Showing 9001 words to 12000 words out of 21816 words

Chapter 4 - WANI AUREN BOOK COMPLETE BY SADIYA ABDULL.txt

12 Sep 2025

38

hankalinsa ya kwanta.

Yana lura ta yi bacci ya tashi tsam, ya tafi zaure, ya ɗauki ajiyarsa ya buɗe, snacks ne da dangin kayan zaƙi su alawar madara da chocolate kala-kala, sai robar wani lafiyayyen yougurt, ya zauna a zauren ya buɗe yougurt yana sha, sannan ya kunna data yana duba sakwanni hankali kwance, ya kai minti talatin kafin ya tashi ya tattara sauran kayan, saɗaf-saɗaf ya shiga ɗaki, ya ɗakko wata babbar rigarsa ta shadda ya bazata ya jure su a ciki, ya ƙudundune ya cusa a sif, ya nemi waje ya kwanta bacci mai daɗi ya kwashe shi.

Yana farkawa ya ga gari har ya yi haske, ya kalli agogo ya ga bakwai saura, ya tashi da sauri ya fito, falo ya leƙa ya tarar da Maryam zaune tana cin abinci ga kuma babban akwati a kusa da ita, gabansa ya faɗi, ya dai fita ya yi alwala ya dawo falon, a bakin ƙofa ya shimfiɗa salayya saboda kar ta fita yana sallah, yana idarwa ya ce"Maryam yanzu duk fushin ne ya sa kika ƙi tashina sallah har gari ya waye?"

Ta ce"Ai dama ba dolena ba ne, kai ne yake dole ka tashe ni".

Ya ce"To shi kuma wannan akwatin fa na mene ne?"

Tana ajiye farantin hannunta ta ce"Gidanmu zan tafi Ali, don ba ƴar iska ka ajiye ba da har za ka kai ƙarfe goma sha ɗaya a waje! Gara na tafi idan ka gama tara kuɗin na dawo, idan kuma ka samu wata ma shi kenan". Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar hijjabi za ta saka.

Ya ƙarasa ya riƙe hijjabin kamar zai yi kuka ya ce"Haba don Allah Maryam, ai na san na yi kuskure tun da na ba ki haƙuri ya kamata ki yi min uzuri, ki gani ko zan ƙara? Naga jiya ne kawai hakan ta faru, kuma na faɗa miki dalilina, tun da ba mu fahimci juna ba na haƙura da aikin daren, wallahi haka ba zai sake faruwa ba, yi haƙuri mana kin ji kyakkyawar matata".

Ta koma ta zauna tana ɓata rai ta ce"Wannan ya zama na ƙarshe, don idan ka ƙara kai wa irin haka a waje ba zan fahimce ka ba, wa ya faɗa maka zafin nema yana kawo samu?"

Ali ya ce"Ba ma zai sake faruwa ba in sha Allah".

"Ina ka bar babur ɗinka jiya?" Ta jefo masa tambaya.

Ya ce"Ai da na ga na yi dare sai na bar shi a gidanmu saboda kar masu ƙwacen babur su tare ni".

Sai da ya tabbatar ta haƙura sannan ya tafi wajen aiki, bayan la'asar sai ga wannan Hajiyar ta kira shi a waya, ya ɗaga suka gaisa take ce masa yau ma idan da dama tana son ganin shi, da sauri ya faɗa mata babu dama, suka yi sallama yana jin rashin jin daɗi, saboda yana son zuwan amma yana son zaman lafiya a gidansa don haka ya kau da kai, ya ci gaba da aikinsa.

Sai bayan magriba Maryam ta ɗauki akwatinta ta mayar da kayan ta jere a sif, buɗe nashi sif ɗin tayi, don ta kwana biyu ba ta gyara ba, tana kwaso kayan ta ji motsin leda, da mamaki ta shiga bincikawa, ai kuwa tana zazzage babbar rigar nan sai ga kayan ciye-ciye sun bayyana, gabanta ya faɗi ta hau duba su cike da mamakin yaushe suka fara haka da Ali? Abun har ya kai ya sayi kayan daɗi ya ɓoye a sif yana ci shi kaɗai? Gefe ta yi da su, ta kwashi kayan ta mayar sif don ta fasa linkewar, ta kwashe kayan ƙwalam ɗin ta je ta baje a falo, ta dinga ci kamar babu komai, sai da ta cinye komai ta sha ruwa ta zubar da ledojin tana ta mamaki, tana kuma jiran dawowarsa don ta ji dalilin wannan sabon salon da ya tsiro da shi.

Ƙarfe takwas tana yi Ali ya kamo hanyar gida, har kwakwa da dabino ya siya mata a hanya, saboda ya san tana so, ya tura ƙofar ya shiga da babur ɗinsa, ransa fes ya shiga ɗakin, ta kalle shi babu yabo babu fallasa ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa yana miƙa mata ledar kwakwar, ta karɓa ta yi godiya tana jinjina rainin hankalinsa, wato ya siyo kayan ƙwala har da dambun nama, ita shi ne zai haɗa ta da kwakwa, ta maze ta kai masa ruwa ya yi wanka, ya fito ta zuba masa abinci ta koma kujera ta kame tana cin kwakwa da dabinon.

Da ɗan mamaki ya kalle ta ya ce"Ya dai Love! Yau kin ci abinci kafin na dawo kenan".

Ta girgiza kai ta ce"Wallahi ban ci ba".

Ya ce"To me yasa?"

Ta ce"A ƙoshe nake, nan da ka gan ni cikina babu masaka tsinke tura kwakwar nan kawai nake don ina so".

Ya yi ƴar dariya ya ce"To ke kuwa me kika ci?"

Ta ce"Abubuwan da ka ci jiya ka ƙoshi har ka kasa cin abincin dare".

Gabansa ya faɗi ya dake ya ce"Kamar ya? Me na ci jiyan?"

Maryam ta ce"Au har ka manta ka yi saura ka ajiye a sif kenan".

Ya ji ƙirjinsa ya ba da sautin dumm! Ya kasa cewa komai.

Ta ce"Hmm! Na yi mamaki wallahi, yaushe muka fara haka da kai? Kuma idan za ka ci kai kaɗai ai da sai ka ci abunka a waje, ban gani ba ballantana na saka maka rani..."

Ya katse ta da faɗin"Wallahi ba haka ba ne Maryam, wata yarinya ce take ta bi na a kwanakin nan ba na kula ta, to shi ne jiya ta bawa Hamza ya kawo min wannan kayan, kuma na san idan ma ban karɓa ba wallahi ba zai mayar ba, kuma zuwa zai yi ya ce mata na karɓa, shi yasa kawai na karɓa ɗin, to da yake na san ba za ki ji daɗi ba shi ne na ɓoye saboda kar ki gani, amma ba wai manufata na yi miki rowa ba wallahi".

Maryam ta yi murmushin takaici ta ce"To mene ne abun ɓoyewa? Kenan jiyan a wurinta kake har sha ɗaya ko?"

Ya yi saurin girgiza kai ya ce"Wallahi ban taɓa kula ta ba ma, ba faɗa miki ai aiki na tsaya, kuma tun da zai kawo mana matsala na daina, ba ga shi yau na dawo da wuri ba?"

Ta ce"To shi kenan magana ta wuce".


GIDAN SADIQ

Sanda Sadiq ya gama uzurinsa ya je zai kwanta, sai ya same ta zaune a kan gadon, yana shiga ta sakko ta fice daga ɗakin, har bacci ya fara fizgarsa ba ta shigo ba, hakan ya sa ya fito don ya lallashe ta, a falo ya tarar da ita kamar yadda ya yi zato, saboda halinta idan suka yi faɗa ta ce za ta kwana a falo, zama ya yi a gefen kujerar da take kwance, yana shafa kanta ya ce"Yusra!".

Ta juya masa baya, ya juyo da ita ya ce"Ni fa ban ce miki zan yi wani auren nan kusa ba".

Ta ce"To me yasa ka hana ni samo ƴar aikin?"

"To ki samo mai hankali" Ta ji furucinsa a bazata.

"Da gaske?" Ta tambaye shi tana jin daɗi sosai.

Ya ce"Da gaske mana, ba shi ne dalilin fushin ba?"

A gabansa ta ɗauki waya ta kira Sumayya ta faɗa mata ya amince da ɗaukar ƴar aikin, cikin jin daɗi ta ce mata gobe za ta kawo mata ita har gida. Sai ga Yusra ta ware har tana yi masa firar yadda za ta kasance da ƴar aikin, suka kwanta tana cike da farin ciki.

Washegari da kuzarinta ta gama komai na gidan, shi kuma ya tafi shago, ƙarfe tara Sumayya ta shigo gidan tare da wata buduruwa, Yusra ta tare su da murna, suka gaisa tana kallon yarinyar da take a nutse daga gani ba ta da hayaniya, Sumayya ta ce"To ga Kursum nan na kawo miki, ban fiya yabon wani ba, amma ina da tabbacin za ki ji daɗin zama da ita, ba ta da gandar aiki, kuma tana da hankali".

Yusra ta ce"Ai na lura da hakan, ke dai Allah Ya saka ƙawata".

Sumayya ta ce"To ya kika tsara yanayin aikin, a nan za ta zauna duka ko zuwa za ta dinga yi tana tafiya?"

Yusra ta ce"Idan ta gama aikinta za ta jira na dawo gidan sannan na tafi, ranar da nake aikin kwana kuma za ta kwana a nan, ta kula da yaran ko dan saboda tashin sassafe ta shirya su su tafi makaranta".

Nan Sumayya ta faɗa mata unguwar da gidan su Kursum yake, sannan ta ɗora da faɗin"Kursum ki yi abin da ya kawo ki shi kaɗai, ki kular mata da yaranta ki rungume su hannu biyu-biyu, sannan idan za ki yi girki ban da almubazzaranci, magana ta ƙarshe babu ruwanki da mijinta! Gaisuwa ce kaɗai za ta haɗa ku, idan kin yi girki ki ajiye a dining, yana dawowa ki shige ɗakin yara a nan za ki na kwana, kar ki sake ki fito babu hijjabi ko mayafi idan yana gida, kin dai ji ko!?" Ta ƙarasa tana ƙanƙance ido alamar gargaɗi sosai.

Kursum ta ce"In sha Allah zan kiyaye komai".

Yusra cikin jin daɗi ta ce"Na gode sosai ƙawata".

Sannan ta ce"Yau babu aikin komai, tun da ina gida, sai dai gobe ki zo da safe, zan bar miki mukulli a wurin mijina, sai ki dinga zuwa kina karɓa a shagon, kin ga gobe aikin safe zan yi, to kafin ki zo mun fita dukanmu, idan kin karɓo mukulli sai ki yi wanke-wanke ki gyara ko'ina, kafin sha biyu ki yi girki idan yara sun dawo su ci ki shirya su su tafi islamiyya, shi ma ki zuba ki kai masa nasa, sai ki zauna a gidan, wajan ƙarfe uku zan dawo kin ga sai ki tafi ko?"

Kursum ta jinjina kai ta ce"In sha Allah babu matsala".

Suka yi mata sallama suka tafi, a hanya Sumayya ta ce"Don Allah Kursum kar ki ba ni kunya, na faɗa miki kuɗin da zan biya ki idan aikin nan ya yi kyau, ki kwantar mata da kai, shi kuma ki san ta inda za ki ɓullo masa".

Kursum ta yi murmushi ta ce"Ni fa dama can yana burge ni wallahi, ballantana kuma za mu rayu a inuwa ɗaya? Hmm Allah Ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya yi ɓarna".

Sumayya ta ce"Allah Ya shi miki albarka Kursum, idan komai ya tafi daidai, wallahi sai na yi wata shida muna raba daidan albashina da ke".

Kursum ta kwashe da dariya cike da farin ciki, ta ce"Riba biyu inji sauro".



08028966015
[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*


BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


FIRST CLASS WRITERS


PAGE 5

Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅


GIDAN HARUNA

A ranar tun tsakar dare zazzaɓi ya rufe Halima, dama tun da rana take ciwon kai, ta kasa bacci, sai gabannin asuba ya ɗauke ta, amma da alarm ɗinta ya buga haka ta daure ta tashi ta yi sallah, sai dai ta kasa komai ta kwanta a sallayar tana ta rawar sanyi, yayinda Haruna yake ta baccinsa bai san halin da take ciki ba. Zainab ganin har bakwai ta wuce Halima ba ta fito ba, ya sa ta ƙarasa ƙofar ɗakinta tana sallama, ta amsa mata da ƙyar tana tashi zaune ta ce"Zainab".

Zainab ta buɗe labulen, ta ce"Halima yau lafiya kuwa ba ki fito ba?"

Halima ta ce"Wallahi ba ni da lafiya, zazzaɓi da ciwon kai tun jiya, yau ba zan iya ba ma".

Zainab ta ce"Ai kuwa babu daɗi a zo nema a ga ba ki yi ba, yau ɗaya da sai na yi miki".

Halima ta ce"Za ki iya kuwa Zainab? Kar ki wahalar da kanki".

Ta ce"Haba wace wahala, ɗakko min kayan, bari na haɗa wuta". Ta fita tana kunna mangal, ita kuma Halima ta tashi ta ɗakko mata kayan wainar, Zainab ta dawo hannunta ɗauke da kofin kunu ta miƙa mata, har da paracitamol ta ce ta sha kafin a kaita asibiti, ta yi mata godiya, ita kuma ta koma ta fara aikinta.

Wajan ƙarfe tara Haruna ya tashi daga bacci, turus ya yi ganinta kwance a daidai wannan lokacin, ya fice don shiga banɗaki, sai dai ya tsaya ganin Zainab a bakin murhu tana ta fifita wutar wake da shinkafa, don har an fita da waina, jikinta ne ya ba ta ana kallonta, ta ɗago ta kalle shi, ta yi masa farr da ido, ƙasa-ƙasa ya ce"Ke dai kina son wahalar da kanki, ki yi ta taya matar nan aiki".

A hankali ta ƙaraso kusa da shi ta ce"Kai ka tattarata ka kai ta gida ta yi jinya, ka ga mun samu ɗaki kafin ta dawo".

Zai yi magana kenan Baaba ta fito daga ɗaki don ta duba jikin Halima, suka waske ya wuce banɗaki, a ransa yana ta tunanin maganar Zainab, domin tabbas shawararta abar dubawa ce, saboda haka yana komawa ɗaki ya tambayi Halima kwanciyar me take yi, ta faɗa masa yanayin jikinta, ya ce"Allah Ya sawaƙe, to ina abun karyawata?"

Ta ce"Ban fita ba fa yau kwata-kwata".

Ya ce"Kuma don ba ki da lafiya ba zan ci abinci ba kenan?"

Takaici ya kamata, tana tabbatarwa kanta lallai Haruna ba miji ba ne, ba ta gama tsinkewa ba sai da ta ji muryarsa ya ce"Daurewa fa za ki yi ki dafa min taliyar nan".

"To!" Ta amsa tana tashi zaune, ta huta na sakanni sannan ta fita ta kunna mangal ta ɗora. Tana fita ya kira lambar Zainab, tana ɗagawa ya ce"Na koro ta ta min girki, kar ki taya ta, ni abincin ma ban so kika karɓar mata ba, idan ta ji wahala za ta nemi zuwa gidan da kanta". Zainab ta yi dariya suka kashe wayar, tana leƙen Halima ta gefen labule.

Zama ta yi a bakin wutar bayan ta haɗa komai na jollop ta ɗora, ruwan yana tafasa ƙamshin ya daki hancinta, nan take cikinta ya fara rugugi, yawu ya taru a bakinta da gudu ta ƙarasa bakin makwarara ta fara kwara amai babu ƙaƙƙautawa, Zainab ta yi kamar ba ta ji ta ba, haka shi ma Haruna, sai Baaba ce da ta ji abun ya ƙi ƙarewa ta fita tana cewa"Subhallah! Sannu Halima, har da amai?"

Halima ta gyaɗa kai a galabaice, Baaba ta miƙa mata buta ta wanke bakinta, ta wanke wurin tana ta yi mata sannu, Halima ta koma ta zauna a wurin girkin, tana buɗewa don ta zubar taliyar wani aman ya sake taso mata, haka ta dinga yi babu ƙaƙƙautawa, wannan karon Baaba cewa ta yi"Zainab je ki ki ƙarasa mata girkin can, ina ga ƙamshin ne yake saka ta aman nan". Zainab ta je kan girkin, Baaba ta yi sallama a ɗakin Zainab tana kiran Haruna, ya fito yana gaishe ta, ta ce"Haruna wannan yarinyar kamata ya yi fa ku tafi asibiti, ka ga duk ƙarfin halinta ta galabaita lokaci ɗaya".

Ya ce"To Baaba bari ta shirya sai na kai ta".

Ɗaki ta koma ta kwanta, ya kalle ta yana taɓe baki ya yi mata sannu, ta gyaɗa masa kai, Zainab tana gama girkin ta yi sallama a ɗakin, ta ɗauki kula a kwando ta juyo taliyar ta kawo musu, suka faki idon Halima suka kashewa juna ido.

Yana cikin cin taliyar yake cewa"Halima asibiti ya kamata na kai ki, ga shi da ɗari biyar kawai na tashi, kin ga kuwa ba ta fi kuɗin adaidaita ba, yanzu ya za a yi?"

Ta ce"Babu komai, ai na sha paracitamol".

Ya ce"To me zai yi miki? Ba ki ga har da amai ba? Ko ciki ne da ke ma?"

Cikin ƙosawa ta ce"Allah masani".

Ya ce"To yanzu dai tashi za ki yi, ki lallaɓa ki shirya, ki saka kayanki ko kala uku ne a jaka sai na raka ki gidanku, idan jikin ya yi dama-dama kya dawo".

Cikin rashin son hakan ta ce"Gaskiya da ka bar ni a nan ɗin..."

"A hakan ba kya iya aikin komai? Daga dafa taliya kin yi amai sau biyu, ina za ki iya wani moruwa? Duk aikace-aikacen gidan waye zai na yi miki?"

Hawaye ya zubo mata, ta san gaskiya ya faɗa mata, saboda haka ta ce"To shi kenan mu tafi ɗin".

Tana jiri ta ɗakko ƙaramin akwatinta, ta zuba kaya, ta saka hijjabi ta kwanta a kujera tana jiransa, yana gamawa ya ce ta tashi su tafi, sanda suka fito Zainab tana daka yaji, Baaba tana zaune a tsakar gida, Halima ta ƙirƙiri murmushi ta ce"Baaba za mu tafi".

Baaba ta ce"Asibitin ne? Ya na ga akwati?"

Haruna ya ce"Ai daga can gida zan kai ta, kin ga yanayin jikinta a gidan sai ta fi hutawa".

Baaba ta ce"Haba ɗan nan! Irin haka ai babu daɗi yarinya tana fara laulayi ka kwashe ta ka kai gida, ban da abunka ba ga Zainab ba? Komai za ta yi mata, ga ni kuma zan dinga kula da ita, idan zazzaɓin ya sauka ai shikenan ma, ka dai duba".

Ya ce"Ai Baaba wannan duk wahalar da ku za a yi, ita ma ta fi son zuwa gidan, ko kwana biyu ne ta yi sai ta dawo, kin san halinta idan tana nan ba za ta huta ba".

Baaba ta ce"Ai shi kenan, kuma abincin da Halima?"

Halima ta ce"Zainab ta dinga yi, sai ta dinga cire ribarta ta ajiye min uwar kuɗin, har mu ga yanayin jikin".

Ta yi mata godiya, Zainab ta raka su har ƙofar gida, tana farin ciki. A ƙofar gidansu ya tsaya ko shiga bai yi ba ya ba ta ɗari biyu ya juya ya tafi, ta shiga da sallama tana jin jiri kamar za ta faɗi, nan ta faɗawa mahaifiyarta halin da ake ciki, Umma ta taɓe baki ta ce"Ke kuma ta ki ƙaddarar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login