Showing 33001 words to 36000 words out of 44948 words

Chapter 12 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

29 Nov 2024

1523

wuyanta kamar wacce za ta filin daaga, tana nishi tamkar wacce aka ɗorawa ƙaton dutse a ƙirji. Wani takaici ne ya mamaye zuciyar Malam ganin ashe dai babu ɗaya daga cikin abin da yake tsammanin ya biyo shi wato gawa ko jaririn sai kawai ya ji saukar wata ajiyar zuciyar mai ƙarfi wacce bai san daga ina take ba.


"Haba Kaka yanzu haka za ki fito ki bar gawar ita kaɗai, ai sai ki zauna a ɗakin" Malam ya samu kansa da furtawa yana mayar da kallonsa kan Kaka da ta yi wurjanjan duk da shi ma ya san da zai duba mudubi tabbas a wurjanjan ɗin zai ga kansa domin ya san sai ya ga kansa tamkar wanda ya kuɓuto daga bakin kura saboda yadda yake a tsorace.


Kaka ba ta ce masa ko ƙala ba haka ta cigaba da rarrafowa sai da ta zo ta ɗan gota shi kaɗan, sannan ta dakata tana ɗan jan ɗan tofinta ta gyara in da ta ji ya tattare, ta sakko zaninta daga wuyanta ta ɗaure a tsantsa sannan ba tare da ta ko kalli inda Malam ɗin yake ba cikin rawar murya ta ce.


"An ƙi a zauna da gawar idan gawar ubana ce, haka kawai kai da kake mijin gawar kuma uba ga jaririn baka tsaya ba ka gudo sai ni da babu abin da ya haɗa ni da jaririn uwarsa ce kawai take jikata sai na tsaya na halaka a ban...


"Dukan ku, ku dakata!" Muryar jaririn nan ta faɗa daga can cikin ɗakin har wani amsa amo take hakan ne ya dakatar da Kaka daga maganar da take wanda tsabar ruɗewa har ta yi gaba da rarrafen za ta fice sai kuma cikin kiɗima ta dawo ta tsaya a kan gwiwoyinta a inda take da ta tuna an ce a dakata. Malam Mammani kuwa idanu ya zaro cikin firgici sai hannu ya kai ya zaro tazugen wandonsa daga cikin wandon da sauri ya ɗaura a tsantsa dan cikin ruɗu ya fara tunanin ko dai zanin da Kaka ta ɗaura zai sa jaririn ya bar ta ta tafi shi ya sa shi ma ya yi hakan dan ya tsira da ransa.




jin wurin da tazugen bai hau ka ba a wandonsa nasa yana saɓulewa yana neman yin tsirara a gaban Kaka duk da ita ma kusan a tsirarar take dan daga ita sai ɗan tofi ya kamo wurin ya ƙudundune ya cusa a jikin tazugen cikin zafin nama ya cigaba da rarrafawa dan so yake ya fice daga ɗakin tun da dai ya tabatar da a kan idanunsa jaririn yana cikin gawar kafin dai ya fito shi ya fice. Kaka ganin ya gifta fa zai fice ya barta ita kaɗai ta miƙa hannu ta kamo rigarsa ƙiiii ta dawo da shi saitin in da take tana aika masa hararar ka yi kaɗan. Kallonta Malam ya yi kamar ya saki kuka dan takaici amma babu yadda ya iya haka shi ma ya dakata.


"Wai dan taurin kai fita za ka yi? To kana zuwa waje za ka ganka ka dawo cikin ɗakin" Muryar jaririn ta ƙara faɗa cikin amsa kuwwa, Malam cikin sauri ya fara girgiza kansa alamar a'a.


" Za ku tafi amma da sharaɗin duk wanda cikin ku ya kuskura ya furta wani abu daga cikin abin da ya faru to ya sani zai dawo cikin gawar nan ne a binne mu tare"


"Babu mai ji" Malam da Kaka suka haɗa baki wajen faɗa.


"Dan haka kar wanda ya razana ko nuna wata alama ta tsoro ku yi tamkar babu abin da ya faru kuma kowanne ya tashi ya kunce ɗaurin tsantsar da ya yi ku fita a nutse" Ana gama faɗar hakan suka ji tamkar an yi ruwa an ɗauke babu maganar jaririn da sauri suka tashi tsaye ƙafafun kowanne suna karkarwa kowa ya shiga ƙoƙarin saita kansa, Kaka baya ta juya wa Malam ta kunce zaninta ta ɗaura a kan ɗan tofinta shi ma da sauri ya sunce tazugen ya ƙara ɗaurawa akan wandon nasa yadda babu wanda wanda zai lura cewa tazugen ba a cikin wandon yake ba dan bashi da nutsuwar saka tazugen a mazagin wandon.




Haka suka fito tsakar gidan Kaka ta shiga salallami tare da sakin kukan mutuwar jikar tata, kishiyoyin murna fal ransu amarya ta mutu shikenan sun huta, Malam ya daina nuna rawar ƙafa a kan ta. Haka aka taru ana nuna al'ajabin mutuwar uwar gidan Malam ɗin da mai ɗakin tsakiya Kaka ta ce su zo su taimaka mata shi kuma Malam ɗin ya tafi gidan su Shamsiyyar ya sanar da mutuwar ta. Kaka a tsorace take dan haka da aka shigo ɗakin ma dai kaffa-kaffa take dan hatta kukan mutuwar da take matsowa take dan tamkar ka ce kamota ta zura da gudu haka ta yi. Ganin Talatuwar tana motsa ƙafa hakan ya sanya ɗaya daga cikin matan ta ce suma ta yi haka suka shiga nuna murna amma ta ciki na ciki dan sun so mutuwa ta yi ba suma ba, amma Kaka a tsorace take dan bata yarda cewa farfaɗowa ta yi ba gani take jaririn ne yake son ƙara dagula musu lissafi. Sai dai ganin ta buɗe idanunta tana magana a hankali hakan ya sanya Kaka ta ji dama-dama wai kibiya a ido. Tana farfaɗowa tamkar ta farfaɗo da naƙudar mai ƙarfi sai haihuwa gadan-gadan jaririya ta faɗo, Kaka ganin haka sai ta hau murna ta manta da damuwar da take ciki. Ƙarfin gwiwar da ta samu ganin yaron ba namiji bane. Haka kishiyoyin suka shaƙi takaici, Malam da ya kira ƴan uwan Talatuwa suka zo da kuka ganinta ta farfaɗo har da jaririyarta sai suka juya akalar kukan nasu da dariya da murnar farinciki. Malam ma haka yake yaƙen ganin matar tashi da jaririyar sai dai kuma bai ji shakkun haihuwar ba tare da UNGOZOMA Gwaggo ba, dan ya san yanzu ko da kuɗi aka kira ta ba za ta dawo ba.






*GWAGGO RAMMA*


Duk labarin dannewar da Laila ta musu da suka shiga bata labari sai ta yi kunnen uwar shegu da su ta nuna abin ma ba wani abu bane kuma ba shi da wani muhimmanci, dan tana ganin ita irin badaƙalar da suka sha ita da su Malam Mammani su Mai Gari ko hanyar basu bi ba. Sai dai tsoron abin da zai je ya zo ya sanya ta kama bakinta ta yi gum ba ta basu labari ba.


Su Mai Gari kuwa haka kowa ya kama wurin kwanciya ya kwanta, Salele da Gwaggo suna ta yi wa Taju masifa a kan kawo musu Laila gida dan suna ganin gashi nan ko kwana ɗaya ba a yi ba suna karɓar hukunci. Gwaggo ban da tsaki kamar wata tsaka babu abin da take yi, dan shafalfalar katifar Salele ta ƙwace ta hau tare da ɗaukan zaninta a cikin kayanta da Laila ta sanya aka kawo aka jibge mata a ɗakin ta duƙunkune ƙafafu ta shiga sakin munshari. Mai Gari ma baccin ne ya sace shi dan sai rubda ciki ma ya yi ya ɗora haɓarsa dan ba zai iya kwantawa da gefen fuskarsa ba sabo da yadda gefe da gefen yake masa ciwo haka dai baccin wahala ya yi awon gaba da su duka har Taju kowa ya kama nasa wajen.


Cikin bacci Gwaggo Ramma ta ji kamar ana ɗan jan zanin da ta rufa da shi, jin sanyi yana ratsata sai ta miƙa hannu ta ja zanin ta ƙara rufa har lokacin idanunata a rufe, ƙara janye mata zanin aka yi wannan karon sai ta ji gaba ɗaya zanin aka janye aka bar ta sanyi yana surar jikinta. Idanu ta buɗe ta laluma ta ga babu kowa ko alamar mutum sai ma ƙaran munsharin su Mai Gari da ya cika ɗakin, zanin ta ja ta rufa dan sai ta ɗauka a cikin bacci ne kawai ba wai jan zanin ake yi ba. Baccin ta cigaba da yi cikin kwanciyar hankali, can cikin baccin ta ji an kamo zanin da yake ɗaure a jikinta, hannu ta kai ta fisga ai kuwa aka ƙara kamo wajan da ta ɗaura zanin.


"Na shiga uku ni Ramma, mene ne wannan ɗin kamar almara, kar dai ɗaya daga cikin yaran nan ne Salele ko Taju suke son su farmini tsakar daren nan, dama in banda jalala ƙwacen kwanan kishiya ta yaya za a haɗa ni ɗaki ɗaya kwana da garadan samarin zamani su rasa wacce za su nemi farwa sai ni uwar gyatumar su" Gwaggo ta faɗa a ranta gabanta na tsananta faɗuwa. Jin ana neman since zanin da ƙarfi ta kai wa hannun da ake neman mana tsirarar ai kuwa cikin sa'a ta kamo hannun sai dai abin mamaki wai ganin siriki a kan gadon matar ɗansa, sai ta ji hannun da ta kama ɗin ɗan ƙarami ne tamkar sillan kara mulmulawa ta yi ai kwa sai ta ji wani lagafgaf cikin mamaki ta ɗan ƙyallara ido ɗaya dan ganin wane irin hannu ne dan jin ƙanƙantar hannun ya sanya ta daina zargin su Taju.


"Ha hayyu ya qayyumu" Cewar Gwaggo Ramma a zuciyarta gabanta tana faɗuwa da ƙarfi, domin abin da ta hango daga cikin idon da ta ƙyallara ya mugun ɗaga mata hankali tana ƙoƙarin tashi sai ta kasa ko da kataɓus.


"UNGOZOMA, kin manta baki yanke mini cibiyar ba" Cewar jaririn nan da suka yi arangama da shi a gidan Malam Mammani. Idanun ta mayar ta runtse da ƙarfi tana fatan Allah sa a cikin mafarki ne.


"Kin binne uwar" Ya faɗa cikin muryar ƴar ƙarama kuma cikin raɗa da alama ma ita kaɗai ce take jin maganar.


"Wayyo Allah, ni ina ganin na baro ka a can gidan ashe dai ka biyo ni nan ɗin ma kenan tahowar tawa ya zama duk ɗaya wai an ce da karuwa hayo gado.


Hannun da ya ɗora mata cibiyar jikinsa ta ɗaga ta warɓar gefe, dungurawa ta yi cikin azama ta bar shi a kan katifar da rarrafe take tafiya taa fatan ta samu mafaka a wajan Mai Gari ko ma mene ne ya same su tare. Da yake a gigice take sai ta faɗa kan Salele da yake baccinsa mai nauyi, cikin abin rufarsa ta shige ta maƙalƙale shi gabanta yana faɗuwa. Salele kuwa bai ma san ana yi ba wai kunu a maƙota dan haka baccinsa yake hankali kwance. Hannu Gwaggo ta kai za ta ƙanƙame Salele duk a tunaninta Mai Gari ne, a tsakiyar kansa wanda ya tara suma ta yi wa hannunta masauki wani irin ɗebe wuta Gwaggo ta yi tana karanto salatin annabi a zuciyar ta dan ta san dai duk firgicewar da za ta yi to kuwaba za ta kasa shaida kan Salele ba bare kuma kan Mai Gari mijinta da wanzami yake salsalewa tas da aska ko ɗigon gashi ba a bari. Da sauri ta janye hannun ta bankaɗo abin rufar ta tashi zaune.


"Allah ka mini aikin gafara ni Ramma, ina zan kai abin kunyar nan idan aka kama ni kwance da jikana kuma na san mutane duk bayanin da zan musu ba za su fahimce ni ba Allah na tuba ko giyar wake na sha, mai zan yi da wani Salele" Ta faɗa tana taɓe baki kamar an ce ta duba gefenta ai kuwa sai ganin jaririn nan ta yi a tsugunne. Wani yawu ta haɗiye tana jin wani mugun tsoro yana dirar mata, kafin cikin sanɗa ta fara jan mazaunai domin neman in da za ta ɓuya. Ganin kamar abin ba zai mata ba sai ta fara mirginawa daga kwancen, cikin azama ta samu nasarar afkawa cikin abin rufar Taju, har lokacin a zaton ta Mai Gari ne hallaw. Garin ƙanƙame Taju ta taɓo belt ɗin da take jikinsa da ya yi ɗamara da ita.


"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ni Ramma mai ya same ni yau daga in shiga bargon wannan sai in fito in shiga na wannan kuma har yanzu ban dace da samun bargon Mai Garin ba, haka kawai na ji hannuna ya taɓo zanzaro (Belt) Ban da Allah ya taimake ni yaran nan suna bacci mai nauyi ai da Taju sai ya ce wani abu na zo nema a wajansa yo ko bai faɗa da gaske ba ya faɗa da wasa dan ya bani kunya" Ta faɗa tana yayyace lulluɓin ta fito daga can gefe ta hangi mutum ya yi goho wanda take kyautata zaton Mai Gari ne dan dama ta dai san su kaɗai ne a ɗakin.


Wurinsa ta nufa ganin jaririn ya rarrafo yana bin ta duk in da ta yi, Mai Gari kuwa shi sabo da yadda gefen fuskarsa yake masa raɗaɗi shi ya sa sai kawai ya yi goho haɓarsa a ƙasa a haka yake baccin. Gwaggo tana ƙarasawa wajansa da rarrafe waiwayawar da za ta yi don ta hango jaririn sai kuwa ta hango shi ya kusa ƙarasowa wajan da baya-baya ta fara ja ba ta san ta ƙarasa in da Mai Gari yake ba dan haka tana zuwa sai ta bangaji Mai Gari da yake durƙushe ya yi goho yana baccin wahala dan babu jin daɗi a baccin nasa ko kaɗan. Mai Gari jin an bangaje shi dama ba wani dogon bacci ya yi ba jin an warɓar da shi daga gohon ya faɗi wacakar sai tunaninsa ya tafi cewar Laila ce wata tusar ta matso ta shi ne ta ƙara dawowa za ta yi tusar a kansa.


"Ya Allah ka mini alam nashra lakasadarak, Allah mugun ji mugun gani Allah ka kare mu" Mai Gari ya fara rattabo addu'o'in a zuciyarsa wasu ƙwallar tausayin kansa yana gangaro masa dan ya san tabbas ya zama abin tausayi in ma bai zama gawa ba matuƙae dai Laila ta ƙara yin zaman cin tuwo a kansa.


MAI BUƘATAR UNGOZOMA ZAI BIYA 400 KAFIN MU GAMA FREE PAGES ZA MU GAMA FREE A PAGE 26 IDAN MUKA GAMA 500 NE. ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 opay SHAIDAR BIYA TA 09013181851




I
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)





NA






MAMAN AFRAH




F.C.W




GARGAƊI⚠️


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.






Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi


Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike


Phone number *08079130166*


Page2️⃣1️⃣➡️2️⃣3️⃣




Gwaggo hannu ta saka a cikin mayafin da ya rufe kansa ta sanya hannu ta rafko kan Mai Gari da ya sha aski rantal ta shiga murzawa tana murtsukawa tamkar tana shafa masa mai, Mai Gari shi duk tunaninsa Laila ce take son samun saitin in da za ta zauna ta saki iskar tusar ta kamar wata bodara.


"Wayyo Allah, ki yi wa Allah Laila kar ki saki iskar nan a tsakiyar rantal ɗin nan nawa, aradu ina ga kan nan nawa zai iya tsagewa saboda ƙaran tusarki" Ya faɗa a zuciyarsa yana jin kamar ya kamo ta ya yi ta duka.


Gwaggo jaririn ne ya yi tsalle ya sauka a kan cinyarta dan haka sai ta muskuta cikin tsoro ta yi zaman ƴan bori a kan ƙafafuwan Mai Gari da yake yashe a gefe fuskarsa har lokacin rufe da mayafin da ya rufa. Jin Gwaggo ta faɗa kan ƙaffafunsa, da duk tunaninsa Laila ce zuciyarsa ya ce.


"Shikenan kuma sai yadda hali ya yi wai agola ya saci motar mai gida, wataƙila ma ni da ƙafafu sai dai in gani a jikin mutane, yo wannan matar tun da ta hau kan ƙafafuna, ai na san sai dai a rinƙa saka ni a layin guragu dan na san dai ƙafafuna ba za su amfanu ba sai dai a yanke mini su a bar mini dungulumi" Ya faɗa a ransa yana raya cewa shi bai taɓa haɗuwa da wannan ibtila'in ba.


"Mai Gari tashi kar a maimaita yaƙin badar a kan ka" Gwaggo ta faɗa kamar ta rushe da kuka.


Ɗif Mai Gari ya yi jin maganar matarsa dan sai lokacin ma ya gane nauyin da yake ji a kan ƙafafun nasa ba shi da wani yawa, wani tsaki ya ja tare da tashi zaune ya wancakalar da Gwaggo daga kan ƙafafunsa ta faɗi gefe guda ya shiga kiciniyar buɗe fuskarsa dan mayafin duk ya tattauye a jikinsa ya kanannaɗe. Ya miƙa hannu ya ɗakko fitila ya kunna haske ya gauraye ɗakin, Gwaggo ya gani ta yi reran tana tana karanto fatiha da salatin annabi dan irin warɓarwar da mijin nata ya mata sai ta ji tamkar wanda aka cillo ta daga saman bishiya yadda ƙashin gwiwar hannunta da kanta a ƙumu a tsakar ɗakin da ko shimfiɗa babu.


"Ke dai wallahi Ramma bakya mutuwar tsakar ɗakin ki sai ta wani, dama wannan jikin nawa akwai ya babu kakar wajen uba, da nake lallaɓawa sanadin hawan ƙawarar da shirgegiyar matar can ta mana jiya, shi ne kika zo kika hau kan ƙwabrina da tsakar daren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login