Showing 24001 words to 27000 words out of 44948 words
Chapter 9 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt
tana tofawa a hannunta da yake maƙale, duk da tana rattabo addu'o'in ne ba tare da ta san ita kanta addu'ar me take karantawa ba. Dan tana ganin yau mai dogon kwana kaɗai ne zai fita daga ɗakin dan ita yanzu ta daina jin nauyin goyon Nasiru da take ɗauke da shi dan gaba ɗaya tashin hankalin da take ciki ya danne nauyin goyon bayanta. Cikin ikon Allah sai ta ga ƙofar ta buɗe, hannun nata har karkarwa yake wurin fito da shi daga jikin Shamsiyya, tana fitar da hannun kuwa ƙofar ta koma ya rufe. A ranta tana ƙiyasta yadda za ta fice ta gudu daga ɗakin ta bar ma gidan baki ɗaya.
Baram, ƙaran rufe ƙofa ya yi dirar mikiya a kunnuwan Gwaggo. Da sauri ta yi wani juyin tamkar yadda ake juya muciya idan ana tuƙin tuwo, ai kuwa ta hangi jaririn nan a jikin ƙofa ya rufe ta ruf ya jingina bayansa a jikin ƙofar yana kallon ɗaya baya ɗaya.
"Ni Ramma yau wace rana ma muke, da wannan sankata-sankatan ƙaddarori suke faruwa a ce jariri ya fasa cikin matacciya ya fito da kansa yana tafiya har da magana abu bai tsaya a nan ba har da su rufe ƙofa" Cewar Gwaggo a ranta tana kallon inda Kakar Talatuwa take a raɓe tamkar ka ce kulle ta ce cass iIdanuna nata ta juya ta kalli Malam Mammani ta wutsiyar ido motsin bakinsa kawai take iya gani, dan bakinnnasa sai lamisawa yake kamar bakin tsohon da babu haƙora a ciki sai kuma yatsunsa da yake ta lazimi da su.
"To uban ɗan ma kenan bare kuma ni UNGOZOMA" Ta sake faɗa a ranta tana jin ina ma ba ta taho karɓar haihuwar ba, tana ganin ta baro Laila a gida tana ganin su Mai Gari suna can ana karɓar gashin aya a tafin hannu ashe dai a nan ma wata uƙubar za ta karɓa
Jariri kuwa takowa ya fara yi har lokacin uwa da cibiyarsa suna riƙe a hannunsa, yana zuwa saitin Malam Mammani kawai sai gani aka yi ya tashi kamar mai tafiya a saman iska bai tsaya a ko ina ba sai a tsakiyar kan Malam Mammani. Malam Mammani jin saukar ƙafafun jaririn a kansa sai kawai ya ji tamkar an ɗora masa iccen wuta, a hankali ya shiga ɗaga idanunsa sama, ai kuwa sai ya hangi jaririn yana tsaye a kan nasa. Kafin ya gama wannan mamaki sai gani ya yi an zuro cibiyar zarere tana reto a saitin fuskarsa ta sauka har wajen ƙirjinsa kallon cibiyar kawai yake tamkar ya ga ajalinsa sabo da yadda yake jin bugun ƙirjinsa.
"Ayyuhan nassss, ku saurara, zan yi muku kuɗubar juma'a duk da yau ta kasance ba juma'a ba" Jaririn ya faɗa cikin muryar jarirai amma kuma yana mata ƙalƙala da maganar uztazai.
Wani fitsari ne kawai ya ƙwacewa Malam Mammani, dan shi dai yau ya ga annoba shiga wutar kara. Kakar kuwa da ta ga jaririn ya ƙwalalo mata idanu lokacin da yake magana sai kawai ta sunkuyar da kai ƙasa.
"Ya Kakar Ummata, shin baki ga na hau minbari ina muku kuɗuba ba? Amma kika sunkuyar da kai"
Da sauri ta fara yaƙi da bakinta har dai ta samu nasarar finciko maganar.
"Na'am,na'am na'am ya jinjirin jikata" Cewar Kaka cikin muryar ustanzanci dan ta ga abin yana neman fin mai rai sai dai ko matacce.
"Ungo..."
"Na'am ya shaik ai tuni mun ji mun bi, kuma mun yi imani da Allah da ranar lahira" Cewar Gwaggo Ramma cikin sauri tun bai gama kiran sunan nata ba. Haka dai ya cigaba da surutansa wani ma ba sa gane abin da yake faɗa. Ƙafarsa ya ziro fuskar Malam, sai da ya kai ta daidai hancin Malam ɗin sai ya tura babban yatsan ƙafarsa a ƙofar hancin Malam ɗin, Malam kuwa yana nn kamar an dasa shi ya kasa cewa uffan sai addu'a da yake a zuciyarsa a kan Allah ya fitar da su daga cikin wannan bala'i. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya fito da ƙafar.
Jim kaɗan sai kawai ya taso luuuu daga saman kan Malam Mammani bai yi masauki a ko ina ba sai a bayan Gwaggo Ramma wato ya sauka a kan bayan Nasiru da yake bayanta.
"Shikenan kuma yau ba zama an ɗaurawa karya zani, an ringa hawa da sauka babu tsayawa sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci" Cewar Gwaggo a ranta a fili kuma sai ta ce.
"Rabbana atina fid duniya hasana wa fil akirati hasana a ƙina azabar naar"
"Sannu Ramma, ina askar yankan cibin naki ki ɗakko ki yanke mini cibiya" Ya faɗa har lokacin yana bayanta a kan Nasiru.
"Yo ni ai jariran da aka haifa nake yankewa cibiya amma kai kuwa da kai ka haifi kan ka, ina ni ina taɓa maka cibiya haka kawai in shiga tara" Ta faɗa a ranta.
"Ko in ɗakko miki askar da zaren lilon da kike ɗaure cibiyar?" Ya ƙara katse mata tunani, Malam kuwa da Kaka har lokacin suna ta ambaton Allah ko dakatawa ba sa yi.
"Ni yau ai son kaje ka saka ni a kogin da zan kasa fitowa wallahi, domin wannan ai wayon a ci ne an kori kare daga bakin ɗinya, wannan ɗan na bayana da ka danne shi girman uwarsa ya fi gaban wasa, dan za ta iya yin ƙuli-ƙulin kubura da ni ba tare da ta saka fulawa ba, ɗan amana ne dan idan wani abu ya same shi na san na kaɗe daga ni har su Mai Gari da basu san hawa ba su san sauka ba. " Ta faɗa a zuciyarta.
"Ba za ki yanke min cibiyar ba?"
"Za a yanke maka"
"To maza un go fara aikin ki" Ya faɗa yana miƙo mata cibiyar saitin fuskarta kafin ta samu zarafin magana ya yi tsalle ya diro gabanta.
"Wannan uwar a binne ta"Ya faɗa yana miƙa mata uwar mahaifar, da hannu biyu ta karɓa sai kuma ya saki cibiyar take binsa zaroro.
"Ki ajiye uwar mahaifar duk ku dawo nan za mu yi wasa" Ya faɗa lokacin da ya koma gaban Malam Mammani da yake tsaye kamar gunki. Kallon kallo aka fara amma ganin ya kafe su da ido sai kowa simi-simi ya taso ya ƙaraso gabansa ga tsoro ga kwanan yunwa.
Su duka ukun ya saka suka hau layi kamar na sahun sallah, Gwaggo da take goye da Nasiru sai lokacin ta ƙara jin bayanta yana ƙage sosai. Suna tsaye suna kallon ikon Allah. Amma shi Malam Mammani abu biyu ne ya haɗe masa goma da ashirin ga tsoron gawar da take kwance a tsakar ɗakin ga kuma tsoron jaririn da yake gabansu yana sabgarsa tamkar wani mai shekara hamsin. Kaka kuwa idanunta ta sauke a kan gawar Shamsiyya ganin cikin nata inda jaririn ya fito ya rufe kamar ma ba ta wurin ya fito ba, hakan ya sa ta ƙara shan jinin jikinta dan tana ganin wannan abu mai kamar almara tun da take bata taɓa ganin ɗa ya fito ta ciki ba sai dai a ce an yi tiyata an fito da shi amma kuma yau ga shi abin ya faru a kan idanunta ita yanzu gaba ɗaya ma tsoro ne ya lulluɓeta har gawar ma yanzu tsoronta ya cika mata zuciya. Bare kuma Gwaggo da take jin kamar bangon ɗakin ya tsage ta runtuma a guje ko waiwaye babu.
Ƙafa ɗaya ya ɗage ɗayar kuma ya saka a cikin kuɓewar da take malale a tsakar ɗakin sululuuuuu ya tafi da ƙafa ɗaya. Cikin ƙwarewa yake ta zagaya tsakar ɗakin yana ta dariya cibiyarsa tana binsa su kuma gaba ɗaya sai lamarin ya ƙara tsorata su, sai da ya yi zagayen sau goma amma ko faɗuwa bai yi ba duk da kuɓewar da tsantsin ledar ɗakin.
"Za ku fara zagayawa kamar yadda na yi amma ku duka ukun a tare za ku yi"
"Haba ɗan albarka kai kuwa mutumin nan baka ganin gawa a ɗakin amma sai mu ɓige da zagaya ɗaki" Malam Mammani ya faɗa cikin muryar kuka dan shi abin ya ishe shi domin abin ya yi yawa wai shege da hauka, yana fatan Allah ya kawo wanda zai kawo musu ɗauki.
"Ni ba mutumi bane ɗan jinjiri ne, kuma da ka ke maganar gawa ba gawar uwata bace, ai muna gama wasan sai ku je ku binne ta" Ya faɗa fuska a ɗaure. Babu wanda ya ƙara cewa ƙala haka suka fara ƙoƙari cika umarninsa. Kafin su fara sai gani suka yi ya yi tsalle ya maƙale cibiyarsa a jikin wani ƙarfe a saman ɗakin sai ya zamana yana rataye yana reto a jikin cibiyar tamkar wanda yake lilo.
Malam Mammani da jikinsa yake karkarwa haka ya ɗaga ƙafa ya shiga cikin kuɓewar duk da dama jaririn ya gama haɗa tsakar ɗakin da kuɓewar taku ɗaya Malam Mammani ya yi a cikin kuɓewa bai ankara ba sai ji ya yi ya tafi luuuuuu lo tsayawa babu tun daga inda yake sai da ya je ƙarshen ɗakin ya je a zaune daɓas faɗuwar da ya yi sai ya ji tamkar wurga shi aka yi. Gwaggo da Kaka suna ganin haka sai suka shiga tashin hankalin da ya fi na farko musamman Gwaggo Ramma da take ɗauke da goyo a bayanta.
"To ku ma ku tafi a tare" Muryarsa ta katse su har lokacin yana maƙale a saman ɗakin yana ta reto. Babu musu haka su Kaka suka ɗora ƙafafu a kan kuɓewar su ma, suuuu kake ji sun tafi da yake ɗakin yana da girma, Gwaggo ce a gaba Kaka tana baya.
"Kar wacce ta kuskura ta yarda ta faɗi kuke ta zagaye ɗakin" Ai gaba ɗaya sai suka daddage dan ganin basu faɗin ba sai suke gewaye ɗakin tamkar masu yawo da takalmin taya.
"Kai ma ka tashi ka bi sahu, ka jaɓe a waje ɗaya daga farawa" Malam Mammani ya ji muryar jaririn ta katse shi.
"Bismil ƙadari maganin masifa" Ya faɗa a ransa yana tashi dakyar jin ƙugunsa kamar ma ba a jikinsa yake ba. Sahun su Kaka ya ci kowa sai baza hannuwa yake irin kamar za su faɗin nan, Kaka jin za ta faɗi aikuwa ta kamo Nasiru da yake bayan Gwaggo, haka ya yi daidai da miƙa hannun Malam ɗin ya kamo zanin Kaka, Kaka jin an damƙo zaninta a take ta saki Nasiru ta damƙe zaninta da hannu biyu tana sakin salati dan ta ɗauka jaririn ne ya ja zanin zai mata tsirara a cikin mutane, haka da ta yi shi ne ya assa sa Gwaggo ta yi sufa, Kaka ta bi bayanta sai Malam ma ya bi bayan Kakar Gwaggo a saitin gawar ta faɗi sai ya zamana kanta a kan cikin gawa, kaka kuma ƙirjinta ne ya sauka a kan ƙafafun gawar, Malam kuma fuskarsa ta sauka a kan fuskar gawa.
"Kowa kar ya motsa daga yadda yake" Muryar jaririn ta katse musu hanzari.
"Mu karanta lahaula ƙafa bakwai Allah sa kar gawar nan ta manne da jikinmu a mana sitira a binne mu tare" Malam ya faɗa cikin muryar kuka da tsantsar tashin hankali.
"Wayyo Allah, na kasa banbance alif da ambaki, gga goyon ɗan ruwa ga ni a kan gawa ga jariri yana tijara Allah ka kaow maa ɗauki ka kawo mai ceton mu" Gwaggo ta faɗa ranta tana jin tamkar ta yi filfilwa ta bar jikin gawar.
"Haba Malam Mammani, in ban da abinka ina muka ga nutsuwar da za mu iya karanta lahaula, lahaular ma ƙafa ɗai-ɗai har ƙafa bakwai? Ina laifin ma ka ce ƙafa ɗaya idan abin ya yi tsamari mu karanta ƙafa uku, ni wallahi ba zan ma iya lissafa wa ba a halin da nake ciki yanzu na rayuwa ko mutuwa" Kaka ta faɗa tana rushewa da wani marayan kuka.
"To Kaka ai sai mu karanta yadda ya sauwaƙa tun d...
Maganarsa ce ta katse jin saukar jaririn a tsakiyar kansa, tsalle jaririn ya shiga yi a kan Malam idan ya yi tsallan sai fuskar Malam ta manne da fuskar gawar tsananin tsoron da yake ciki na ganin fuskar gawa a jikin fuskarsa muraran sai ya saki kuka amma sabo da tijara jaririn nan bai bari ba sai da ya tabbatar ya gama sanya Malam a ruɗani sannan ya yi tsalle ya sauka a kan Gwaggo idan ya yi tsalle sai goshin Gwaggo ya manne da ciki gawar, goshin nata kuma a saitin inda jariri ya fasa ya fito, Gwaggo bakinta ne kawai yake motsi amma ita kanta ba ta san abin da take cewa ba sai ruwan hawaye kamar wanda aka ce kar ta daina zubo da su. Sai da ya tabbatar sabo da tsabar tsoron Gwaggo ko yatsanta ba za ta iya ɗagawa ba sabo da yadda ta tsure yana gamawa ya yi tsalle ya sauka a kan Kaka da ta gama tsurewa ma, idan ya yi tsalle a bayanta sai ƙirjinta ya manne da ƙafafun gawar, fat-fat-fat kawai kake ji, sabo da tsabar yadda ƙirjinta yake bugawa tamkar zuciyarta za ta fito dan a duniya duk abin da take tsoro to ya bi bayan gawa.
Yana gamawa ya sauka ya je saitin hannun gawar ya maƙala cibiyarsa a hannun nata sai ya nannaɗe ta.
"Mu je zuwa gawar mama" Suka tsinkayi muryarsa, Gwaggo da sauri ta miƙa hannu ta damƙo aska da zarenta, na aikin UNGOZOMANCI basu ankara ba sai suka ji ana yin sama da su ma'ana gawar ta tashi da su, kowa baki yana karkarwa yake kiran sunayen Allah, haka suka shiga shawagi a ɗakin
"Allahumma salli ala muhammadin" Malam ya daddage ƙarfinsa yana faɗa tsabar ruɗewa. Kowa ya dage da addu'a babu sassutawa, suna cikin yin addu'a sai kawai suka ji gawar ta sauka ƙasa, ɗifff suka ji a kiɗime kowa yake kallonsa yashe a gefe guda kamar an jefar da shi. Kallon ɗakin suke amma babu jariri babu alamarsa, ga Talatuwa nan kwance da cikinta a jikinta Gwaggo da sauri ta tashi tsaye a kiɗime duk da santsi yana ɗaukanta amma babu abin da ta tsaya yi ta nufi ƙofa ta buɗe ta fice ko takalminta ba ta tsaya ɗauka ba ta nufi hanya ta fice daga gidan, tinƙan-tinƙan ta kama hanyar gida ko tsoro babu sabo da tana ganin halin da ta baro na tsoron gawa ya take kowane tsoro a ranta. Haka ta zo ƙofar gidan nasu tana hakin goyon Nasiru da yake bacci har lokacin kamar gawa, tana zuwa ta shigo gidan a kiɗime so take kawai ta ganta ta shiga ɗakinta ta rufe. Tana ƙarasowa barandar wani ƙara ya mata sallama a kunnuwanta wanda ba ƙaran komai bane sai na tusar Laila da ta ƙara saki a kan su Mai Gari.
MAMAN AFRAH 09013181851
*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*
ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?
TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)
NA
MAMAN AFRAH
F.C.W
GARGAƊI⚠️
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi
Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Muna da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau yarika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike
Phone number 08079130166
Page 1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣
"Ikon Allah na zaune ya faɗi, ƙaran mene ne wannan kamar motar tan-tan ta wuce?" Gwaggo Ramma ta faɗa a zuciyarta gabanta yana matsanancin bugu tamkar ana bugawa da guduma. Cikin sanɗa ta fara lallaɓawa ta tura ƙofar ɗakin nata, ta shige tana shiga amma ganin kayan Laila a ɗakin ta hasken farin watan da ya haska ɗakin sai gabanta ya faɗi, cikin kiɗima ta juyo ta fito daga ɗakin dan ganin kayan ya ruɗa ta, domin hakan yana nuna mata kenan ɗakin ya zama mazaunin Laila kuma ita alal haƙiƙa ko ana ha maza ha mata babu abin da zai sa su haɗa ɗaki da wannan matar mai kamar dunƙulalliyar giwa. Duk da tunaninta bai bata ta tuna inda sauran mutanen gidan suke bare ma mai gayya mai aiki Laila, amma a haka ta yanke hukuncin shiga ɗakin Salele dan tana ganin can ɗin tamkar hanyar tsira ne, sai ma ta shiga tunanin cewa ƙaran da ta ji wataƙila ma kawai gizo ne kunnuwanta suke mata. Tana zuwa ƙofar ɗakin baram ta bankama kofar ta shige, hasken fitilar Laila da ke yashe a tsakar ɗakin shi ne ya sanya ta hangi Laila a zaune a kan wani abu wanda tunaninta bai kawo cewa mai gidanta Mai Gari ne da jikokinta ba, dan ita ganin Lailar ya sanya cikin inda-inda ta ce
"Allahu akbar kabiran, shi ya sa aka ce tunani baiwa ne nutsuwa da hankali kuma aikin ƙwaƙwalwa ne, rashin sani ne wanda ya fi dare duhu, aradun Allah ranki ya daɗe ba nan na yi niyyar shigowa ba hasali ma ban san kina ɗakin nan ba ki mini afuwa ki yafe ni dan Allah