Showing 6001 words to 9000 words out of 44948 words
Chapter 3 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt
irin ta dabba har ki kasa banbance uwaki tinkiya da ta kawo ki duniya, ki nufo bil adama kina neman kindirmo(Nono) Ko dan kin jiyo ni ina kukan tumakkai, to ba tunkiya bace Malam Mammani ne, jafa'in fatallu ne ya kawo ni turken dabobi" Ya gama faɗar hakan yana aikawa ɗan tunkiyar harara ganin ɗan tunkiyar ya yi wajjen wata tunkiya yana kuka.
"Wuya in ji tsula, ɗan kare ashe ka san uwaka shegantaka ,a ka min" Ya ƙara faɗa a ransa.
"Kai jama'a ni rago zai yi wa barbara a tunaninsa ya ɗauka tinkiya ce, ga kuma ɗan akuya a gefe yana neman yi mini kilisa(Kiss) Ya faɗa a ransa a fili kuma sai ya shiga tura mazaunan na shi baya dan ya zame ragon ya faɗi kar ya je ya masa aika-aika. Jin da alama dai rago da gaske kan ƙudurinsa.
"Wallahi gwara na yi zamiya ka faɗi a kan ina ji ina gani ka mini fyaɗe, in je in yi ciki cikin ma na shege, shegen ma na dabba wato ɗan rago ko tinkiya" Cewar Malam Mammani a ransa har lokacin yana nan a duƙen sa, gwiwoyin ƙafarsa durƙushe sai kuma tafukan hannayensa da suke a kife ɗaya hannun a saƙale da igiya.
Duk tutsun nan da Malam Mammani yake yana ɗaga mazaunai sama sai kuma ya yi ƙasa da su jin ragon ya ƙi janye ƙudurinsa na masa barbara amma ragon ko gezau bai yi ba. Wasu hawaye masu ɗimi rigis ne suka gangarowa Malam ɗin tare da wani kuka marar sauti.
Mai Gari bai lura da Malam Mammani ba, dan haka shi ma yana ta ƙoƙarin ɓoye kansa ne a cikin dabobin, Malam Mammani kuwa gabaɗaya tashin hankalinsa ya linku jin rago yana masa barbara ga kuma kallon fatallun da yake yi wa Mai Gari dan haka sai ya danne kukan nasa ya buɗe baki domin ya cigaba da kwaɗa kukan tinkiya dan kar fatallun ta gane cewa shi bil adama ne ta cutar da shi dan haka sai ya hangame baki da shaƙyaƙƙiyar murya ya cigaba da kukan tinkiya suka haɗu da kukan sauran dabbobin ba tare da Mai Gari ya fuskanci wani abu ba.
Malam Ganin Mai Gari yana dogon wuyan da ya kasa gane leƙen mai yake, dan dai a ransa yana ta tunanin dama su ma fatallum suna jin tsoro ne? Ganin kamar fatallun ma a tsorace take. A hankali Mai Gari ya zame ya kwanta a ƙasa cikin takin dabobin da rubda ciki ya kwanta tamkar yadda sojoji suke yi idan za su yi harbi in suna bakin daga.
Bayan ya kwanta sai shi ma ya buɗe baki ya shiga kukan akuya, mamaki ne ya cika Malam Mammani ya ma rasa ma'aunin hankalin da zai ajiye al'amarin.
"To fa! Abin na Allah ne budurwa da ciki gwaro da yaye, ai da ganin wannan abin ba zai iyu ba auren ɓera da mage in banda abin banza hanci babu ƙafa ya za a yi ni ina jin tsoron fatalwa ita ma fatalwar tana jin tsoro, in banda ma sabon salo kiran sallah da usur ya za a yi fatallu take kukan dabobi...
Ƙafar Mai Gari ce da ta zunguri Malam Mammani hakan ne ya sanya tunanin Malam ɗin tsayawa cak! Wani tsoro ya baibaye shi jin kofaton ƙafar fatallu ta taɓa shi, a take wani guntun fitsari da ya maƙale ya shiga zubowa kamar an buɗe lalataccen famfo.
"Oh ni Mammani, abin daga Allah yake matar takaba ta yi ciki, yo abin duniya mene ne ? Kaza ta jawo muzuru kwanan gida" Cewar Malam Mammani a zuciyarsa yana fatan ƙasa ta tsage ya shige ciki ko ya samu salama daga wannan uku bala'in da yake ciki.
Mai Gari kuwa jin ya zunguri wani abu kamar jikin mutum dan ya ji abin da ya taɓa babu gashi ko kaɗan bare ya yi zaton jikin dabba ne, ai a take ya dakata daga kukan akuyar da ya fara ya maƙure a waje ɗaya wani tsoron yana turnuƙe shi jin ashe dai an gudu ne ba a tsira ba tun da ga shi ya ɓuya a turƙen dabobi amma kuma ashe dai ya kashe miciji ne bai fitar masa kansa ba tun da ga shi dai fatallun ta riga shi isa turken dabobi.
"Almuhaiminu, Aljabbaru, Almutakabbiru" Mai Gari ya shiga jero subayen Allah, domin ya ji faɗuqae gabansa da tsoron da yake ciki suna hauhawa kamar fulawar da aka kwaɓa da yis.
Gwaggo Ramma da take cikin duro ɗin dawa jin kukan dabobi ya kwamutsa da na mutane sai kawai ta cigaba da kukan tausayin kanta, domin hakan ya tabbatar mata akwai wata gagarumar matsala, tun da ta san dai mutum ɗaya ne a waje wato mijinta dan tun kukan da ya saki ta fahimci Salele bai bar Mai Garin ya shiga ɗakinsa ba,amma kuma yanzu tana iya jiyo kukan ba na mutum ɗaya bane domin abin da ya fi ɗaure mata kai ma ne yadda take iya tsinkayo kukan mutanen kamar dai kukan dabobi suke yi. Ƙara takure kanta ta yi a cikin duron tana ƙara gyara zaman fantekar da ta kifa a kanta, kafin daga bisani ta shiga ambaton.
"Ƙuliya ayyuhal kafirun, li'ilafi ƙuraishin, inna anzalnahu fi lailaitil ƙadr" Haka take jero karatun tana rawar ɗari tamkar mai cutar masassara duk da ba wai tana jeranta ayoyin bane sai dai kawai ta tsinto waccan ayar a cikin wata sura sai ta ƙara ɗakko ra wata surar amma ita a ganinta daidai take yi wai tsoho ya durƙusa ya gaishe da yaro.
Salele ma shi tsabar shiga tashin hankali bai san lokacin da ya tashi zaune ba daga kwancen da yake sai gani ya yi ya fara dungura goshinsa a kan katalalliyar katifarsa alamar sujada dan ya ga dai karatun ya gagare shi.
"Gwara in ke yin sallar ko iya sujadar kaɗai na yi Allah ya ga niyyata, sallolin yau karkaf nake haɗa wa yanzu gudun kar in mutu mala'iku su tisa ƙeyata zuwa wuta" Ya faɗa a ransa dan shi a yau ko sallah ɗaya bai yi ba daga cikin farillan salloli guda biyar dan shi ba ya ƙaunar yin sallah sai yanzu da ya ga mutuwa tana neman zuwa ɗaukansa shi ne ya fara gabatar da sallolin ta hanyar yin sujada.
"Anya Salele sallar nan taka za ta karɓu kuwa? Kai da ko alwala baka yi ba hasali ma ɗazu ka shiga bayi ka gandara kashinka" Wani sashe na zuciyarsa ya faɗa.
"Allah ka yafe mini ni bansan ma iya adadin raka,'o in da zan yi ba a salloli bakwai ɗin nan ban san kowacce raka'a nawa ake yi ba, sai dai in yi ta yin sujjadar iyaka iyawa ta" Ya ƙara faɗa a ransa dan shi sabo da rashin zuwa makarantar arabi ma bai san adadin sallolin da ake yi a rana ba bare har ya san raka'o'in su. Haka ya shiga dungura sujjadar da yake wacce daga ya ɗora goshin sa sai ya ɗago da sauri kamar ya ɗora a kan wuta, ba komai ya kawo hakan ba sai rashin nutsuwa da tashin hankali da yake ciki.
Malam Mammani jin an taɓa shi sai gabansa ya shiga dakan lugude, a take ya ji wani tsoron ya linku a kan wanda yake ji ga kuma barbarar da ragon nan yake masa a ransa dan yana ganin shi ba tinkiya ba ya za a yi rago yake masa barbara dan yana jin har da fitsari ragon ya masa. Hannunsa na hagu ya miƙa ya farɗo ƙafar ragon cikin ƙarfin hali ya janyo shi, sai ga rago ya dawo gaban Malam Mammani da yake durƙushe baki yana mismis alamar addu'a. Mai Gari kuwa ƙafar ragon ce ta sauka a kan ɗan yatsunsa da suke wurin wani zafi da raɗaɗin yadda kofaton ragon ya ratsa hannunsa, a take wani inu ya ƙwace masa da bai san lokacin da ya saki ihun ba tare da wani guntun fitsarin wahala. Ihun Mai Gari shi ya ƙara razana Malam Mammani a take Malam Mammani ya kaiwa wata akuya cafka da hannu ɗaya ba ya rungumeta bai san lokacin da ya fara faɗin
"Iya ki taimaka mini ga fatallu nan" Ya faɗa cikin gushewar hankali. Mai Gari jin furucin nan sai ya ƙara ruɗewa bai san lokacin da ya firgita ba sai ga shi ya ƙwaƙumo Malam Mammani cikin rashin sanin inda ya damƙa a take tsoro ya game musu zuciya su duka dan kowa ya ji ya rungumi mutum a tare kuma a lokaci guda suka saki wata tusa mai ƙara kamar bugun shantu. Mai Gari fuskar da ya ɗago sai ya sauke a kan fuskar Malam Mammani da ta sha garin tuwo ta ƙoshi sai kuwa ya ganshi tamkar fatallun ga kan nan nashi da ya sha askin tanƙwal ya yi buɗuɗu da farin garin tamkar an shafawa biri fulawa.
Jikin Mai Gari ne ya shiga karkarwa tamkar an jona shi da wutar lantarki dan shi dai ya ji ya taɓa abu ɗazu amma ganin fuskar nan ta saka shi a tashin hankalin da bai shiga rabinsa ba ɗazu.
Abin da yake saka shi ƙara shiga kogin mamaki bai wuce yadda jikin Malam Mammanin da yake tunanin fatallu bace yake karkarwar da ya fara tunanin ta fi wacce jikinsa yake.
Gwagwarammmmmm
Wani sautin yadda aka buga ƙofar gidan har ta bugu da bango ta koma aka sake banko ta shi ne abin da ya saka Malam Mammani sakin akuyar da ya daƙuma ya fara kiciniyar ƙwace kansa daga riƙon da Mai Gari ya masa.
"Fatallu ki mini rai dan Allah wallahi matata ce take naƙuda shi ne na fito kirawo mata UNGOZOMA" Malam Mammani ya furta cikin jin tsoro dan bai san ba ma maganganun suna rige-rige fitowa ba sai da ya ji ya fesar da su sannan ya fahimci abin da ya yi. Bugun zuciya da kuma numfashin Mai Gari ne suka tsaya cak, jin muryar Malam Mammani maƙocin gidansa da ya taso mamaki al'ajabi ne suka baibaye masa zuciya tambayoyi fal bakinsa yana son ya amayar da sh.
"Malam Mammani!!! " Ya ambaci hakan a zuciyarsa. Ƙaran wani abu kamar dirifkiya shi ne ya dakatar da Mai Gari da kuma Malam Mammani suka shiga jin bugun zuciya a hankali suka ji ƙaran yana ƙara shigowa cikin wanda suka ji tamkar da ƙafafu a ke. Wani hasken fitila ne ya gauraye gidan wanda ya haske har wajen dabbobin da su Malam suke. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Malam Mammani da Mai Gari, da sauri Mai Gari ya saka hannu ya shafo fuskar Malam Mammani ya ce
"Malam Mammani" Ya faɗa a ransa. Shi ma Malam Mammani baki
sai lokacin hasken fitilar da aka haska ya ganar da shi cewa Mai Gari ne, sai dai su duka basu gama dawo wa daga mamaki ba sai kawai tsoro ya yi wa zukatansu ƙawanya, ganin mai haska fitilar ya haska musu wata ƙatuwar mata wacce ƙibarta ta wuce misali kuma ƴar duƙurƙusa bata da tsayi ko kaɗan dan tsawonta bai fi tsawon buhun gero ba. A tare cikinsu ya murɗa kafin su dawo daga tsoron da firgicin sai kawai mai haska fitilar ya mayar da akalar hasken zuwa ƙafafunsa, su duka idanu suka zaro ganin ƙafarsa sanye yake cikin kayan sojoji a haka ya cigaba da haska wa har zuwa fuskarsa.
n "Taju" Suka haɗa baki wajen faɗa a fili.
Asalin labari
Mai Gari Kailu, shi ne asalin sunan Mai Gari yana da mata ɗaya mai suna Ramma ana kiranta da Gwaggo Ramma. Ƴar su ɗaya Habiba wacce ta rasu wajen haihuwar jikansu Salele, ƴaƴan Habiba biyu Tajuddin shi ne babba sai kuma Salele.
Gwaggo Ramma ƴa ce ga wani hamshaƙin bokan yankin na ƙauyan Gumurzu, mai suna Boka Mai Zilli, wanda babu abin da ya iya sai tsubbu da bokanci, cikin sana'ar bokancin nasa ne ya ba wa ƴarsa Ramma laƙanin INGOZOMANCI domin take karɓar haihuwa a kaf ƙauyan hakan a matsayin jarin da za ta yi sana'a. Hakan kuwa aka yi har ya koma ga Allah Gwaggo Ramma ce take karɓar haihuwar kowace mace da take cikin garin Gumurzu da sauran ƙauyukan yankin dan ko mace za ta mutu idan tana naƙuda, to babu wanda zai taimaka mata ta haihu sai dai a nemo Gwaggo Ramma.
Taju da Salele sun kasance yara ne marar sa ji, sai dai shi Salele ba ya ƙaunar karatu da zuwa makaranta, inda suka sha banban da Taju da yake son zuwa makaranta musamman ta boko sabo da yana so ya zama soja. Bayan ya kammala sakandire ya ce ya tafi birni domin ya je ya samo aikin soja tun da ya tafi sama da shekara guda sai yau ya dawo.
MAMAN AFRAH WHATSAPP 09013181851
*META FORCE ARZIƘI DAGA ALLAH*
ƳAR UWA SHIN BAKI DA LABARIN META FORCE? DA IRIN ƊINBIM ARZIƘIN DA AKE KWASHEWA A CIKINSA, YA AKA YI BAKI YI REGISTER BA? KO BAKI DA BUƘATAR KUƊAƊEN DA ZA KI YI HIDIMAR YAU DA KULLUM?
TO KI ZO NI MAMAN AFRAH NA ZO MIKI DA HANYAR SAMUN KUƊI TA WAYAR HANNUNKI KUƊIN YIN REGISTER KAWAI ZA KI TANADA 9K DUBU TARA DOMIN ANA YIN REGISTER DA DALA 5 NE SAI DAI ALLAH KAƊAI YA SAN IRIN RIBAR DA ZA KI SAMU DA KUMA ALKAIRAN DA YAKE CIKIN KASUWANCIN. IDAN KINA SO SHIGA KUMA DA GASKE KIKE KI MINI MAGANA A WANNAN NUMBER 09013181851 IDAN BA YI ZA KI YI BA KAR KI MINI MAGANA DAN BANA SON ƁATA LOKACI!
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: INGOZOMA
(Mai karɓar haihuwa)
NA
MAMAN AFRAH
F.C.W
GARGAƊI⚠️
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.
Page 7️⃣➡️8️⃣
*Dawo wa daga labari.*
Tsoron da su Malam Mammani suke ji ne ya ragu ganin Taju da kayan sojoji sun san kuwa dole fatallu ta ji tsoron bindiga. Wata ajiyar zuciya mai ƙarfi suka saki a tare dan suna ganin ai kakarsu ta yanke saƙa.
"Mamaki kwalli a kunne, yau kuma Taju ne ya dawo" Mai Gari ya faɗa a ransa cikin murna dan babu wani abu da ya daɗaɗa masa rai sama da ganin Taju da kayan sojoji kuma a lokacin da yake cikin halin buƙatar taimako.
Cikin sauri Malam Mammani da Mai Gari suka shiga ƙoƙarin tashi sai dai Malam Mammani gabaɗaya ya sha'afa da hannunsa na dama da ke ƙulle a jigon dabobi dan haka zai tashi tsaye sai ya ji hannun a maƙale a take ya shiga fitar da hannun dan yanzu tun da halin da suke ciki ya zo ƙarshe to kuwa burinsa bai wuce ya gan shi a gaban matarsa da ya baro ta a cikin halin naƙuda ba.
Mai Gari ko ta kan Malam Mammani bai bi ba ya nufi wajen su Taju har yana neman yin tuntuɓe, dan shi yana ganin shikenan waraka ta zo masa wai mazaunan matar mai bayar da maganin wuta ya ƙone.
"Taju, taɓ lallai abu rabo ne tsintar ƙwan jaki, kai ne wannan" Ya faɗa yana dab da ƙarasowa wajen su Taju har ya kusa ƙarasa wa kamar wanda aka ce ya tsaya ai kuwa ya ja tunga ya shiga rafkawa Gwaggo Ramma kira.
"Ramma! Ramma! Ramma, Salele, Salele Salelee" Mai Gari da ya wawake dogon maƙogwaronsa ya shiga faɗa ko jan numfashi ba ya yi.
"Kai jama'a, a yi a gama ai ya fi a ƙarasa gobe, in banda dai lokacin da mage take wuri ɓera ba ya wasa ta yaya kai da kake hannun fatallu za ka shiga kiran sunana son a gano maɓoyata a zo a tafi da ni to wallahi ta Allah ba taka ba, dan wallahi sai dai a yi abin da za a yi wai mahaukaci ya ɗau rigar kura dan wallahi wanda za shi sama ya taka leda haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya kuma nan gani nan bari farar tumfafiya" Cewar Gwaggo Ramma tana ciko hannunta taf da dawar cikin duron da take ciki ta tura a bakinta, ta ƙara cunkusowa ta ƙara cusawa a bakin wai duk dan gudun kar ma ta yi suɓutar baki ta yi magana a jiyo ta. Ko kuma Mai Gari ya yi abin da za ta tausaya masa kar ta yi magana.
"Ramma" Ta ƙara tsinkayar muryarsa tamkar dai ba a tsakiyar dare yake kiran ba.
"Ka yi haƙuri Mai Gari tun da dai sa'i ya yi to sai dai mu ce Allah rahama maka, ya kai haske kabarinka, kuma mundahanar da ka sha yi da kayan jama'a talakawanka sai dai in ce Allah yafe maka" Ta faɗa a ranta lokacin da ta ji dawar bakinta wata har tana wuce mata maƙogwaro amma dan ƙarfin hali haka ta cigaba da daurewa dan a kan ta fito fatallu ta yi watanda da namanta ko ta kashe ta ma lokaci guda gwara ta cigaba da zama a cikin dawar. Dan da ta ji ma kiran Mai Garin yana ƙara kaɗa mata hanjin cikinta sai ta cusa fuskarta a cikin dawar ya zamana numfashi ma dakyar take shaƙa.
Mai Gari kuwa jin Gwaggo bata amsa ba sai ya ƙara mayar da akalar kiran kwacakwam ga Salele.
Salele da yake ta faman yin sujada a kan katifarsa har lokacin bai dakata ba, dan yanzu ko shi kansa bai san iya adadin sujadar da ya yi ba, jin muryar kankansa Mai Gari yana kiran sunnansa a take ya kasa dungura goshin nasa.
"Wallahi kai dai mutumin nan an yi ɗan nema wallahi, haka kawai dan son ka ɓallo mini ruwa za kake kirana kuna can cikin halin ƙaƙanika yi,