Showing 1 words to 3000 words out of 17786 words
Chapter 1 - Tawa Ta Same Ni Book 3 Complete pdf by Halima Abdullahi k Mashi .txt
TAWA TASAMENI
__________ NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI________
Tindaga nan bansan inda kaina yake ba sai a Rimi
Clinic lokacin ma bayan magriba ne na farfado,Dakin
dam da mutane, Babana shine kusa dani yana rike da
hannuna,ina farfadowa shina soma gani na shiga 'yan
dube dube ina kokarin tuno me ya faru?Babana ya
dubeni sannu uwata ya jikin?duk yan dakin kowa ya
shiga yi min sannu,hannuna na daga zan share fuskata
sai naga lalle sai na tuna ashe fa ni Amarya ce nan
take na tuna mai ya faru da sauri na tashi zaune nace
Babana kaji abinda Adams yayi min ko?yace ya fasa
aurena, babana ya rungume ni kiyi hakuri kar ki
damu,sai a sannan na dubi mutanen dakin Alhajine da
yaya Kabir da yayanmu sai Mama da Aunty Yagana
nace ashe har su yayanmu sun iso dako Adams yace
min tare zasu zo sai kuka ya kwace min babana da
Alhj sai lallashina suke mama kam cewa tayi saiki yi
tayi tunda yace bai sonki dole ne?cikin kuka nace
mama yace har yanzu fa yana sona saidai ba zai aureni
ba kila ma yana tsokanata ne,na dubi yaynmu nace dan
Allah yayanmu tare kuka zo?harara ya sakar min
sannan yace kiyi wa mutane shiru ynxu da kike magana
gobe ne daurin aurenshi a yola can garinsu kuma
iyayenshi sun. bada hakuri dan da yarinyar suka so ya
aura yaki tashi daya yace yanajin inbai auri yarinyar ba
mutuwa zai yi ina ganin shima ba laifinshi bane da
akwai wani abu,mama tace ba komai Abdulrahim
wulakancin shine kawai dan cin mutunci sai da ya bari
ana saura kwana uku biki sannan zai ce ya fasa ga shi
mun gayyaci mutane ya zamuyi kenan?ai gsky abinda
Adamu yayi mana sai dai muce Allah ya saka
mana,Babana yace ku dai ku yi hakuri ynxu mu samu
kanta in yaso sai mu san abin yi,da sauri nace yawwa
Babana don Allah ku taimaka min ku shawo kan Adams
ina sonshi, Mama ta kawo min duka Alhj ya tare har
suna hada baki shida babana suna cewa Habiba haba
menenebna duka?shi ko yaynmu fita yayi, jim kadan sai
ga su Doctor yace ciwona bai tashi ba na dai firgita shi
yasa amma a guji tashin hankali dan haka ynxu ya
sallameni,mun fito kan titi gurin da suka ajiye motoci
Alhj yace na shiga motar nace ni ba zani can gidan ba
baba yace to muje nan ma nace a'ah,mama haushi ya
kamata tace to ko gidansu Adamun zakije?sai kin dawo
nace ni Anty Yagana zan bi Alhj yace to kuje,ya dubi
yayanmu yace kai su Abdulrahman,a mota ina jikin Anty
Yagana a kwance shi kuma yana tuki Anty tace
Abdulrahim yaya abokinka yayi mana haka?yace anty ni
kaina na rasa gane kan abin jiya fa muna tare da shi
bayan mun tashi daga wani wasa wanda dama ranar
zamu gama yau mu taho gaba daya da abokanmu dan
har na ma Kabir waya akan ya kama mana Hotel zamu
sauki baki a jiyan da daddare sai ga shi wai shi Ghana
yake son zuwa ya je yaga Aisha,nace wacece kuma
Aisha?sai yace yarinyar nan da aka ce ya aura yaki
yanzu kuma ita yake so,da kyar ya kai safe, yau da
sassafe ya dau hanya babanshi ya min waya wai ko da
wata matsala ne tsakaninshi da Iman?nace ba komai
shine babanshi yace to ynxu yace yau ya ke son ya
auri Aisha ba sai gari ya waye ba koda suka ce a'ah su
ba zasu yi karanta ba sai ganinshi sukayi ya fadi
sumamme shine fa ba shiri suka dau hanyar
Yola,Babanshi din yace in sun dawo zasu zo nan su
bada hakuri.Jin wannan lbr sai wani sabon kuka na saki
dan lokacin sai naji wani son Adams din ma
nakeyi,yaynmu ya daka min tsawa yi mana shiru ko na
tsaya na bubbuge ki, wannan bakin ya yi tsit nayi shiru
har mukaje gidan anty yagana.
Washe gari ina kwance anty yagana ta shigo ta dubeni
tashi Iman kiyi wanka ko kya ji dan dadi nace dan Allah
anty ya zanyi wannan lallen ya fita ne?na tsaneshi tace
ba zai fita ba sannan ke da kike Amarya ya za'ayi ki
goge lalle da sauri na tashi Adams din ya dawo yace
zai aureni ne?Anty tace ni dai ban sani ba Babanki da
Alhj sun ce a ci gaba da shirye shirye biki ba fashi sai
dai ina zaton ba da Adams din ba ne nan na koma na
kwanta na dora sabon kuka nace TAWA TA SAMENI ni
iman aure ban san mijina ba?na shiga uku,Aunty yagana
tayi ta bami hakuri gami da lallashi.. Ashe abinda ke
faruwa shine boka yayi aiki sun hada Adams da aljani
ya juyar mishi hankali dan haka da suka samu lbr
zancen aure ya rushe da Adams sai murna da farin ciki
hatta Aunty Mimi tayi murna dan dama tace bata son in
auri Adams dan kar mu zama abokai,a cewarta in auri
abokin mijinta taci baya(hahhhah lallai a gaisheki
mimi)ita tana auran mai kudi nima na auri mai kudi ba
zai yiwu ba..Zaune gaban boka Haj Yaya ce da Haj
Laure suna murna gami da godiya boka ya katse su to
ynxu kunsan wanda za ta aura ko?Haj yaya tayi sauri
tace duk ma wanda zata aura Allah gafarta boka taje ta
tayi ta aura tunda dai ta rabu da abokin dana ai shi
kenan dama bani son ta rabu dana kusa da dan nawa
ne bare shi kansa,ta cigaba dan haka tun da duk
kanmu....Haj Laura ta karasa da cewa ya fada kan
kowa,sun bashi kudi da alkawarin in wata matsala ta
taso zai gansu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Yaune juma'a kuma yaune lunchn,nace ma anty yagana
nifa ban san wanene mijin ba anty yagana tace inje don
kada mutane su gane halin da ake ciki tun da ba kowa
ne ya sani ba ki kwantar da hankalinki Babanki yaba
Alhj damar ya fidda miki miji a cikin kwana ukun da
suka rage shi kuma ya fitar miki da miji dan gaske ki
dauka haka Allah ya tsara,cikin kuka nace Aunty
wanene?tace nima ban sani ba dan ko mamanki bata
san kowa ye ba sai dai tace tasan ba zai miki mugun
zabe ba shi yasa ma kikaji nace dan gaske.Ina ji ina
gani ta shirya ni suka zuba min dubai less da gwala
gwalai nace anty ni dai kayan Adams ne ku cire
min,tace a'a ba nashi bane ai ke yar gata ce wannan
cikin kayan da babankk ya hado maki ne daga dubai
sannan mamanki da Alhj sun maki gwala gwalai shima
Adams ya bar maki akwatuna,dan haka in kinje gidan
ango sai kiyi ta kwaliya,na share hawayen idona,Anty
Saudatu ta miko min kayan shafa nan na kuma yin
wata kwaliyar.
Gurin lunchn yayi guri ko ina ya tsaru mutane kamar
kasa har abin ya bani mamaki ni da kawayena muka
hau high table shalele ya cashe sosai su Mami da
Amira da sauram kawayena sun yi min kara wajen buga
abubuwa,na sha liki gurin dangi da yan uwa sun min liki
baran ma Kabir har nace a raina kodai da Kabir din aka
hadani ne?yaynmu ne ya bani mamaki ko leke duk
yanda muke dashi shine ko yazo bikina niko a na shi
nayi rawa nayi tsaki ba komai duniya ce.Bakwai aka
tashi daga gurin lunchn, gidansu Anty Yagana muka
koma kuma can aka min kamu sai dai banga dangin
miji ba kamar yanda naga ana yi a al'ada
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Washe gari daurin aure tun safe direban babana yaxo
ya daukeni ya maidani gidan Babana nan na samu
gidan cike da yan garinmu har da tsohuwa jikinta na
fda na soma kuka tace kuji mun sakarai ai ni murna
nayi da dan Ball yace baya yi dan Allah ya sani tunda
akace Adamu Ball yake sai naji bana sonshi ynxu da
babnki ya mana bayani yace ya fasa nace gara haka
kila ma yace ba zai iya rike ki bane yace ba yayi tunda
Ball ai ba sana'a bace, duk da halin da nake ciki sai da
na yi murmushi a raina nace to shi wannan baki san ta
sana'ar ba kila ma gara Ball.Karfe biyu gidan babana
ya soma cika da yan daurin aure niko ina can dakin
Babana na kudundune sai kyarma sanyi nake zazzabi
ya rufe ni ba wanda ya san inda nake ban sani ba har
an daura aure su Amira sunzo muje gurin sai nemana
ake gidan cike yake dam da jama'a can babana ya
shigo bedroom dinsa yana cewa bari ya karoma baki
dabino sai ya sameni kwance ina ta rawar sanyi da
sauri ya iso gurina,uwata menene?dama kina nan?ya
dago ni jikina zafi rau ya shigo falo ya shiga kiran Anty
Maijidda a waya data zo yace mata gani nan ba lfy shi
kuma ya fita ya sallami baki ya dawo,Anty Maijidda ta
dagani ta zaunar dani ta dubi babana tace to baban
Iman ya za'ayi ynxu?ga gidan dinke da mutane ko zaka
kira likitan mu ne?yace a'a bari na kira wata likitar kin
san tana da matsalar zuciya ya dubeni kin san number
Doc dinki na girgiza kai alamar a'a yace to bari na kira
yaynku ai shi yana da no dinsa ko?nayi alamar eh,ya
shiga neman layin yaynmu Anty Yagana ta yowa Anty
Maijidda waya wai inzo yan walima sun soma zuwa
Anty Maijidda tace yagana ga Iman nan kwance babu
lfy ynzu ma likita muke kira,Anty Yagana tayi salati
tace gamu nan zuwa babana ya samu yayanmu ya
sanar dashi yazo da likita gani nan ba lfy yayanmu cikin
rikicewa yace ba dai ciwon ta bane ko,babana yace shi
yasa nace kazo da liktan ta dan kar abin yayi nisa,jim
kadan sai ga yayanmu shida likita daga dakin babana
aka daukoni zuwa falo kan doguwar kujera aka kwantar
dani likita ya shiga dubani can ya dago ya dubi su
babana da yaynmu yace ba ciwon ta bane damuwa ce
ta saukar da zazzabin sai dai ayi kokarin ganin ta rage
damuwar dan tana iya kawo barazana ga ciwon
nawa,ya rubuta magunguna yace zaije da kansa ya siyo
sannan yace da yaynmu asamu tawul karami mai kyau
asa cikin ruwa mai tsafta a dinga goge min jikina nan
da wasu yan mintuna daga kafa har zuwa goshina
Na zaci tare da yaynmu zasu fita sai naga yaynmu ya
zauna Babana da Anty Maijidda suka fita Anty tace
bara na dauko tawul da ruwa a zatona anty ce zatayi
min gugar jikin sai naga yaynmu ya amsa ita kuma ta
fita har da kulle kofa..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
yaynmu ya iso gabana ya tsuhunna sanye yake da rigar
boyel fara tas kamshin turare sai tashi yake a jikinsa ya
cire farar hular shi ya ajiye sannan yasa hannuwanshi
ya jawoni yaja zif din rigata kasa gabana sai faduwa
yake tsoro da mamaki suka cikani a raina nace yaya
zasu ce yayanmu ne zai min wannan aiki to ko
dakinmu daya ai bai dace ba inaji ina gani ya cire min
riga da breziya ta daga ni sai zani iya cibiya sannan
yajuyo dani naso in sa hannu in kare kirjina amma
kasancewar jikina babu kwari sai na kasa dan haka sai
na runtse idona ina jiran naji ruwan a jkina sai naji shiru
a hankali na bude idona yaynmu na gani a gurin da
yake idonshi kyam a kan Kirjina da sauri nasa hannu na
rufe ya dauko tawul din ya soma goge saman cikina
zuwa kirjina sannan fuskata duk da yayi kokarin
kamewa dan kada na gane na fuskanci ya dimauta da
ganin halittar kirjina haka yafi goge min gurin can aka
kwankwasa kofa ya yi sauri ya samin riga sannan yace
a shigo, likita ya shigo da magunguna yace a bani
abinci naci sai nasha ynxu,bayan tafiyar likitan ne yayi
ma Anty Maijidda waya a kawo min ruwan Tea, su da
yawa suka shigo Anty Maijidda da Anty Yagana,Mami
Amira harda tsohuwa kakata sun min sannu sannan
suka fita,a raina nace a rasa mai bani tea dinma sai
yaynmu kadan na sha nace ya isheni ya harare ni karbi
da sauri na karba na kafa kai na shanye yace ko
kefa,kafin ya rufe baki sai amai na wanke mishi jiki tas
da amai yana rike dani sai da na gama sannan tsoro ya
kamani na tuna Mami ta taba bani lbr wai wata rana
Bilkisu bata da lfy tayi amai a dakin Haj Yaya ya shigo
ya taka sai da ya mareta duk da bata da lfy wai ya
zatayi amai a daki da sauri na dube shi cikin tsoro
nace yi hakuri dan Allah......shiiii ya katseni sannan ya
dubeni yace kin gama na daga kai yace Anty Maijidda
ta shigo tana ganina tace ya kika ma yayanku amai kin
bata mashi jiki Iman yace ba komai ta kuskure bakinta
ta sha maganin yanxu zanje gida na dawo anjima,
bayan na sha maganin na kwanta kawai sai barci, bani
na farka ba sai magriba Anty Yagana suka sani nayi
wanka sannan naji suna cewa tun da jikin da sauki a
kaita tayi sallama da mamanta,na dubi Anty nace dan
Allah Anty Maijidda bani da lfy kar ku kaini wani gurin
suka ce naje naji sauki a dakina ina kuka ina komi suka
kaini gurin mamana tayi min nasiha mai ratsa jiki
sannan ta kara da cewa tsafta da girki suma manyan
makamaine na kara karfin zaman aure dana haka ki
kula,yan uwan mama da suka zo da yan uwan
Maska,dangin Alhj suma sunyi min tasu nasihar amma
har ynxu banji wanda yace min ga mijin ba gurin Alhj
aka kaini shima yayi min nasiha sosai har ya kara da
cewa duk wanda kika gani a matsayin mijinki to kiyi
mishi biyayya haka Allah ya tsara ni dai sai kuka
nakeyi,mun taso tsakar gida,gidan cike yake da mutane
yawanci dangin mama ne da kawayenta daga nan sai
gidan kawu malam shima yayi min nasiha sosai kuma
yace min na rike mijina haka Allah ya hukunta,Bamu
shiga cikin gidan ba da yake su Baba suna can gidan
mamana gidan babana muka koma a gurguje kafin
motar daukar amarya tazo suka kuma min wani gyaran
na dubi Amira da Mami nace ina wayata suka ce tana
gurin Saudat suka kirata ta kawo min na kunna ta ina
budeta text ne ya fara shigowa na bude shi naga ansa
"dama nace miki i am always lucky gashi kuma.. kaina
ya daure nace me kenan sai naja tsaki na soma del din
text dinshi nace koma wanene ya karata can har yana
cewa baga shi nan ba yana nufin shi aka aura min?me
karya ina ma su Baba suka wani sanshi,su Mami suka
ce ke da wa kike wannan fadan?na dan kishingida nace
um Amira tace kinsan mijinki kuwa?da sauri na tashi
zaune nace wanene Mami tace itama fa bata sani ba
Amiran,nace um ni ko wanene ma na hakura zan zauna
dashi tun da rufa mini asiri ma yayi bayan an kini kuma
shima wanda ya kini din dama bashi zuciyata take so
ba na rasa wanda nake son ma na hakura bare Adams?
sai naga Amira da Mami sunyi dariya nace in ma kun
sanshi baku son ku gaya min ai zan ganshi ne,suka ce
har ma ku zauna har abada,muna cikin haka Anty
Maijidda ta shigo tace Babana yana san ganina ina
zaune gabanshi yana mini nasiha gami da nuna min
nayi biyayya nayi koyi da hali irin na uwata sannan
yace yaji dadin mijin da Alhj ya zaba min domin shi
kansa lokacin da ya ganshi ya so ace ya kasance
mijina,na soma kuka yace na daina kuka duk abinda
nake bukata kar na zama mai rokon mijina na mishi
waya zai bani kamar na tambayeshi wanene mijin sai
naji kunya nayi shiru,mamakin da naji shine ganin
abokan yaynmu sune dai suka zo daukar Amarya,a
motar Isma'il aka daukeni a raina nace to ni Iman me
ya kawo yaynmu kai amarya kuma?to ko dai Adams din
ne tsokanata sukeyi?wa zan samu ya amsa min
wadannan tambayoyi?ina cikin tunani har muka iso
gidan,Anty Yagana ke rike dani fuskata rufe har cikin
gidan ta umarceni dana shiga da kafar dama gami da
yin Bissimila nayi yanda tace tafi tafi har dakina inda ta
zaunar dani akan gado nan da nan mutane suka cika
gidan yan ganin daki nan na bude idona tsayawa fadar
kayan da aka zuba min a dakin ai kauyanci ne komai na
dakin green ne bedroom din kenan falon dai ban fita ba
hatta setin gadon dasu madubin duka green ne,ban
taba ganin setin irin setin nan ba haka kowa yake cewa
Mama,Mami ta shigo ta dubeni kai Iman kin more kaya
kinga falonki da bayinki kuwa?Amira tace ai kallo yana
kicin nace uhm! ina bayin suka nuna min gashi nan
ashe ma a cikin bedroom din yake haka dai mutane
sukayi ta zuwa suna leka bayi da sauran wurare har
suka soma tfy
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Ya rage sauran kawayena,Nasir ma yayiwa Mami waya
wai ta fito su tafi ta dubeni matar yaya sai kinji ni a
waya da sauri nace wanne yayan?ta fita tana dariya
Amira ma ta fita tana dariya, tace to Iman sai ki ganni
dan wannan mijin naki baya wasa da mutane bare
muce zasu shigo da aboka ango na riketa nace sai ta
gaya min ko wanene tace bansanshi ba na dai ganshi
dazu ne naga kamar ba shi da fara'a,ta kwace nace
dan Allah Amira kada ki tafi ko saurarona batayi ba sai
da ta kai kofar fita daga bedroom din sannan tace Anty
Yagana tace in ce maki sun wuce sai sunzo kawo maki
akwatuna amma akwai kaya cikin wardrp nace shine
suma suka gudu harda Saudatu,Amira tace eh na taso
nace bari na rakaki da gudu ta fita kamar dama ta san
riketa na so nayi tace sai wata rana har falina na fita
tausayin kaina ya kamani nan tsakiyar falon na tsaya
ina duban dukiyar da iyayena suka narkar cikin katon
falon komai na ciki tunda ga Carpet har zuwa Kujera
Labule marun ne,wata yar kofa na gani koda na bude
ashe kicin ne ya tsaru kayan aiki masu amfani da
lantarki gasu nan,na dawo na daga labulen window na
leka sai naga wani katon falone na alfarma falon da
kamar naso na sanshi a hankali na bude kofar dakin na
leko gabana yayi wani mugun faduwa ganin gidan
yaynmu tabbas gidan yaynmu ne kenan shi na aura
wata zuciyar tace min ko Kabir ne,shine zamu zauna
anan kafin ya gama gida?na koma bedroom kaina daure
na leka Toilet din da naji ana ta kwarzanta koda na
ganshi sai da nace Allah yasa ka ma iyayena da
albarka na shiga nayi alwala nazo nayi shafai da wuturi
da yake nayi isha a gida na idar na bude wardrof na ga
kaya kala kala kusan cike na dauko rigar barcina mai
hawa biyu nasa na kama gashina na tufke sai a lokacin
na kula da wani show glass cike da kayan kwalba a
cikin kwalban akwai turarukan wuta masu kamshi,na
hau gado na kwanta zuciyata cike da tsoro da tunanin
wa na aura ga tsoro ni kadai ce dan da na saba ni dasu
Jamila muke kwana nace gobe zanyi wa su Jamila
waya su dawo nan,can barci ya soma daukana naji
motsin kofa da sauri na juya don ganin mai shigowa
.Yaynmu na gani tsaye cikin kayan barci riga da dogon
wando kyanshi da annuri yana tashi a tare dashi ya
taho a hankali har kusa da gadon nima na tashi zaune
fuskarshi babu yabo ba fallasa yace ya jikin?a hankali
yake magana,da sauki na fada ina dubansa farin ciki da
dadi suja cikani sai dai na kanne,yace ina yake