Showing 12001 words to 15000 words out of 21010 words
Chapter 5 - MAI SAKO Garin Neman Gira Book Complete Document by Billy Galadanci .txt
ya shiga duba motar ba jimawa ya fito yana kallonta kafin ya ce "Hajiya gaskiya wank electrical problem ne dole sai an nemo ruwaya ni panalbita ne a garejin ban ƙware a wannan panning ba abin da zai faru ki bawa masu shagunan tsaron motarki idan ya so muje inga gidanki in ajiye idan kin amince fa kenan sai in kira wani ruwaya yanzu yazo ya duba inyaso zan maida miki motar har gida." Shiru taɗan tunani tare da ƙarewa motar kallo kafin ta yi magana ya ce
"Hajjaju nasan yanzu yadda zai yi wahala kam musamman da dalleliyar mota irin wannan idan ba matsala zaki iya tsayawa a motar sai in kira miki yaron ya yazo ya duba." Agogon hannunta ta ƙara kalla kafin ta ce
"Ko zaka taimaka ka kirasa please sai muji inda ya ke ko zai samu zuwa?" Batare da ya tanka mata ba ya juya ya shiga kiran wayar yaron bayan sun gaisa yake gaya masa buƙatarsu yaron ya ce
"Daga Anguwar Rimi nake wurin wani oga na na masa gyara bari ganinan zanyi branching banida nisa da ku ma." A hankali ya ce "Alright sai ka zo na gode." Ya juya yana kallon ta kafin ya ce "Hajiya yanzu zai ƙaraso idan yazo ni zan kama hanya, Allah ya sa a dace."
"Na gode Malam Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan iyayenka." Sunata tsaye wurin bayan 17:mns ya ƙara suka gaisa sannan ya mata sallama bayan ya nuna masa motar ta zaro 2k ta miƙa masa ya kalleta sosai ya ce
"Noo Hajiya ki barshi ni taimakon ki kawai na yi domin Allah." Yana gama faɗar hakan ya juya ya shiga Napep ɗin sa ya bar wurin. Bayan kusan 35mns ya fito daga ƙasan wurin zaman driver da ya ke ya ce
"Hajiya kiyi haƙuri dare ya yi kuma gyaran nan ba zai taɓa yiyuwa yanzu ba wata waya ce ta ƙone dole sai an sauya wata kuma dare ya yi ko ina ma sun rufe yanzu." Shiru tana kallonsa kafin ta ce
"To ai kuma malam barin mota a wurinan ba security ba wata dabara da zaka mun don Allah in samu in ƙarasa gida." Gyaran tsayuwarsa ya yi ya ce
"Hajiya barin motar nan anan ya zama dole fa, zamu cire batry kuma ba inda zataje adai yanda ta ke, bari in kira miki Saif yazo ya kaiki gida da Batrry ɗin da zamu cire a motar na miki alƙawarin gobe ƙarfe goma zan kiraki in kai miki motarki a gida." Ba yanda ta iya haka ta zauna acikin motar ya kira abokinsa da ya kirasan har ya shiga gida haka ya taso yazo ya ɗauketa suka nufi gidanta dake cikin GRA. Babban gida ne sosai da ke ɗauke da flat kusan huɗu manya manya da wani challet ɗaya a baya gida ne mai kyaun gaske wanda ya amsa sunansa gida horn ta saka ya yi me gadi ya wangale masa gate ya wuce ciki bayan ta sakko a nutse shima ya sakko ya zaro jakarta da wata leda ya mika mata a cikin ladabi, ta karɓa tana kallonsa da murmushi kafin ta ce
"Ya sunan ka ma?" Yana shafa sumar kansa ya ce "Saif." Tana murmushi ta ce "Ka shigo ciki mana ka sha ko ruwane Saif." Yana shafa kansa still ya ce "Ba komai Anty zan koma gida kawai dare ya yi." Jakarta ta buɗe ta zaro 10k ta miƙa masa ya saka hannu biyu ya karɓa yana dubanta da mamaki ya ce "Anty kuɗin nan ai ya yi yawa " tana faɗaɗa murmushinta ta ce"Ba komai Saif ka riƙe kuma don Allah gobe ka dawo by 8:am ka kaini office akwai theater da zan shiga by 9:am." Ya russuna ya ce "In Shaa Allah karfe bakwai da rabi anan zaimun." Har ta yi gaba sai kuma ta dawo ta ce "Saif a gidannan akwai motocin dana daɗe ban hau ba Please ko zaka tayani kaisu garrage goben a musu service." Ya ƙara russunawa ya ce
"Ba komai Anty idan na ajiyeki a office sai ki faɗi yanda za'ayi." Godiya ta masa ta juya shi kuwa ya shiga Kekensa ya tayar ya wuce gida."
Meenal ta kafe Bashir da ido dake magana bata ko ƙiftawa cikin tsawa ya ce "Is that clear?" Sauke idon ta ta yi da ya kawo ruwa kafin ta ce "Yes yaa Bashir." Ya ce "Oya jeki saka kizo in ganki." Ba musu ta miƙe ta shiga ɗakin da ta ke ta sako jilbab ɗaya ta fito ta tsaya a gabanshi ya ƙare mata kallo sama da ƙasa sannan ya yi murmushi ya ce "Daga yau i mean from this moment onwards ko so ɗaya na tsinceki a waje da ƙananun kaya ba hijab a jikinki sai na miki duka wallahi, ban hana ki saka mayafai ba Meenal amma idan kin saka atamfa haka ko wani kayan kirki kina jina?" A sanayaye ta ce "A zan kiyaye." Hajiyar Sama dai sai kallonsu ta ke tana jinjiga ƙafafuwanta da carbi a hannunta baki a taɓe bata dai ce komai, Baba indo dake gefenta ta ce
"Kai Bashiru wannan fitsararriyar 'yar ta maliku ba wai jinka zata yi ba, tunda shi da Ruƙayya sun rigada sun gama bata yarinyar yanda kasan yar wanda basa dubin gabas yo ko ƙabilun ba kowa yake irin shigar da ta ke ba, ranar da na zo gidannan ta ce Baba indo ina wuni na ce lafiya Ribeka yo kaga laifina na zata jikar arna ce ai." Wani kallo Hajiyar Sama ga wurga mata kafin ta ce "Haba Indo to su waye kakaninta arna?" Kyaɓe baki Baba indo ta yi
"To kya tambayeni? Ki tambayi wannan bakamoren jikar taki." Kwafa Hajiyar Sama ta yi amma batace komai ba Bashir ya ce
"Ku daiyi haƙuri ai da ita zanje Abuja tunda hutu ta ke na kula ko ruwan zafi ma bata iya dafawa ba." Murmushin takaici Hajiyar Sama ta yi sannan ta ce
"Ruƙayya dai gwara da Allah ya taƙaita mata haihuwa don bansan kalar ɓaragurbin da zata dasa a zuri'a ta ba, gwara Zuhair yaron gaba ɗaya Allah ya banbanta halayyarsa da ta uwarsa don ni Maliki ba haka yake ba, haɗuwarsa da Ruƙayya ne ya koyo fitsara suka haife mun fitsararriyar Amina anan." Meenal dai bata ce komai ba sai kallonsu ta ke abin da ya isheta ya isheta arai, Bashir ya ce
"Wuce kawai." Juyawa ta yi har ƙwallan idon ta ya soma gangarowa ƙasa ta taka har zuwa ɗakin tana shiga ta fashe da kuka ta yi me isarta sannan ta bawa kanta haƙuri.
Tunda suka dawo tace sai ta bisu Abuja Mom ke sufafa faɗa
"Amma kinsan bana son zuwa gidan kowa ko ZM kinga yana yawon abuja gidan uncles ɗinku ne? Banason rashin hankali fa Meenal." Meenal ta turo baki "Mom to me nake miki a gidan? Just buy me a small smartphone in je yanda zamu riƙa waya and na miki alkawari just 2weeks zan dawo." Kallon Dad ta yi
"Honey you are not saying anything." Ya kalli matarsa yana murmushi kafin ya ce "let her go please, ai ba komai bane once in a while and akan issue na wayar i will give her the Samsung galaxy da na saya bana using sai ta riƙe a hannunta akwai Airtel sim da na rike sanda naje wannan ƙauyen daba MTN ntwrk so that you both can keep in touch." Ɓata fuska Mom ta yi ta kalleshi kamar zata fashe da kuka, kusa da ita sosai ya zauna yana rungumota "Haba 'yan matan Malik muna haka da ke dama." A wani shagwaɓe ta ce "You know i can't say no to you right? Shikenan ta je but she should take care of her self for me please." Ya kalli Meenal da ke kallonsu tanajin wani iri a jikinta ya ce
"Alright Then dear Allah ya tsare hanya." Murmushi kawai ta yi "Thanks Day Thanks Mom." Ta ƙarashe maganar tana miƙewa duk ƙafafunta basa iya ɗaukarta take ji tsabar wani fizgarta da jikinta keyi. After Magrib ta roƙi Zuhair ya kaita gidansu ƙawarta Amrah bayan sunje suka zauna a ɗakin Amrah ta ne kallonta ta ce
"Amrah Dad gave me a phone yace inje Abujan da shi, i came to collect your number." Amrah na jin daɗi ta karɓi wayar ta saka mata number sannan ta an kallonta ta ce
"Ya naga kamar kina cikin damuwa Friend whats wrong with you please?" A sanyaye ta ce
"You know what ?" Amrah was just looking at her ganin har idon ta ya kawo ruwa ta ce
"Amrah My Cousin caught me red handed watching pone in my laptop and the guy is just too arrogant and harsh for my liking imagine ya ƙwace laptop da Nike kallon cartoon abuna after that ya hanani saka ƙananun kaya ke ki bari the guy is so mean yanzu shine ya takura zaije da ni Abuja ." Amrah na kallonta tace to yanzu ya zakiyi? Ni fa bana son takura duk da kema na gaya miki kin matsawa kallon abubuwan nan ba kyau ba Mu'allim yanata wa'azi akan kallon su duk sanda zaice BF su yake nufi fa kawai ni ba ruwana dasu amma Kinsan me?" Meenal dai sai kallonta take ta tsatsareta da manya manyan idonta yarinyar ta rage muryarta ƙasa ƙasa ta ce
"A wayar Mami akwai da yawa wallahi, amma ita browsing take coz ranar dana karɓa wayar xanyi assignment sai na fita a googe ɗin dama nayi minimizing ne to in gaya miki ina dawowa na shiga mininimized app sai naga mace da namiji tsirara kawai na kasa haƙuri ina duba na ga wannan abin da kike bani labari, haka nake kalla nima duk na ara wayar sai na shiga crome na duba and you know what? Wallahi haka na zama addicted ko jiya da wayar Mommyn kano na kalla tana gidan na ara nace zan kalla cartoon naje ni crome na danna abuna kawai mu riƙa addu'a Allah ya yafe mana." Meenal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Amrah don Allah wai kinsan menene sha'awa its like ni fa na fara son aure kuma nasan ko mutuwa zanyi Dad da Mom bazasumun aure ba at the age of 14 ni wallahi sai riƙa jin ina son wannan abubuwan." Gwalo ido Amra tayi tana kallonta kafin tace
"Ba uban da zai mana aure in gaya miki kinsan me kiyita haƙuri idan muka gama secondry sai mu haɗa mai muyi musu bori." Dariya Meenal ta yi sannan ta ce
"Yanzu idan na shiga Google sai in je ina?" Karɓar wayar Amrah ta yi ta shiga ta rubuta abinda zata rubuta ta gana nuna mata tana kallonta ta ce makesure you Always delete your crome and Google history idan aka kamaki da wayar nan sai buzunki nima dai Dad ya ce tunda na gama GSS zai tahomun da iPhone daga Istanbul dake yana can." Meenal ta ce wow "Zaki rabu da rakani kashin kenan a whole minister's daughter with rakani kashi." Amrah na dariya tace "Ai kinsan ƙa'idar gidan kenan zasu baka keypad incase of emergency idan ka shiga GS one kana gamawa zuwa gs 3 zasuce ka fara hankali." Nan suka zauna suna kallon abunsu bayan Zuhair ya kira akan ta fito ta suka fara goge history da duk wani trace da zai nuna sun kalla abu sannan suka fito ta rakota waje suka yi sallama.
A hanya Zuhair ya kalli Meenal ya ce "Next week zan samu hutun mid-semester break zanzo Abujan Please Meenal be a good girl a gidan su Bashir kina kallo dai duk wani abin da zakiyi cewa suke laifin Mom ne ba wanda yake shakkar zagin Mom a gabanmu a family try as much as you can karki bar abin magana a Abuja and lastly bana son ko kusa ki sake kallon wannan ƙazantar haramunne zasu kaiki ga halaka kimada ƙananun shekaru just 14yrs ace irin wannan abin ne a kanki haba Meenal." Shiru ta yi ta sauke kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta
"Don Allah kar ki ƙara har yau ina ji miki kunyar Bashir and beside ke me kikeji idan kina kallon abubuwan." Kanta ta ɗaura akan cinyoyinta ta fara kuka a hankali bata kalleshi ba bai ƙara ce mata komai ba sai da suka isa gidan bayan sun shiga ciki zuwa part ɗinsu ya riƙo hannunta "To menene abin kuka kuma don kawai na miki magana." Shiru bata daina kukanba bata kuma kulashi ba jan hannunta ya yi har ɗakinsa sannan ya zauna kan gadon ya zaunar da ita ya bata side hug "Shikenan daina kuna nasan dai kinji abin da na gaya miki ko." Kanta ta daura a saman ƙirjinsa inhaling his aromagic scent tayi shiru kusan 20mns sai da ya ɗagota idon ta duk sunyi wani luuu kamar mejin bacci da haka anan ta kwanta akan gadon shi abin har ya bashi mamaki cox kwata kwata ta daina zuwa ɗakinsa kwana har yana cewa yanzu Meenaluwa ta zama big girl yau sai gashi dai.
*****************
Washe Gari tun 7:30 saif yana Kofar gidan Hajiya Nasare, bayan me gadi ya sanar da zuwanta baifi da 15mns ba ta fito da kayanta na alfarma atake ƙamshin ta ya cika wurin ko ina, ta zauna a napep ɗin batace masa komai ba a hankali ya ce"Barka da safiya Anty." Matar da bazata wuce shekaru 40 ba ta amsa mai da fara'a amma ba kamar jiya ba yau batada walwala, suka ɗan taba tafiya ya ce "Anty wane asibitin zamuje." A hankali ta ce
"Malik specialist governor road." Kaii tsaye can suka nufa bayan sun isa ta ce
"Abokinka yace by 10 zan gama gyara ka kira ki karɓamin motar idan ya gama, bani nunber wayarka." Ba musu ya bata ta kwashe nunber a waya ta kirashi yaga number ta sannan tace "Ka turamun acc details ɗinka ko nawane kuɗin gyaran zan tura maka ka bashi, Please ka ajiye napep zuwa 4 sai kazo ka ɗaukeni anan akwai inda zaka kaini." A hankali ya ce "Hajiya zuwa ƙarfe huɗu ina gareji zan iya kawia shida fa." Kallonsa ta juyo ta yi kafin a hankali ta ce
"Please make time for me kazo akwai inda zaka kaini ne and it's only yon i trust." A hankali ya ce
"Ok Ma." Ya juya yabar wurin.
Mom Nu'aiym.
Free pages.
07084161619
*(GARIN NEMAN GIRA..)*
*BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
*My sister you can't have that big tommy and still look fresh,young and beautiful, munada haɗaɗɗen Flat Tommy powder da zai taimaka wurin narka kitsen ciki which is 100% natural ingredients.its just a tea da zaki tafasa kisha ba ya saka gudawa in shaa Allah. Munada abubuwan gyaran buje iri iri kayan matan mu a top notch munada turarukan wuta da kuma khumrahs na asali masu siyo mutunci. Always send us a DM ki amshi rabonki.*
1.Deep beach
2.Deep Ocean
3. Deep sea
4. Date syrup
5. Coconut syrup
6. Tightening herbs pills
7. Aci a laƙe
8. Breast enlargement powder
9. Breast firmin oil
10. Ci da kaza
11. Manta uwa
12. Khumrar Mallaka
13. Flat Tommy powder
14. Infection flusher
And lot's more. Mun fara end of year sells ɗinmu so maza ku hanzarto a Sweetner zone by season 7 ku kwashi rabonku. 07084161619
07.
Saif da ƙyar ogansa ya bari ya wuce karfe 3:30pm saboda zuwa ɗaukar Aunty kamar yanda yake kiran Anty Nasare, karfe huɗu daura mintuna goma ya isa asibitin, fara tsayawa ya yi yay sallah a masallacin da ke asibitin sannan ya kirata a waya, bata ɗaga ba hakan ya sanya ya zauna a inuwar wata bishiya yana duba whatsapp a wayarsa. A ɓangaren Hajiya Nasaree kuwa zaune take a office ɗin Dr. Ruƙayya ranta a tsananin ɓace ta sake dubanta lokaci guda idon ta ya cika da hawaye ta ce a raunane
"Wallahi tallahi da ba dan ke ba Dr. Rash wallahi da tuni na bar auren nan, makomata kawai nake dubawa amma menene amfanin auren da ke kaina dai in shafe shekara banga miji ba? Yanzu Fisabilillah Dr. Ace duk irin gyaran da na kashe kuɗi na yi ga yawan sha'awa ace zan ɓuge da shan lemon tsami sabida wahala, nufi yake in ƙara shafe wasu satuka uku bayan watanni takwas da ya yi baya nan, wallahi na gaji." Ta ƙarashe maganar muryarta yana rawa ƙiris ya rage ta fashe da kuka, Sauke numfashi Dr. Rash tayi kafin ta ce
"Wallahi ina ganin ƙoƙarin ki Dr. Nas ni kinga Allah baxan taɓa iya shafe wata ɗaya ba tare da Malik ba mutuwa kawai zanyi, ni nasan nafi Malik ƙarfin sha'awa saboda haka kowane lokaci nake zuba mai desire tablet and that herbs da Season 7 take sayarwa a stew ake sakawa ko shayi kawia bankamai nake kuma duk da zamanshi Dr. Banaji yana fahimtar ina saka mai kawai ya tafi akan baya iya resisting desire indai muna tare, amma kiyi haƙuri bari ya dawo kuyi magana ta fahimta ban taɓa ganin auren shekaru goma saduwa so tara ba sai a aurenki." Shiru ne ya ratsa wurin kowa da abin da yake saƙawa, wayar Dr.Nasaree da ya fara ringing ne ya dawo da su duniyar tunani ta ɗaga kiran a wannan karon cikin ladabi Saif ya ce "Barka da yamma Anty." A taƙaice ta ce "Saif ya aka yi ne?" Cikik Husky voice ɗin sa ya ce "I am at the hospital ma."
"Alright I will be with you in just 10mns." Cikin girmamawa ya ce "Ok Ma." Haka ya zauna zaman jiranta kusan 15mns sai gata ta fito bayan motar ta buɗe ta shiga ciki ta zauna duk mai hankali kallo ɗaya zai mata ya fahimci cewar tana cikin damuwa, bayan ya tashi motar suka haura titin sosa ta centre mirror ya kalleta ya ce
"Aunty wane anguwa zamu je?" Shiru ya ji ba amsa ya ƙara ɗaga kai ya kalleta ya ce "anty nace wane anguwa zamuje?" Mayar da duban ta ta yi tana kallonsa kafin a hankali ta ce"Me ka ce Saif?" Ɗauke kansa ya yi daga dubanta ya na driving a hankali ya ce
."Wane area ne zamu je?"
"Muje gida akwai maganar da nikeso mu tattauna da kai."