Showing 150001 words to 153000 words out of 347556 words

Chapter 51 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

178

isace gareki nasu diyan idan sun isa mazan su kaisu Kano mana .
Kawai ki kwantar da hankalinki tafiya insha Allahu kamar kinyisa kin gamane su fadi su mutu don bakin ciki idan Allah ya dawo dake lafiya kibi yan iska da ruwan zamzam i mutum ya isa kada yasha.
Waisu yan bakin ciki basuma iya sheri ba ai dadin abin dai ko wacece ta samu wanan daman zai ji dda
Nan Gwaggo tayi ta lalashina tana kara ban baki tare da shawara wanda hakan yayi min amfani yakuma sa na aje zancencen ta a raina kan zan akan zan kasance karan dafi da suke kira min a kullun suna aibantani dashi.
Abincin data kawo min ta tillasta min tashi naci taliya yar hausace sai markaden souces da akayi yaji albasa da mangyada sosai naji dadin abinci na zauna ina ci ina tunane.
Na gama na tashi na fara gyara daki na packer komai a wuri daya wanda zai lalace na fitar naba gwaggo da Aliyu daya shigo yana tayani aikin muna hira har yake fada min yana son asashi karatu makarantar boko.
Nayi mai alkawarin cewa insha Allahu dana dawo daga saudiya zanje na roki malamin su ko zai yarda a sakashi makarantan.
Kwana uku kawai nayi tafiya ya taso gani kaduna ban tafi ba saida naga babana a gaban shi nashiga wurin screning shine rabuwa mu dashi yana ta zabga min adduan neman kariya da tsarin ubangiji.
Harda da kukana kamar ba zamu sake haduwa dashi ba haka natafi ina sheshekan kuka har mutane wasu suna kallona.
Yau ni fadimatu diyar baba garba nice ke zaune a cikin jirgin sama hanyar zuwa saudiya kuma ba tare da sisin kwabona ba kuma bana ubana ba.
A hankali na gyara zama ina lumshe idanu don babu kowa a sit dake gefena babu kowa a wurin yadda nake idona lumshe nake jin wani kamshi na shiga hancina a hankali.
Kamshine mai dadi irin na yan birni da suka goge suka waye suka san kan duniya jin hakan baisa na bude idona ba duk da dadin kamshin da nake ji har kasan raina.
Jin kamshin yayi yawa yasa na dan bude idanuna don ganin waye a kusa dani din zaune yake wanan kamshi haka wani farin mutum nagani zaune kusa dani din.
Zaikai kimanin shekara hamsin ko atba,in da wani abu yana saye da yadin maza fari mai zane fuskanshi yana da saje wanda bai boye shekarunsa da sauran kurciyarsa ba lokacin.
Fuskanshi saye da glass ya rike dan karamin kur,ani a hannunsa ya bude yana karatu a zuciyanshi da sauri na dan dukar da kaina kasa don kwarjinin da dattijon yai min a idona.
Yar jakata dana rike dake saman jikina na gyara rikewa a hankalin ina kara jan jikina daga yadda muke zaune duk da ba wani kusa muke ba a zaman namu din.
Sallamu alaikum ya fada jin hakan yasa na dan kalloshi kadan naga ni yakewa sallaman na amsa mashi tare da dora ina wuni akai don tashin dare mukayi lokacin.
Lafiya ya fada na koma yadda nake zaunen na kurawa sarautan Allah ido ina faman raraba idanu inama cikin jirgin kallon kwam.
Nan wata ma,aikaciyar jirgin tazo ta fara muna bayani har ta gama ta wuce akai sanarwan jirgi zai tashi a lokacin don haka a kashe waya a natsu kuma duk nayi yadda sukace ina ruwan bakauye a birni.
Nan dai jirgin ya tashi daidai lokacin da wanan mutumin yake addu,a ya shafa naga ya rufe kur, anin nasa ya gyara da kyau ya zauna yana dan jan tsuki.
Jin hakan yasa na dan kalloshi kadan computer ya dauko cikin wani jakkarshi ya bude yana dan dubawa ya maida hankalinshi sosai a kan abinda yakeyi din.
Haka muke zaund idona kuri akan kkmai dake gudana cikin jirgin don banjin komai har tunane da yake aikina a lokacin koshi ya gushe a zuciyana sai addu,a nake jerowa a zuciyana.
Can ya dan mika hannu a cikin jakar nasa dabino naga ya fito dashi ya aje a gefenshi kadan ya tsinka ya fara ci a hankali lokacinne ya dan kalloni yace min bissimillah ko ?
Na dan juyo na kalleshi yace ga dabino nayi saurin girgiza kai tare da sauke idona kasa nace nagode sai lokacin yayi magana yace dabinone fa zakice a,a da sauri haka ?
Kici don Allah yana da amfani sosai yana fadin hakan yana miko min jin hakan yasa na mika hannu na, karba nace nagode.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 6??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Duk abuncin da aka bamu a jirgi bai taba komai ba nima hakan ban taba ba shinema yayi min tayin naci mana na girgiza kai tare da fadin Alhamdullahi.
Tunane nayi bansan lokacin dana sauke wani irin ajiyan zuciya da har ya fito fili ba a lokacin hakan yasa wanan bawan Allah ya dan dago kai ya kalloni yana fadin.
Lafiya dai ko na dan juyo cikin murmushi ina fadin ba komai na kawar dakai da sauri ya duka yaci gaba da abinda yakeyi lokacin hakan yasa na kara natsuwa har dan barci ya dan daukeni.
Can kuma na falka yana zaune yayi shiru kafin yace dani are you single or marred haushin tambayan naji yasa banyi saurin bashi amsa ba lokacin.
Murmushi naji yayi tare da fadin kiyi hakkuri na dameki da tambaya ko nayi hakan ne don yawan ajiyan zuciya danaji kinayi tun zaman mu nan har a cikin mafalki.
Hakan yasa na gane cewa akwai abindake damuwan zuciyanki da kike yawan tunane wanda ke damunki kiyi hakkuri ba shishigi bane amma zan baki shawara akan ki rage don kinyi karama da irin hakan.
Nagode na fada don ko a haife ya haifeni kuma bansan koshi waye bama don haka babba babbane dole a bazashi girmansa idan bashi ya zubar da girman nasa ba.
Har yayi shiru kuma ya juyo yace dani zuwanki na farko ke nan saudiya na dan daga mashi kai kadan yace nagane hakane ai ta yanayin tsoron da kike nunawa.
Ki saki zuciyar ki babu abinda zai sameki lafiya kalau zamu isa insha Allahu kinga muna a tsakiyan teku yanzu addua da hamdallah ya kamata kinayi a zuciyar ki.
Daga yanzu kuma insha Allahu tsoron jirgi zai fita daga zuciyarki zakije ziyarane ko ibada zai kaiki koda yake naga alaman kamar hira ya isheki hakana don kamar na dameki ?
Zanje gun yan uwanane na fada zuwan ki na farko ke nan dai ya fada yana murmushi na dan daga mashi kai ba tare danayi magana ba hira sosai yake jana dashi sai na danji zuciyana ya sake har naji nadan sake a lokacin na manta da komai.
Kina min kama sosai da wata wace nasani sosai kusan yanayin ku da da komai dayane da ita don haka nake ganin ki kamar ita Allah sarki na fada.
Wani lokaci muyi shiru na dan lokaci mai tsawo wani lokaci kuma ya dauko min hira haka dai mukai zaman har lokacin da Allah ya kawo mu lafiya aka fara shirye shiryen sauka.
Don kafin a sanar wurinshi na kula da hakan saboda yawan duban lokacin dana kula yanayi lokaci lojacin yanzun kuma sai naga ya fara hada komai nasa ya mayar cikin wanan jakkar tasa daya riko.
Ganin hakan na kula kusan wasu da dama sun mike daga barcin da suka danyi lokacin haka yasa na juya ina kokarin saka wayata da dan tabarau dina dasu kawai ke a fili a lokacin .
Karbi wanan naji dadin zaman a kusa dake a wanan tafiyan don kin cire min nima damuwan dake a zuciyana a dan zaman mu tare sunana Abbas ibrahim gadon kaya ni dan kasuwane.
Kallon abinda yake mika min din nayi tare da kuma sauraren abinda yake fada min lokacin ya kara miko min da kyau na dan girgiza mashi kai tare da furta nagode a hankali.
Ai baki rokeni ba baki kuma nuna baki dashi ba alheri kawai nayi maki don Allah ki karba ya fada ya sake miko min kudin kai tsaye.
Haka yasa na dago kai wanan karon kallon ido da ido nayi masa na sauke kaina da sauri ina karba tare da fadin nagode ya danyi dan murmushi yace ko kin raina abinda ke cikine na karo maki ?
Da sauri na dago na dan kalleshi ni yake kallo nace a,a ha nagode kwarai sosai ina saka kudin a cikin jakata lokacin naji yace gashi har zamu sauka baki fada min sunan ki ba ?
Murmushin dole na kakaro nace Fatima Garba kd yace masha Allah karbi wanan ko wata rana mu gaisa ai don nasan da wuya yanzu ki ban phone nurmber din ki wanan zaisa ki kira mu gaisa.
Bakin karba ba duk na gaji dashi na karba na danbi katin da kallo ina karantawa da sauri na dago kai ciki mamaki ina kallonshi a daidai lokacin da matar jirgi ke sanar muna cewa kowa ya shirya jirgi zai sauka a baban birnin jidda ke nan.
Haka yasa banyi magana ba kuma na aje katin cikin jakkata ina daura belt kamar yadda naga tayi shima naji yana furta Alhamdullahi a fili.
A zuciyana nace ku manyane kun saba da irin wanan ya zama jinin jiki a gareku mukan sabon shigane a wajen nan arziki da rabo ya kawoni nan din ma yanzu.
Alhamdullahi mun sauka lafiya dama banje da wasu kaya masu yawa ba daga jakata na hannu sai yar karamar traveling bag dana saka laptop dina a cikinsa sai kuma kaya kala biyu don anban shawara kada naje da kaya da yawa saudiya don zan debo wasu acan koda gumamane kuwa sai nayi kayanyasu zuwa Nageria.
Alhamdullahi don mutunin nan Alh Abbas bai barni ba saida akai muna clearancen muka fito daga cikin airport din lokacin da kowa ke zirga zirgan neman nasa da kuma abin hawa a lokacin ne yayi min sallama ni kuma na kara mashi godiya na fito.
Ina dan waige waige don neman Al, amin da maman saudiya tace zaizo ya daukeni ina faman raraba ido daga bayana naji ana fadin Nageria ?
Muryan Al,amince don ba zan taba mancewa da muryansa ba na juyo ina dan murmushi tare da fadin saudiya ya kwashe da dariya yana fadin wai mafalki nake kece ko kuma dai zahiri nake kallon yarinyar nan ?
Waini kece kodai gizau idona ke mun ne gun wata nazo ban sani ba kada aimun duka a yanzu na kwashe da dariya ina fadin kaida kazama wani bulele a yanzu na rigasa fadan abinda yake son fada min din.
Hannu ya mika ya karbi jakkar dake hannuna muka jero muka bar wurin zuwa inda ya aje motarshi muka shiga tafiya ce mai nisa sosai ashe ya kaimu birnin madina muna tafe muna hira a tsakanin mu dagani sai shi a motar.
Tunane na fadayi lokaci guda yauni Bantun babace a cikin kasa mai tsarki da kafata ba a mafalki ba nida akewa kallon mara galihu kaskantata a idon jama, a musanman ma mutanen gidamu da har gobe suke min kallon mara gata da asali nake a idanunsu don kawai suna cikin yayansu sukuma yayan suna cikin iyayyensu.
Hakan yasa suke min kallon mara gata a cikinsu yasa tozarci da tsamgwama har yanzu suke sauke min shi a kaina duk abinda zai kai ya bata min rai shine burin da yan gidan mu suke fatan a wayi gari ace sun ganni a cikinshi.
Sai gas????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  hi ubangiji maji kan bayinsa ya tarfawa garina nono ni din kaf gidan mu Allah ya nufa in fara taka kasa mai tsarki a cikin fadin gidan namu.
Kuma ta dalilin arzikin wasu bayin Allah wanda hakan baisa sun barni hakan ba saida aka dauki zargin cewa tare da wani namiji zanyi tafiya ko kuma wani kato nabi ya kaini saudiya din don kawai ban da gata.
Ashe ba rashin uba bane da wasu ke fadin rashin gata ko kana da uban idan baka tare da mahaifiyanka shima akwai rashin gata a cikinsa wurin dan dan adam.
Dare yayi koda muka shiga madina garin yayi kamar mutum a cikin mafalki yake ganin kansa haka lalai komai wayewan dan adam akwai abinda zai gani kuma ya bashi mamaki a duniya.
Don gaba daya nidai bakauya na koma ina kallon ikon Allah don ban taba sanin abind muke jin labari ba gani yafi ji garine na kamilalun mutane wanda ba hayaniya a cikinsa.
Abin mamaki Al,amin haka yake kutsa kai da mota yana ratsa birnin zuwa masaukinsu na can har yakai wani gida me hawan sama biyu ya danna horn aka bude get ya kutsa kai cikin gidan kai tsaye.
Man muka fito motan zuwa ciki babu kowa a falon sai wasu mata irin mu bakake guda biyu suna ta aiyukan su a a kitchen suka leko don jin motsin mu suna muna sannu da zuwa sai suka kara komawa kitchen din kuma bayan mun gaisa dasu.
Falone dayaji wasu kalan kujeru na alfarma nan muka shiga dashi saiga daya matar muna shigowa ta zo dauke da ruwa ta aje a gaban mu .
Harshe suka juya dashi suna zuba larabci a tsakaninsu ina zaune na zuba ido sai kallon mamaki nake masu ina bin duk wanda yai magana da kallo a cikinsu.
Muna nan zaune hjy ta shigo gidan wai aishe suje sallah masallacine tana sallama tana raba ido taganni lokacin na mike naje yin alwala .
Ina fitowa falon muka hade a nan da ita da dan gudu gudu muka rungume juna sai kuka na fashe dashi don bansan lokacin dayazo min bama.
Dagoni tayi tana fadin Subbahanallahi meya faru haka meke faruwane kuma mamana Al,amin daga gefe yake magana a cikin larabci sai naga hjy ta dago min haba tana fadin keko uwata.
Ashe ba godiya ya kamata kiyiwa ubangiji ba kan hakan da Allah ya nufi sake saduwan mu kuma a nan birnin madina.
Lah lala kul na sake ganin ko jin hawaye a fuskanan nake saina bata maki rai kiyi sallah mu zauna muci abinci don kina da gajiya a jikinki na zaman jirgi.
Gefe inda suke sallah a falon ta nuna min da gabas din garin da zan fuskanta baka jin komai gida sai larabci ke tashi a tsakaninsu.
Nan dai na sallame kamar jira take in gama aka cika min gabana da abinci hade da madara mai kauri a wani farin gora dake da hoton shanu.
Yunwa nake ji sosai don haka na kai abincin da zumudi a bakina ina hadewa naji dan danonshi daban da namu na najeriya dana saba ci wanan ko magine ba a saka ba ko warin tafarnuwan dake tashi ya hanani cin don bansan yadda zan kara kai wani spoon a bakina ba.
Don haka saina wayence da daukan shi nono din don insha nan ma dai satab yake babu dandanon shuga ko kadan a cikinsa.
Haka na daure na hadiye har na kusa shanye kofi guda na aje koda hjy ta fito kallon kayan abincin tayi tana fadin mamana bakici abincin ba ai.
Nace naci na koshi wanka nake son yi nan ta nuna rashin jin dadin cin abincin da banyi ba sai kuma ta dauka kawai dai don ina da gajiyane a jikina na kasacin abincin lokacin.
Wani daki ta kaini mai kyau inda na samu kayana a cikin dakin an kai mun acan dakin ya hadu don komai akwai ga sanyi kamar cikin fridge mutum ya shiga.
Wani irin kasalane ya sauka min lokaci guda naji gajiya yana kara sauka min a hankali zama nayi bayan fitan matan danaji suna kira da Ummah hani
Na kai kwance rigingine a hankali ina kallon silin din dakin kafin na maida idona na runtse ina cigaba da sake sake a zuciyana.
A hakan barci mai nauyi yayi gaba dani lokaci guda har hjy ta shigo dakon ta sameni hhakan kwance ta kashe min wutan dakin dake kunne ta fice daga dakin tare da rufo min kofan.
Ban tashi farkawa ba sai hudu na asuba don ka,idane ko ban sallah saina tashi a lokacin saboda sabon da nayi da tashi a lokacin.
Mikewa nayi sai lokacin na tuno da inda nake wayata nayi amfani dashi wurin ganin haske nashiga bandaki zama sai a lokacin naga amfanin sani su ogana Abbas danayi a yanzu.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login