Showing 12001 words to 15000 words out of 21816 words

Chapter 5 - WANI AUREN BOOK COMPLETE BY SADIYA ABDULL.txt

12 Sep 2025

39

kenan Halima, wannan mijin naki sam ba mutum ba ne wallahi, amma babu komai lokaci ne".

Ta haɗa mata shayi ta sha da biredi, ta dafa mata ruwa ta yi wanka, ta fita ta siyo mata magunguna ta sha, ta kwanta bacci ya ɗauke ta.

Haka Zainab ta gama abinci ta siyar ta ware ribarta, ta yo cefanen wanda za ta yi gobe. Tun kafin dare sun tsara yadda komai zai kasance, saboda haka dukansu babu wanda ya iya yin bacci, ƙarfe ɗaya na dare Baaba ta yi nisa a bacci, Zainab ta tashi ta zare sakata a hankali, ta fito ta tura ɗakin Halima da yake a buɗe babu sakata, dama yana zaune a falo yana jiranta, ya tashi da farinciki ya saka sakata, ya ja ta suka shiga uwar ɗaka, har kan gadon Halima.

GIDAN ALI

Washegari ƙalau suka tashi da Maryam komai ya wuce, ya ci abinci ya tafi aiki, wajan la'asar Hajiya ta kira shi, take tambayarsa yau zai samu lokacinta?

Ali ya ce"Wallahi Hajiya ina wajen aiki ne..."

Hajiya ta ce"Haba Aliyyu aikinka ai babu abin da zai tsare maka, idan ka tashi ba sai ka zo ba? Na ji daɗin haɗuwa da kai ne fa, shi yasa ka ga har ina nemanka, dubu goma zan baka wannan karon".

Ali ya yi jimm yana jinjina dubu goma, da dubu goman nan fa zai rage aiki, don haka gaskiya ba zai bar wannan damar ta wuce shi ba, ya ce"To zan zo idan an yi sallar magriba, sai dai gaskiya ba zan daɗe ba".

Ta yi murmushin jin daɗi ta ce"Babu damuwa, Allah Ya kawo ka lafiya".

Yana aiki yana tunani, ga Baby Farha ma ta takura masa sai ya je gidansu, sai kaucewa yake don so yake ya yi sabon ɗinki, idan kuwa yana so da wuri dole ya jajje wurin Hajiyar nan idan ya tattara ya gama buƙatunsa ya watsar da ita daga baya, ana idar da sallar magriba ko gidansu bai shiga ba, ya buga babur ɗinsa ya tafi.

A ƙofa ya tsaya ya faɗa mata ya zo, ta fito ta shiga da shi har babur ɗinsa, cike da farin ciki ta buɗe firji ta ba shi lemo me sanyi ya sha, sannan ya ce mata zai yi wanka, ta ce ita ma za ta yi dama, ba dan ya so ba suka yi wankan tare, ta kawo masa kayan ƙwalam yana ci tana kallonsa, sosai yaron ya shiga ranta, ta ce"Aliyyu kana burge ni sosai, kuma ina hango faruwar wasu muhimman lamura a tarayyarmu da kai, ga ka matashi mai jini a jika, a ina kuka haɗu da Reza?"

Ya sosa kai ya ce"Hajiya kenan, Reza a ƙasan layinmu take, mun daɗe da ita".

Ta ce"Waye kai? Ka ba ni labarinka, me yasa ka zaɓi neman mata a maimakon aure?"

Ya ce"Hajiya ai ina da auren, wannan ana yin sa ne saboda nishaɗi kawai".

Da mamaki ta ce"Da gaske kai ma kana da auren?"

Ya ce"Wallahi ina da mata, yanayi ne kawai ya sa ban daina harkar nan ba".

Ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Ni ma ina da miji..."

Ya zaro ido da mamaki ya ce"Yanzu haka maganar nan da muke yi da auren wani a kanki?"

Ta ce"Ƙwarai kuwa, amma ga ni nan ina dai amsa sunan matar aure ne kawai".

Ya ce"Amma Hajiya me yasa kika zaɓi wannan rayuwar?"

Ta yi murmushin takaici ta ce"Aliyyu Wani Auren ba ya amfanar mutum da komai sai cutarwa, wani auren na jeka-na-yi-ka ne, wani auren sai dai ya kai mutum ga halaka, wani auren ana yinsa ne saboda mugunta da ƙuntatawa, wani auren ana yinsa ne saboda asiri ya rufu, kamar dai nawa auren, ina zaune a gidan nan ne kawai saboda asirina ya rufu, tun ina yarinya a haka rayuwar take, an aura min wanda ba sa'an aurena ba, ya rufe ni a gida saboda mugunta yana can yana yawon ƙasashe da sunan aiki, ko yana nan babu abin da yake iya taɓukawa, girma ya kama shi duk ya gajiya, kuma a hakan mu uku ne matansa, cikinmu babu wacce ta taɓa ko ɓatan wata, rashin haihuwa daga shi ne, ga shi zan tsufa babu ɗa ballantana jika, gani yake tun da ya bar min dukiya ya sallame ni, ya manta ni mai lafiya ce ba kamar shi ba, ina buƙatar abokin rayuwa, shiyasa nake amfani da kuɗin da yake taƙama da shi ina yin abin da ya kasa yi min, Aliyyu ka ga laifina?"

Har zuciyarsa ya san ba a kan daidai take ba, hujjarta ta yi rauni, tun da ai akwai hukuma, za ta iya kai shi a raba auren tun kafin abun ya yi nisa, amma dayake ya san ba wa'azi ya zo yi ba, sai ya ce"Gaskiya Hajiya ban ga laifinki ba wallahi, ai wannan shi ne daidai, mace sai da namiji, tun da har ya bar kuɗin ki ji daɗinki kawai, sai ki ta istigfari Allah gafurur rahim ne".

Ta yi murmushin jin daɗi ta ce"Na gode sosai Aliyyu".

Sun ɗauki tsawon lokaci suna aikata masha'a, shi kansa ya yi mamaki, saboda ya manta rabon da ya yi irin wannan daɗewar da mace, yau kam wasai ya ji shi kamar ya gama juye duk wata damuwarsa ta wannan ɓangaren, wani abu da bai sani ba Hajiya ta faki idonsa ta kashe wayarsa, Maryam har ta gaji da kira tana ji a kashe, sam ƙin ba shi damar tashi Hajiya ta yi, shi ma ya gaji sosai, don haka da taimakon sanyin AC bacci ya yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai ƙarfe biyu na dare.

A firgice ya tashi zaune tunowa da inda yake, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi lokacin da ya kalli agogo, ya ɗauki wayarsa yana mamakin yadda aka yi ta mutu, ya kunna gabansa yana faɗuwa, ya sakko daga gadon, ya zura kayansa sannan ya tashi Hajiya.

Ta tashi tana mirtsika ido ta ce"Aliyyu ina zuwa? Ka kwana a nan don Allah".

Da sauri ya ce"Ina? Ba zai yiwu ba wallahi".

Ta tashi zaune tana narkewa kamar yarinya ta ce"Don Allah ka kwana, zan ƙara maka dubu goma".

Ya ce"Ba ki san masifar da take tunkaro ni ba ne, wallahi ko a dubu ɗari ba zan kwana a nan ba".

Ta tashi ta ɗakko masa dubu ashirin ta ba shi, ta ce"Amma ka san ba za ka keta unguwar nan a babur ba cikin daren nan".

Ya ce"Wallahi zan tafi ko a ƙafa ne, iya wuya dai a gidana zan kwana".

Hajiya ta ce"Ina zuwa" Ta ɗauki wayarta ta kira wata lamba, ta faɗa masa ya zo gidanta yanzu da sauri, tana sauke wayar ya ce"Waye?"

"Ɗan sanda ne". Ta faɗa tana ajiye wayar ta zauna tana dafe kai, don ta tsani a katse mata bacci.

Ba ta lura da daskarewar da Aliyyu ya yi ba, sai da ta ji cikin tashin hankali ya ce"Ɗan sanda fa kika ce! Hajiya me na yi miki?"

Ta kalle shi ta kwashe da dariya ta ce"Aliyyu kenan!"


ANA TA TAMBAYATA WAI WANI AUREN NA KUƊI NE? E NA KUƊI NE, A KAN NAIRA 300 KACAL!


08028966015
[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*


BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


FIRST CLASS WRITERS


PAGE 6

https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h


*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

ALI

Sosai ya shiga tashin hankali, kamar zai yi kuka ya ce"Hajiya me na yi miki don Allah za ki saka mini da wannan?"

Ta yi dariya ta ce"Ni kuwa ko butulu ce ai ba zan saka maka da sharri ba a yau, ko don faranta min da ka yi, haka kake da tsoro? Idan ka fita yanzu za a iya kama ka da laifin yawon dare, shi yasa zan saka Ɗan sanda ya mayar da kai har gida".

Ya sauke ajiyar zuciya duk da haka bai samu nutsuwa ba, Hajiya ta ce"A gaskiya Aliyyu wannan matar taka ta yi dace, ina ma ina da damar yin wani auren! Ai da kai zan aura, don Allah gobe ma ka zo ka ji?"

Ya ce"Hajiya kenan, ki bar ni na fara fita daga bala'in da na shiga yau, kafin komai ya biyo baya".

Ta ce"Bala'i kamar ya?"

Ya ce"Daga baya zan ba ki kabarin wace ce matata". Suka yi shiru, har Ɗan sandan ya kira ta ya ce ya ƙaraso, suka fita tare Ali ya hau bayan babur ɗinsa ya kai shi har ƙofar gida, ƙirjinsa yana ta bugawa ya ɗakko waya ya kira lambar Maryam yana haɗawa da ƙwanƙwasa gidan.

Maryam da ba ta daɗe da yin bacci ba ta tashi a firgice jin ƙarar wayarta, tana dubawa ta ga shi ne, ƙwanƙwasa gidan da ake yi ne ya tabbatar mata da dawowarsa, ta duba lokaci ta ga ƙarfe biyu da mintuna, ta yi huci mai zafi zuciyarta tana ƙuna, ta sakko ta buɗe loka ta ɗakko mukullin shago ta shiga falo ta ɗakko tabarma tana buɗe gidan ta watsa masa ta mayar da sakata.

"Maryam!" Ya kira sunanta yana buga ƙofar, amma ko waige ba ta yi ba, ta koma ɗakinta, zama ta yi a kan gadon tana tunanin wace rayuwa mijinta yake son faɗawa? Zargi ne kala-kala yake ɗarsuwa a ranta, ciki har da na neman matan, amma ta saka a ranta ko ma mene ne ya zo ƙarshe daga yau, ta share hawayen da ya zubo mata, duk yadda yake buga gidan ba ta sake bi ta kansa ba, ta kwanta da baƙinciki tare da fargabar sabuwar rayuwar da ya ɗakko.

Shi kuwa Ali sosai ransa ya ɓaci, don tun da take cewa za ta ba shi tabarma ya kwana a waje bai taɓa zaton za ta iya aikatawa ba, sai ga shi ya ga zahiri, haskawa ya yi ya ɗauki mukullin ya buɗe ƙaramin shagon dake manne da gidan, ya shiga da bisimillah, duk ya yi ƙura don ba a taɓa kwana a cikinsa ba ma, haka ya shimfiɗa tabarma ya zauna, ya yi jugum yana nadamar wannan rayuwar da yake yi, ga shi aurensu ko shekara bai yi ba za su fara samun matsala, ya san gobe Allah ne kaɗai ya san irin bidirin da za su sha da Maryam, sai dai duk rintse ba zai yarda ta tafi gida ba, idan ta je ta faɗi dalili a ka titsiye shi da tambayar inda ya je me zai ce? Da wannan tunanin ya kwanta ya yi matashi da hannunsa, sai dai ya kasa bacci duk da babu sauro, tunani yake yi yanzu ya baro lafiyayyiyar katifa a makeke gado cikin AC, cikin abin da bai fi minti talatin ba rayuwarsa ta canza ga shi kwance a tabarma cikin ɗaki mai ƙura.

Tashi zaune ya yi, ya lumshe ido yana tuna duk abubuwan da suka wakana a daren na yau, tsakaninsa da Hajiyar da ko sunanta ba ta faɗa masa ba, yana buƙatar kuɗi kuma ya ga alamar zai samu alkhairi sosai ta wajanta, muddin ya kwantar da kai, saboda haka dole a yi ɗaya cikin biyu, ko dai ya nunawa Maryam dole ta yarda da cewar ya samu sabon aikin dare na gadi a wani kamfani ko kuma ita Hajiyar ta yarda ya dinga zuwar mata da rana, sai ya dinga tashi daga aikinsa da wuri, idan ya tara abin da yake nema sai ya rabu da ita, da wannan tunanin zuciyarsa ta nutsu, ya ɗakko waya ya kira ta don ya sake yi mata godiyar kuɗin, sai dai ba ta ɗauka ba, ya kunna data yana duba saƙonni, sai wajen uku da rabi ya yi bacci.

Da safe ƙarfe shida ya farka, ya fito ya ci gaba da buga gidan, ta ƙi buɗewa, ya kira wayarta sai ta ɗauka, ya ce"Maryam ki buɗe min alwala zan yi".

Ta ƙashe wayar, ta zo ta buɗe, ya shigo a sanyaye ta kalle shi ta kau da kai, ya yi alwala ya yi sallah, yana zaune a falo ya ga ta ɗora tukunya, sannan ta koma ɗakin gado, ya tashi ya bi ta, yana shiga ya ga tana birkito kayan cikin sif tana watso su kan gado, ya ƙarasa ya tsaya a gabanta ya ce"Maryam mene ne haka? Wai me yasa kike sha'awar yin yaji ne? Ko ba ki san abun kunya ba ne? Yanzu ko cewa na yi ki tafi gida sai ki tafi ɗin? Sai ka ce kin manta da muna da magauta masu jiran su ga ranar da za ki yi nadamar aurena? Haba Maryam, komai fa nake yi dominki ne, na san tun farko na yi kuskure da na ɓoye miki abin da ya kamata a ce kin sani".

Ganin ta ba da ni nutsuwarta, ya sa na zaunar da ita, ni ma na zauna na ci gaba"Maryam tsakani da Allah wani aiki ne na samu, na gadi da za mu dinga yi ni da a Hamza a wani kamfani, mu ne masu night duty, to shi ne dalilin kai wa daren da na yi jiya, ba a tashi ba ma na gudo saboda na san ba za ki samu nutsuwa ba, tun da ba ki san inda nake ba".

Har yanzu ba ta ce komai ba.

Ya ce"Gani na yi kuɗin da za su dinga biya da kauri shi yasa, kin ga fa kullum dubu uku, kin ga ai za mu toshe wani wajen ko?"

Sosai ta yarda da shi, amma ba ta jin za ta yarda da wannan aikin daren, ta kalle shi ta ce"Yanzu saboda dubu uku za ka dinga kwana a waje kullum? Da rana kuma ka tafi wani aikin? Shi kenan ba ka da lokacin hutu? Shi baccin da wane lokaci za ka dinga yi? Tara shi za ka yi ya zame maka matsalar da sai ka sha maganin da ya ninka dubu uku sau goma? Ina ta faɗa maka zafin nema ba ya kawo samu, saboda haka ka kwantar da hankalinka, indai ni ce kar ka damu, ba ga shi ina sana'ata ba? Idan nauyin gidan ne ya maka yawa zama ya kamata mu yi mu tsara komai na san ta inda zan rage maka nauyi, ko magi da kayan miya ne, ba wai ka ɗauki wannan matakin ba".

Ya ji daɗin yadda ta yarda da shi sosai, ya ce"Na gode Allah da ya ba ni mace ta gari, Maryam Allah Ya biya ki da gidan aljanna, yanzu dai aikin ne ba kya so ko?"

Ta ce"E gaskiya ban yarda da shi ba".

Ya ce"Dama shi komai ɗan maslaha ne, in sha Allah na haƙura, sannan Maryam ni ban amince ki taimake ni da abin da yake nauyina ba, zan dinga yi miki komai daidai ƙarfina, fatana dai mu samu zaman lafiya da farinciki mai ɗorewa".

Tana murmushi ta ce"Allah Ya dawwamar mana".

Ya ce"Yanzu dai tun da komai ya wuce shi kenan babu sauran rigima ko?"

Ta ce"Da saura fa".

Ya ce"To me kuma ya faru?"

Ta ce"A gaskiya wannan majalisar taku ba na sonta kwata-kwata, kawai ana idar da sallar magriba ka dawo gida mu zauna ina buƙatar ganinka, mu yi fira na yi maka kwalliya kuma ka samu isasshen bacci".

Ya yi dariya ya ce"An gama ranki ya daɗe, in sha Allah yau ana magriba za ki gan ni".

Daga haka ta fita ta sauke shayinta, suka karya ransu fes, ya fita aiki cikin kwanciyar hankali.


GIDAN SADIQ

Da Sadiq ya dawo ta yi masa bayanin duk yadda komai zai kasance da ƴar aikinsu, ya amince ba don ransa yana so ba, sai dai a zauna lafiya kawai. Washegari da safe Yusra ta tafi aiki, don ta riga yaran fita a gida ta bar su da Sadiq, wajan ƙarfe takwas yana shago sai ga yarinya ta shigo, ta gaishe shi, ya yi zaton ma wani abu za ta siya, ganin ta yi shiru tana sunkuyar da kai ya ce"Me kike so?"

Ta ce"Mukulli na zo karɓa, ni ce Kursum, sabuwar mai aikinku".

"Ok" Ya faɗa yana kallon yanayinta, sannan ya ɗakko ya ba ta, ta duƙa ta karɓa ta ce"Na gode, sai anjima". Ta fice.

Tana shiga gidan ta cire hijjabi ta yi gefe da shi, tana ƙarewa ko'ina kallo, mukullan ta fara gwadawa tana buɗe ɗakunan, sai ta lura babu na bedroom ɗin Yusra, ta taɓe baki ta shiga kitchen ta yi wanke-wanke, ta fito ta share ko'ina ta goge, ta share tsakar gidan har da wanke kayan su Afna duka, sannan ta ɗora girki, a cikin jakarta ta fito da leda mai ɗauke da magi, curry kala biyu da niƙaƙƙen nama soyayye, ta tsara haɗalliyar jollop, sannan ta kunna ɗayan gas ɗin ta ɗora wani girkin, ta saka magi da curryn da ta tarar a gidan, kafin ya dahu ta yi wanka ta ci kwalliyarya ta canza kaya, don da wasu kayan ta taho, tana gamawa ta zuba ta ci ta ƙoshi, ta juye ɗayar tukunyar wacce ta dafa kaɗan don Yusra, ta zuba na Sadiq ta rufe gidan ta tafi kai masa, a lokacin sha biyu saura kwata, tana zuwa ta ga ƙofar shagon a rufe, ta jira har shiru bai dawo ba, ganin har sha biyu ta yi ya sa ta koma gida saboda kar yaran su dawo, babu jimawa kuwa suka dawo, da saurinta ta tare su ta rungume su, suka tsaya suna kallon juna, duk da Momynsu ta faɗa musu ita za su dinga tararwa a gidan, kuma sun ganta ranar da ta zo.

Hannunsu ta ja suka ƙarasa ɗaki, tana cewa "Sannunku ƙawayena kun gaji ko?" Suka gyaɗa mata kai.

Ta cire musu unifom, ta yi musu wanka suna ta bin ta da ido, ta saka musu kaya marasa nauyi, sannan ta zubo musu abinci a faranti ɗaya, ta zauna tana ba su a baki tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login