Showing 3001 words to 6000 words out of 21010 words

Chapter 2 - MAI SAKO Garin Neman Gira Book Complete Document by Billy Galadanci .txt

09 Dec 2024

1068

ya tasheta ya nufi toilet ya ɗauro alwala ya fita ita ma sallah ta yi ta wuce shirin school atare suka fito daga balcony na ɗakunansu suka nufi dining inda suka tarar Dad yana bawa Mom chips a baki tana ci tanata shagwaɓa wai zatayi late yana kallonta ya ce "But Wife ba na ce ki ajiye aikin gwamnatin nan ba ki mayar da hankalinki akan aikin daya shafi asibitinki ba, ke kinfiso ki riƙa tarawa kanki aiki haka." Langwaɓar da kanta ta yi kafin ta ce


"Ina so inyiwa al'ummata hidima Dr. Idan na ce sai clinic sai fa masu halin zuwa clinic ne kawai zasu je." Murmushi ya sakar mata


"To Allah ya bada lada good Samaritan." Dariya tayi yaran suka gaishesu suka zauna suma Zuhair ya zubawa ƙanwarsa ta dawo kusa dashi akan lallai sai ya bata iyayen suna kallonsu suna murmushi suna jin daɗin bound ɗinsu sosai, Dr. Malik ya gyara mata zaman rigar likitocin da ke jikinta ita kuma ta ta tayashi saka botiran shirt ɗinsa biyu na sama ta ɗaura rigar suit a saman shirt ɗin, haka suka yiwa yaran sallama suka barsu suma a gaggauce ya gama feeding nata ya riƙo lunch box da Baba Audi me aiki ta kawo mata suka fice daga gidan sai da ya yi dropping nata school sannan ya wuce makarantar shima.


***************
Da yamma daga school ya tafi ɗaukarta don dama ya gayawa driver shine zai dawo da ita. Gidan granny ɗinsu suka biya suka tarar tana waje wurin ababen kiwonta da aka yiwa gida da waya babba doguwa an sassaka electric wire saboda barayi wurin tsaf ta shiga ta basu abinci ta fito kallon yaran ta yi ta taɓe baki kafin ta ce "To kai kuma duk bayan kwana ɗaya sai ka ƙara tsawo yaron kamal fal waya sandandan kamar wani jikan samudawa." Murmushi kawia ya yi yayinda ita kuwa Meenal ta taɓe baki a daƙile ta ce "Good Evening granny." Granny ta taɓe bakin itama tana shiga gate ɗin gidan ta ce "Uban kine haka ni idan bazakicemun Hajiyar sama ba ki kirani Fatima kanki tsaye bana son munafurci meye wani ginanny?." Dariya Zuhair ya yi ita kuma ta ɓata fuska dama basa ga maciji da Hajiyar Sama saboda faɗanta da shegen gwasale mutane da ya cika mata ciki. Shiga cikin sukayi ta zauna a saman kujera suna ƙokarin zaunawa ta kalli Meenal ta ce "Kul kika haumun akan kushin saina mareki zauna a ƙasa ko ubanki Maliki a ƙasa yake zama bare ke karan kaɗa miya, ko ki zauna a ƙasan dai ko kiyita tsayuwa wannan kuma ke ta shafa." Zuhair dai ƙasa ya zauna badon Meenal tasona tana turo baki ta zana kusa dashi a ƙasan, Hajiyar Sama ta ce "Ya aka yi kunzo kun wani mun zaune me ya kawo ku?" Murmushi ya yi ya ce "Hajiyar Sama munzo gaisheki ne kawai kwana biyu makaranta nike zuwa shiyasa ban zo ba." Tsaki ta ja a jagule ta ce "Kaga ni ku riƙe gaisuwarku, bakwa ƙaunata saboda ina gayawa ku da iyayenku gaskiya shiyasa bakwa zuwa yanzu Fisabilillah ganɗamemiyar budurwa kamar Amindago ace tana saka wannnan shegiyar rigar iya gwiwa? Ƙauri duk a titi tsabar lalacewa kuma ba kallabi sai wata matsiyaciyar hula wai da sunan uniform fuk faɗin kaduna ma karantar musulmai ne sai ta arna, to ubangiji Allah ya sakamun a wurin Rashida don duk abin da kuke tana gani ina ji ina gani Maliki sai abin da uwarku ke so ya ke ni me zance?" Sauke numfashi Zuhair ya yi be dai ce komai ba ta miƙe tsaye ta nufi fridge ta ɗakko masu ruwan roba da kofuna, ko kallonsu Meenal batayi ba ta koma ta zaune ita dai zuciyarta fal baƙincikin halin da matar ɗanta ta koyawa yaranta na rashin sanin darajar musulunci kwata kwata, shi dai Zuhair bayan ya sha ruwan ya ce "To Hajiya zamu koma mu." Taɓe baki ta yi


"Allah ya tsare hanya ka gaida Maliki." Haka suka bar gidan gaba ɗaya ran Zuhair ba daɗi da basu zo ba ta kira uban ta kai ƙara idan sunzo ta yi ta zagin uwarsu, ga shegen ikon bala'ee wai ita me kuɗi.


*************
A gida da dare yauma kamar kullum Momy na maƙale jikin Dad tana shagwaɓa akan zata bishi tafiya holland shi kuwa yana lallaɓata kamar ƙwai, sajensa take shafawa muryarta kamar za ta yi kuka ta ce "Honey Please kasan yanda nike maganar wata biyu fa naji kana yi.? Sauke numfashi ya yi underneath his breath ya ce "Alright young lady ki shirya mu tafi." Wani ihu ta yi ta maƙalksleshi yaran suka bisu da kallo dama bajin abin da suke cewa suke ba muryoyinsu ƙasa ƙasa kamar sunsha sun bugu. Haɓarsa ta riƙo ta cusa bakinta a nata ta bashi wani short but deep kiss ta sake in just 3 to 5 seconds da sauri Zuhair ya ɗauke idon sa daga kallonsu ganin Dad yana wani murmushi ya kafe ta da ido yana shafa sumar kanta da har sun saba ganin yana wasa da shi kullum. Ƙanwarsa da ya ga ta shagala da kallonsu ya bugarwa cinya ta juyo tana kallonsu tare da cunno baki ta ce "To me na yi." Hannunta ya kama duka bar wurin zuwa balcony na ɗakunansu ya rufe ƙofar suka wuce ɗakinta ta ƙarasa assignment ɗinta. Bayan sun kammala assignment ɗin da suke a tare tace mai zata je ta ɗakko ruwa a store Baba Audi bata saka mata ruwa a fridge ba, agogon hannunsa ya fara kallo ya tabbatar zuwa yanzu su Momy sun shige yace ta je maza ta dawo ta kwanta gobe friday akwai school. Ganin ta shafe 20mns bata dawo ba ya sanya ya fito nemanta anan balcony ya ganta tana leƙa cikin parlor shima bai motsa da yawa ba ya taka ya tsaya bayanta kasancewar yana da tsaki yana leƙawa da sauri ya ɗauke kansa zuciyarsa na bugawa da ƙarfi ya kalleta yaga ta shagala da abin da take kallo ya ɗanja baya daga can ya ce "Meenal." Da sauri ta juya tana kame kame ya dubeta sosai ya ce "Me kike anan?" Muryan Dadd dake wata irin hargowa ya sanyashi janye hannunta da sauri ya rufe kofar balcony ɗin ya rumgumeta a tare suke sauke numfashi kusan 4mns sannan suka wuce ɗakinta ya zaunar da ita yana mata wani kallo.


Free pages....


Mom Nu'aiym.
07084161619
08039424298






*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)*


*BILKISU GALADANCHI*


*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*


Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8


03.


Fuskarsa a daure sosai ya ce "Meenal me ya sa kike leƙen su Momy? Ko kunsan wallahi zan zaneki in kuma daina shiga harkarki idan baki sauya wannan attitude din banzan da kike ba." Shiru ta yi tana kallonsa trying so hard ta ɓatar da tunanin abin da ta gabi a idon ta da kanta gaba ɗaya, sauke idon ta ta yi a ƙasa kafin hankali ta riƙo hannunsa ta ce "What was that Ya Zuhair, is Dad beating mom why was she crying da zanje in turesa akan ta sai na ga basuda kaya ajikinsu shisa nake kallonsu tausayin mom nake ji she was shouting." Sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce "Yes he was beating her saboda ta masa laifi to ke ina ruwanki?"


"Amma ba zai mata faɗa kawai ba? Why beating her after all ko ni baya dukana sai mommy, but wait i heard him screamed also dose that mean itama ta rama dukan ne?" Runtse idon Zuhair ya yi ba yau ya saba sanin abubuwan su Momy ba tun baya ganewa har ya gane ba ruwansu, Anty Khadeeja duk tazo gidan sai ta yiwa Momj magana a akaikaice amma basa dainawa, hannunta ya riƙo ya ce


"Look lil sis ba ruwanki da abin da kika gani a parlour yanzu, idan kika ƙara tashin maganar ko da a kanki ne saina zaneki kina jina ko?" Shiru ta yi har lokacin a ranta tana so ta gano wannan menene sukeyi wai?? Amma dai bata ƙara cewa yayan nata komai ba."


***********
Washe gari driver ne ya kaita school don baccinsa ya ke kuma kasamcewar ranar friday ya bashida lecture wuraren ƙarfe goma na safe ya fito daga part ɗin su ya na kallon Mom da mamaki ganin bata fita ba, zama ya yi kusa da ita ya gaisheta ta amsa fuskarta a sake, ya na dubanta ya ce "Bakije aiki ba yau Mom meyasa?" Tana ci gaba da danna laptop ɗin ta ta ce batare da ta kallesa ba


"Yea zamu tafi Holland da Daddynku Monday muna shirin tafiyar ne shiyasa." Shiru ya ɗanyi kafin ya ce


"Mu kaɗai kenan zamu zauna a gidan." Ɗagowa ta yi ta kallesa cikin madubin idon ta kafin ta ce "To kai yarona mr.man? Ka kusa 19 fa and beside ga masu gadi ga masu aiki burjik a gidan you can takecare of your sister." Jinjina kansa ya yi kafin a hankali ya ce


"Da ki bari muje wurin Hajiyar Sama mom zai fi." Tana watsa masa wani mugun kallo ta ce "Amma kasan Meenal ba za ta so zuwa wurin Hajiya ba, hajiya da komai mita fisabilillah ga kewar rashina da daddy ga fitinar Hajiya gaskiya ka ma dai a wannan maganar kwata kwata ba mai yiyuwa bane ba." Shiru ya yi kafin ya miƙe yana cewa "Zanyi breakfast mom zan tafi gidansu Muhsin." Batace masa komai ba sai bayan da ya kammala ya ce zai wuce sannan da hannu ta nuna masa wani jaka ta ce


"Kayan Hajiyar sama ne ka kai mata, sannan ga 50k can Dad ɗinku ya ce ka yi fuiling motarka." Murmushi ya yi ya dauka yana godiya sannan ya fita, har ya kai kofa ta kalleshi ta ce


"ZM ka bi ta school ka ɗauki Meenal after mosque saboda tana lesson sai kuje gidan Hajiyar ku gaisheta a tare ku kai saƙon sannan ku dawo." A hankali ya ce "To." Kafin ya nufi motar sa ƙirar mercedes ya shiga kawia ya bar cikin compound ɗin bayan me gadin ya buɗe masa tangamemem gate ɗin gidan. Kai tsaye gidansu Muhsin ya nufa suka gaisa da mahaifiyarsa sannan ya wuce ɗakin Muhsin suka gaisa kafin ya kama kefe ɗaya akan kujera ya shiga danna wayarsa, Muhsin ya kallesa bayan ya dauke fruitsalad bowl da ke hannunsa ya ce "Friend what's wrong? Na ganka wani iri is everything alright." Shafa matashin gemunsa ya yi sannan ya ce "Ba komai fa, kawai dai ban daɗe da tashi ba duk baccin be wani isheni ba." Jinjina kai Muhsin ya yi kafin ya ce


"Yaa Ameerah ta gayamun baka ɗaukar wayarta me ya sa?" Murmushi ya sakarwa abokin nasa kafin ya ce "Me zan ce mata to? Look Muhsin don Allah ka rufamun asiri da maganar 'yan matan nan." Dariya Muhsin ya yi kafin ya ce "To kai kasan ba kyau ace yarinya na sonka kana mata yanga Fisabilillah fa, idan ka ɗauka kuka gaisa wani abun zai ci ka ne.?" Bai dai ce masa komai ba ya ci gaba


"Gobene birthday ɗin ta, don Allah ka saya mata gift muje kawai mu bata mu dawo." Murmushi kawai ya yi be ce masa komai ba haka sukaita zama hira jefi jefi saboda halin Zuhair na shariya da kowa ya sanshi da shi, bashi yabar gidan ba sai time da zasu masallaci suka fito a tare bayan masallaci kai tsaye school ya tafi ɗaukar Meenal taba hango motarsa da gudu ta taho ta buɗe gaban sai kuma ta yi murmushi ta na kallon sa ta ce "Good afternoon yaa Muhsin." Yana washe haƙora ya ce "Our Chubby Meenal kina lafiya." Da fara'a ta ce "Fine." Ta buɗe bayan motar ta shiga tana kallon Zuhair ta ce "Yaa ZM good afternoon." Bai kalleta ba ya ce "Mimi how are you." Batace komai ba sai murmushi sai can ta ce "Yaa ZM can you please buy me some chocolate na gida baifi saura 15pcs ba and my friend a islamiyya ask me to bring some to her gobe." Batare da ya kalleta ba ya ce "Idan mun fito gidan Hajiyar sama zamubi ta AC Mall mu saya." Ɓata fuska ta yi


"Me zamuje mu mata, yanzu zaga fara mana shouting akai ni bana so." Muhsin ne ya juyo ya kalleta yana dariya kafin ya ce "You and your granny kullum rigima." Bata dai ce komai har suka isa kamar bazata shigaba ta daure ta shiga a bakin ƙofar parlour suka sameta taci wani ubansun atamfa cote d' voir anji dauri ga sabon ƙunshi a hannu da ƙafa idon nan ya sha kwalli sai sheƙi fatar ta keyi an lantsama mata mai, duk gayar da ita sukayi ta amsa kamar ko yaushe fuskar nan a murtuƙe batada sakin fuska kwata kwata, duka shiga parlour ta bi Meenal da kallo har ta zauna tabe baki ta yi tana kallon Zuhair kafin ta ce "Wai Zuhairu ba nace a canjawa waccen lukutar masifar makaranta ba ashe ban kira ubanta na shaida masa ya mayar da ita makarantar musulunci ba to aci gaba." Shidai Zuhair baice komai ba sai ita ce ta turo baki


"To wai granny ke ina ruwanki da school da nike zuwa ne." Salati ta saka kafin ta zaro charger a fusace ta yi kanta nan da nan ta fara zuga mata a jiki


"Ke don ubanki ni kike mayarwa da magana? Banda lalacewa yaushe aka haifi ubanki ma bare ke da zaki kalli tsabar ido na kice ina ruwana,kafin in nakasaki tashi ki barmun gidana." Meenal dake runtuma ihu kamar an zare mata rai ta miƙe aguje ta fita a parlour ta je jikin motar tana kuka, Zuhair dai be ce komai ba daga bisani ya bata saƙon suka mata sallama sai huci ta ke taba masifa suka fito gidan a waje Zuhair na fitowa Meenal ta rugo ta rungumeshi tanata ƙarawa muryarta sauti a hankali ya ce


"Ya isa bar kukan haka muje gida kawai rabu da ita." Da ƙyar ya rarrasheta ta shiga motar tanata shesheka ya tayar sai da suka yi dropping Muhsin gida sannan suka wuce gida har lokacin Meenal kuka take suna isa gida kuwa ta faɗa jikin Momy dake zaune parlour tana duba wasu files da ke akan cinyarta


"Momy kinga grannj tamun duka ko." Da mamaki Momy ta kalleta kafin ta mayar da dubanta xuwaga Zuhair ta ce "How true?" Kanshi ya shafa kafin ya ce


"Ta san halin granny sai ta yi ta mayar mata da baƙar magana rashin kunya ne da Meenal wani zubin ita kuma ba hakuri kawia ta zaneta." Gyara zaman madubi momy ta yi


"Amma wane irin rashin kunya akan me?" Zaunawa ya yi "Tun ranar da muka je gidanta da uniform tace in sanar da ku a canjawa Meenal school batason mai irin wannan uniform ɗin, to shine fa yau da ta maimaita Meenal ta ce ina ruwanta shine ta zaneta da charger." Tsaki Mom taja kafin ta ce


"Fitinanniyar tsohuwa kawai, rabu da ita Meenal jekiyi wanka kizo kici abinci kinji." Miƙewa ta yi tana goge hawayen idon ta ta wuce ɓangaren su.


Yau ne tafiyar su Daddy wanda hakan ba ƙaramin ɗagawa Meenal hankali ya yi ba saboda tsabar shakuwar da ke tsakaninta da iyayenta, daddy's pet kowane lokaci ta a kusa da su, a airport sai kuka ta ke kamar wacce aka aikowa da manzon ranar gamuwarta da Allah duk ta gama rikicewa haiƙan, da ƙyar dai aka rabu yayan nata ya rungumeta a bayan motar sai sheshekar kuka take har bacci ya ɗauketa, ya kafeta da manyan idanuwansa yana tunanin shin hakan daidai ne barinsu su kaɗai su Daddy suyi tafiyar tsawon sati huɗu ko da yake wannan ba shi bane karon farko. Har suka isa gida Meenal bacci ta ke shikuwa dukda kananun shekarunsa yana cikin damuwar halayyar mahaifansa, ya daɗe zaune a motar tare da ita gudun karya tashe ta ta fara mai rigima.


***************
Washe gari da kanshi ya kaita school har lokacin kuwa fuskarnan nata ba wata walwala ko magana bata masa, shi dai abin da ya isheshi a rai ya isheshi don haka ko bi ta kanta ma beyi ba yana ajiye ta zata sauka ya ce


"Kee." Ɗagowa ta yi suka haɗa ido bata tanka shi ba ya ce mata "Idan kun tashi a makarantar driver zaizo ina 4 kuke tashi." Kai kawai ta gyaɗa masa sannan ta sauke, shi kuwa kai tsaye gidan grandmom ɗinsa ya tafi wacce ta haifi mamansu ya tarar tana zaune akan lafiyayyen carpet mai laushi ya zauna kusa da ita ya gaishe ta ta amsa fuskarta a sake ya ce


"Papa fa?" Da hannu ta nuna mai sama ta ce "Yana sama." Jinjina kansa ya yi kafin ya ce komai ta ce


"What's wrong Zuhair? you look disturbed." Ɗan rausayar da kanshi ya yi kafin a hankali ya ce


"Mama kinga su Momy sun ƙara yin tafiya kusan one month sun barni da rigima ko?." Shiru ta yi tana kallonsa kafin a hankali ta ce "Ba akwai masu aiki kusan uku a gidan ba? Kuma ita me sunan manya ai ta girma ko? Ta zama budurwa zata iya duba kanta danma gaba ɗaya Ruƙayya ta sangartar da ita ba abin da yarinya ta iya amma sa'anninta ai duk sun kama jikinsu don Raudah har girki an fara koya mata." Ɗan shiru ya yi kafin a hankali ya ce


"Mama don Allah idan Momy ta dawo ki tayani mata magana ina so zan koma BQ a waje gaba ɗaya sannan ki musu magana su daina kwanciya a ƙaramin parlour ita da Dad tunda akwai parlour a ɓangarensu duka suke kwanciyar acan idan kwanciyar parlour suke so." Kallon sa ta ke da mamaki tana son harhaɗa zancensa ko zai samu ma'ana a kanta da ƙyar ta ce


"Su Ruƙayyar ne suke kwanciya a parlour me ya ci bedrooms dake gidan rututu?" Cikin fargabar yanda zata ɗauki abin ya ce


"Ba kowane lokaci ba ne amma wata rana a parlour suke kwano to kuma gaba ɗaya ni takurani suke saboda kinsan anan nike kallon ƙwallo." Ssuke numfashi ta yi saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login