Showing 78001 words to 81000 words out of 347556 words

Chapter 27 - KARAN DAFI HAUSA NOVELS By Zainab Makawa.doc

24 Sep 2025

179

dinner din ke nan na juyo ina fadin .
Zamu daije mu gani ko zamu samu mota a labamu muje wa nike dashi mai mota da zai kaimu kinada kuwa uwata keda keda diya mai mota zaki tsaye labe labe idan kun shirya ki kirashi kawai dama son zuwa yake ya gani.
Na dauki ledan nan na shago mai rubutun arbiya nayi wa mama godiya na fito bari dai na dan taka maki kona motsa jikina ya fada yana mikewa muka fito tare dashi daga gidan.
Hira muke sosai na yanayin garin nace kai yanzu har kana son nan mu gashi muna rokon Allah ya nufemu da zuwa saudi ko yaushe tun muna yara.
Haba dai ai inda can kike kema garin zai ishekine ga uncle nan yaso ya dawo nan Nigeria yayi aiki amma Abba ya hana yace ba yanzu ba sai nan gaba.
Kinsan shifa tunda ya tafi yana karami bai zuwa Nigeria saboda yanayin karatun shi saidai yaje America yayi shekara hudu Chana kuma yai shekara biyu.
Shiyasa har ya Aliyu ya rigasa aure ai donshi bai zauna a gida ba kamar mu saboda kokarinsa yayi yawa suketa turashi karatu yana karo ilimi a can .
Donshi fanin su Abba ya dauka shima enginer ne yanzu ko yaya karfe yake zai hada maki shi shiyasa kikaji mami na fadin kudi gareshi sosai.
Shi ya Aliyu kuma da ya Abubakar karatun likita sukayi yanzuma shi ya Abubakar yana Germany a can yake aiki yanzu dasu kaifa na tambaya yace ni lauyane Fatima.
Na kalleshi da mamaki yace kina mamakine na danyi dariya yace su Aisha kuma da khariya suma sunyi karatu a famin business ne .
Yanzu kana nufin duk mama ta haifeku yace ko biyar din nan maza uku mata biyu itace ta haifemu don ma biyu sun rasu a cikin mune don babban yayan mu rasuwa tayi ana zancen aurenta tayi ciwon kai ta rasu.
Allah yaji kanta nace ya amsa da amin mun dan jima a kofan gidan muna hira yayi min sallama ya tafi da ledan dana saya mashi masara gasasa a cikinta.
Na shiga gida na bude dakina na saka kayan na fito kallon da mama tayi min yasa na gane tasan nasani don mama uwa zata fada mata ai can na tafi.
Sannu da aiki mama na fada ina shiga dakin mama uwa banji ta amsa min ba ni dai na shige muryana da Samira taji yasa ta fito daga dakinsu tana fadin.
Akwai zancen dinner din ne ko an fasa wallahi ban sani ba ko an fasa tace ba daga can kikeba ke nan nace a,a ina gidan maman saudiya nakai mata abincin dana dibar masu .
Amma dana san zaki tafi dana biki mun tafi tare don na jima ban lekata ba yaro dai yarone ina za a dake an samu wuri ana rarakar banza.
Indai sun an rarakesu suma ai zasu raraki banza don bamai narkama dukiyanshi haka banza koda kuwa shine karunan zamanin nan maman biyce ke fadin hakan kamar tanayi da wani.
Dadin abindai kowa ya haifa don bani kadai uwata ta haifo a duniyaba ban kuma tsarewa kowa hanya ba balle a dora min kazafi aiko ta jiyo tana fadin wa kike fadawa wanan zancen ?
A,a mama a,a suna zancensu an saka bakinki ciki nifa bana son hakana mama gaskiya yarinyar nan kin kakabeta a jikinki ko mu,amula arziki baki kaunar yi da ita don me suna maganan su zaki saka masu baki kina fadan hakan gareta.
Kai kai wai yayane meke faruwane kuma haka da yamman nan unguwa duk ya cika da jama,an arziki ku kuma zaku tara min tsiya a cikin gida da yamman farkon nan.
Mama uwace ta fito tana mayarwa baba da yadda akayi jin hakan yasa na fito nace baba dazun mama ta tafi gidan hjyn saudiya ta batani a can tace su kula ina masu sata agida.
Salati kowa ya dauka ita kuma cewa tayi ni nidin nan ni naje gidan ta na kare mata kwarin gwiwan danagani a lokacin nace ai ta dauki komai in kinyi mussu mama waya baya karya ai komai ta nade a wayanta ko .
To aida naje ba laifin bane don naje bincikan ta gaskiya ko don ana tsoron ki sai a saka maki ido kiyi abinda kikaga dama a gidan nan kina kallon kowa baida wayau.
Kin dai je din ke nan suwaiba tace ai bance maka banje ba kuma zuwan da nayi naje inji gaskiyane ai don kada a debo kayan mutane azo ana rabawa yayan mu a gani ace sunyi sata.
Amma tir da halin nan naki suwaiba wallahi tir da halin bakin ciki irin naki yanzu sata kuma kika koma dorawa yarinyar nan bayan maita ?
Baba bar zancen nan kayi hakkuri ni dai nasan bana sata kuma an fada mata bani akayi kayan yartane da tayi aure ta rage a gida shine ta bani da nazo kuma nabawa yan uwana kowa kala guda guda muka saka.
Kaiya amma kinji kunya Suwaiba wallahi kinji kunya wanan hassadan ina zaki dashine haka wai kinawa yar nan hassada da bakin ciki tun tana kankanuwa dai bakici riba ba baki bari don Allah ?
Yanzu ki duba ita an bata batayi bakin ciki ba ta fitar ta bawa yan uwa suma su samu wallahi dakece da baki bata ko kyale a cikin kayan nan.
Yanzu kuma tunda an gwaleki bari ki hada har hjyn ki dora masu sherin ki da kika iya ko dadin abin yanzu kowa ya gama fahintar ki cikin unguwa ai.
Amma mama gaskiya mu kina zubar muna da aji kullun dai zance guda tunda kika fara maganan nan nace kada kiyi hakan don Allah ashe saida kikaje.
Ke rufamin baki don wanan sha tusar data dan baku har kuke ganin tayi maku daidai inbanda kun mayar da kanku wani iri har yaushe bantu take nawa take a cikin wai ?
Mu zuba mu gani tunda ubanki da sauran munafukan gida sun kama maki muna nan zaune zamuji duk iskancin da kikeyi a zaria karta na aje maki kayan dadi kina yadda kikeso dashi meye bamu sani ba wai a gidan nan.
Ba kayan dadi suka ajemata ba Allah yasa gidan dadi suka gina mata babu ruwanki da wanan kama diyanki in kama diyata shike nan ba don hjyn nan ina ganin mutuncin taba wallahi da nakai karan wanan zancen .
Malam akan me zaka kai kara bayan mata bata da laifi gadai me laifin n???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?an a gida ita yaya data tashi taje masu gida da wanan maganan da bai dace ba ai.
Ruwa nafito na diba a daidai lokacin da suka kaure da mama uwa din ta fadi su fadi nayi wanka tare da dauro alwala don na shirya muje wurin dinner.
Na zata kan wanan maganan koba zasu tafi ba sai gashi ita hussai din mane kecewa dani kun shiryane mu fito kada a wuce da Amarya muna nan.
Nace gani dai ina shiryawa Samira ke fadin yanzu mu wani mota zamu shiga bandai bata amsa bani sai naji Nura nafadin ai motan ya habibi tana nan kuje dashi mana.
Koda yake suma zasu ai sukace ballema bamu rasa mota barin kira Al,ami yazo ya kaimu idan mun gama naci gaba da shirina har na gama sannan na daga waya na kira Al,amin da yazo mu tafi mun shirya.
Ba,afi minti ashirin ba ya bugo min mu fito ya iso na fadawa yan uwana suka fara fitowa nice ta karshen fitowa nasha kallo a gidan muma kawai nan mama uwa ke fadin indai zakayi maula kaci riba ko gobe ka koma don wasu sunje basu sha da dadi ba.
Lafiyen mota ya dauko shi muka shiga don bamuko tsaya biyawa gidan su zainab din ba daga gida muka wuce wurin event din mun samu wurin ya cika da jama,a.
Samira da hussainace suka shiga suka duba wurin a can ta ciki sosai suka samu inda zamu zauna hussaina ta dawo ta shiga damu don saida muka wuce mutane muka kai ga sit din mu Al,amin yana tare damu har zuwa wurin da zamu zauna din.
Sai bayan mun zauna ne andan dade na kula da wa yandake daga gefen hangun mu su ya ibrahim ne da ya habibi tare da matansu an basu table dinsu daban.
Sau daya na daga ido ina dariya da Al,amin yake fadin shi baiga table din nama a jere ba wanda kowa zai diba son ransa shine nake dariya caraf ina idona ya hade da nasa a daidai lokacin.
Take na mayar da fuskana na lokaci guda na murtuke fuskan nabar dariyan yayinda shagalin keta gudana karo na biyu muna kallon wani buki a wayanshi daya nuna muna yadda suke dina dinsu a can.
Kowa yana zaune a kasa saman shimfida masu kyau a cikin shigar farar jallabiya ga raguna an bamkare a gabasu sai tukuyar shisha da wasu ke zuka ga kayan icce nan kala kala a jere kai dama ace ina wurin nan wallahi in debi rabona hussaina ta fada.
Dariya na danyi mai sauti hakan ya jawo hankalinsu garemu tundai wasila da tayi wani shiga wai ita daga Fatakwal take tayi irin daurin dan kwalin yeme Ade yayi mata timtim a saman kai.
Hararansu nayi a fakaice murmushi ya sake daidai lokacin wasila ta rankwafo tana masa rada da cewa yaushe Bantu ta goge hakane wai take dagawa mutane kai kamar bata sansu ba ?
Yaushe rabonki da ita ya fada cikin dakewa kila tasan sirin mutum ne yake zargin tana daga kai yanzu gareshi kallonshi tayi ta dan kauda kai tana daure fuska.
Don maganan dana fada game da ita ya tsaya masa a rai tun lokacin sherewa kawai yakeyi a cikin mutane don saboda shi tazo garin.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

KARAN DAFI ?
YAFI DAN DAWA AMAFANI ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA ?


????????
2?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DARI BIYAR KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DON MIN AMANACE HAKKI, , , , , , ,

Washegari misalin goma naje gidan hjy da kayan hadina don nabarwa mama uwa ta hada min komai wanan shine dadin zaman lafiya da wani a inda kake don na zama kamar ball a cikin gidan mu.
In wanan ya garani wanan ya tara shi yasa kona bata da mutum bani yarda mu bata da yaranshi don na fahinci su yaran suna kau da kai ga abinda iyayyen suke min.
Yanzu dai ita mama uwa adduanta da cika bakinta a kaina shine Binta Allah ya kawar da shedan tsakanin mu Allah ya nufa in kaiki dakin aurenki da hannuna shine kusan wakan bakinta a yanzu.ashi ta hado min komai da safe ina tashi barci dauka nayi naje gidan hjy iya kawai na samu muka gaisa na fada mata abinda nazoyi tace na huta da girka wani abu ke nab dama ruwan shayi kawai da kwai na hada masu.
Ruwan zafi na dora na fara hada garin filawan wanda mama ta rigata tankade minshi ta dan zuba garin wake har kuka da dan kanwa da zaishi taushi ta zuba min shi daidai gwargwado.
Ruwan yana tausa muka fara kadawa tare da ita tana tsame min idan yayi muna jefawa a ruwan sanyin da muka tanada a cikin wani roba cikin dan lokaci muka hada na tsame masu shi a cikin wani babban kula na zuba ruwa mangyada na dora na yanka albasa saida ya soyu na tsame na kara kada wani wanan din na biyun ban bari ya kone kamar na farko ba na sauke na zuba a cikin inda na tanada na dauko wani bowl na zuba yaji da gishiri ko wani gefe daya muka dauka muka kai falo muna jerawa hjy ta fito tana fadin.
Ikon Allah ina bayi nake jin kamshin suyan mai ana basarsa yana bin hancina na dauka na wani gidane ya biyo iska zuwa nan gidan.
Ashe a cikin gidan nan kamshin yakema ina kwana mama na fada ina murmushi tace lafiya ke baki hutawane wai mamana ban dauka kin iya fitowa hakaba sai gaki kyau abinki kin huta wallahi da son jinkin yaran zamanin nan gaskiya.
Allah ya hore maki miji mai albarka da zaisoki da zuciya daya yadda kike har kowa naki suci albarkacin ki iya ta karba da amin tare dora wanda ya samu fatima mata ya more gaskiya ga tsabta ga iya girki da kanmun kai.
Ai iya duk ni kadai wanan yabon haka ke kadai kuwa mamata don kinfi hakanma gaskiya nima na dade ina tunanen hakan wallahi.
Mama ni zan tafi na fada ina zaki tafi nayi kasa da kai nace zan koma zaria yau din nan insha Allahu ina son karfe ukku in shiga school ina da lecture a lokacin don yau Monday.
Ikon Allah nasan don aikin nan ne bakiyi sammakon komawa bako gaskiya ki koma tunda kince kina da lectures da yamma amma bari inzo da sauri na dago nace a,a mama don Allah ki barshi.
Nikan nagode wallahi kin min abin da har rayuwata ta kare ba zan iya mantawa dake ba Allah ya saka da alheri ya tsare ya kare maki zurianki amin.
Suka amsa da amin tace amma dan jirani dai kadan don Allah kicin din su ta shiga ta kira iya taje nan ta hada man gyada dambun nama yaji maggi mai yawa harda kilishi dasu drinks sabulai omo madara ta ruwa irin na waje masu yawa iya ta fito min dasu cikin wasu ledoji irin manyan nan na waje.
Lokaci daya idona ya sako hawaye na don na daga kai inyi magana sai hawaye shar da dan gudu naje na rugumeta kuka sosai nayi a lokacin don ni kadai nasan me zuciyana yake ayyana min kan hakan da wanan matar take min.
Hjy Allah ya nuna muna auren yar nan naki ta amsa a cikin raunin murya da amin iya aiko ina saudi naji insha Allahu inga rai ga lafiya zanzo ni insha Allahu .
Kara rugumeta nayi tace iya taka mata zuwa waje kisa driver ya sauketa gida don Allah jeki uwata kada ki makara kinji Allah ya tsare ya kare ya bada sa,an karatu ki kula da rayuwanki banda shiga rudin shedan banda biyewa shedanun yan adam na amsa da kai ina sharan hawaye.
Zuciyana cike da tunanen kaunan da ban samu a cikin gidan mu ba yau gashi ina samu a uwar wasu cikin kulawa da saka albarka a gareni da zuciya daya.
Na juya zan tafi take fadin gashi baku samu sallama da mutuminki ba zaki tafi suma su Aliyu ba lalai bane ki dawo ki samesu don zasu koma kwanan nan insha Allahu da zaran matarsa ta dawo.
Ace su yafe min idan na saba masu Allah ya hadamu da alherisa mama tace amin insha Allahu zasuji motana tashi Al,amin ya fito ganin yanayin mahaifiyar tasu yasashi fadin lafiya mami kike zaune haka ?
Lafiya meka gani kawai dai yarinyar nan ne data tafi yanzu ta saka jikina mutuwa don irin kukan da naga tanayi kukan ya nuna da biyu takeyinsa gaskiya.
Waiwa kike nufi mami Fatima ?
Ta gyada masa kai tace ita din yace ta tafi ina tace ta koma zaria yanzun ta fita daga gidan nan tana kuka wallahi shine donda ganin kukanta kasan akwai abinda ke cin zuciyarta kan hakan.
Ayyah Allah sarki da ina nan dana bata hakkuri ai zata dawo ai kafin mu tafi ko tace ban tsamanin haka din jerabawa zasu fara tace da wuya ta dawo yanzu gaskiya sai idan sun gama.
Gaskiya zan je zaria na ganta kafin in tafi ai uncle yasan gidan da take a zaria din idan ya sani kaika zaiyi saidai kuyi waya da ita tayima kwatance zaifi ba zata nakeson mata ai.
Yanzun nan ma tana cikin garin nan don batafi minti ashirin da barin gidan nan ba ai nasan ko bata bar garin nan ba ai yanzu gaskiya.
Niko ina shiga gida dakina na nufa tare da yaran da suka kama min kayan gashi kowa na gidan yana waje lokacin nabawa yara dari biyu suna godiya zama nayi na hada kayana tsab na dibi wanda zai kaini wani lokaci a zarian .
Shirgin kaya na hada kamar zanbar gari saidai na dan dibarwasu mama wani abu cikin abinda maman saudiya ta bani a lokacin na fara fito da kayana waje ina tarawa suka bini da kallo.
Na dauko wanan abin na nufosu dashi nace gashi maman saudiya ta bani dazun da naje sallamanta na debi nawa wanan a raba a bawa baba shima .
Wai yau zaki komane Bintu nace eh mama gara na dan zauna a can na fuskaci karatuna yanzu don ko anyi hutu bansa zan dawo gida ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login