Showing 6001 words to 9000 words out of 21816 words
ɗaki.
Ita kuma ta je ta ɗakko ledar ta shiga ɗaki, ta baje ledar cike da zumuɗi, Baaba ta ƙure ta da kallo ta ce"Ke Zainab a ina kike samo balangun nan ne?"
Ta haɗe gira ta ce"Haba Baaba ai kin san saurayina ne yake kawo min".
Baaba ta ce"To me yasa ba kwa zancen ne sai dai ki leƙa ki karɓo ya tafi?"
Ta ce"Aiki ne yake yi masa yawa wallahi, kuma shi dayake aure ne a gabansa ba ya son ma dogon zance, sai ya ce duk ƙarya ce ake shararawa".
Baaba ta sauke ajiyar zuciya tana karɓar balangun da Zainab ta ɗibar mata ta ce"Ni dai don Allah ki kama kanki Zainab, kin ga dai amana na karɓa, ki taimake ni na aurar da ke kar ki sake jajibo mana wani abun kunyar a nan, na bar waccen unguwar saboda ke, nan dai kin ga mu baƙi ne babu wanda ya san tabonki ballantana ki rasa miji, ki nutsu don Allah kin ji?"
Ta ce"In sha Allah Baaba ba zan ba ki kunya ba".
08028966015
[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
FIRST CLASS WRITERS
PAGE 3
Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
GIDAN HARUNA
Halima ta tashi daga ƴar kwanciyar da ta yi a sallaya bayan idar da sallar isha'i, idonta fal bacci, saboda gajiyar da take kai wa dare da ita dalilin kujiba-kujibar da take wuni tana yi na sana'o'inta, ta yi murmushi tana yi wa mijinta sannu da zuwa, Haruna ya zauna yana amsawa, ya bata ledar hannunsa, da dubu ɗaya, ta karɓa tana yi masa godiya, sannan ta kawo masa abinci ta shige ɗaki ta kwanta, kafin ya gama har ta yi bacci. Ya ɗauki wayarsa ya kira Zainab suka yi fira, don ya san Halima tana da nauyin bacci ba za ta farka nan kusa ba. Can wajen ƙarfe goma har ya kwanta, Zainab ta kira shi ta ce ya kunna data, jansa ta dinga yi da maganganun banza, har ta tabbatar ta tada masa hankali sannan ta roƙe shi kan ya zo ya taya ta wanka, da farin ciki ya tashi tsam ya fice daga ɗakin, duk da yana fargaba, a tsakar gida suka yi kiciɓus suka yi wa juna murmushi ta cikin duhun, tana shiga banɗaki ya mara mata baya, ba su daɗe da shiga ba suka ji muryar Baaba tana cewa"Da mutum?"
Lokaci ɗaya ƙirjinsu ya buga, suka fara muzurai, jin ana ƙoƙarin buɗe ƙyauren Zainab ta yi saurin cewa"Da mutum, ina ciki Baaba".
A hankali ya ce"Yanzu ya za mu yi kenan?"
Ta ce"Idan ta gaji za ta koma".
Ya ce"Ta ya za ta koma tana buƙatar shiga banɗaki, kema wallahi kin fiya jaraba, ga shi za ki tona mana asiri".
Ta ce"Tsautsayi ne, wallahi na gaji da marmarinka..."
"Ni uwar me kike yi ne Zainab?" Baaba ta faɗa a fusace.
Ta ce"Ina masai kuma yanzu na shiga".
Suka ɗauki lokaci a haka kowa tsuru-tsuru musamman Haruna, sai Zainab ta tuna da ai da waya a hannunsa, da sauri ta ce"Ka kira lambata wayar tana ɗaki".
Yana kira, ta ɗaga murya ta ce"Baaba ga wayata can tana ringing don Allah ki ɗaga kawo ne".
Baaba da fitsari ya matse ta, a fusace ta ce"Ke buhun ubanki, wai kwana za ki yi a banɗakin?"
Ta ce"Don Allah Baab, kuɗi ya ce zai turo, kin san kuma ba ya kira biyu, don Allah je ki kar ta katse kafin na fito".
Baaba ta koma ɗaki tana tsaki, wuf Haruna ya fito ya yi zaure da sauri, sannan Zainab ɗin ta fito, ta tarar da Baaba tana kokowa da wayar, don ba ta iya ɗagawa ba, ta karɓi wayarta Baaba ta koma banɗaki tana mita, ita kuma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, sosai take son Haruna don haka dole ta san yadda za su ɓullowa lamarin nan, ta riga ta saba da maza yanzu jinta take tamkar a keje, don tun da suka dawo gidan nan ba ta haɗu da wani namijin ba, kuma a satin da za su dawo ɗin aka cire mata cikin da wani saurayinta ya yi mata, dalilin hakan ne ma kakar tata ta ce a bata Zainab ɗin su bar unguwar, saboda kowa ya ji zancen zubar da cikin nata, ta san idan Zainab ta ci gaba da zama a unguwar ba lallai ƴan ba ni na iya su barta ta yi aure ba.
Shi kuwa Haruna sai da ya ji Baaba ta shiga banɗaki, sannan ya shiga ɗakinsa ya saka sakata, tashin Halima ya yi ya ragewa kansa zafi, saboda Zainab ta gama kunna shi, daga nan bacci mai cike da nutsuwa ya kwashe shi, saɓanin Zainab.
GIDAN SADIQ
Washegari da damuwa Yusra ta tashi, idan ta tuna maganarsu ta jiya sai gabanta ya faɗi, sosai ta shiga tsoron kar Sadiq ya ƙara aure, tana da kishi sosai, ba ta jin za ta iya raba mijinta da wata macen, a yadda take ji indai ta tabbata Sadiq zai ƙara aure ita za ta iya haƙura da aurensa bakiɗaya ma, ta je ta yi wani auren ta rayu ko da babu ƴaƴanta a kusa da ita, muddin za ta rayu babu kishiya kuma ba za a hana ta aikinta ba ta amince, a sanyaye take yin komai har ta kammala abun karyawa ta kai dining ta jera, sai da ta yi wanka sannan ta tashi yaran daga bacci, kasancewar yau Asabar ce babu makarantar boko, ta yi musu wanka, da suka ƙaraso dining ɗin shi Sadiq har ya gama cin nashi abincin ya tashi, yana kallonta ya san tana cikin damuwa, sai ya ɗauka ko yanayi ne jikin da jini, tun da ya tashi ba su haɗu ba sai yanzu, don tana idar da sallah kafin ya dawo daga masallaci ta koma ɗakin yaranta ta kwanta.
"Zan fita, me za a kawo?" Ya tambaye ta yana yi mata kallon tsaf.
Hankalinta a kan abincin da take zubawa ta ce"Ba sai ka aiko komai ba, yau ina gida me za a dafa maka?"
Yana tafiya ya ce"Ki dafa zaɓinki kawai ya yi". Ya fita yana mamakin sauyinta, ko a dawo lafiya ba ta ce masa ba, ballantana ta raka shi, ya sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin kau da abun.
Da rana bayan ta gama komai yara sun tafi islamiyya, ta kwanta tana ta tunanin wannan maganar tasa da take neman tarwatsa mata farin ciki, idan ta tuna za su rabu sai idonta ya ciko da ƙwalla, kanta ya kulle ta rasa abun yi, saboda haka ta kira Sister Sumayya a waya, babbar ƙawarta tun ƙuruciya, kuma abokiyar aikinta a yanzu, ba sa ɓoyewa juna sirri damuwar ɗaya ta ɗayar ce, bayan sun gaisa Sumayya ta ce"Sister na ji kamar akwai damuwa a muryarki, ba ki da lafiya ko daga bacci kika tashi?"
Yusra ta sauke ajiyar zuciya ta kwashe duk abin da yake damunta ta faɗa mata.
Sumayya ta yi murmushi ta ce"Haba ƙawata, ke daga wannan kawai sai ki yi zargin Sadiq zai iya ƙara aure?"
Yusra ta ce"Kamar ba ki san butulcin namiji ba?"
"Butulci?" Sumayya ta tambaya da mamaki, sannan ta ɗora da faɗin"Don zai yi abin da Allah Ya halatta masa sai ki kira shi da butulu? Haba Yusra ki dawo cikin hayyacinki...".
Ta katse ta da faɗin"Wallahi Sumayya ba zan zauna da kishiya ba, don haka zan ba shi zaɓi, ko ya sake ni ko ya manta da ana ƙara aure a duniya".
Cike da mamaki Sumayya ta ce"Da gaske duk son da kike yi wa Sadiq za ki iya rabuwa da shi saboda zai ƙara aure?"
Yusra ta ce"Ƙwarai kuwa, wannan abu ne mai sauƙi a wajena, saboda na tsani kishiya".
Sumayya ta yi makirin murmushi mai ɗauke da manufofi da dama, wannan wata dama ce da ta jima tana neman hanyar samunta, domin kuwa ko maye ya manta uwar ɗiya ba za ta manta, amma za ta biyo mata ta bayan gida, kuma daki-daki har ta cim ma burinta.
"Sister ya zan yi? Duk na damu". Yusra ta faɗa kamar za ta yi kuka.
Sumayya ta ce"Dole cikin uku a yi ɗaya, ko dai ki haƙura da aikinki kamar yadda yake so, ko kuma ki samo ƴar aiki wacce za ta dinga zama tana yi miki aikin gida, idan kina aikin kwana ta kwana da yara ko kuma ki haƙura ya ƙara auren".
Yusra ta yi shiru na sakanni tana nazari, sannan ta ce"Ba zan iya ajiye aikina ba fa, zan gwada yi masa zancen ƴar aikin dai ko zai amince".
Sumayya ta ce"Idan ya amince sai ki yi min magana, zan samo miki mai hankali da nutsuwa, kin dai ƙi kishiyar ko? Ni ba ga shi ita ce take kula da ƴaƴan ba idan ba na nan?"
Yusra ta taɓe baki ta ce"Zuciyarmu ba iri ɗaya ba ce Sister". Daga haka suka ɗan taɓa hira sannan suka yi sallama, da wannan matsayar ta samu sauƙin damuwar da take ji.
Da daddare bayan sun gama cin abinci, yana lura da yanayinta na rashin sakewa da shi har yanzu, amma ya share, sai da ta gama jujjuya maganar tana tunanin karɓuwarta a wajensa sannan ta ce"Masoyi ina da magana mai muhimmanci".
Ya ce"Ina sauraronki".
Ta gyara zama ta kama hannunsa tana wasa da shi, ta ce"Na san ba na sauke duka nauyin da ya rataya a wuyana ta ɓangaren kula da gidan nan, ni ma ba na son zaman yara a maƙota, ga shi kai ma ana katse maka kasuwa, da safe a katse maka bacci ka tashi ka shirya su, su tafi makaanta..."
"Ai duk na san wannan Yusra, ki tafi gaɓa ta gaba" Ya katse ta da faɗin hakan.
Ta ce"Dama tunani na yi, na ce me zai hana na samo mana ƴar aiki, sai ta dinga kula da gidan idan ba na nan ko?"
Ya yi shiru yana nazari, saboda bai taɓa zaton jin haka daga bakinta ba.
"Ka amince na samo?" Ta tambaye shi jin ya yi shiru.
Ya girgiza kai ya ce"Yusra ba na son ƴan aikin nan, kuma ma gidan nan bai yi girman da za a buƙaci ƴar aiki ba, indai don kula da yara ne, zan duba yiwuwar duk ranar da kike yin aikin kwana a kai su gidanmu su kwana a can, ni kuma zan kula da kaina, sai ki taya ni addu'ar Allah Ya ba ni ikon riƙe kaina, idan kuma na ga hakan duka bai yi daidai ba to ina ba ki haƙuri, don gaskiya zan iya ƙara aure..."
"Wai da gaske?" Ta katse shi da tambaya, idanuwanta sun kawo ruwa, ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.
Ta ce"Sadiq ka san zan iya haƙura da aurenka saboda kishiya?"
Ya yi guntun murmushi ya ce"Ban sani ba, kamar yadda ke ma na tabbata ba ki san zan iya ƙara aure saboda na tsare mutuncina da tarbiyyar yarana ba ko?"
Tashi ta yi za ta bar wurin, ya ruƙo hannunta, ta fizge hawaye suna sakko mata, ta shige ɗaki ta kwanta, tana kuka mai cin rai.
ALI
Bayan sallar isha'i yana shirye-shiryen komawa gida kwatsam sai ga Reza ta zo har majalisarsu, ya haɗe rai duk da yana ɗan fargaba saboda ya san ba ta da kirki, gefe ya ja ta don kar ta yi masa tonon silili a cikin mutane, ya ce"Haba Reza don Allah ki sakar min mara na yi fitsari!".
Ta ce"Kai dalla can, ni harkar arziƙi ce na zo maka da ita, kana so na ka biya ni kuɗin?"
Ya ce"Wallahi ina so, rashin kuɗin ne kawai, idan akwai ai ba zan bari ki yi ta bibiyata haka ba".
Ta ce"To albishirinka".
"Goro!" Ya faɗa cikin ƙosawa.
Ta dafa kafaɗarsa ta ce"A daren nan za ka iya biyana cikin daɗin rai, wataƙil ma ka samu jari sanadin hakan".
Ali ya ce"Don Allah Reza ta fi kai tsaye, sai kwana kike sha".
Ta ce"Wallahi wata ƙawata ce take neman mai ɗauke mata kewa, ta kira ni ta ce na lalubo mata mai jini a jika, za ta ba shi dubu biyar, sai na ga tun da kana ta ƙoƙarin biyana awon shinkafa ya hana me zai hana ka je kawai, ka ga sai na riƙe kuɗin da za ta ba ka, ka biya ni kenan?"
Ali ya ɗan sosa kai yana tunani, yana son zuwa yana fargabar kar ya daɗe ya shiga komar Maryam, amma wannan wata babbar dama ce, ko babu komai zai sauke duka kewar dake tattare da shi, sannan ya huta da nacin Reza na neman biyan bashinta, ya sauke numfashi ya ce"Ina ne gidan?"
"Biyo ni!" Ta faɗa tana wucewa gaba, ya kai wa abokinsa Hamza mukullin babur ɗinsa yana faɗa masa yana zuwa,ya bi ta a baya zungui-zungui, suka shiga adaidaita sahu suka ɗauki hanya.
Suna fara tafiya sai ga kiran Maryam ya shigo wayarsa, ya ƙi ɗauka don bai san me zai ce mata ba. A ƙofar wani babban gida suka tsaya, suka fito ta ɗauki waya ta yi kira, babu jimawa wata babbar mace ta fito ta ba wa Reza kuɗi idonta a kaina, sannan muka shiga Reza ta koma, sai ƙarewa gidan kallo nake, wanda nake mamakin a ce mace ce ita kaɗai take rayuwa a cikinsa, haka dai nake biye da ita har cikin babban falon da ya ji kayan more rayuwa, sanyin Ac sai ratsa ni yake yi, babu wani tsayawa bayani ta nemi gudanar da abin da ya kawo ni kai tsaye, ni kuwa ban yi ƙasa a gwiwa ba wurin faranta mata, har ban san tsawon lokacin da na ɗauka ba.
Kafin na fito daga wanka ta kawo min abinci mai rai da lafiya, dama yunwa nake ji, na ci na ƙoshi na kora da lemo mai sanyi, sai a lokacin ta kalle ni ta ce"Ya sunanka?"
"Aliyyu" Na ba ta amsa ina murmushi.
Ita ma murmushin ta yi min ta ce"Gaskiya na ji daɗin haɗuwarmu, nawa Reza ta ba ka?"
"Dubu biyar" Na ba ta amsa.
Ta ce"Ni zan ƙara maka dubu biyar yanzu, sai dai babu cash a hannuna, kuma ATM ɗina ya samu matsala, ka kwanta ka huta bari na shiga maƙociyata ta ara mini, ko na daɗe kar ka fito".
Ya jinjina mata kai cike da farin ciki, sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga sha ɗaya saura mintuna, ga miss call ɗin Maryam rututu har da massages, tsoro ya kama shi, gabaɗaya hankalinsa ya tashi, Allah Ya taimake shi ba ta daɗe ba ta dawo, ta ba shi dubu biyar, sannan ta shiga kitchen ta fito da leda ta ba shi, ta ce"Ga mai adaidaita nan zai kai ka sauke ka, ka ga dare ya fara yi".
Ya ce"Na gode sosai Hajiya". Suka yi musayar lamba, ya fita ya shiga adaidaita sahun yana yi masa kwatance har suka ƙarasa.
A sanyaye ya ƙarasa gidan nashi, yana tura ya ji shi a rufe kamar yadda ya yi zato, ya ciro waya ya kira ta, bugu ɗaya ta ɗauka "Ki zo ki buɗe min, ina ƙofar gida". Ya faɗa da fargaba.
Yana jin motsin buɗewarta, ya mayar da ledar hannunsa bayansa ya ɓoye, tana buɗewa ko kallonsa ba ta yi ba ta juya ta koma, ya rufe gidan ya ajiye ledar a zaure, ya shiga yana karanto la haula wa la ƙuwwata a hankali.
08028966015
[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
FIRST CLASS WRITERS
PAGE 4
Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅
GIDAN ALI
Ɗakin gado ta shige kamar kububuwa, kafin ya ƙarasa har ta kwanta, ya ƙaraso ya zauna a sanyaye ya ce"Love ba ki san mene ne ya tsayar da ni ba..."
Ta katse shi da faɗin"Babu ruwana da ko mene ne ya tsayar da kai, ka raba dare a waje, ni dai ba zan iya ba, don haka gobe ƙarfe shida a gidanmu za ta yi min in sha Allah!".
"Innalillahi! Haba Maryamata, ai ya kamata ki ji hanzarina, wallahi aiki ne ya sha kaina, ganin ga azumi yana matsowa kuma ban tanadi komai ba, shi yasa na ce bari na dinga ƙara lokacin tashi saboda na linka samun kuɗin, amma tun da hakan bai yi miki ba, shi kenan na haƙura kawai".
Ko juyowa ba ta yi ba, ballantana ta nuna ta san yana yi. Ya zaro dubu biyu yana miƙa mata ya ce"Ga wannan kya sayi hoda".
'Ko uwar hoda ba!' Ta faɗa a zuciyarta, tun da ba ta ga amfanin yin kwalliyarta ba, kafin ta yi wanka yake fita, sai dare ya dawo, da daddaren za ta yi ta zambaɗa hoda kamar wata aljana? Ta yi ƙwafa a bayyane.
Ya tashi a sanyaye ya canza kaya, ya kashe wayarsa ya kwanta, sai kuma ya ba ta tausayi ganin bai ci abinci ba, bai yi wanka ba, duk da gajiya da yunwar da ya kwaso, kuma duka saboda ita yake yi, ya nemo mata abin da za ta ci ta sha da sutura, sai ta ji ba ta kyauta ba, to amma mazan zamanin nan ne sai kana saka ido sosai a kansu, idan ka ce za ka ɗaga musu ƙafa sai su fanɗare maka kana ji kana gani.
"Baka yi wanka ba kuma abincinka yana falo" Ta faɗa ba tare da ta juyo ba.
Ya ce"Babu komai, zan kwana a hakan".
Ba ta sake cewa komai ba, ta tashi ta fita, ta ɗauki a bincin ta kai kitchen ta buɗe ta rufe da kwando saboda kar ya lalace, shi kuma yana ta fargabar kada tsautsayi ya sa ta leƙa zaure, wata fitinar ta ɓallo, sai da ta dawo ta kwanta sannan