Showing 42001 words to 44948 words out of 44948 words

Chapter 15 - UNGOZOMA Book Complete Original by Maman AFRAH F.txt

29 Nov 2024

1528

gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅


Page2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣




Gwaggo tana buɗe gida ta ga mai unguwar gabas Malam Lawandi, shi da babban ɗansa Audu matashin saurayi ne.


"Ina wuni Malam Lawandi" Gwaggo ta faɗa tana muzurai ita ba dan ba dan ba da ta daina INGOZOMANCIN nan dan dai kawai babu yadda za ta yi ne.


"Haba Ramma ai gaisuwa ma ƴar ta yi daɗi ce Zuwai da Talatu suna can hajaran majaran kamar ba sa yi ba naƙuda kowacce haihuwa ta zo gadan-gadan amma ke kina ta gaisuwa" Ya faɗa a ruɗe dan shi gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake, shi kuma Audu ɗansa sai muzurai yake alamar daga bacci aka taso shi ba da son ransa ba. Gwaggo tana shirin yin magana Laila ta zo ta banko ƙofar gidan baram har ta kusa bige Gwaggon da take tsaye a kusa da jikin ƙofar ta matsa gefe da sauri ganin za a haɗa da hannunta, dariyar yaƙe kawai ta yi tana faɗin.


"Allah sarki to babu damuwa ai sai mu ɗunguma zuwa gidan naka, ashe su duka biyun ne ma suke naƙudar ai da na ga ita Zuwai cikin nata ya fi yin tirtsitsi zatona sai ta rigayi Talatu" Ta faɗa lokacin da Malam mai unguwar gabas ya shiga gaba ita da ɗan nasa Audu suka take masa baya.


"Ni Ramma ina ganin abin al'ajabi wai ango ya kwana da ƙunzugu, shikenan ni haka zan ke rayuwa kullum daga wannan sai wancan duk dare kowa yana can yana bacci amma ni in ƙare a gantale ina wa mata INGOZOMANCI ta faɗa a zuciyarta tana sakin wata ƙatuwar hamma ta rashin bacci da kuma guntuwar yunwar da take addabar ƴaƴan hanjinta.


"Ku dakata da tafiya zan baku tsaraba" Wata murya daga saman bishiyar kuka da take gefen hanya ta faɗa lokacin da suka zo setin ta. A sukwane Gwaggo ta yi taku ɗaya biyu sai ga ta sun jera da Malam Lawandi, su duka suka cure a wuri guda dan babu halin gudu, ba ta yi wata-wata ba ta ɗaga babbar rigarsa da take jikinsa ta shige sai ga kanta ya fito daga hannun babbar rigar.


Audu ma ganin haka sai ya shige cikin rigar Malam ɗin daga ɗaya gefen da yake ita Gwaggo ta gefen hannun hagu ta shiga, shi kuma sai ya shiga ta gefen hannun dama, sai ya zamana kan Malam Lawandi ne a tsakiya su kuma nasu yana gefe da gefe.


"Ku ungo tsarabar tsamiya a yi wa masu jego kunu, ga kanwa kuma in za a dama musu kunun kanwa" Aka sake faɗa daga saman bishiyar.


"Matan Baba ne dama masu naƙudar shi ya kamata ya karɓa musu tsarabar" Audu ya faɗa yana rarraba idanu.


"Wannan yaro da kaifin basira kake ni ma bani da haɗi da masu haihuwar INGOZOMANCI kawai zan je tun da ai ba laifi bane, duk cikin taimako ne gani na yi abin duniya mene ne ? Kaza ta jawo muzuru kwanan gida"Gwaggo ta faɗa tana kallon Audu muryarta har karkarwa take.


"Shikenan yau kashina ya bushe na yi angamo da fatalwar nan da ake ta labari" Malam Lawandi ya faɗa a ransa yana jin kamar ya kurma ihu.


"Malam ko in sakko in kawo maka" Aka faɗa dai daga saman bishiyar.


"To fa abin na yi ne an biyawa bazawara aikin hajji" Gwaggo ta faɗa a ranta tana jinjina maganar.


"Dan Allah ka mini rai, wallahi in haihuwar ce ma bakwa so a yi ina zuwa gidan sai kowacce a ce ta rufe mafitar ɗan nata (HQ) Da ɗan diras(Pant) su daina naƙudar, ko kuma a ɗinke musu wurin haihuwar shikenan ba sai sun haihu ba, amma ni ina zan kai tsamiya da kanwa a talatainin daren nan" Malam ya faɗa yana jan hanci dan ya ɗan kalli fatalwar saman bishiyar farin kaya ne a jikinta sai wata baƙar leda da take miƙowa.


"Haba kai kuwa ka karɓa mana so kake sai ya sakko kai da ka samu tsuntsu daga sama gashashshe? An hutashsheka da siya In ba abin rabo bane tsintar ƙwan jaki ta yaya haka za ta faru" Gwaggo ta faɗa tana fatan Malam Lawandi ya karɓo ledar kar abin ya shafe su gaba ɗaya.


"Ke kuwa Ramma ki karɓarwa ƴan uwanki mata saƙon nan mana, kin ga ai abin babbane INGOZOMA da adda"


"Eh Gwaggo Ramma" Audu ya faɗa dan shi zuwa lokacin fitsari ya fara sirnano masa saboda tsurewar da ya yi.


"Baba dan Allah ka karɓi tsamiyar nan da kanwa kar fatalwar nan ta sakko kusa da mu" Audu ya faɗa cikin raɗa-raɗa


"Babu abin da zai sa in karɓi abu a hannun fatalwa, kai ba ɗana bane ka wakilce ni mana"


"Baba kai fa ka sha miya ni kuwa yanzu nake ganiyar shekaruna"


"To dan ubanka ba miya ba ko kukar kaɗi zalla na haɗiya ba zan karɓa ba, kai ko ma baishire kukar kanta na cinye ba zan karɓa ba, kuma an ce maka duk tsufan mutum yana son mutuwa ne" Shi ma ya faɗa duk cikin raɗa. Gwaggo kuwa idanunta a kafe a bishiyar nan ganin fatalwar ta fara tasowa daga saman bishiyar a saman iska.


"Ƙalu innnalillahi wa inna ilaihir raji'un abin sai ido bebiya ta auri makaɗi, amma dai Malam Lawandi da ka sako ni a wannan matsala ka takaice ni kuma ban yafe muku ba an ce da karuwa hayo gado, dama ni ma ganganci ne haihuwa damuna" Gwaggo ta faɗa a zuciyarta. Gwaggo da Audu ganin fatalwar tana neman sakkowa da sauri suka ƙanƙame Malam Lawandi da ya buɗe baki yawu yana kwaranya shi bai ma san ma'anar buɗe bakin yawu yake zuba ba shi dai ya tsinci kansa ne da aikata haka.


"Allah ka yafe mini na rungumi mijin da ba nawa ba, wuya in ji tsula wallahi ba dan ana yanayin tsoro ba ba zan iya rungume mijin Zuwai da Talatu ba suna can a halin rayuwa ko mutuwa suna naƙuda a ce ni ina maƙure da jikin mijin su kamar wata kyanwa abin na dubawa ne" Cewar Gwaggo a zuciyarta.


Gwaggo ganin abin ya sakko ƙasa sai dai ba wai ya dira a ƙasa bane kawai dai a saman iska yake, cikin rigar Malam ta ƙara shigewa har ta yi nasarar saka kan nata a wuyan rigar Malam Lawandi in da kansa yake sai ya zamana kawunan su ne su biyu a cikin wuyan rigar. Audu ma ganin za a yi babu shi sai ya turbutsa nasa kan shi ma Mai unguwa faɗi yake.


"Audu rigata ce fa ta ƙaramar sallah, ko baka gane shaddar ba, yau ma ɗaurin aure na je da ita da na dawo na rataye shi ne kiran nan, na gaggawa da aka mini na naƙudar su Zuwai na sako ta na taho dan Allah kar ka mini sanadiyyarta" Ya faɗa jin Audu yana tutsa kansa, ɓeeet ƙaran yavewar rigar Mai unguwa ta ziyarci kunnuwansa wanda sai a lokacin ne ma ya lura da kan Gwaggo duk a cikin wuyan rigar tashi.


"Oh Allah na shiga uku ni Lawandi Allah ka kawo mini agaji, ashe shi ya sa nake jin wuyan rigar ta matse ni, ashe har da kan matar Mai Gari a cikin wuyan rigar, shikenan sun nakasta mini rigar shaddata ta ƙaramar sallah shaddar shiga taro" Ya faɗa a ransa yana jin kamar ya yi kuka, musamman idan ya kalle su ta wutsiyar idanunsa ya ga kan nasu a ciki sai ciccira idanu suke musamman Audu. Su duka ukun sai a lokacin suka lura da kan fatalwar da yake gabansu na ƙwarangwal ne ba na mutum ba. A take Audu ya saka hannunsa na dama yana shafo hawayen da suka ɓalle masa tamkar an buɗe famfo sai kuma ya saka hannunsa na dama ya tara tafin hannun ya tara ruwan hawayen a cikin hannun, da shi kansa bai san dailin yin hakan ba tsabar tsoron da ya shiga ne. Malam Lawandi hannu biyu ya saka yana ta shafar kai tamkar mai alwala, haka yake shafar kan tun daga gaban goshin har sai ya kai ƙeya sai ya sake dawowa, sai kuma ya yi shaƙar hanci ya face ya sake yin wata shafar kan ya yi hakan ya maimaita sama da sau goma, kawai sai yi yake kamar wanda aka ba umarnin yin hakan.


Gwaggo Ramma tun da ta yi ido biyu da kan ƙwarangwal ta runtse ido ta buɗe ta tabbatar da ƙwarangwal ne ramin idanun ma babu komai a ciki a take ta buɗe idanun tare da sako hannunta, ita ma ta zame kan hijabinta ya dawo wuyanta babu shiri ta cire ɗankwalinta ta jefar ba ta ma san inda ya faɗa ba kitso kawai ta fara yi wa kanta da kanta sai ta kai rabin kitson sai kuma ta saka yatsunta ta tuje kitson, da yake dama ba wani kamuwa yake yi ba tsabar tsoro da fargaba ne ya sa ta rasa mai ma za ta yi. Wuyan rigar Malam Lawandi kuwa ya yage gaba ɗaya dan yanzu har wajen kafaɗarsu wuyan rigar ya je.


A hankali fatalwar ta ƙara matsowa gaban su, wanda hakan ya hassada su duka ukun suka ji saukar fitsari ba tare da burki ba, daga saitin Gwaggo ta tsaya har lokacin a kan iska take ƙafafunta a naɗe tamkar wacce take a zaune Gwaggo da numfashinta ma ya tsaya cak ganin ga ta ga fatalwa sai ta ji fatalwar ta kai hannu kan gashin kan nata ta ce


"Bari na miki kitson ko"


"Yau na ga abu banbarakwai wai namiji da suna Hajara, in ba dan fallasa auren bashi ba, ni cewa na yi ki mini kitso ki bar ni mana in yi da kaina, ai guntun gatarinka ya fi sari ka bani, duk da dai na san idan makaho ya ce a yi wasan jifa to ya taka dutsi ne amma dai kai ka faɗa? Uwar sarki a doki ai kura ma ta san gidan mai babbar sanda sai dai kamar da gaske wai karuwa ta ga noman ɗan koli" Gwaggo ta faɗa a ranta jikinta yana karkarwa jin hannun fatalwar ya taɓa gashin kanta, da alama dai da gaske fatalwar kitson za ta mata.


"Wa ƙulna ya naru kuni bardan wa salaman ala ibarahim" Gwaggo ta daddage ƙarfinta ta faɗi addu'ar da ake tofawa mutum a wajen ƙuna idan ya ƙone ita kanta dakyar ta yi yaƙi da baki da ƙwaƙwalwarta ta samu furta lafazin, duk da muryarta tana rawa har da disko ma. Fisgar gashin fatalwar ta yi da ƙarfi sai kuma ta sake shi yadda Gwaggo za ta ji a jikinta.


"Wayyo ni a garin nana wayyo ni, ni dodo na yi ya kai autan iya da baba har na fi" Gwaggo ta ƙara samun nasarar karanto wata waƙa daga cikin tatsuniya da ake yi wa yara, yadda jikinta yake karkarwa za ka ɗauka a cikin frezer aka saka ta ta ɗau mugun sanyi amma ba komai bane sai tsoron da take ciki.


Suuuu fatalwar ta tafi a kan iska ta tsaya a daidai kan Malam Lawandi da har lokacin yana ta shafar kai da shaƙar hanci ganin layi ya zo kansa bai san lokacin da ya ƙara ƙaimi wajen shafar kai da shaƙar hancin ba, ganin tana dab da shi sai ma ya ƙara haɗa wa da ƙwaƙwalar kunne.


"Ai sai an yi shaƙar hanci ake wanke fuska sai kuma a wanke hannu sannan a yi shafar kai sai kuma ƙwaƙwalar kunne ya biyo baya"


"Allah bada lada!"


"Bari ka gani" Cewar fatalwar tana miƙa hannun ta da Malam Lawandi ya ji kamar wani ƙarfe sai uban farata zaƙo-zaƙo, ta shiga shafa masa fuskarsa tamkar dai tana masa wankin fuska.


"Iza waƙa'atil waƙi'eh, laisa li waƙa'atiha kazibe, kafidatur rafi'eh, iza rujjatur ardu rujje" Malam Lawandi ya shiga karanto suratul waƙi'a cikin kira'ar warshu yana karatun yana kuka. Kuka yake hawaye yana zuba kamar an buɗe bakin famfo ga shi har lokacin suna kaɓace a cikin babbar rigarsa su duka ukun Audu jin mahaifinsa yana karatu yana kuka sai shi ma ya shiga rusa nashi kukan, saboda an ce wai yi wa kanka hisabi kafin a yi maka, domin shi bai iya karatu ba sai shegen yawo sai gagara ya sa a gaba yau ga ranar addu'a da karatun alƙur'ani to shi da bai iya ba.


"Yau ni Audu, Aududu ɗan Malam na ga ta kaina, ga shi zan ga abin da ya turewa buzu naɗi, na yi saki na dafe wai mace ta rabu da mai kuɗi ta auri talaka, ga shi na ga fatalwar nan ta sako mu a gaba sai in da mai ya ƙare shiga motar mai taɓi" Ya faɗa yana rushewa da kuka tare da cigaba da tara hawayen nasa kamar yadda yake yi, dan ya fara sarewa tun da ya ga mahaifinsa ma da ya iya karatu ga shi yana yi yana kuka yana ganin kamar ma dakyar ya warto karatun saboda ruɗu bare kuma shi da cikakkiyar fatiha ma bai iya ba gwara ma wasu abin sai dai in ji ya yi ana faɗa.




Gefen Audu ta matsa ta tsaya ta ƙura masa idanunta da babu ƙwayar idanu a ciki abin da ya ƙara ruɗa masa ciki kenan har yana jin tamkar zai fara gudawa, dan zuwa lokacin ya ji fitsarin nasa ya ɗan ƙafe da alama ya ƙarar da fitsarin marar ta shi.


"Bari a tare maka haway... Tun kan ta ƙarasa faɗa Audu ya ce


"Na hutar da ke dan Allah ki mini rai"


"Haba ɗan samari kyakkyawa ai aiki bai kamaceka ba" Ta faɗa tana kai hannu ta shafo fuskar Audu.


"Baba dan Allah ka bani addu'a ko ta korar sheɗanun mutane ce ba sai ta sheɗanun aljannu ba, ni ko addu'ar saka tufafi ce ma ka bani, dan Allah Babana Allah dai ya maka albarka, Baba ka bani addu'ar shiga kabari in za a saka ni a ciki in yi dan kar in yi fatalwa in ke tsorata mutane in na mutu" Audu yake ta faɗa a gigice dan duk ya fita a hayyacinsa saboda tsabar tsoro.


"Wa alfaya sayyidaha ladal baab, ƙalu ma jaza'u man arada bi ahalika su'an illa an yusjana au azabun aliim" Malam Lawandi da ba ya ma fahimtar maganar ɗan nasa Audu yake janyo ayar da bai fara daga farkonta ba, shi kansa da za a saka masa wuƙa a wuya bai ma san a wace sura take ba ya sai ji ta zo masa a bakinsa ne.


"Ba zan iya ba Baba, ya kake faɗa mini karatun kamar kana mini ɗori, kai da za kake faɗa da ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya amma ka kamo aya mai wahalar faɗa dan Allah ka faɗo mai saukin faɗa ko ni ma na kuɓuta" Ya faɗa yana kuka yana karkarwa dan har lokacin hannun fatalwar yana kan fuskarsa tana share masa hawayen.




"Ma agne anhu maluhu mawakasab, sayyasla naran za ta lahab, wa mar'atuhu hammalatal haɗab" Malam Lawandi ya cigaba da karanto duk ayar da ta zo bakinsa.


"Zan bige kar ka bige birin kano azumi ne. Baba ka je gida ana nemanka rabu da ita ƙyale ta ƙashin miya ne babu" Audu da ya samu nasarar faɗar waƙar tashe da ake yi da azumi ya faɗa yana kuka.


"Wayyo Audu na sani ana nemana dama, to ka san dai halin da muka tsinci kanmu a ciki, amma na san dama dole a buƙace ni a gida musamman Zuwai da Talatu masu naƙuda amma babu yadda na iya ne faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi" Malam Lawandi da jin Audu ya ce Baba ka je gida ana nemanka karaf a kunnensa dan tunaninsa ko fatalwar za ta sallame shi ta ce ya tafi. Audu bai ma san ana yi ba wai kunu a maƙota, shi fatansa kawai ya zo kan gaɓar faɗar wani abu wanda zai sa fatalwar ta ɗauke hannunta daga fuskarsa kuma ta matsa daga wajensa ko ya daina jin tashin hankalin.


"Ma ji ma gani wai an rufe tsohuwa da ranta " Gwaggo ta faɗa a ranta jin Malam Lawandi yana neman hanyar kuɓuta.




"Assalamu alaikum, alaikum, alaikum a wannan rana. Za ki ɗauki ɗayansu, ɗayansu, ɗayansu a wannan rana, wane ɗayan kike so kike so, kike so a wannan rana za na baki INGOZO, INGOZO, INGOZOMA, sai ki haɗa da Baba da Baba da Baba a wannan rana, ni kuma sai ki bar ni, ki bar ni in tafi gida" Audu ya faro wata waƙar dan ya samu fatalwa ta ƙyale shi ya tafi.


"Ka ji ɗan ƙwal uba, ƙwal uba, ƙwal uba a wannan rana, sai dai ka bada ubanka, ubanka amma ba da ni ba" Gwaggo ma ta faɗa cikin baitin waƙar da Audu ya yi.


"Wallahi ba ni ba, ba ni ba , ba ni ba a wannan rana" Malam Lawandi ma ya karɓi baitin dan ganin ya janye kashin kajin da suke son yaɓa masa.


"Ku kaɗai za ta ɗauka dan kuntsufa a wannan rana" Audu ya faɗa.


Fatalwar dai ba ta ce komai ba ta dai ɗauke hannunta daga fuskar Audu ta yi gaba wato ta fara zagayowa ta bayansu, Audu kuma wani sanyi ya ji a ransa dan tunninsa fatalwar ta ji daɗin waƙarsa ne, kuma ta ɗauki shawararsa za ta ɗauki Gwaggo Ramma da Malam ta tafi da su shi ta ƙyale shi.


A NAN NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGES MAI BUƘATAR SHAƘATAWA DA LABARIN UNGOZOMA HAR ƘARSHE ZAI BIYA 500 TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09013181851 KAR KI BARI A YI BABU KE DAN LABARI YANZU AKA FARA ABIN DARIYA YANA GABA😂🙋‍♀️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login