Showing 15001 words to 18000 words out of 21010 words
Chapter 6 - MAI SAKO Garin Neman Gira Book Complete Document by Billy Galadanci .txt
Shiru ya yi baice komai ba amma a ranshi yana mamakin wannan wace irin macece mai saurin sakewa da aminta da mutane haka daga sama anyama tana da gaskiya kuwa? Har suka iso gidan ba wanda ya yi magana aka wangale musu gate suka shiga ya samu ƙarƙashin bishiya ya parka saboda ilahirin farfajiyar ajiye motocin a cike ya ke da motoci irin na alfarma, bayan ya tsaya ma sai da ya maimaita mata cewar sun ƙaraso har so biyu sannan ta amsa tare da ce masa sakko mu shiga ciki." A nutse ya ce
"Aunty a wurin aiki da ƙyar aka bari na fito komawa zanyi ina sauri kinga sai na je titi neman abun hawa."
"Karka da mu Saif ba daɗewa zaka yi ciki ba magana kawai za mu yi." Ba don yaso ba ya fito ya karɓi jakar hannunsa suka nufi ciki a wani irin tangamemen parlour da ya sha tsari da kayan duniya suka zauna inda atake ya takure a ƙasa yana kallon makeken hoton ita da mijinta kamar ka kirasu su amsa ka saboda girmansa sunyi kyau ainun yasha jinin jikinsa ganin wanene mijinta don sanannen ɗan kasuwa ne da aka sani sosai, Da hannu ta muna masa kujera
"Saif meye haka? Ka xauna akan kujera mana." Yana sussune kai ya ce "Anty ai nan ma ya wadatar." Ɓata fuska ta yi "Haba Saifullah, nanfa ba falon oga bane ba falon baƙine kurun kuma baƙin bana oga na mawa so please feel at home and make yourself comfortable." Yana ɗan murmushi ya koma akan kujerar a takure, wata hanya tabi ta wuce ciki kusan 35mns sai gata ta sake dawowa da hijab har ƙasa kamar kullum wata matashiyar mata da bazata haura shekaru 40 ba biye da ita da tire a hannunta lemo ne da ruwa sai snacks a gefe a wani plate ta durƙusa kusa da shi ta tsiyaya masa lemon sannan cikin ladabi ta miƙa masa ya karɓa yana godiya sannan ya matsa sha biyu ya mayar ya ajiye akan tray data bar masa akan side table. Bayan shiru na kusan mintuna uku Hajiya Nasare ta ce
"Saif nasan abubuwa da yawa zasu gitta maka arai musamman ganin na kawoka gida ban sanka ba, yanda duniya ta lalace sai kaga abin kamar ba gaskiya to ba haka bane alkhairi ne a tafe da ni, da farko dai ni Sunana Hajiya Hauwa Kabir Samaru haifaffiyar garin nan a ƙaramar hukumar Zaria a samaru, mahaifina Alhaji Kabir shi kaɗai iyayensa suka haifa har suka rasu basu kara haifar wani ba, haka nima mahaifiyata Hajiya Uwani da mahaifina ni kaɗai suka haif, Babata kuma a wurin iyayensu du biyu rak ƙaninta daya ya rasu kuma yabar mace da yara biyu itama daga baya ta bishi. Duk wannan ne dalilin da ya sa bamuda dangi na kusa sosai sai ni kaɗai bayan rasuwarsu na dawo abar tausayi ga tsaiko a wurin samun mijin aure don kuwa sai da na zama cikakkiyar likitar mata sannan na hadu da Me gidana a lokacin inada 29 yrs muka yi aure inada 30yrs yanzu haka ina 40yrs a shekarun haihuwa, mai gidana matafiyi ne sai ya shekara ma bai zo ba saboda sabga ya masa yawa, bani kaɗai bace matarsa yanada wata macen ɗaya suna tare yanzu haka a istanbul take ita, ni saboda aikina yace in zauna anan, ban taɓa haihuwa ba kuma shima bai taɓa haihuwa ba koda ɗayan matarsa kuwa har yanzu Allah bai kawo ba, kaji kaɗan daga cikin tarihin rayuwata na biyu kuma shine "Ni bansan daɗin kowa ba irin 'yan uwa haka sai in manta ana baƙi ma sai abokan arziki wallahi Saif ina cikin damuwar kaɗaici shiyasa muna haɗuwa na yaba da hankalinka ka kwantamun arai dama ina neman direba idan bazaka damu ba don Allah ko personal driver na ne ka zama kaji?, nayi direbobi sunfi bakwai sata suke mun kamar ɓeraye, akwai ma wandaa gudu da mota ma, oga bayaso ina tuƙi ni ba wani namiji makusanci ko 'yar uwa mace ba ganinan dai damuwar kaɗaici ma ya isheni, ada mahaifiyar me gidana ke zaune tare da ni yanzu shekaru biyu kenan da ta rasu." Jin tayi shiru ya sanya ya ɗago ya kalleta kafin a hankali ya ce
"Kiyi haƙuri Aunty amma ina da mutanen da nike kulawa dasu, aciki akwai mahaifiyata da ƙanwata mace ɗaya saboda me bina tana can tana aure a Zaria wannan kanikancin da nike da shi nike taimaka musu, Adaidaitan da nike hawa ma na abokinane yake bani aro da dare bayan na taso daga wurin oga na safe sai in kai masa shi a lokacin yake fita, waɗannan sana'o'in guda biyu sun rufamun asiri shekaru sama da bakwai haka nakeyi har nayi nasarar kammala degree na a fannin engineering as a mechanical engineer sai dai Nigeria ba aiki, kada kiga kamar nayi turning offer ɗinki zanyi matuƙar takura idan na ajiye duka waɗannan ayyukan na dawo yin wannan." Shiru ya biyo baya na kusan mintuna biyar kafin a hankali Nasare ta ce
"Saif na fahimceka sosai amma wannan rejecting na tayi na da kayi ya sanya na ƙara tabbatar wa kaina cewar kai mutumin kirki ne, don Allah ka tausayamun kaji duk abin da zaka samu a harkarnan da kake zan linka maka shi har so huɗu ko nawa ne." Shiru ya biyo bayan maganar kafin a hankali Saif ya ce
"Ya tsarin fitarki ya ke?" Tana dubanshi ta ce,
"Ni ma'aikaciyar lafiya ce ƙwararriya a fannin mata, kowane lokaci aiki yakan iya tasomun musamman acikin dare wannan ne dalilin daya sanya Yallaɓai baya son ina zama ba standard driver sabods fitan dare ga duniyan ya lalace, amma idan ba wani emergency zakaga fitana daga 8 na safe ne zuwa 4 na yamma."
"Hajiya hakan yana nufin kenan komai dare idan akwai emergency case i have to come over to your place in kaiki?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce
"But Saif you can stay here at the chalet mana, em even if it means you bring your mom here dama ina neman abokanan zama wallahi." Yana ɗan murmushi ya ce
"Munfi shekaru ashirin muna haya a hayin rigasa, tun ma mahaifinmu yana da rai, na tabbatar yanzu ba inda zataje komai zance mata kuwa ba zata ɗaga ba." Tana ɗan murmushi ta ce
"Saif mahaifiyarka tana raye kaje ka yi shawara da ita akan wannan aikin, na tabbatar ko ma'aikacin da zaiyi aiki a ƙaramin ma'aikata ba zai karɓi salary na 150k ba ni kuma su zan baka duk wata in shaa Allah, zamanka anan yana nufin kai abinda zakaci da wanda zaka sha da ƙananun buƙatunka duk zan maka ai kai ƙanina Saif, idan ka kirani Anty daɗi sodai nikeji saboda ban taɓa su an kirani da hakan ba masu aikina duk Hajiya suke cewa kaga ko ai na samu ƙani." Murmushi kawai ya yi ta ciro ATM ɗinta ta miƙa masa tace
"Kaje kayi fueling motar hannunka ka cikata naga takai quater tank, ka ciromun 100k kuma zanyi amfani da shi gobe yanzu tashi ka tafi da yamma idan na dawo aiki zanji yanda kuka yi da Mama." Hannu biyu ya sa ya karɓa tana karanto masa pin kafin ya miƙe ya mata sallama.
**************
*ABUJA*
Tunda suka iso gidan suka gaisa da iyayensu Sawwama ta kai Meenal ɗakin da zata sauka har aka shafe awa huɗu bata sake ganin kowa ba sai masu aikin gidan, bayan isha ta kira yayanta, yana daga kwance ya ɗaga wayar yakai kunnensa ya ce "Mimi" a hankali ta ce "Yaya its bored over here, bakaji gidanba shiru fa tunda muka zo muka gaida da Maminsu ban ƙara ganin kowa ba sai mai aikinsu dake sintiri a kaina da kayan ciye ciye kamar wata mayunwaciya." Murmushi ya suɓuce masa yana yi ya ce
"Mimi haka suke rayuwarsu, kema ai kin sani ba sabon abu bane just kill or you call Bashir kice kin gaji da zama ke kaɗai." Kamar zata yi kuka ta ce
"To yaya yaushe zaka zo?" Matashin gemunsa ya shafa yana murmushi "Next week Mimi are you already missing me?" Tana shagwaba ta ce "Ba kowa ma anan da zai tayani bacci kaga tsoro nikeji kamar ni kaɗai ce a wurin."
"Just pray and nothing will happen in shaa Allah kinji." Nan suka yi sallama ta ajiye wayar tana tunani har bacci ya ɗauke ta.
Washe gari aka fito breakfast gaba ɗaya gidan wuraren 7:30 am sai a sannan taga Yaya Bashir, kowa ya gaida iyayen sannan na ƙasa da kai zai gaisheka, suna tsakiyar cin abincin Mimi na kallon Bashir ta ce "Yaa Bashir don Allah ka kaini yawo inga gari." Abba na kallonta ya ce "We need some table manners here keep quiet young girl." Shiru ta yi ta na mamakin yanda aka yi tsit kowa na cin abincinsa a nutse har aka kammala daga nan aka tilasta kowa fadan Bismillahillazi aɗa'amani haza, sannan manyan iyayen suka fara tashi, yaya bashir ya miƙe sannan su Inteesan suka miƙe Meenal ma haka ta ce
"Intee Please kinada any cartoon a laptop ko wani movie ki bani aro in kalla Please?" Intee na kallonta ta ce
"Kin koma ɗaki kin maƙale ba dole damuwa ta miki yawa ba kizo ɗakinmu koda kallon zakiyi dai." Bin bayansu ta yi Bashir ya bita da ido saboda duk sun girmeta amma kalli dirinta ko idan ta kai 18yrs wane abu ya rage kuma.
Bayan magrib Bashir na zaune a babban parlour gidan Meenal tazo ta zauna kusa dashi tana kallonsa da manyan idonta ta ce "Yaa Bashir zaka sayamun kaza Please?" Kallonta ya yi fuskarsa ba yabo ya fallasa ya ce "Duk kajin da ke gidan?" Langwaɓar da kanta ta yi a hankali tace
"Yaa Bashir i hardly eat fried chicken sai gasashiyar kuma wannan fried chicken nem" har lokacin idon sa na kanta ya ce"Then you grill it your self mana." Kwantar da kanta ta yi akan kafaɗarsa ta zagaye waist ɗinsa da hannayenta biyu "Yayanmu Please mana kaji." Bashir wani iri yaji a jikinsa ya janye da sauri yana kallonta cikin ido ya shafe few seconds kafin yace"Naji tashi zan saya miki." Ƙara rungumarshi ta yi "Ohh Thanks alot bro, in ɗakko Hijab ɗina muntafi tare." A kasale ya ɗan tureta jikinsa ya ce "Yea ki sameni waje." Ya miƙe da sauri itama ta miƙe ta shiga ɗakin data sauka ta shirya acikin riga da wando ɗamammu as alwasy sannan ta bar saka hijab iya gwiwarta ta babbaka turaruka don wannan momynta ta sabar mata tun tana karama. A mota ta samesa ta shiga ta zauna nan take ƙamshinta ya haɗe ko'ina a motar ta Bashir ya lumshe idonsa ya ƙara buɗewa kafin ya ce "Mimi." Kallonsa ta yi tana Murmushi ta ce "Bro." A hankali ya ce "Ki rage saka turare da yawa kinji ba kyau haramunne mace ta saka turare mai tashi idan zata fita." A hankali ta ce "Alright bro zan riƙa shafa kala biyar me makon goma." Dubanta ya yi da kyau amma baice komai ba ya mayar da hankalinsa akan tuƙin da yake, suka saya kaza da youghurt sannan suka juyo zuwa gida, kai tsaye ɗakinsa ya nufa tabi bayansa acan suka zauna ta cire hijab ɗinta shi dai tsoron kar Maminsa tazo part ɗin nasa ya ke saboda ko ƙannensa sai lalurar dole ake barinsu zuwa wurinsa shima ba zama ba ta ci wando kam sai ƙamshi take sumar kanta sai sheƙi take bazawa, anyi parking nata a tsakiya jelar yana reto saida taci sosai ta shiga toilet ɗinsa ta wanke baki ta ɗaure alwala tazo ta yi sallan isha sannan ta kwanta akan gadon sa yana takure shidai ya kalleta ya ce
"Mimi bzakije ɗakinki ki kwanta ba?" Turo masa baki ta yi "Yaa Bashir wallahi ni tsoro nikeji don Allah ka barni in kwanta anan zuwa 12 saika tasheni in zaka kwanta naga ku bakwa kwanciya da wuri." Ta juya masa baya ya ce
"To da wannan kayan xaki kwana?"
"Idan ka tasheni anjima zan canja." Shiru ya yi taja duvet ta rufe jikinta ta lumshe idonta. Bashir parlour gidan gaba ɗaya ya koma yana zauna yana kallo, wuraren 10:pm Mami ta shigo parlon ta kalleshi ta ce "Bashir baka kwanta ba." Yar dariya ya yi kafin ya ce
"Ban kwanta ba Mami ina kallon wani film ne ." Jinjina kanta ta yi kafin ta ce
"Alright ni zan kwanta gobe ka tashi ƙannenka Sallah yallaɓai yana gari bazan sakko daga daman ba sai zuwa 10 acan yace zamuyi light breakfast so karku jiramu breakfsat, ina ita waccen sangartacciyar." Da sauri ya ce
"Ai tunda mukaje gidan Hajiyar Sama ita da zaran anyi isha take bacci ɗabi'arta ce ta kwanta tuni." Mami bata kawo komai a ranta ba ta juya kawai bayan sunyi sallama sai da safe.
Bashir yanata zaune wurin har sai wurin 11:30 ya kashe wutar parlon ya kashe komai sannannya nufi balcony zuwa ɗakinsa, tashin duniya ya yiwa Meenal da ƙyar ta miƙe shikuwa dama baccin gaske yake ji kawai ya nemi wuri ya kwanta ita kuma toilet ta shiga ta yi fitsari ta dawo wutar ɗakin kawai ta kashe ta ƙara shigewa duvet ɗin sai bacci wuraren ƙarfe huɗu Bashir ya farka yaganta jikinsa dumu dumu, ba ƙaramin bugawa zuciyarsa ta yi ba yanda ta kamashi ta rungume gamgam, duk da acikin duhune hakan ba zai hanashi ganin baccin da ta ke mai zurfi fa hankali a kwance, ƙoƙarin janye jikinsa ya ke ta kamashi gamgam ya sauke wani kasalallen ajiyar zuciya haka Bashir ya farka tun lokacin sai asuba ta sakesa ta juya kwanciyarta a wahale ya sauke wata irinyar nannauyar ajiyar zuciya ilahirin ƙamshin jikinta ya gama hallakar da shi.
Washe gari kuwa Mimi ko a jikinta ta saba kwanciyar ɗakin Zuhair ita da gaba ɗaya batama saka komai a ranta ba don haka daya tasheta sallah wucewa kawai ta yi ta yi sallan ta a ɗakin sannan ta wuce ɗakin da ta sauka ta cire kayanta tayi wanka ta daka dogurwar rigar atamfa ja fitted gown ce da ƙyar take motsi a cikinta ta tafi breakfast Bashir sai kallon gefen ido yake wurga mata, Intee ta ce "Yaa Bashir kaga fa kayan da Meenal take ɗinkawa ko tafiya da ƙyar ta ke amma mu sai dai a banka mana wasu maka makan riguna kamar ba Abuja girls ba." Dariya Bashir ya yi hana kallon Meenal ya ce "Mimi jikine da ita ba kamar kuba ita ma wurin tailor ɗinku zan kaita yau a ɗinka mata maka makan bubu ta daina takura a cikin waɗannan wahalallun kayan ko Mimi?" Murmushi ta sakar masa "A yaya Bashir ina so wallahi, irin ɗinkin su yana burgeni?" Yana motsa shayin gabansa ya ce "Karki damu xan ɗinka miki ashirin ku kuma goma goma." Kujerarta ta ja baya ta bashi side hug tare da pecking chicks ɗinsa "Thanks bro." Ta faɗa tana murmushi mu intee suka kalli juna, shi dai Bashir ta kuda dasƙarar da shi a wurin don yama kasa ɗagowa Sawwa da bata iya shiru ta ce "Ke dai Meenal rayuwar yahudawa ya aureki wallahi, Dad yaga kina hugging brother Bashir sai ya kusa karyaki." Kallonta kawai Meenal keyi as if trying to assimilate what she just said a hankali ta ce "Why? Isn't he my brother?" Bashir ya ce "Table manners please." Shiru duk suka yi sai da aka gama breakfast sannan suka koma parlor yanzuma Meenal kusa da Bashir ta zauna kamar zata koma cikinsa, duk abin da Zuhair take masa shi ta ke wa Bashir, daga ƙarshe haƙura Bashir ya yi da zama wurin kawai ya tashi.
**************
Saif na durƙushe gaban mahaifiyarsa bayan ya gama ya mata bayani yana jiran ta ce wani abu sai can ta ce "Bashir ka daɗe kana neman aiki ko da na gwamnati ne kuwa baka samu ba, kampaninma babu, ni bana buƙatar ka da komai sai Alkhairi duk sanda baka wurinta ka tafi garage abinka ka gayawa oganka yanzu ba kamar da ba ka samu aiki, maganar komawa gidanta kai ka koma, dama ai kwanan wahala kake a gidan ɗaki ɗaya a tsuke mu uku ina maka fatan alkhairi." Godiya sosai ya yi sannan ya bar gidan.
Free pages
Mom Nu'aiym.
07084161619
*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)*
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
My sister you can't have that big tommy and still look fresh,young and beautiful, munada haɗaɗɗen Flat Tommy powder da zai taimaka wurin narka kitsen ciki which is 100% natural ingredients.its just a tea da zaki tafasa kisha ba ya saka gudawa in shaa Allah. Munada abubuwan gyaran buje iri iri kayan matan mu a top notch munada turarukan wuta da kuma khumrahs na asali masu siyo mutunci. Always send us a DM ki amshi rabonki.*
1.Deep beach
2.Deep Ocean
3. Deep sea
4. Date syrup
5. Coconut syrup
6. Tightening herbs pills
7. Aci a laƙe
8. Breast enlargement powder
9. Breast firmin oil
10. Ci da kaza
11. Manta uwa
12. Khumrar Mallaka
13. Flat Tommy powder
14. Infection flusher
And lot's more. Mun fara end of year sells ɗinmu so maza ku hanzarto a Sweetner zone by season 7 ku kwashi rabonku. 07084161619.
08
Saif na zaune a parlor Antynsa kamar yanda yake kiranta fruits ne a gabansa an baza mai su ya kasa sha shi wannan ɗawainiyar ne bai gane ba kwata kwata, shigowa ta yi ko yanzu ma da Hijab a jikinta da carbi ta zauna a nesa da shi sosai akan wata kujera tana fara'a ta ce "Azumi na yi yau Saif yamma kaxo bazan iya fitowa ba ya aikin?" A ladabce ya gaisheta sannan ya ce
"Ga kuɗin Hajiya da safe kince in ajiye a wurina." Ya haɗa da ATM ɗin ya taka har kusa da ita ya miƙa mata ta sanya hannu biyu ta karɓa tana masa murmushi ta ce
"To Sannu Saif na gode sosai."
Komawa ya yi ya zauna ta miƙe tace taho shigo kaci abinci mana." Ya kalleta amma bai tashi ba har takai kofa ta juyo tana kallonsa "Saif bakaji bane wai?" Muje kaci abinci mana in samu ladar ciyarwa dama yau na yi azumi." Jiki a sanyaye ya