaye a can ƙasan zuciyarsa yana jin zafin wannan zaman banza da matan suke yi, kullum fatanshi ya samu gidan da bashida nisa da office mamar wannan ya ɗauketa acikin matan. Bai wuce 10mns da shiga ciki ba Mijin Amrah ma ya shigo ya samu wuri yay parking ya ƙaraso wurin ya musu sallama sannan duk suka gayar dashi ya wuce cikin gidansa, haka suna nan zaune sai da tas mazan gidan suka dawo banda mutum ɗaya wato Mujib da ya tsani ganinsu duk yammaci ya sanya kwata kwata ma ya daina sha'awar dawowa da yamma sai after Isha. Yusrah ce ta fara miƙewa kafin ta ce


"Yanzu zanje ina isa ta baya zanbi in shiga ɗakina sai na gabatar da sallah har isha zai ganni kunsan kalan nawa takun daban dana sauran mata, yanzu zan ɗauki wani arnen wanka in baza Her royal highness khumrah na magana ya ƙare." Duk aka kwashe da dariya a wurin ta juya ta ce "Sister's ma haɗu gobe da yamma." Ta juya tana wani mulmula katafaren kunkurunta cikeda shaƙiyanci, Sameerah kallo ɗaya ta mata ta taɓe baki sannan taci gaba da dannan wayarta acan ƙasan zuciyarta kuwa takaicine sosai aranta kasancewar moha ba mijinta bane sam sam ta gama raina ajin mijinta dama dukiyarsa saboda yanda matar Moha Yusrah ke zuzuta girman abin wandonsa ma kawia ya isa ta gano mijinta bai wani kai ba, underneath her breath taja wani gajeran tsaki mara sauti, Salima ce ta miƙe alright my giant MB ya dawo i have to now mu haɗe gobe kawai." Nan duk suka watse ya saura Sameerah ce kawai miƙewa itama ta yi ta shiga gidan Yusrah ta main parlour mai aikinta ta leƙo take ce mata tana ciki, kutsa kanta tayi ta isa har tsakiyan parlour tana kallon Moha ta washe baki "Uncle Moha good day." Kallonta ya yi so ɗaya ya ɗauke kai kafin ya amsa kamar baya so a taƙaice "An wuni lafiya."


"Alhamdulillah, afuwan na shigo muku wallahi abu nake so dama in karɓa a hannun Yusrah." Baice mata komai ba ta wuce tana wani lanƙwasa kunkuru kallo ɗaya ya yi wa bayanta ya ɗauke kai yaci gaba da shan Coffee da ke gabansa saboda yanayin sanyi a garin, acan ta shiga Yusrah na wanka ta fito tana wani kwarkwasa ta kalleshi


"Uncle Moha ina saurin bazan iya jira ta fito daga wanka ba, kuma na tabbatar Mujib yana hanya yanzu bana so ya dawo bana gida, idan dai ta fito kace saƙon ta ajiyemun gobe." Batare da ya kalleta fuskarsa yana TV ya ce "Ohk." Juyawa ta yi sai kuma ta dawo


"Uncle yi haƙuri ina ta damunka wayana ba chargy zan kiran Mujib ya tahomun da fruits ko zaka bani aron wayarka?" Da hannu ya nuna mata wayar "Here you can use it." A saman table ɗin ta ɗauki wayar ta yi dialing number ta ya soma ringing ta kashe ta goge kiran sannan ta ajiye mai wayar


"User busy bara in haƙura kawai." Baice mata komai ba ta juya kawai ta fita sannan ta ƙulle ƙofar. Tana isa balcony ta dafa ƙirjinta this is the 10th time tana trying samun number wayarshi sai yanzu Allah ya yi a saɗaɗe ta koma gidanta ranta fess.


**************
*Bayan 2 weeks.*


Tuni su Meenal sun bar Abuja bayan sunsha dogon zama, Bash yayi iyakar ƙoƙarinsa wurin shawo kan Meenal da ɗabi'unta kuma ta masa alƙawarin zata gyara duk wata ɓarnarnar da ta ke aikatawa. Ta dawo da suturun hausawa sama da talatin duk Bashir ne ya ɗinka mata yana ji da Meenal ainun, can ƙarƙashin zuciyarsa kuwa ya ƙudirta aransa komai turancin mahaifinta da zaran takai 18yrs zai aureta don kuwa tuni yanzu ya gama shigewa jikinta yanaso ya koya mata son shi tun tana cikin ƙuruciya yanda nan gaba baxata ce masa a'a ba, yau tana kwance a ɗakinta a gida wayarta ya soma ringing ta kai hannu ta ɗaga ganin Yaya Bash tayi azamar kai hannunta ta ɗaga tare da kaiwa kunne


"Yaya." Ta kira sunanshi a shagwaɓe yana murmushi ya ce "Cuty menene?" Cikin shagwaɓar ta ce "Bakai ba ne inata kiranka baka ɗagawa tun safe." Gyaran kwanciyarsa ya yi sosai kafin ya ce "Kiyi haƙuri ina school ne ina dawowa na tafi shagunan mu na duba dannsn na taho gida." Shiru ta masa ya ce "kinci abinci?" Tace "Bana son porridge." Ya ce "To me zaki ci?" Buɗa hannu ta yi ya ce "Fried rice and chicken?" Ta ce


"Gasashiyar kaza da youghurt." A hankali ya ce "To zan tura a saya miki nan da 1hour zai iso miki." A hankali ta ce


"Yaa Bashir." Ya ce "Na'am." Ta ce "Me ake nufi da french kiss?" Shiru ya yi na wuccin gadi kafin ya ce "Ke a ina kika ji?" Shiru ta ɗanyi kafin ta ce "Noo a wani novel ne nagani ance miji da mata suna yi." A ɗan fusace ya ce


"Meye novel? Wato Meenal bakya ji ko? Ina ruwanki da wnai novel st your age? Idan na rabaki da wannan ki koma wancen ko? Inata lallaɓa ki amma sai gaba gaba abinki yake yi ko? Tunda har sukace anyi French kiss ai sun faɗa yanda akeyi so banda shashancin ni meyasa zaki tambayeni kina son mayar da kanki 'yar iskar yarinya duk abin da y'an iskan yara sukeyi kema shine burinki ko?" Cikin tsoro ta ce


"Allah yaya ba haka bane ba i have no one to ask shiyasa na tambayeka." Cikin ɗaga murya ya ce


"If you really want to ask questions why don't you ask about your religion or anything concerning education na wani aspect kiss ɗin kawai ya isa kisan cewar kalmar iskancine, look Meenal daga yau ba ruwana da ke kar kuma ki ƙara kiran wayana na gaya miki dai." Ɗif ya katse wayar jikinta a sanyaye ta ƙara dialing number shi amma har ya gama ringing bau ɗauka ba, a kasale ta mayar da kiran zuwa wurin ƙawarta Sauda suka gaisa tace "Sauda is there anything wrong in asking your brother cousin brother what a french kiss is?" Sauda dake zaune kusa da Mamanta ta miƙe tana cewa "Ntwrk rawa Meenal me kike cewa?" Ƙara maimaita tambayarta ta yi a nutse ta ce


"Tooh lallai babbar magana ma kenan, to indai ba rashin kunya da tashen balaga ba me zai kai mace tambayar namiji irin wannan abun ko ubanta ne ko, ai ƙarshen rashin kunyaf da mace zatayi namiji ha mata kallon 'yar iska kenan." Hankali tace Meenal ta ce "Na shiga uku, wallahi Sauda Yaa Bashir na tambaya kawai ƙawata ɗinnan nacewa anmun wa'azi yayuna da suka kamani ina kallon wannan abun na tuba na daina shine nace mata yanzu da bama zuwa school ina yaw0 fita akaina shine tace idan na shiga Google a saka hausa novels zangansu da yawa inke karantawa shine naga wai ango da amarya akace french kiss sukayi i just wanna know what that was shine na kira Yaa Bashir and at the end he insulted me like hell and hang up, shine duk na damu." Sauda ta kalli ƙofa sannan ta ce "Gaskiya Meenal ke matsalarki wowta wallahi ke basai n ki kiran ba meye wani kiran sa? Yanzu kinsan zaton zaiyi ke 'yar iska ce maza suna taɓaki?" Da sauri Meenal ta tashi zaune "Maza kuma? A ina na gansu ni wallahi ba ruwana da wannan abin kawai ni i was curious about it shiyasa amma ba haka bane ba."


"To shi ya zaiyi ya gane Meenal?" Kawai send him a text ki bashi haƙuri next time ki raba kanki da wannan shirmen zamu koma SS1 soon focus on your books ki raba kanki da biyewa ƙawayen banza." Jiki a mace tayiwa Sauda sallama ta ƙara kiran Bashir yaƙi ɗagawa ta tura masa message nan ba ba reply gaba ɗaya jikinta sai da jikinta ya mace murus.


Saif yau yana zaune a parlor ɗin Antynsa wuraren ƙarfe 9 na dare bacci yake ji amma ta tasashi a gaba da kallon wani film ita da Munira, har yanzu ya kasa sakin jiki da ita a matsayin sa na ɗan gida, ganin kallon ba mai ƙarewa bane ba ya ce


"Anty Bacci na ke ji wannan film dai ina ga banda ni a masu ganin ƙarashensa." Dariya ta yi tana kallonsa "Saif kenan kana son baccin wuri, mai gidan ya kusa dawowa next week zai dawo saboda haka akwai yawo gaskiya, sai kayi haƙuri idan yazo saboda akwai aike kamar me." Murmushi kawai ya yi ya miƙe tace "To shawarmar fa? Kaife kace sai dare zaka sayomun." Dariya ya yi mai sauti"Idan kince inje yanzu ai sai in je." Tana mayarda dubanta ga TVn ta ce "A a sai nace kaifa kamun alƙawari."


"Wannan kallon ne ya ɗauken hankali ai." Ya fada yana shafa sumar kansa "Gyaran zamanta ta yi "Jeka da yamma gobe ka saya mun." Sallama ya musu ya fita ya tafi challet ya kwanta bayan ya yi alwala saboda baya kwanciya sai da alwala shikam.


*********
Tunda Daddy ya dawo tafiyar da ya yi zuwa lagos ta kwana uku Mom ta rasa inda zata sakashi, suna zaune a parlor kamar ko yaushe amma, tana manne a jikinsa kamar wata jinjira, yaran kuma basanan sun tafi siyo abu, tana shafa lip's ɗin sa da ɗan yatsanta tana sakar masa murmushi ta ce "Honey i missed you kwana uku sai naji kamar shekaru uku da badan emergency da muka samu ba da ba abin da zai hanani binka." Kalabar kanta yasoma shafawa yana kashe mata wani kallo "Really 'yan matan malik ai ni na zata kin manta dani jiya good 4hours bamu yi waya ba and i called bakiyi picking ba." Narkewa take a jikinsa "Ɗan saurayin ɗawisu ai kaima kasan bazan taɓa iya mantawa da kai ba, ko na minti ɗaya bare 5hours wani theather muka shiga mai wahala shiyasa." A hankali ya ce "Can i?" Tana wnai shagwaɓe mai ta ce "Sure mana." Bakinsu ya haɗe wuri ɗaya nan da nan suka faɗa wata duniyar ma'aurata. Isowar su Zuhair gidan ta sauka da ledar abubuwan da suka sissiyo, shi kuwa ya tsaya waya da Bashir a mota, da sallama ta shiga parlour turus ta tsaya tana kallonsu bata ko ƙiftawa duk da ba wadatar harke a parlour don dama idan suna nan wani deep light suke kunnawa a parlour da dare amma kamar a screen na tv take ganinsu suna sambatu Dad is just giving momy kisses all over her neck and ears, sai surutai sukai suna smooching juna, tanata tsaye kusan 3mns basu ganta ba har Zuhair ya shigo baiko lura dasu ba sai da yaga tana kallon direction ɗin sannan ya sake baki yana kallon ikon Allah shima ganin tsayin bazai fisshesu ba yaja hannun ƙanwarsa da har ta zune ledojin a wurin suka dawo balcony giving her warm hug ranshi a tsananin ɓace da abin da iyayen suke, ita kuwa sai kawia ta fashe da kuka lokaci ɗaya jikinta yana rawa, haka kawia itama bataji daɗin ganinsu haka ba, yanzu ta fara hankali kuma yayanta yana yawan nuna mata su momy abin da suke shine halastacce sabosa zamtowarsu mata da miji amma yanda suke ba haka annabi ya koyar ba a ɗaki akace suje su kashe fitila, a hankali a wurin kunnenta ya ce "Stop crying dear ai ke bakisan suna cikin ba so laifin su ne kinji daina kukan, next time da zaran kin gansu a haka just leave the place immediately and make sure baki tsaya kallon komai ba ba kyau." Da ƙyar ya lallaɓata ta yi shiru amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login