Showing 144001 words to 147000 words out of 347556 words

Chapter 49 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

180

Wani iri nake jin wanan labarin yana zo min a kunnena koya fahinci hakan ne yace kwarai kinji inata zuba haka ko akwai abinda nake so gareki ne nan gaba yasa nake fada maki wanan a yanzu.
Na sake kallon shi yace sosai kuwa duk da zaki danyi tafiyan da bamu da tabbas akansa amma nasan saboda karatun ki ba zaki dade a can ba yadda kika fada don Allah idan kin dawo zamuyi wanan maganan dake insha Allahu.
A daidai nan ya sha kwanan shiga erean da suke a kofan gidan ya tsaya kafin ya danna horn aka bude har lokacin ba wanda ya sake magana a cikin mu kuma dagani harshi din muka shiga gidan.
Lokacin na kalloshi nace ni ka barni a duhu kuma kaina ya daure da wanan maganan naka a yanzu yace nasani don shine ban maki bayani tun farko ba ko yanzu ma din don tafiyan nan danaji kince zakiyi yasa na fara wanan zancen dake a yanzu.
Naso sai nan gaba in fada maki manufata na nemoki don a zahirin gaskiya bawai na kawoki cikin mu bane don kawai ki muna talla a,a na kowakine bisa wani manufa da nake son cinmawa a rayuwan Bashir.
Ban fahince kaba dani kake nufin zakai amfani ka samu wani manufa taka a wurinshi kome yanzu ?
Na kasheshi da manyan idanuwana dana sauke masa ina masa kallo irin ta tuhumar mutum ga mugun nufi sai naga ya girgiza kai yayi murmushi yana fadin.
Haba kanwa yadda kike zato ko tsamani ba hakan bane dani dake zamuyi aikin nan ai kada ki manta na fada maki saboda shakuwana dashi mun koma kamar ciki daya muka fito dashi ma,ana kamar yan uwa a yanzu.
Ta yaya kike tuhumar cewa zan iya zaluntar shi ta hanyar hada kai dake wanan ba zai yuyu ba muje yanzu na kara fahintar zargina idan mun fito zan sanar dake komai in hakan kike sonji din.
Ajiyan zuciya na dan sauke yayin da ya bude motan ya fito nima na fito daga dayan gefe na daga kai ina kallon gidan mai hawa biyu da aka tsara mai gina kamar a turai mutum ya shiga kuma cikin garin Abuja.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

.KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
4?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Dan kararawan gidan ya danna wani matashi rike da sandan goge goge a hannusane ya bude kofan tare da turo kai yana gaida Abbas din da zuwa.
Ya amsa yana shiga daga ciki tare da tambayan matashi ko oga ya sauko yayi breakfast kuwa yace yana kallon fuskanshi bai fito ba tukun yana sama matashin ya bashi amsa.
Lokacin na karasa shigowa falon kai tsaye ina raraba idanu kamar an aikoni ina famam ba ido abinci sai bin ko ina nake don tsarin gidan yaban sha,awa sosai.
Don komai nagidan idan ba karya nayi ba farine kal a falon abin gwanin ban sha,awa kamar gidan wata yar gatan amarya naga abin.
Ya karaso yana fadin yana sama mai aikin ya kara fadin bayan mun shigo daga ciki sai dai bamu zauna ba Abbas din ya juyo yana fadin bari mu hau saman mu sameshi a can din.
Ya kara fadin ina ganin bai fito ba ko can din don yanzu na fito na gyara saman jin hakan yasa na dan kalloshi cikin mamaki muje Abbas din ya fada kafin na kare mamakin a zuciyana.
Matakalane irin na yanzu ba irin na gidan maman saudiya dana saba dashi ba wanan din an kerashi da karfe mai santsi da ties nake zato haka na hau a hankali ina takawa.
Muka samu wani falon kuma a sama wanan kuma nashi kalan kujerun dabanne su kuma milk color ne aka jera set din masu kyau dasu tsarin saina rasa wanda yafi kyau dashi dana falon kasan dana gani.
Saidai da alama falon kasan yafi dan kankanta da wanan din ki zauna in dubashi Abbas din ya fada yana shiga wani daki daya nufa nan nagane rashin girman wanan falon don akwai dakunan kwana a nan din.
Ina zaune nasha jinin jikina ina tunane barkatai a zuciyana naji muryanshi yana fadin son me zaka daukota ka kawo man ita har nan haka mukayi dakai ba inda zan fito yanzu na fadama.
Zubur na mike tsaye da zumar in fita don naji abinda ya fada a kunnena a kaina kuma jin an bude kofan yasa na dan juyo Abbas nagani ya fito yana ganin zan sauka yake fadin ina kuma zaki gashi fitowa ai.
Naji yace baice kazo dani gidansa ba ai yasa zan fita mai gida Allah ya gani ba roko nazoyi ba ko wani abu zuwa nayi kawai don in masa godiya tare da masa ya jikin nasa kafin in wuce shi kuma ya,,,,,
Shina gani ya fito daga dakin fuskashi a daure da alama barci yake a lokacin shi Abbas ya tadashi yasa yake fadan don yadda naga ya fito din yabini da wani kallo mai kama da ki kama da gargadin ki kama kanki a nan yarinya.
Ya kafeni da manyan idanuwanshi da suka rine launin ja yana tafiya har wurin kujera ya tsaya ya kalleni yace
Ke baki tafi bane ya fada daga inda yake tsaye a cikin muryan nan nasa dake magana da dan sauri sauri hakan nan hakan yasa cike da rauni ko tsana nace.
Ehh yanzun zan tafi shine yace baka da lafiya nace ya kawoni in gaida kai kafin in tafi din, ashema kuma ciwon ba sosai bane yadda yake nufi har na zata.
Zama yayi niyar yi don zaikai zaune din yaji na fadi hakan har ya yunkura zai zauna ina fadin hakan ya dan kage wuri daya yana kallona kafin kuma ya kai zaune din ba tare daya fadi komai ba.
Murmushi Abbas din yayi daga inda yake tsaye nima din kuma ban dawo na zauna a inda na tashi ba ina tsaye daga matakalan ina kallon su na sake fadan Allah ya bada lafiya ni zan tafi.
Fatima dawo ki zauna muyi breakfast kafin ki tafi Abbas ya fada har lokacin yana dan makale murmushi a fuskanshi don kada ya gani,a,a nagode yaya na fadama ai rana bana karya kumallo da safe haka sai rana ya danyi .
Amma ba a gidan nan ba tunda kin shigo dole sai kin karya kafin ki fita nan ya fada ba tare daya dago kai kallo inda nake ba ya bani amsa.
Wani dan abu ya danna yana magana da Abbas din ta fita batuna Abbas din ya zagoyo yana fadin zo kanwata ki zauna mu karya kinsan ba aiwa babba gardama kinji.
Ya dan dago yana min alaman inzo din kada inki zuwa hakan yasa na tako a hankali cikin mutuwan jiki zuwa kujeran dake kusa dani na zauna tare da dukar da kai ina wasa da yatsuna a gefen kujeran.
Shigowan mutum danaji yasa na dago manyan idanuwana na dan kallo wanda ke zuwan wani matashine na daban ba wanda muka sama a kofan yana aiki ba, shi wanan kana ganinsa zaka gane yarene kuma arne don sarkan cros dake wuyanshi rataye.
Plate ya dauko da niyar zuba muna sai ya dakatar dashi ta hanyan daga mai hannu da sauri ya daga yana furta sorry sir ya fita daga wurin shi da kansa ya jawo plate ya ajewa Abbas gaban shi kana ya dauko dayan ya bude abincin ya fara lodawa a ciki dankaline irish da wani ganye sai kwai daya zuba gefe daya sai daya kusa cika plate din .
Na dauka kanshi ya lodawa hakana sai gani nayi ya turo min plate din gabana yana fadin ka zuba muna muci ya koma ya maida bayanshi jikin kujera.
Faduwan gaba daga cikin zuciyana saida ya baiyana fili na dago kai ina mashi kallon mamaki idonshi a lumshe yake lokacin don haka na mayar da kallona kan Abbas dake murmushi.
Kanwa????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ta koyayi kadan na karo makine Abbas din ya fada yana bude kulan abincin ga wanan ma ai bai zuba maki ba ya kara fada yana son zubo min wai ferfesu insha kuma.
Jan plate din nayi alaman ya isa hakana yake fadin kici muje na saukeki idan na hada nawa jin hakan yasa na dan jawo plate din zuwa gabana na fara dan juya cokali ciki a hankali.
A hankali na dan saci kallonshi yana zaune yadda yaken ya dora hannu saman goshinshi kamar yana tunane ko gyangyadine a lokacin.
A hankali na dan diba nakai bakina abincin ba laifi yayi dadi sosai gaskiya amma ta ya zan zage haka a gabansu in kwashi abinci kamar wata wagila mara kamun kai dani.
Hakan yasa ina kai cibi ukku na aje na dauki kofi na dan tsiyayya ruwa zankai baki yake fadin well zuwan nan naku wani damane a garemu yanzu don jiyan nan na danyi wani tunane.
Ya kamata ace office din nan da zamu bude ya zamanto kuda kuke kaduna mu bude daku don a can ma din kusan zaikai wanan girma don hakan da kin dawo zai baki takarda na dindindin da zaki zama ma,aikaciyar mu ba wanan na contrac din ba da kike amfani dashi a yanzu ba.
Dariya ya kubcewa Abbas din dake cin abinci ya kalloshi yana fadin na fadi wani abinda ba daidai ba ke nan, da sauri yace kamar ya gani nayi kawai sa,an kanwata fatima yana da yawa a gurin ka.
Amma ai nafi kowa murna da jin hakan karona farko da naga kabawa wata mace muhinmanci tare da tausayawa irin haka ai abin farincikine wanan gareni .
Ban fahinci inda maganan ya dosa ba hakan yasa na dan gyara zama tare da kallon agogon dake falon yace lokaci na kurewa ko kanwata ?
Ina son in sauka kadunane kafin in koma zaria a yau din nan idan na isa kuma gashi ban tashi da wuriba yadda na zata zanyi din .
Kallon abincin dake gabana yayi yace wanan wa zaki barwashi a nan kinsan banda wanda zaici ragowa a gidan nan dai , ?
Kaima kasan rayi kokari duk da bata cin komai da safe haka gashi ta kusa cin rabin plate din ai tayi kokari sosai tabe baki yayi yana fadin wanan kuma kukuka sani kaida ita nidai na fada maku ka, idan gidana yanzu.
Mikewa Abbas din yayi ya nufi hanyan sauka kasa yake fadin ina zuwa kuma gun Ema zani ya bashi amsa ba tare da juyowa ba ya fice daga falon ya barmu a zaune.
Falon yayi shiru kamar babu wani rayuwa acikin sa lokacin dake numfash muryansane yasa na dan dago yana fadin for how long da kika san yan gidan Ambasardor dake saudiya ?
Wani kallo na danyi masa don in karacin wani abu a wurinsa sai naga bai ma dago kanshi ba hakan na bude baki nace dashi Almost three years zuwa four ke nan.
Kuma kinsan kowa na gidan ke nan hjy kawai na sani sai wasu daga cikin diyanta amma ba duka ba ke nan a wanan unguwar kuke kuma ?
Eh na fada sai yayi shiru zuwa can kuma sai naji yaja tsuki yana fadin da ina da iko dake ba inda zaki tafi a yanzu don banga dalilin da zaisa ki bar karatunki da komai naki ba zuwa wata kasan me zakije nema saudiya wani kallon mamaki na sake dago kai ina masa lokaci guda ?
Kafin na bashi amsa lokacin Abbas din ya shigo tare da mai aikin nan nasa daya kawo muna abincin yace pack it All ya fada yana zama mu tafine na fada ina mikewa tsaye , , ?
Ki bari ya gama ya kira azo a tafi dake don ku yaran yanzu kasada yai maku yawa kina zaki sauka kaduna kuma kina kokarin mikewa zuwa bin motar kasuwa a wanan lokacin.
Koda yake ba laifinki bane hakan kamar kin saba nake gani don ke ba abinda ya damu rayuwanki a yanzu sai abinda kike ganin daidaine kikeyi a rayuwan ki.
A lokacin zuciyata takawo min wuya ba zan iya controling din kaina daga abinda nake jin yana kokarin fada min a fakaice ba don kamar magana yake kokarin gasa min a hakan na dauki zancen shi.
Ba laifinka bane tun farko ninayi kuskuren fahintar ku a matsayin mutanen arziki masu kamala da mutunci a idona har na yarda da imanin ku farat daya.
A zaton ka don ina yar tallaka ko mai aiki a karkashinka hakan har yakai kai min mumunan zato a rayuwa yadda kake dauka sam ba hakan nake ba don nasan daraja da kimar kaina a ko ina na samu kaina kuwa.
Da kasan wanda ya sani zaka tambaya kaji wacece Bantu nasan a cikin goma tara zasu shedeni insha Allahu sam ban damu da arzikin mutum ko abin hannunsa ba.
Dan nazo aiki dakai har naga kirkinka gareni naji baka da lafiya naga rashin dacewa in wuce ba tare dana gaida kaiba shine zaisa ka dauke yar iska ko wulakanttana a idanunka wace bata san me takeyi ba.
Saudiyan da nace zanje ba wai wani abin asha zan tafiyi ba acan alheri da mutuncine zai kaini can yanzu don kamar uwa na dauki hjyn a zuciya yadda kuma nake kallon mutunciku a wurina yanzu kamar yan uwa na jini a gareni.
Tasowana ni kadai a gidan ba dan uwa ya saka min son duk wanda ya nuna yana tausayina koda shi din ya kansace ba da uwa bane a gareni nakan mututa mutum a matsayin da naga ya daukeni.
Wanan persanal issue din rayuwatace da har nake saurin yarda da mutum farat daya lokaci guda ta fuskan da mutum din ya daukeni dashi don haka banzo nan ba ta wani dalili sai dalilin kokarin kare mutuncina da kimata da nakewa rayuwata a yau.
Fatima kanwata zafine dake haka ashe meya faru kike wanan maganan haka cikin zafin rai ai gaskiya boss ya fada donke din mace ce kina bukatan kulawa ko yaushe.
Don haka inma wani abune karki dauka ko rainine ko wullakanci a gareki sam ba hakan muke nufi da ke ba don tun farko da mun gane hakan gareki mun auna fahintarki ta hanyoyi da dama mun san ke wacece a yanzu.
Shiyasa muma muka rikeki a cikin gaskiya babu ha, inci a zuciyarmu game dake kema kiyi nazari mana ki gane hakan a kanmu haka kawai ba zamu daukoki muna kokarin mannaki a jikin mu ba ba tare da munsan halinki ba ai.
Mun sani ke macece da take bukatan a taimaka mata na don da ganinki kin fito gidan tarbiya ba wani abin asha ko makusa a wurinki da zakiyi wanda ba daidai ba don haka kada ki fahince mu ta baibai damuwa dake yasa muka nuna maki hakan.
So be cool kada ki fahincemu ta baibai don Allah idan bamu damu dake ba ba zamu taba ko kallon inda kike ba Allah ne ya jefoki cikin rayuwan mu muyi tafiyan nan tare dake a yanzu so ki saki zuciyar ki da kowa a nan .
Don muma yadda kika dauke mu mun sani ba wani abu a cikin zuciyarki a tare damu a kanki tunda Abbas din ya fara magana ya soma cin abinci bai dago kai ya kalli kowan mu ba lokacin saida yaji yayi shiru yake fadin.
Da wanan dogon zancen da ka tsayayi gara ka tashi ku tafi kada ku batawa kanku lokaci a nan azo ba aga kowan mu a office ba a dauka wani abune babba yasa bamu fito ba.
A hankali na fara takawa ba tare da juyowa na kallesu ba bakin mota na tsaya ina bin gidan da kallo sai ga hawaye ina kokarin mayarwa ta hanya dan share fuskana muryan Abbas ne a gefe ashe yake fadin.
Kuka kuma kanwa akan me kike kuka yanzu kuma ina munyi maganan nan ya wuce an fahinci juna damuwa dake yasa ya furta hakan bada wani manufa ya fadi hakan gareki ba ai.
Kawai dai kukan yazo min don haka kai na girgiza mashi kawai ya bude motan gefen da zan shiga na zauna ya rufe ya zagaya zuwa inda zai zauna ya tayar da motan muka bar gidan saida muka hau titi da kyau yake fadin.
Bana fada maki ba kanwata na fada maki keta dabance wallahi kina da sa, a sosai a rayuwa ki ya dan kalloni yace kada kiyi mamaki idan kinji ina fadan hakan gareki.
Nan gaba zaki gane hakan zaki fahinceni so kada ki dauki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login