Showing 30001 words to 33000 words out of 44948 words
Chapter 11 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt
ya ɗumame ba ita kwanciyar hankalinta ɗaya ta bar ɗakin kar ta je Laila ta mata hukunci.
Laila kuwa lokacin da Gwaggo take bayanin idanunta a rufe suke tana sauke lumfashi da sauri da sauri tamkar mai naƙudar da ta haihu yanzu, sabo da fitar tusar shi ne samun lafiyar ta da haka ba ta ma san abin da Gwagho take faɗa ba.
"Ramma kin ganni manne da mazaunan ranta ya daɗe, tun ɗazu take sakin iska kamar tayar motar lodin shanu, in ban da ma duk nisan tashin tsuntsu sai sama ta ga bayansa ta yaya za a yi matar nan ta danne ni, take sakin iska a kaina ina Mai Gari, yau na tabbatar duk girman dutse bai kai ƙaramin goro amfani ba, amma dai yau na ga fallasa auren bashi domin kuwa wayon a ci ne ya sa aka kori kare daga bakin ɗinya" Cewar Mai Gari a zuciyarsa yana danne hawayen da ke ƙoƙarin kwaranyo masa dan shi haƙiƙa ya san alhakin mutane ne da suke ɗauka, ya sa Allah ya kawo matar nan take azabtar da su.
"Gwaggo kin gammu nan fa daga Malam har ni da kuma Taju muna karɓar gashin ƙuma, lallai ba a yi wa uwar kwarto gorin ɗa, ko ba jima ko ba daɗe sai ya dire mata nashi" Salele ma ya faɗa a ransa yana jin nauyin Laila tamkar an ɗora musu duron ruwa.
Gwaggo kuwa ko waiwaye ba ta yi ba, ta juya ta nufi bakin ƙofa za ya fice daga ɗakin, har zaninta yana kuncewa tana kamowa ta riƙe da hannu ɗaya dan ɗaya hannun kayan aikin INGOZOMANCIN ta ne.
"Ina za ki je kuma" Ta tsinkayi muryar Laila a kunhuwanta tana dab da fita daga ɗakin" Wani uban birki Gwaggo ta ja tamkar motar da ta kusa faɗawa kwalbati. Laila kuwa lokacin da ta daddage ta tashi tsaye domin kuwa ta gama yin abin da ya kawo ta, tashin ta ke da wuya ta hangi Gwaggo tana shirin fita daga ɗakin, dan ita har ga Allah ba ta san Gwaggo ta shigo ba ma.
"Dama yaron albarka na kawo miki, wannan yaro mai ɗan karen kirki ko nauyi bashi da shi shafalfal tamkar na goyi leda, ga shi tun da muka je har na karɓi haihuwar nan ko kuka bai yi ba yana ta baccinsa" Gwaggo ta samu kanta da faɗar hakan dan maganar da Laila ta yi ya nuna mata ba ta ma ji abin da ta faɗa ɗazu ba.
"Zan sakko" Cewar Nasir da ya tashi daga bacci yanzu.
"Ka ga ɗan halak ya ƙi ambato, ashe ma kana kan hanyar tashi daga bacci ni duk tunanina ma baka tashi ba" Gwaggo ta faɗa, kai da ka ganta ka san babu nutsuwa a tare da ita, dan dama har yanzu bata gama dawowa hayyacinta ba daga abin da jaririn gidan Malam Mammani ya musu ba yanzu kuma ta dawo ta tarar da wani sabon salo wai kiran sallah da usur, Dariyar yaƙe ta saki dan ita kwata-kwata ta ƙi jinin haɗa hanya da Laila ko da kuwa ta magana ce,
"Mu je ɗakina ki sauke shi" Tun kan Laila ta rufe bakinta Gwaggo ta juya cikin sauri ta fita duk da bata san ma ina ne ɗakin na Laila ba amma dai tun da ta san iya ɗakuna biyu ne a gidan to kuwa kenan ɗakin ita Gwaggon shi ne a matsayin ɗakin da Laila ta ɗauka a matsayin nata.
"To ni ƴasu yanzu a ina zan ke kwana ni Ramma, ba dai nufin matar nan ba a ɗaki ɗaya za mu zauna ni da ita tun da mu biyu ne mata ni da ita, haka kawai in je in ke shiga uku da abubuwan da za ta ke mini ko kuwa dai manufarta mu kwatsu a ɗaki laya da Salele da Mai Gari da Taju sai ka ce a gidan arna" Gwaggo ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta, sai dai ba ta buƙatar amsa yanzu kuma abin da take so bai wuce ta sauke yaron daga bayanta ba.
"Ki kai wa mijinki da jikokin ki taimakon gaggawa" Cewar Laika cikin halin ko in kula tana zaunawa a bakin gadon Gwaggo wanda ya bada saurin " ƙiƙar".
"To,to,to" Gwaggo ta faɗa dan son ganin an zauna lafiya, amma ba ta fahimci komai ba a maganar sai dai ta shiga ruɗani jin ta ce a kai musu taimakon gaggawa zuciyarta ba ta barta da tunanin abin da ya samu su Mai Gari da su Salelen ba.
Tana fitowa daga ɗakin ta sunkuya a waje tana danna bayanta da hannunta jin wata irin gajiya ta riƙe mata gadon baya, ba komai bane kuwa ya kawo hakan ba sai goyon Nasiru. Tana cikin hakan sai ta fara jiyo ana tari, ana kuma sakin wani nishi daga ɗakin Salele lamarin da ya ƙara jefa kwanyarta a kogin tunanin dan ita dai ba ta ga kowa a ɗakin ba hasali ma ta ɗauka ko su Mai Gari bayan ɗakuna Lailar ta mayar da su. Da ɗan sarsarfa ta nufi ɗakin tana shiga lokacin Salele ya miƙa hannu dakyar ya kunna fitila amma har lokacin babu wanda ya yi wani ƙwaƙƙwaran motsi, sun yi lifet a tsakar ɗakin.
Salati Gwaggo ta shiga rattabowa sabo da tunaninta sai ya bata cewar Laila fyaɗe ta yi wa maza guda uku, wato ta tirsasa su suka yi tarayya da ita hakan ya sanya ta ji kishin Mai Gari ya turnuƙe mata zuciya dan ita akwai kishi hakan ne ma ya sanya ba ta son Mai Gari ko da wasa ya raɓi wata mace, amma sai gashi yau a aikin banza a sadaka wata ta zo ta yi mu'amala da mijinta, a gefe guda kuma tana tausayin Salele amma ko kaɗan ba ta ji tausayin Taju ba dan tana ganin shi ya jaza musu halin da suke ciki, domin shi ya kawo musu Laila gida kuma dama ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka.
"La'ilaha illallahu, muhammadur rasulullahi S.A.W, ni Ramma yau na ga ɗan jijjiɓin hau zalla, yanzu shirmemiyar matar nan ta haike muku ku duka uku rigis sai ka ce ta samu wasu agwagi, fisabilillahi ina laifin ma ta samu ɗan maraƙe (Namijin saniya) Ko dai ta samu (Doki) Ai su ne daidai da ita amma ba mutane ba, yo ina dalili ina ɗan mafari wane ɗan adam ne zai iya da wannan mata, amma dan wulaƙanci gaida sirika da mazaunai shi ne ta zo har da Mai Gari ta haikewa gashi na sai nishi yake kamar an lodowa jaki kaya, to ƙur'anin Allah sai in ja carbi mai dubu in karanta mata addu'ar da za ta saka matantakar ta(HQ) Ta manne tamkar an saka ruwan dalma an rufe tillar kwanon silba, ko wurin ya koma kamar an saka sufagilu an nane kai ko ma wurin ya ɓace ɓat ta neme shi ta rasa
dan gani za ta yi babu ƙofar babu dalilinta, in ga nan gaba da wane wurin za ta yi wa wasu fyaɗe" Gwaggo ta faɗa a zuciyarta tana jin kamar ta koma ta shaƙe Laila a kan wannan tozarci da ta yi ko ma ta mata dukan kawo wuƙa sai an ƙwace ta amma hakan ba mai yowuwa bane domin kuwa shi faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi. A fili kuma sai ta nufi wajen nasu tana faɗin.
"Sannu Mai Gari, sannu Salele, ashe kuma ku haka abu ya auku, kai amma matar nan tausayinta da sauƙi, dan rashin imani auran mijin maƙociya, sai da ta ga kun jigata babu mamora sannan ta ƙyale ku, amma matar nan ta iya ganganci haihuwa da damina, sai da ta mayar da ku akwai ya babu kakar wajen uba, sannan ta bar ku, haba ni fa in ce ashe shi ya sa na zo na gama burunkaɗuwar maganata har zan fita sai a sannan ta ganni, ashe dai lokacin da nake maganar ba ta ma san ina yi ba yo tana huce gajiyar da ta tarawa kanta, tabbas na yarda kowa da kiwon da ya karɓe shi wai maƙocin mai akuya ya sayi kura, amma kai dai Taju an yi shegen yaro, ai ni bata birgeni ba da bata maka ligigif ba, ai na so rigi-rigi ta maka yadda nan gaba ko amfanuwa ba za ka yi ba, haka kawai ka ɗakko mana mace tausayinta da sauƙi ka kawo mana gida, ga shi a rana ɗaya duk tana neman mayar da ku mata -maza, yo mata maza mana, yadda ta yi kalaci da ku, ku duka ukun ai ba ƙaramin nakasta ku ta yi ba" Gwaggo da take maganar ƙasa-ƙasa tamkar tana raɗa ta faɗa dan gudun kar ta ɗaga murya a yi rashin sa'a Lailar ta jiyo ta.Ta faɗa tana ɗora hannunta a kan hannun Mai Gari da ya yi lifet ya yi reran hannuwan nasa kowanne ya kalli nasa wurin da ban.
"Ana tsoronka ɗan mayya, ya ce daga ni har uwata" Cewar Salele a zuciyarsa ganin yadda Gwaggon take magana tamkar an riƙe mata maƙoshi ita ala dole raɗa take ba ta so Laila ta ji.
"Ramma, Ramma, Ramma" Mai Gari ya faɗa cikin muryarsa da ba ta fita sabo da wahalar da ya sha.
"Na'am Mai Gari ka ganni a kusa da kai, sannu ka ji, sannu da dole, Allah sa zakkar jiki ne, wallahi ba zan ji haushinka ka ba, ai na san ba da son ranka ba ka aikata, dole uwar na ƙi aka maka, haka kawai, da na san abin da za ta aikata da tuni na dawo da wuri to sai dai a lokacin da mage take nan ɓera ba ya wasa, kuma dama ana marin mai rai ne dan matacce ya ji tsoro, dan dai hakan da ta yi ba abin ƙwarai bane tun da a yi a gama yau ya fi a ƙarasa gobe, kuma ni ma da kuke gani tun da na bar gidan nan, ba a hayyacina nake ba wallahi gamo muka yi dan ba na ce na yi ba tun da ba ni kaɗai ba ce, amma abin ba a cewa komai kuma da a ce INGOZOZANCIN nan ba gado bane wallahi da na watsar da shi daga yau, to amma abin sai ido bebiya ta auro makaɗi, amma kam tabbas yau na ga larura auren namiji da ƴaƴa. Sai dai na san komai nisan dare gari zai waye, kuma komai nisan jifa dole wata rana ya dawo ƙasa " Ta kai ƙarshen maganar tana sharɓar hawaye.
"Gwaggo wai duk warin nan da ya ciki ɗaki yake neman sumar da mutane ke bakya ji?" Salele ya yi ƙarfin faɗar hakan ganin Gwaggo ta dage sai zuba take kamar bishiyar kanya.
Hanci ta ɗaga sama, tana jan hancin wai ko za ta ji warin amma dai sai ba ta ji ba.
"Allah sarki Salele yo dama ɗakin da aka aiwatar da saɓon Allah, mai zai yi ban da wari, to da yake ni hancin nawa duk mura ta ƙudundune shi, ban da zuba kamar hancin tinkiya babu abin da yake" Babu wanda ya sake cewa uffan Taju ya shiga ƙoƙarin tashi zaune, duk da yau ba ita ce rana ta farko ba da Laila ta taɓa yin tusa a kansa amma dai tabbas yau ya jigata fiye da tunanin mai tunani. Tun da yake ƙoƙarin tashi Gwaggo take aika masa harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa, dan ta san hatta halin da gadon bayanta yake ciki na ƙagewa ta samu ne sanadin goyon Nasiru kuma duk Tajun ne ya jaza mata hakan dan haka a halin da ake ciki yanzu ji take tamkar ta samo kulki ta shiga dukansa tamkar an aiko ta.
"Matso ki yi aikin lada Ramma, taimaka mini Ramma" Cewar Mai Gari da yake baza hannuwa shi a dole ta taimaka masa ya tashi zaune.
"Kai gaskiya matar nan ta muku aika-aika ba aiki ba ma" Gwaggo ta faɗa cikin alhinin zaton ta na fyaɗe Laila ta musu, ba ta san cewa tarzomar sakin tusa a kan su ne kaɗai ya haifar da halin da suke ciki ba. Haka ta kama Mai Gari ta ɗaga shi da taimakon nata ya tashi zaune, har lokacin yana sakin numfarfashi tamkar wanda yake gargarar mutuwa.
"Ramma, Ramma, Ramm"
"Haba Mai Gari ya kake rafka mini kira kamar wani makaho bayan gani nan muraran a gabanka, kana gani to kiran kuma na mene ne kake yi tamkar za ka ari baki"
"Ramma duba mini wuyan nan nawa ki gani, maƙogwarona yana wurin ko kuwa ya fincike"
"Na dawo in ji ɗan yawon duniya, da tada zaune tsaye naman asalin amarya a wajen ɗaurin aure, yaya ana zancen fyaɗe kai amma ba ta jikin naka kake ba kar a je ma ko ta maka lahani amma kana zancen ko maƙogwaronka ya fincike sai ka ce kan keken ɗinki" Ta faɗa tana masa kallon mamaki ganin bai tanka mata ba ta sake cewa.
"Ko dai mansileta za ka shafa ko ka ji dama-dama yo ai dama in lela ta ƙiya sai a koma caca" Gwaggo ta faɗa dan ita har yanzu ta ɗauka fyaɗe aka musu.
"Kai amma gaskiya Gwaggo kin iya shiga shari ba shanu sai ka ce a shirin film za a ce an mana fyaɗe sai ka ce wasu mata, yo ai mace ce ake yi wa fyaɗe amma namiji kuwa fa, ko dan shi ma idan aka tirsasa shi duk ana kan hanyar cewa fyaɗen aka yi" Taju da yake gyara zamansa ya faɗa a ransa yana jiran yaga yadda doguwar diramar za ta kasance.
"Ni dai na fi ji da maƙogwaron nawa, tun da daga nan nake samun haɗiyar abinci da ruwa, ki duba mini dan wallahi wajen muƙamuƙin nan nawa kamar ana yin faskare" Mai Gari ya faɗa yana miƙa hannu wajen saitin muƙamuƙin nashi yana nuna mata.
"Ana maganar masarrafar aure, kai kana batun maƙogwaro" Gwaggo ya faɗa a zuciyarta.
"Hatta kaina ma sai in ke jin kamar ya mugaɗe, fatana ɗaya kar in koma tamkar ɗan ruwan mai mogaɗaɗɗan kai" Ya faɗa cikin muryarsa da yake magana ba ta fita."Kai dai ana ga yaƙi kana ga ƙura, kai da ake maganar mafitsara amma kana maganar maƙoshi da maƙogwaro ko dai mai ɗungurugum ta muki ku haihuwa har hanji" Gwaggo ta faɗa tana kama haɓa.
"Gwaggo duk wannan abin da kike faɗa fa ba shi da nasaba da abin da ya faru, ba wani abu bane fa illa zaman ƴan bori da ta yi a kawunanmu ta ringa sakin iskar tusa kamar an buɗe salansar babbar mota" Salele da ya yi nasarar samun tashi zaune ya faɗa yana ɗan yamutsa fuska jin duk wuyansa yana ciwo har kansa ma sarawa yake yi.
"Zaman ƴan bori, yanzu sabo da kawai ta yi zaman ƴan borin a kan ku kuke wannan baloƙoƙon?"
MAMAN AFRAH 09013181851
*Littafin Ungozoma 500 ne ga mai buƙata zai iya biyan 400 kafin mu gama free pages, za mu gama free pages a page 26 idan na gama free pages zai koma 500. Za a biya ta acc ɗin Fa'iza abubakar 9030283375 opay bank* shaidar biya ta 09013181851
[8/19, 17:57] Mom mashkur & Afrah: UNGOZOMA
(Mai karɓar hihuwa)
NA
MAMAN AFRAH
F.C.W
GARGAƊI⚠️
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ta kowace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowace kafa ba sai da izinina a kiyaye.
Ina mata ƴan ƙwalisa, babbar mace alkyabbar mata, macen mai gyara ita wacce ta isa da miji su o'o sai dai su ga ƙeyar mijinta idan ya wuce amma basu ishe shi kallo ba domin babu abin da za su nuna mata. Gyaran gashi babbar martaba ce da take ɗaga darajar mace, musamman kayan gyaran gashin MAMAN ZEE da ya yi fice a ko ina ake labarinsa. Gani ya kori ji sai an gwada akan san na ƙwarai siyan na gari mayar da kuɗi gida💃💃💃💃💃💃💃💃
Hadaddu Kuma ingantattun kayan gyaran gashin mamanzee(chebe hair set)
Wadanda suke dawowa da martabar gashin Kai komai lalacewarsa biiznillahi Rabbi
Ga kyau ga inganci ga saukin kudi muddin kika fara amfani da kayammu sekindawo Mana da kyakkyawan labari
Kanki zeyi kyau ya rika sheki yayi tsayi yayi laushi duk matsalar da ke cikin kanki zata kau in sha Allah
Munada set complete
Kuma Muna Bada pieces
Haka Kuma Muna Bada Sari
Muna turawa akowanne gari kike Kuma Ako wacce kasa kike
Phone number *08079130166*
Page1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣
*MALAM MAMMANI*
Da rarrafe Malam Mammani ya iya tahowa daga ɗakin, rarrafan ma dakyar yake iya jan gwiwarsa dan duk ya ruɗe da ganin wannan ibtila'in. Yana zuwa falon yake jin ƙaran nishi-nishi a bayansa alamar ana binsa ɗif ya yi ya tsaya a da rarrafan dan cikinsa har ya murɗa masa dan tunani ɗaya ne ya fara zuwa masa, na ɗayan biyu ko dai gawar ce take biye da shi ko kuma jaririn ne ya sake fitowa daga cikin zai masa taƙidaranci. Daga inda ya tsaya bai motsa ba sai bakinsa da yake ta kai kawo da shi kansa bai san abin da yake furtawa ba ga uwa uba ruɗanin da ya baibaye shi dan ya kasa juyawa bare ya tabbatar da abin da yake biye da shi. A take ya samu nasarar fara jero kalmar shahada domin samun ya cika da imani dan a ransa ya fara tunanin ajalinsa ne zai sauka, dan jira kawai yake ya ji gawar ko jaririn ya damƙi wuya ko bayansa. Jin motsin da nishin ya matso daf da shi sai ya ji kamar ya zura da gudu ya tsira amma ina! Ya san gwiwa da hannunsa ba za su bashi damar hakan ba dan ba ya jin ƙarfin ko misƙala zarratin da har zai iya taɓuka wani abu.
Ta wutsiyar ido ya fara ɗan kallon saitin bayansa cikin firgici tunanin abin da zai je ya zo wanda zai yi tozali da shi, sai dai ganin Kaka tana rarrafowa daga ita sai ɗan tofi (Siket ɗinsu na tsofaffi) Zaninta kuwa yana rataye a