Showing 9001 words to 12000 words out of 21010 words
Chapter 4 - MAI SAKO Garin Neman Gira Book Complete Document by Billy Galadanci .txt
kici abinci." Da sauri ta fara tafiya ya ce "Kee" waigowa ta yi kamar zata fashe sa kuka take ji ta ce "Na'am." A tsawace ya ce "Ba za ki rufe gashinki ba haka zaki fita, da sauri ta dawo ta ɗauki net cap ɗinta ta saka sannan ta wuce a dining ya zauna sai da ta gama cin abinci sannan ya ce "Me ya sa kika koma ɗakin da kike yanzu." Cikin saburcewa ta ce
"Yaa Bash kawai dai wallahi ba komai bane dalili." Shiru ya yi yana kallonta kafin a hankali ya ce
"Meenal kinsan cewa yanzu you are no more a kid ko?" Da sauri ta gyaɗa masa kai ya ci gaba
"Then why are you behaving like one?." Ya ƙarashe maganar yana kafe ta da ido rashin fahimtar inda ya dosa ya sanya ta langwaɓar masa da kai shi kuwa yaci gaba
"Ke musulma ce Amina meyasa kike ɗabi'unki kamar ba musulma ba kuma hausa Fulani? Ɗazu ba mayafi kikazo gidannan shekarunki sha huɗu fa gaki da girman jiki kuma ko ba'a faɗa ba na tabbatar kin girma ina nufin kin balaga, Please little sister ki gyara kinji gobe zamu tafi zan saya miki wasu abubuwan amma bazamu shiryaba idan bakya son suturta jikinki da kyau." A hankali ta ce
"In shaa Allah Yaa Bashir ba zan ƙara fita ba mayafi ba." Hannunta ya riƙo kafin a hankali ya ce"Yauwa ko ke fa." Yana kallonta nan da nan taji wani irin kasala ya saukar mata, wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki mara misaltuwa da sauri ta ɗauke idon ta a cikin nasa ta yi shiru tana sauraren yanda yake murza tafin hannunta tana jin wani tsoro haɗe da wani abu da bazata iya cewa meye shi ba da sauri ta janye hannunta ya bita da kallo sai kuma shima ya ga rashin dacewat hakan da ya yi, miƙewa ya yi sannan ya ce "Je ki kwanta pray before you sleep." A hankali ta a ce "To." Ta juya ya bita da kallo ganin sauyawar yanayinta har ta shige ɗakin, sauke ajiyar zuciya ya yi shima ya juya, a ɓangaren Meenal kuwa da ƙyar wuraren 1 bacci ya ɗauketa.
***************
Washe gari Zuhair ya wuce school, Bashir da su Intee da Sawwa kuwa suka ce zasu tafi gidan yayan mahaifiyarsu, Meenal ta ce kanta na ciwo ba inda zata je, da haka suka bar gidan dukkansu bayan kusan awa da fitarsu Hajiyar Sama ta shigo ɗakin da Meenal ta ke da sallama Meenal ta yi hanzarin rufe laptop da take kallo da shi a gabanta Hajiya ta ce
"Baka more ƙasarin kalwa zan je gidan Hajiya Beebah matar ɗanta ta haihu zamuje barka sai yamma zamu dawo, abincin dai an kammala anyi tuwo safe zuwa dare don bazamu iya ba ke kuma da kika tsiri lalaci da son jikin tsiya kanki ki ka yiwa ki ta zaman." Daga haka ta juya tabar ɗakin a buɗe Meenal dai komai bata ce mata ba ta mayar da hankalinta akan kallon da ta ke bilhaq. Shigowarsa gidan sai rafka sallama ya ke ba amsa hakan ya sanya ya nufi kitchen acan ya tarar da Me taya Granny aiki take gaya masa cewar ai granny ta fita juyawa ya yi zuwa ɗakin Meenal saboda dama sabida ya mata alƙawarin fita ya dawo gida, mutuwar tsaye ya yi yana kallon ta ita da abin da take kallo, ta bawa ƙofar baya amma daga inda ya ke tsaye yana iya ganin duk abin da je cikin screen na laptop ɗin tiryan tiryan, ta saƙaka airpeace wannan ya sanya bataji shigowarsa ba ga alama batasan ƙofar ɗakin a buɗe ya ke ba, shi kuwa Bashir gaba ɗaya tsoron Allah ne ya kamasa don kuwa koshi da je namiji baya kallon BF bare wannan mitsitsiyar abar takawa ya yi har kusa da ita inuwarsa ta ce ta ankarar da ita da sauri ta rufe laptop ɗin kafin ta juyo tana ganin Yaa Bashir ta fara komawa da baya har ta mannu da kan gadon bai motsa ba tsabar shock, lokaci guda ta fara kuka tana haɗe hannunta wuri guda amma ta kasa magana ya fi mintuna biyar yana klallonta amma ya kasa magana tsabar mamaki, ganin ya kasa magana kawai ya juya kansa har wani sara mai ya ke wannan wace irin masifa ce Meenal ta ke ƙoƙarin jefa kanta a ciki? Meke damunta me kallon wannan abun zai amfaneta shi? Tukunna ma shin a ina tasan da wannan ya sani dai Granny ƙa'idarta ne bata barin a basu waya sai sunyi candy kuma Allah ya isa taja akan hakan to a ina ta san wannan abin, tsabar shock da damuwa nan take kansa ya fara ciwo.
Meenal kuwa tunda ya fita take kuka har aka yi magrib dawowar su Intee suka shigo aka soma hira amma ba wanda ya nemeta sai bayan isha da Zuhair ya shigo, bayan yaci abinci kai tsaye ɗakin da take ya jufa ya shiga da sallama tanajin muryarsa ta mike daga kwancen da ta ke tana kallon sa, kafin ma ya fara magana ta rungumeshi ta fara rera masa kuka, da makaki ya ce
"Me ya faru kuma Mimi wani abin aka miki ne." Jikinta har na rawa ta ce "Yaa Zuhair na yiwa Yaa Bash laifi don Allah ka tayani bashi haƙuri." Da mamaki ya janyeta a jikinsa ya ce "Me kuma ya haɗaki da Yayanki bayan ke ba tsokanar faɗa ne da ke ba." A rikice ta ce
"Ni to ka maidani gida kaji wallahi tsoro na keji." Kafin ya yi magana Bash ya shigo ɗakin tana ganinsa ta yi saurin zubewa akan gwiwowinta tana haɗe hannayenta alamar haƙuri amma ta kasa magana, girgiza kansa ya yi sannan yana kallon Zuhair ya ce
"Wai yanzu ZM ace kana duniyar har Meenal ta yi lalacewar da zata rika kallon BF a laptop? A gidan uban wa ta san wani BF?" Da tsananin Mamaki Zuhair ya mayar da dubansa akan Bash bakinsa hangame kafin ya ce "How?" Da hannu Bashir ya nuna masa Meenal ya ce "Ask her." Zuhair na kallonta ya ce "Meenal start talking now." Ya ƙarashe maganar da tsawa kaɗan, tana kallon Yas Bashir ta ce
"Don Allah ya bashir kace to Yaa Zuhair ya tafi waje kaga har ya fusata zan maka bayani i promise." Zama yayi sai a sannsn taga doguwar wayar cable a hannunsa nan da nan ta ƙara shiga razani,.yana kafe ta da ido ya sanya ƙafa ya tura ƙofar ɗakin kafin ya ce
"Gayamun inda kika samo, kuma uban waye ya koya miki kallon wannan mugun abu ?" Cikin rawar murya ta ce
"Wallahi Yaa Bashir ba kowa, kaji na rantse." Wani kallo yake mata a fusace kafin ya ce
"Zaki fara gayamun gaskiya ne ko sai na sassaɓa miki." Shiru ta yi tana kallonsa daga ta bayan kanta taji wani knock da ya kusa sumar da ira a tsorace ta juya dafe da kai tana kallon Zuhair da shima ita ya ke kallo kafin ta gama jin wannan Bashir ya zuga mata wayar hannunsa a gigice yanzu kam ta miƙe zata shige toilet ya riƙota ya shiga zuga mata tana tsala ihu sai da ya mata yakai goma sannan ya sassauta zuwa lokacin Xuhair ya rufe ɗakin da key sai da ya zauna ya ce
"Kee!" Da sauri ta miƙe akan gwiwowinta har lokacin tana sosa jikinta da har wasn wuraren sun tattasshi sunyi ja saboda farar fata, Authoritatively ya ce "Explain to me now how? Why? And who thought you that?" A hankali tace
"A parlour Daddy na gani shine nike ɗakko CD's ɗin ina kalla idan na gama sai in mayar in canjo wani saboda sunada yawa, kuma wallahi da biyu kawai nazo nan yau." Shiru ya yi yana kallonta na wani lokaci kafin ya ce
"Me ya sa kikewa Daddy bincike?" Tana saukar da hawaye ta ce
"Ba bincike nake masa ba, kwanaki ne da zan sha ruwa da dare shine kawai sai na ji TV na part ɗin su yana a kunne still numa nasan sunyi bacci shine da naje zan gashe naga wannan a ciki i was wondering me suke saina kalla har 2 na dare from that time kuma idan ba kowa nike zuwa ina kallo acan kuma sai naga CD plate da yawa irinsu shine nake dubawa kullum, da zamu nan sai na ɗakko biyu nake sakawa a laptop Yaa Bash wallahi gaskiya nake gaya maka Please karka dukeni kuma Allah bazan ƙara ba daga yau." Wata iriyar zufa ce ta shiga tsatsafowa Zuhair da wani ɓacin rai nan take idonshi ya kaɗa ya yi ja jajir, sai wani sara mai kanshi ya ke batare da ya ce komai ba ya buɗe ɗakin ya fito gaba ɗaya ya ƙulle musu kai tsaye gidan gaba daya ya bari a kafa ya hau zaga layin, bayan dogon shiru Bash ya ɗaga bulalan zai zabga mata tayi saurin rungumeshi
"Yaa bashir Please don't beat me again i promise never to wach it again kaji." Zare ta ajikinsa ya yi ya wurgar da bulalan ranshi yana suya cikin dakiya ya ce
"Look Meenal aure zan gayawa Daddy ya miki saboda kin lalace abin da kike kallo ko ni da nike yayanki bazan iya kalla ba, wannan abin banzar menene amfanin kallonsa ko kinsan duk mai kallon irin wannan abubuwan bayan zunubi da kike kwasa bazaki tsufa kina gani da idon ki ba? Makancewa zakiyi kuna su Daddy sa'anninki ne? Idan ma kina tunanin kalla suke ke meye na ki? Dahar zaki mayar da abin sana'a ki baje kina kalla." Jikinta na rawa ta ce
"Don Allah ka yi haƙuri ni da zan zama likita za ka ce amun aure bayan kasan na daina don Allah ka yi haƙuri." Shiru ya yi yana kallonta kafin ya ce
"Amina." Kallonsa ta ke a tsorace ya ce "Amina Kinsan Allah." Ita dai sai kallonsa ta ke, a nutse ya ce
"Daga yau zan saka miki ido wallahi ko mai nike duk ƙarshen wata zanzo Kaduna ko duk sati kika bari na ƙara kamaki da abu makamancin haka wallahi tallahi sai kin yabawa aya zaƙinta sakaryar banza kawai lastly nextweek idan zamu tafi ke zaki gayawa du Mom kina so ki bimu idan baki aikata hakan ba zan gayawa kowa abin da naga kina yi kuma in ƙara zaneki." Cikin sauri tace "A zan biku amma ka yi haƙuri." Yana mata wani kallo ya ce
"Tashi ki bani wuri " da sauri ta nufi waje ya bita da kallo.
***************
Sai wuraren 11:30 Zuhair ya dawo, ga mamakinsa har lokacin Bashir bai kwanta ba, gefen sa ya zauna trying his very best kar ya gano yana cikin damuwa ya ce
"Me kake baka kwanta ba?" Cikin damuwa ya ce
"Bashir ya zanyi da su Dad da rayuwar yahudawan da suka ɗaukarwa kansu? Bashir yaya zan yi da nauyin zuciyata ace masu kwaɓarka su suke aikata abin da zaka gani? Bashir dududu fa shekaruna ba su kai 20 ba tayaya za'a ce in fi su Dad hangen nesa, kafin yarinyar nan ta gama girma haka ta taɓa leƙensu a parlour suna aikata irin abin da suke kalla, ta sha mun tamabaya surutan me suke? Nayi iyakar yina wurin ganin na nesantata da su amma abun ya faskara iyayenta ne, Bashir idan yarinyar nan ta lalace da wane ido zamu kalli duniyar ne? Basa tunanin waɗancen yahudawan addininmu da al'adunmu ba iri ɗaya bane ba?." Sauke numfashi Bashir ya yi kafin a hankali ya ce
"Duk lalacewar iyaye haka zamuyi haƙuri da su, Dad da Mom rayuwarsu haka suka taso suna yin komai free tun kan a haifemu, kowa ya shaida irin so da suke nunawa juna agaban koma waye, shekarun da suka yi a turai sai ya ƙara lalata abin saboda suna ɗaukar wannan ba komai ba ne da sukeyi, to kai da ka san illar hakan sai ka saka wa ƙanwarka ido sosai mana, tafi zama a tare da kai akan su duk da zuwanka makaranta sai ka fito a sarari kana nuna mata illar abubuwa da yawa da su suka kasa nunar mata, Zuhair wannan ba lolacin zafin kai bane, lokaci ne da zaka janyo ƙanwarka a jiki kake observing ɗin ta sosai saboda abubuwannan da take kalla sun shiga jikinta ko ba komai yanzu zata iya fara masturbation bayan haka lokacin girmanta ne she can do anything to get what she want, zanje da ita Abuja tunda hutu take yanzu zanyi nawa ƙoƙarin har yau ni da kai bazamu iya rantsewa akan Meenal batasan namiji ba wannan abin da take kallo dai, kai idan ma bata sani ba to zata nemi sanin nan gaba kaɗan, so zan mata sa ido akan hakan." Cikin lumshe idanu da buɗewa Zuhair muryansa har na rawa ya ce
"Please Bashir go with her, she really need that therapy yarinyar nan wallahi ita ce jinin jikina ina son Mimi bana son wani abu ya sameta, bana son ta lalace banason ta tashi da abubuwan da ta ke gani a gidan." Riƙo hannunsa Bashir ya yi kafin ya ce
"Ka kwantar da hankalinka blood in Shaa Allah zata nutsu zan ware mata lokaci sosai ta nutsu bazan bata damar shiga wani mummunan abu ba kake mata addu'a nima zanyi in Shaa Allah zata daina." Godiya ya masa lokaci ɗaya yana ɗauke hawayen idonsa da hannunsa.
A wannan daren kuwa Meenal kasa bacci ta yi saboda tana son ta kalla wannan abun gashi an ɗauke mata laptop, ilahirin jikinta har wani tsamin wahala ya ke mata saboda juyi, shauƙin abun take ba dama ta rufe ido sai abun ya dawo mata akai, ta kasa gano halin da take ciki daga bisani pillow ta janyo ta rungume ta ƙanƙame pillow sosai tana mayar da numfashi kafin a hankali bacci ya kwashe ta cikin mafarkai iri iri.
Free pages
Mom Nu'aiym
07084161619
*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)*
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
06.
Meenal sukuku ta wuni washe gari har zuwa bayan la'asar cousin's ɗin nata mata basu wani damu da ita ba after all sun ɗan girmeta sannan kuma ta cika shariya batada sakin jiki, ƙarfe huɗu da rabi Bashir ya shiga ɗakin da ta ke a kwance a sameta ta lumshe ido kamar me bacci duk da ba wai baccin ta ke ba
"Kee" ya kira ta a ɗan tsorace ta tashi zaune jin muryarsa lokaci guda gana gyara rigar jikinta "kinyi salla?" Ta ce "Nayi." Ya ce "To tashi shirya mu fita." A hankali ta ce "To yaa Bashir." Juyawa ya yi ya na cewa "Don't waste my time Meenal." Da sauri ta sakko daga kan gadon ta ɗauki wani desighner ɗan kwalin turawa ta ɗaura a saman sumar kan data baza saman kafaɗunta sannan ta saka wani ubansun wage hill ta ɗakko wata desighner side round bag ta saƙalo daga wuyanta ƙarƙashin gashinta zuwa shoulder ya crossing in between her big boobs ya tsaya side sannan ta shafa lip balm da zallan eye liner a idon ta ta fesa turaruka na tashin hankali ta fito tana taku ɗaiɗai duk da kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar cewar ba shakka batada walwala, ta yi kyau ainun na kallo ka lara kallo amma shigar sam ba ta yaran musulmi ba, Ba kowa a parlour ya sanya ta fita ta wuce parking space inda anan ta ke tsammanin ganin Bashir, daga sama har ƙasa bash yake kallonta har ta ƙaraso kusa dashi, yana kallonta ya ce "Meenal are you insane! Wait where on earth do you think you are going dress like this?" Da mamaki ta kallesa sannan ta kalli simple dresssing da ta san ta yi, lafin tece
"Yaa Bash what's wrong with my dressing or you want me to wear to something classy sorry kace nai sauri shiyasa na fito a haka." A ƙufule ya ce
"So you are just big for nothing ko? In your own tiny brain and empty skull you think wannan ne wayewa ko? My friend go and change to something worth your body as muslima." Jikinta a mace ta juya cikin gidan ba jimawa ta fito sanye da ɗamammen wando da wata round neck crop top sai ɗankwalin still da ke kanta ta canja takalminta zuwa wasu fine and classy unique lowpass farare ƙal, sake baki ya yi hangota tana tahowa har zuwa sanda ta ƙaraso kusa da shi, a cikin rashin walwalar da take don har ga Allah har lokacin abubuwa biyu tsaya a rai na farko dai ganin da Bashir ya mata ya gayawa Zuhair ya sanya ganajin kunya da nauyin dukkansu na biyu kuma rashin kallon abubuwa da ta saba kalla ya saka takeji a jikinta tamkar mara lafiya, kallonsa ta ke ta ce "Yaa Bash is this ok?" Yana wurga mata wani kallo ya ce "ke bakida atamfa ne wai ko wani kayan bahaushe sai wannan tsigaggun kayan?" A hankali ta ce
"Bana zama comfortable duk sanda na saka shiyasa Momy ta daina ɗinkamun banida anan yanzu sai a gida, yana saurin takurani yaƙi shiga jikina." Tsaki yaja kafin ya ce
."get in." Ya buɗe driver's sit ya zauna ya ja suka bar gidan.
*************
Ta jima tsaye a wurin tana tunanin ta inda zata fara ga ƙarfe tara ta wuce kuma wayar bakanikenta yaƙi shiga, tsaki taja a karo na barkatai, mai adaidatan ne ya tsaya kusa da ita ya ɗan leƙo kai waje sannan ya ce "Hajiya zakije wani wurin ne?" Dubanta ta mayar a kansa sannan a raunane ta ce "Wallahi bawan Allah kaga dafa office nike kuma kawia motar ta mutu nayi iyakar dubana ban gane menene matsalar ba kuma makaniken da ke dubamun motar wayarsa a ƙulle ya ke."
"Subhanallahi Hajiya bara inzo in duba miki duk da ba kayan aiki a tare da ni amma ai ni ɗinma makaniken ne wannan keken ba hawa nike ba sosai ba sai dare idan na baro wurin aikin kanikancin nawa." Cikin jin daɗi ta ce "Kai wallahi daka taimakamun saboda gaskiya na makara a komawa gida." Gyaran parking ya yi sannan ya sakko