Showing 342001 words to 345000 words out of 347556 words

Chapter 115 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

181

Su mama guda taje zamfara suka kwana da yan uwan mama guda kuma taje abuja suma a can suka kwana wajen jeren sun dawo suna fadin irin abinda suka gani budan bakin ta cikin mutane sai cewa tayi duk wanan abinda kuke fadi kuma duk da haka gidan bantu yafi nasu.
Sau dubuma hjy balaraba ta fada tace gidan bintu ai duniyace don shi ake kira da aljannan duniya wanan gida ai santinshi bai karewa gare mu ko shekaran jiya saida Ibrahim yayi hiran wanan gidan.
Gashi ko tashi zasuyi wai ya sayi wani amma a cikin unguwa dayane zai dai dan kara matsawane kadan daga wanan gidan shuru tayi tana tunane kafin ta mike ta shige dakin su.
Mun gama da wanan sai kuma aka shiga sha,anin buki wanda yasa natako zuwa gidan mu tare da mukarrabaina gishir muka tsura da Samira har mama a tsakar gidan namu.
Basu da yadda zasuyi aka shiga gaishe gaishe na dai tsaya mun gaisa da mama a tsatsaye nayi mata ya karfin jiki tana amsawa na wuce ban tsaya kulataba ashe hakan yai mata zafi.
Mamane kecewa matar dake dauke da Abdallah kayo yaro mu gani tace a,a barci yakeyi idan yana barci ba,a tayar dashi tace tooo dama karab baninane ya kaini ai suka wuce suna biye dani basu ce komai ba.
Bin bayan matan dake biye dani a baya tana lokacin charaf a idon mama uwa tace iska na wahal da mai kayan kara fada da gaskiya kuma tsorne.
Tsuki tajawa mama ta mike ta shige dakinsu tace haka zaki kare da bakin ciki yar banza kadan kika gani idan sherine halinki.
Ba abinda take ji lokacin sai zallah bakin ciki na yadda taga wai yau Bantuce haka akewa fadanci irin na matan manya ga yadda bantu din tayi wani haske tayi kyau kamar ita ta zauna ta tsara kanta gaban mudubi.
Don baka taba cewa Bantu ce yar tsakar gida data sha wullakanci da gori wace suke dauka mara galihu a cikinsu wace bata da gata da asali yau ita Allah ya mayar hakan fiye da abinda ta dade tanawa kanta fata yau shi ubangiji ya mayar da Bantu din itako tama kara lalace yanzu fiye da da can baya da suka tsso.
Wani kululun bakin ciki taji ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ya tokare mata zuciya lokaci guda nan ta fara sake sake da mafalkin iska tana hango in batayi hankali ba kosu yan biyu nan da wani dan lokaci zasu zama wani abune a rayuwansu su barta nan.
Wanan ya tsaya mata a rai yadda ake fadin su yan biyu sunyi dacen dakuna kana kuma ana sakawa Bantu albarka sai take jin tankar itace ake sakawa magana.
Gashi an baketa a gefe daya ba a komai da ita kamar yadda ta nuna ba hannunta ciki da farko ta dauka za a bita sai gashi an shareta an mayar da ita banza da ita da babu duk daya a gidan.
Shigowan mahaifiyarta dakin ya katse mata tunane har uwar zata fita saita dakata ta kalli yar tace ke yanzu abinda kika daukarwa kanki ke nan ?
Ki ware kanki cikin yan uwa kina hadiyan bakin ciki kinyiwa kanki adalci ke nan yanzu kuma me nayi mama ta dago tana tambayan mahaifiyar nata rai bace itama.
Tace nikan bazan zubar da mutuncina ba don kwadayi kome Bantu ta zama haka me zata bani tunda bata fini ba niba irin masu wulakanta kansu bane don abin wani.
Oh muke nan ko muda muke bi mune yan kwadayin ko tace ni dai bazan bi bantu ba kema da kike bi meta taimakawa dakinki dashi har yanzu ta kullemu a rai tana bakin ciki damu.
Ke rufe min bakinki kinyi na farko ba zaki kara nabiyu ba bata min komai ba sai alheri idan rabona yazo wata rana ci zanyi ko wani dana yaci tunda abinta bai rufe mata ido ba.
Keda kika samu dawa kikaci gidan nan kullun cikin babu kike har yau din nan wayayi magana kan hakan dakikeyi sai kece zaki kawo wani zance a kan Bantu.
Tafice daga dakin tabar ta kwance tana maganganu ita kadai a dakin anyi buki sosai aka kai amare dakunan su ni banje ba don boss ya hanani zuwa wai zamu koma mu shirya zamu fita yace.
Nasha kira wajen hassana amma ban samu zuwa ba don ba lokaci yayiwa jamila da sadiya visa tare dasu mukaje don su ke dawainiya da Abdallah mun dawo gab ana zancen bukin gidansu.
Sai kuma hamkali ya dauku a nan kwatsam sai ga wayan hassana tana kuka zata kaduna a ce mama tana cikin wani hali tun bayan buki ta kwanta ciwo.
Zuwa rana kuma baba ya kirani yana sheda min halin da mama din take ciki yace sunje asibiti ance lalura ne sai anyi mata aiki an cire mata mahaifa in son samune.
Hankali dai ya dagu bansan
ya akayi ba sai ga Boss ya dawo yana fada min za a kawo mama asibiti nan garin Abuja sai ko gasu sun iso tare da ya Ahmed ya Altine da maman tudun wada.
Asibitin suka sauka da yamma mukaje ganinsu ya Altine duk ta fige ta zamo kamar an tsamo kaza a ruwa nake ganinta duk kunya ya kamani wai ace itace babban yarmu ina nan hassana suka shigo da mijinta.
Shike bayani aikin mama yana da wuya yanzune aka samu likitansa aikin zaikai million biyu da dan kai gaskiya bayin Allah nan a gode masu don in badon su ba sai dai ayi hakkuri.
Sai bayan fitan mu ya Altine tace aiba rokonsu mukayi ba balle yazo yana wanan maganan kuma ai ba mai mutuwa sai wanda kwanansa ya kare dama.
Altine kibar wanan maganan ko in debe maki albarka ke yaushe zaki hankali irin na mutane ko don ciwon ba a jikinki yake ba zaki furta hakan ai gaskiya ya fada bai fadi karya ba.
In ba haukan irin na Altine ba har yaushe zaka tsaya iri wanan haukan cikin wanan halinda muke ciki na tashin hankali haka ina wani baki garemu yanzu da zamu tsaya irin haukan nan na baya ai yanzu bamu da baki gun yarinyar nan sai fatan alheri don ta gama muna komai a duniya.
Kallon mamam tudun wada tayi cikin mamaki tace eh man ko mu muka haifeta ayau ya tsaya iya nan wanan abinda yarinyar nan ke muna rashin sani yakai kaza wuta ai da munsan hakan tun farko aida bamu nufeta da wani abu ba.
Damukayi din me muka tsunta a ciki yaya banda wahala daya biyo baya a yanzu in zakibi yar uwarki kibi yarda kowa yake biye da ita yake cin arziki kina ware.
Don fadan dayafi karfin ka sai idanu na daina ganin laifin su yan biyu a yanzu don sunyi amfani da iliminsu sun fimu hango abinda ke nan tunda wuri mu kuma mun kasa fahintarsu kan hakan.
A nan gidan mu kuma abinci kai da kai muna kai komai da zasu bukata muna kaimasu tankar dai mahaifiya haka nakewa mama gata idan naje zan tsaya in lalasheta in bata magana in kwantar mata da hankali.
Har akai aiki lafiya muna kaida koma ga mama ta fara jin sauki yan gida sukazo dubanta kwana daya suka koma gida.
Banje gun wasu event ba saboda jikin mama sai wajen mothers day koshi girshi suka ganni na shigo tare da yarana da mukarabai na su iy masu bina .
Abinda yasa suka gane don ganin yadda ake shirya muna wajen da zamu zauna an tayar da wasu an kawo kujeru da sauri anjera muna an aje komai special hakan ya jawo hankalin mutane suna son ganin mai shigowa wajen.
Duk su hjy laila dake zaune ba ai masu hakan ba suka zubo ido cikin mamaki suna kallon sit din can sai gamu mun shigo ina tsakiya suna bina nan hankalin jama,a ya dawo kan mu.
Mc din take muna maraba take sanar dani ko wacece a wajen wasu ke fadin dama matar nan kayan jikina kawai na miliyoyin naira zai nuna maka nice ga zubin halittana koke mace yar uwana zaki yaba dashi don banda inda zaki kushe min saidai dan abinda ba,a rasa ba don dole akwashi.
Ransu hjy laila ya sosu dama gata da bakin cikin Bashir a ranta na yadda ya hanata shiga sha,anin koma ga bukin yasa ta kara kullashi a zuciyanta duk data fahinci sauran sunyi sanyi ga bakarsu amma hakan baisa gwiwanta ya sare ba ita don yanzu take da ga dan iskan yaron nan da baijin sara da suka.
An fito da Amarya suka fito su iyayyen ango suna watsi da kudi suna iya shegen manyan mata ban tashi ba ina zaune don dama nikan ba gwanan bidia bace ko kadan ko na bukina na wahala akan irin yadda ake fito da amarya din.
Ina mikewa bayan an rage yawa har amarya ta juta zata koma ta zauna suna ganin sun burgeni a wajen sai gashi mc tana fadin amarya dawo ba yanzu ba don ga big sister nan tafe ta taso zuwa wurinki da alherin ta.
Tare da jamila da sadiya sai hassana da Ussai a tare dani mun burge kowa mun haska muka fito tsaye sukayi na fara ruwan doles dama don haka ya bani su nakuma kashe na daga mashi suna mc kuma na zugawa.
Muna gamawa su iya na mikewa muka taso muka bar wajen taron don yamma yayi a lokacin nan muka dawo mukaci abinci ana maida fadi abinda akayi wajen wayana yayi kara na dauko sakone daga wajen maigidan.
Hjy ta kin kyauta min yau kin hauka hjy laila har tayi kara a gaban mutane anji ta kin fita kin barsu da kunya kin kyauta min gimbiyata kin mun komai ki gaida min dasu sister.
Nayi dariya ina nuna masu nan muka kwashe da dariya muka shiga hiransu bamu sake haduwa ba sai wajen dinner nan kan tare dashi mukazo da Abbas Yusuf hamza jafar mijin hassana da Auwal mijin Usaina table biyu aka ware masa muka zauna kowa da matanshi.
Abu kamar gaiyya kamar hauka kamar kuma gasa haka akaita abubuwa kamar kowa na jirace da dan uwa a wajen yan kaduna sinzo sai don iyayyen amarya da ango duk daga sako ya shigo mai naga yana duban wayan nasa kafin ya yafito Abbas suka danyi magana sai Abbas din ya tashi da sauri ya fita daga holl din.
Zuwa can suma suka mike suka barmu a waje iya mu mata ina kule da hakan nakej ganin yan family din nasutyjjjjj suna fita daya bayan daya nan nasan akwai magana.
Can aka fara sanarwa jama,a ana basu hakkurin da abindake faruwa a wajen nan dai kus kus ya tashi ga mazajen mujama,mutum daya bai dawo cikinsu ba can sai gaYusuf yazo yana fadin cewa mu tashi a maidamu gida an samu matsala jin hakan yasa da sauri muka mike don barin wajen .
A can wajen dafifin jama,a da muka sama a wajen ana hayaniya da gani wani tashin hankali sukeyi sai ya kara firgita mu yana gaba muna biye dashi zuwa wajen wasu motoci sabanin wanda muka zo dashi a wajen
Aka dauke mu zuwa gidajen mu ni dai har lokacin hankalina bai kwanta ba don ganin yadda suka fita da dafifin jama,an dana gani waje agun hassana na fara jin abinda ke faruwa don mijinta daya dawo yana sheda mata matsalan da aka samu wajen saiga kiranta.
Tana fadin ke ashe da in-law ake wanan rigiman wai an turo ayi mai wani sheri sai security suka kama mutum biyu cikin su biyar shine ake dukansu a wajen sukaki fada.
Da sukaga za a kadhesu shine sukace wata mace tasasu aiki amma basu santa ba yanzu dai doctor yace suna hannun security sunce dole sai sun fada.
Innalillahi na ambata a bakina nace sister bakowa bane Allah na tuba sai matan babaninsa din nan sune zasu iya hakan ni dama jikina ya bani cewa zasu aikata irin hakan don koda bukin auren mu lokacin sunyi irin haka.
Wai kina nufin hjyyotin nan su maman saudiya nace kwarai saidai bai faye zargin ita maman saudiya din ba ya daifi zargin wanan hjy laila din kamar itace shugabansu kaf gidan .
Tambayana tayi mijinta yafi nasu haline halan take wanan iya shigen nace ashe ban tsamanin hakan gaskiya Abbu ma fa yana da halinsa don ya kafu a saudiya din nan gaskiya.
Nan dai mukai ta zancen har muka gaji muka kashe wayan na zauna ina tunane muryan sadiyace yasani dagowa tana fadin mum gamu nasan Abdallah ne don yanzu rainon yaron ya dawo kansu saidai idan suna school iya zatayi ta fama dashi.
Don na fadawa Iya cewa yace a nemo mai raino sai cewa tayi yau ko diyanshi sun kai goma idan tana raye ta bari aka dauko mai raino ai ita taji kunya.
Nace iya aikin zai maki yawa take fadin yawan me da uwa ke haihuwa goma sha kuma ta kula da yaran ta kula da yaran ta kumayi aikin gidafa duk lokaci guda.
Wanan yasa bamu nema masa mai raino ba ko yaushe iya tana makale dashi a baya idan yaran na gida kuma su kama mata shi da sauran aiyuka don ban yarda na bar Jamila tana kwanciya ba don akwai gidan aure ni kaina akwai ranakun da nakan shiga kitchen inyi girkin da kaina inyi wasu aiyuka duk da inya gani fada hakam yakeyi sosai dani.
Koda ya dawone bai fada min abindake faruwa ba kwantawa yayi da safe kuma yayi sammako ya fita bai dawo gida ba saida dare a gajiye ga kuma ransa bace ganin hakan yasa ban masa magana ba ni kan.
Shida kansa bayan kwana biyu yake fada min abinda ya faru yace dani baki tambayeni abinda ya faru a wajen dinner ba dai ranan nasa aka dawo daku gida.
Nace naga kamar ranka a bace yake yace sosai ma mun kai karshe dai da hjy lalai ai don an yi zama har sau biyu mun zauna a nan mun kuma je gida mun zauna.
Na kafa sheda a gaban kowa duk abinda ya sameni ya samu dana ko matana itace kai har wani wanda ke tare dani kut da kut ba zan kyaleta ba ko in dubi wani halakan dake tsakanin mu zan dauki mataki mai muni akanta ne.
Abin har ya kaiku haka yace kwarai don tana neman rayuwan mu yanzu haka ai ba karamin kudi suka kashe ba aka rufe zance don hukuma sunce sai sin hukuntata kan attempt to murdering.
Tayi kuka ranan taji kunya diyanta sunyi kuka har uncle yace ya saketa da kyat aka samu ya hakkura da ganin yadda na dago ina kallonshi yasa ya kalloni nace boss baka tsoron kiyayyansu ya kara akan mu ?
Yace ba wanan zancen yanzu kuma dul sun sani sunsan nasha gabansu a yanzu insha Allahuma har abada inAllah ya yarda ta kuma rokeni gafara ita da kowa da zancen ya shafa haka kuma mazajensu sun rokeni nayafe acigaba da zumunci kada zimunci ya lalace a sanadin hakan an sulhunta sosai a wajen.
Saidai hakan bashi zaisa in yarda dasu ba zan dai sake sama sama in auna fahintarsu don abinda sukai min tun ina yaro ban boye komai ba na zayyanawa kowa gaban kuma mai,martaba da wasu nagida cikin yan majalissa.
Hjy maryam ma har cewa tayi idan nazo ince wai tana gaidake ita ta rasa me tayi maki haka kike shareta a yanzu nace nina hanata hurda daku sai tayi murmushi tana fadin ta sani .
Bayan haka ya faru komai ya lafa abubuwa suna tafiya daidai naga har yan uwa sun fara zuwa shi kuma yana shiga sha,aninsu ko ya aika hakan yayi min dadi koba komai hankalin mijina damu ya kwanta da hakan daya faru.
Na sake haihuwa da namiji aka samai suna Abu sifyan muna kiransa da Amir yakai mahaifina da matanshi duka saudiya sun yan biyu sun haihu duka kowace diya mace wata daya tsakaninsu munsha buki.
Muna zaune ranan akace yayi baki yace ace su shigo ya fito ni ina sama da yara don suna wajen mu alokacin na zata sun fitane da bakon yasa ina saukowa daga bene ina magana da yaran muna daddy oyoyoyo caraf idona ya saukan kan na uncle dake zaune yana facing din benen.
Saida na dan girgiza da ganinsa kafin na dawo na saita kaina na karasa saukowa ina fadin sannun ku da zuwa na tsaya muka gaisa Amir dake hannuna yana zillewa yana mikawa ubansa hannu yace dani miko minshi nan na zagaya na mika mashi yaron ya karba Abdallah ya zo ya kwanta a cinyar uban.
Zancena dashine na ranan bukin su maman saudiya ya fado min a rai na kara hade fuska sai naji yace kina waya da mutuminki Al,amin kuwa har yanzu nace wallahi mun dade bamuyi waya dashi ba tunda nayi aure yana wani kasa yanzu yace yana Kuwait a can ya samu aiki yake zaune.
Ban tsaya ba na shige ciki can yaran suka zo muna dan hira dasu naji kiranshi ta intercoms hakan yasa na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login