Showing 3001 words to 6000 words out of 21816 words

Chapter 2 - WANI AUREN BOOK COMPLETE BY SADIYA ABDULL.txt

12 Sep 2025

33

ta zaɓo mata, sai ta fara sana'o'inta, tun da idan ya kawo abin da za a dafa shi kenan, babu ruwansa da mahaɗi, ita ce gawayi, mai, magi, kayan miya, omo, sabulu da siyan ruwa, sai dai duk ranar da ya samu yana ba ta dubu ɗaya, saboda haka take ƙara dagewa a kan neman na kanta don ta rufawa kanta asiri.

A zaure suka yi kiciɓus da Zainab ta sha gabansa tana cewa"Haruna ni me kake nufi da ni wai? Jiya ko biyar ba ka ba ni ba yau ma..?"

Tana direwa ya ce"Ki yi haƙuri Zee, wallahi jiya ban shigo da komai ba, shi yasa ma kika ga na yi dare, saboda shinkafa ma a tata na ɗiba na saka a leda na ajiye kawai, saboda ta yi zaton da ita na shigo, amma yau dole zan shigo miki da wani abu, ai za mu haɗu ko tawan?"

Ta ruƙo hannunsa ta ce"Ko na karyawa fa ba ni da shi".

Ya sauke numfashi cikin sarewa da halinta, ya ciro ɗari biyun da Halima ta ba shi ya ba ta, ya fice. Ta soke a hularta, ta shigo gidan tana gyara rigarta da ta zame ta don ta ɗauki hankalinsa, ta shigo ta fara fifitawa Halima wuta tana ɗan ɗaga murya ta ce"Halima fito da barkonon na daka miki".

Tana murmushi ta fito da shi, a ranta tana jin daɗin irin kirkin Zainab da kakarta wanda yau satinsu uku kenan da tarewa a gidan, amma har sun saba.


08028966015
[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*


BY
SADIYA ABDULRAZAƘ


FIRST CLASS WRITERS


PAGE 2



Da ƙyar Maryam ta iya tashin Ali ya tafi masallaci sallar asuba, saboda nauyin da bacci yake yi masa, amma da ya idar da sallah sai da ya zauna a masallacin ya kunna data, ya dudduba saƙonni, lambar Baby Farha ya duba ya ga ba ta hau online ba, ya yi murmushi yana ayyana tana can tana bacci a cikin AC. Lokacin da ya dawo tana zaune a sallayar da ta idar da sallah, ya kwanta yana jira ta gama ita ma ta zo ta kwanta, ganin shiru ba ta da niyyar tashi ya sa shi cewa"Love me kike yi ne? Jiranki fa nake"

Nan take ta haɗe rai, dama ta san kwanan zancen shiyasa ta zaɓi ta yi zamanta har gari ya yi haske ta fita ta dafa shayi, sai ga shi dai ba ta tsira ba, ita kam tana son mijinta, tana kishinsa sosai, amma ta tsani ya neme ta a shimfiɗa, wannan shi ne babbar matsalarta, a zatonta rashin sabo ne da farko amma yanzu ga shi har auren ya yi wata shida a haka ake, ta sani ba ta ba shi haƙƙinsa yadda ya kamata, kawai yana ƙyale ta ne saboda a zauna lafiya kuma ta san yana shakkarta, hakan kuwa ya samo asali ne ta yadda yake bala'in sonta, sannan ya kasa maza da dama kafin ya same ta, ciki kuwa har da waɗanda suka fi shi komai na rayuwa, a lokacin an zuga Maryam sosai a kan aurensu, masu rufin asiri suna sonta amma za ta auri kafinta wanda zai kai ta gidan haya, ta ce ita ta ji ta gani.

"Ko ba zan samu ba?" Ya tambaye ta yana karaya da lamarinta, shi mutum ne mai ƙarfin sha'awa, wanda har yake ganin hakan shi ne ƙaddararsa, don tun da ya fara sana'a yake samun na kashewa ya fara neman mata bisa shawarar abokai, a yadda suke faɗa masa, ai shi saurayi ne ko a shari'a idan an kama shi ma bulala ce kawai, kuma yana yin aure zai daina, hakan ne ma ya sa shi dagewa ya yi auren don ya samu cikakkiyar nutsuwa da halalinsa, sai kuma Allah Ya haɗa shi da mace mai gudunsa, sosai abun yake ci masa tuwo a ƙwarya, don haka ya kasa yakice wa kansa wannan halayar, ko chart ɗin batsa duk yana yi ne saboda ragewa kansa damuwar nan da kuma sabo.

Haka dai ta je gare shi ranta babu daɗi, kuma ya san yau a haka za ta wuni da ƙuncin nan, shi yasa idan aljihunsa da nauyi yake gwammacewa ya tafi wurin matan banza inda za a faranta masa ya biya, a haka ne har bashin dubu goma ya shiga tsakaninsa da Reza, wanda ba dan haka ba da dubu biyar ɗin da ya ba ta jiya sai dai ya yi musu buƙatun cikin gida, ita kuwa ƙarya da yake yi wa ƴan mata a waya dama halinsa ne, ba ma zai taɓa iya dainawa ba.

Suna gama karyawa ya tafi aiki, ita kuma ta shiga harkokinta na cikin gida, tun tana gida sana'arta ce kitso da ƙunshi kuma har yanzun ma tana yi ba ta watsar ba, gidan nata ba ya rabo da mata, maƙotanta masu sana'a ma duk nan ne majalisarsu, ana kitso ana kitsa gulma, don ma dai ana shakkarta don ba ta da wasa, sai dai ko ba ta gama ba magriba tana yi ta rufe sana'a, ta gyara gida ta ɗora girki sannan ta yi wanka ta yi kwalliya, ta jira dawowar mijinta, idan da abin da ta tsana bai wuce duhu ya yi ta ganta ita kaɗai ba, da ƙyar ta amince da cewar sai takwas da rabi zai dinga dawowa gida, kuma tana gotawa za ta fara mita tana kiransa a waya, idan ta gaji sai ta rufe gidan ta jira shi a ƙofar gida. Yau ma kamar kullum, ta gama komai ta idar da sallar isha'i, ta kame tana jiran dawowarsa.

Tun da Ali ya fita da safe, wajen aikinsa ya wuce, ya shiga aiki tuƙuru, babu zancen kula kira da plashing ɗin da ƴan mata suke yi masa, yawanci waɗanda ba su daɗe da haɗuwa ba ne suke kiransa, amma duk wacce suka daɗe ta san da cewa Aliyyu ba ya haɗa aikinsa da komai, idan yana office ba ya ɗaukar wayarsa sai ya fito, da haka yake neman na kanshi domin ya samu asirinsa ya rufu, wajen aikin babu nisa da gidan iyayensa, a nan yake zuwa ya ci abincin rana ko a aiko masa, sai magriba ya tashi daga aiki, sallah ya yi ya shiga gidansu suka taɓa fira da ƴan'uwa, sannan ya tafi majalisar unguwar bai jima da zama ba Reza ta kira shi, ya ɗauki wayar kamar zai yi kuka ya ce"Reza idan kin yi haƙuri ma ai zan kira ki".

Ta ce"To ina jiranka...".

Ya katse ta da faɗin"Ki ƙara min haƙuri don Allah, wallahi ba su samu ba, sai dai ko gobe".

Ta ce"Ali kar fa ka mai da ni ƴar iska".

Ya yi dariya ya ce"To da mece ce?"

Ta ce"Dariya ma kake yi kenan! Wallahi idan ban zo gidanka na tona maka asiri ba shegiya ce ni, ɗan iska ka yi auren ma ba ka daina cin bashi ba".

Ali ya ce"Ni dai ki yi haƙuri, tsautsayi ne ya ja ni, da ba ki zage ni ba".

Ta ce"Ka nemi kuɗina ka ba ni".

Ya ce"Gobe zan kawo miki in sha Allah!" Suka ajiye waya.

Ya fito daga sallar isha'i kenan sai ga kiran Maryam, yana ɗauka ta ce"Na ji shiru, wallahi yunwa nake ji yau, don Allah ka dawo da wuri".

Bai ce komai ba ya kashe wayar, ya buga babur ɗinsa, abokansa suna ta yi masa tsiya, Madam ta yi kira, shi dai ya ɗauki hanyar tafiya gida, yana takaicin yadda take kafa masa takunkumin nan, sai ta ce ba ta iya cin abinci ita kaɗai, kuma ta yi ta kiransa tana ce masa yunwa take ji, ya dawo su ci.

Tana zaune tana kallo a waya ya same ta, ta yi masa sannu, ta kai masa ruwa ya yi wanka, sannan ta kawo musu abinci, suna cikin ci sai ga kira a wayarsa, sai da gabansa ya faɗi saboda harƙallar rashin gaskiya da yake yi, indai aka kira shi a gaban Maryam sai ya ji faɗuwar gaban nan, da ya ga abokinsa Hamza ne mai kiran sai ya ji dama-dama, ya ɗaga yana cewa"Hamza ya ne?"

Daga can ɓangaren Hamza ya ce"Wallahi aboki wani kaya ne mai zafi ya samu, sai ka gani dai ka fito muna bayan layinku".

Ƙirjinsa ya ba da rass, ya kalli Maryam wacce ta dakata da cin abincin ta kafe shi da ido, don duk a abokansa ta fi tsanar wannan Hamzan, tun da ta lura ya fi maƙale masa, kuma tana jin sautin wayar ta ji ana magana da kurman baƙi, ta fara tunanin wane kaya ne me zafi mijinta zai siya?

Tsam ya tashi zai fita, yana hello hello, alamar babu network, bai ankara ba ya ga Maryam ta ruƙo rigarsa ta zaunar da shi, ta yi masa nuni da abincin dake gabansu.

Cikin karaya ya ce"Hamza wai katakon ne aka samu masu kyau?"

Hamza ya ce"Kai dalla Malam ina yi maka zancen kaya kana ce min katako, wata mai zafi aka samu fa, kuma wallahi babu tsada..."

Da sauri Ali ya katse shi da faɗin"Au shadda? Ai sai ka ce min wannan shaddar da zan siya wa Maryam an samu, ka tsaya kwana-kwana?"

Hamza ya ce"Kana gida ne?"

Ali ya ce"Ina gida, amma ka ajiye min gobe za mu yi magana, duk da ba ni da kuɗin ma". Suka yi sallama, ya kalli Maryam yana sauke ajiyar zuciya, suka ci gaba da cin abincin tana auna maganganunsu a zuciyarta.

Yau ma dai gajiya ta yi da ƙarar radionsa ta je ta kwanta, hakan ya ba shi damar dulmiya duniyar wayarsa, ya yi mamaki da har Baby Farha ta fara yi masa zancen yaushe zai je gidansu? Hakan ya ba shi tabbacin ba ƴar ƙarya ba ce, don ƴan ƙarya yana cewa zai je suke kawo masa uzuri har a bar zancen, ya faɗa mata zai zo cikin satin, sai kuma ya fara tunanin kayan da zai saka, don hotunan da ya tura mata sun kwana biyu, yanzu kayan sun sha wanki, ya fara tunanin dole nan gaba ya fara aron kayan sakawa kafin ya ɗinka sababbi, da wannan tunanin ya yi bacci, bayan ya gama tashin kan ƴan mata da ƙarya.



GIDAN SADIQ

Yau tun magriba ya rufe shagon, ya je ya kwaso ƴaƴansa, saboda ba ya son barinsu a maƙotan nan don dai babu yadda zai yi ne kawai, gida suka shiga ya canza musu kaya, ya wanke unifom ɗin, sannan ya saka musu tuwo, shi ma ya saka, suna gamawa ya ɗakko littafansu babu home work sai ya yi musu bitar karatu, ya kunna musu surar da suke a islamiyya, suna saurara har bacci ya ɗauke su, a gida ya yi sallar isha'i, ya yi musu shimfiɗa suka kwanta ya tofe su da addu'a, sannan ya kira lambar Yusra har sau uku ba ta ɗauka ba, tun jiya yake cikin yanayi na buƙatuwa, amma babu yadda zai yi kamar dai gwauro, sau da yawa yakan yi tunanin duba shawararwarin da mahaifiyarsa take ba shi akan aikin Yusra, ko dai ya mata tilas ta ajiye ta kula da gidanta, ko shi ya ƙara aure, amma idan ya tuna yadda take da kishi sai ya kau da zancen, saboda yana ƙaunarta, ba ya son abin da zai kawo rabuwar kai a tsakaninsu, duk da ya san ba za a taɓa dawwama a haka ba, don hanyar da gidansa ta ɗakko ba mai ɓillewa ba ce, da wannan tunanin bacci ya ɗauke shi. Sai wajen sha ɗaya ya ji ringin ɗin wayarsa ya duba ya ga ita ce, kamar ya share sai kuma ya ɗaga don wataran takan dawo cikin daren ta ce ta gudo, jin tana tambayarsa ya gidan yara sun yi bacci? Kawai sai ya kashe wayar ma duka ya ci gaba da baccinsa.

Da safe shayi ya dafa musu da ɗumamen tuwo, ya yi musu wanka ya shirya su suka tafi makaranta, shi ma ya tafi shago. Tana dawowa ta gyara gida, ta sha sauran shayin da biredi, ta yi wanka ta zauna har za ta kira wayarsa ta fasa, don kar ma ya ce zai zo, ta yi kwanciyarta, da wuri ta yi girki, ta zuba na yara ta kai musu maƙota, sannan ta zuba na shi ta bawa yaro ya kai masa, ta zuba nata a kula ta tafi kemis, daga nan ta wuce asibiti.

Yau dab da magriba ta dawo, kusan lokaci ɗaya da yaranta, ta shiga ta taho da su, suna ta farin cikin yau Momynsu tana gida, sosai suke kewarta idan tana yin aikin kwana, don ma wani lokacin tana zuwa har islamiyyar ta gansu, cike da farin ciki suke ta ba ta labarin makaranta, su suka zaɓi abincin da za a dafa, ta ɗora, suka yi sallah tare, sannan ta yi musu wanka, tana taya su home work har ta gama girkin, suka ci a faranti ɗaya cike da ƙauna irin ta uwa da ƴaƴanta, bayan sun gama ta ba su wayarta suna ta kallon bidiyoyin yara na ilimi har suka yi bacci, ta gyara shimfiɗa ta kwantar da su, sannan ta yi wanka ta shirya cikin kayan bacci.

Tana kwance tana ɗan taɓa chatting ya dawo, wajen tara da rabi, ta je ta karɓi ledar hannunsa tana yi masa murmushi mai cike da ƙauna, ta kai kitchen ta taho da abincinsa, kafin ta fito har ya shiga wanka, a bakin gado ta zauna ta ɗauki wayarsa da ke ajiye, wacce ta san babu ruwan shi da saka cord, ta duba call long ta yi murmushi ganin duk amintattun kira ne babu na zargi, haka ma massages, shi babu ruwansa da chart, babu ma App ɗin whatsApp a wayar, sai facebook da yake da tsirarun abokai, wannan tana yawan dubawa ta wayarta don ta ga abokansa, tun da nan ma bai wani saka tsaro ba.

Tana ajiye wayar yana fitowa daga banɗakin, ta sakar masa murmushi, ya yi mata murmushin gefen baki, jikinta ya ɗan yi sanyi, don ba haka suka saba ba, a hankali ta ƙarasa inda yake tsaye a gaban sif yana duba kayan da zai saka, gabansa ta je ta tsaya ta riƙe duka hannuwansa daga ɗaukar kayan, ta shiga jikinsa ta kwanta, ya shafa kanta bai ce komai ba, ta ce"Na ga kamar kana cikin damuwa".

Kai tsaye ya ce"Ai ke ce".

Ta ce"To ka yi haƙuri, yanzu ba ga ni ba?"

Ya ja hannunta zuwa gadon, tana ta narke masa, har suka samu nutsuwa cike da ƙaunar juna, sun yi wanka sun fito suna cin abinci ta lura da yadda har lokacin ba ya cikin shauki kamar da, ta tattara hankalinta gare shi ta ce"Masoyi akwai abin da yake damunka bayan kewata, don Allah kar ka ɓoye mini".

Ya yi saurin girgiza kai, ya ce"Babu komai Masoyiya yanayi ne kawai, kwana biyu kamar zan yi zazzaɓi, kuma kewarki ce take haddasa mini irin hakan, ina da mata amma na kwana da kewa kamar mara gata...".

Ta katse shi a shagwaɓe ta ce"Don Allah kar ka ce haka, yanzu ba ga shi kewa ta tafi ba?"

Ya ce"Amma haka zan rayu ba kodayaushe zan samu kulawarki ba?"

Ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, yanayi ne ya zo da haka".

Ya ce"Amma idan na ce miki yanayi ya saka ni son ƙara aure za ki fahimta?"

"Sadiq! Aure za ka yi?" Ta tambaye shi a tsorace

Ya girgiza kai ya ce"Sam, kawai tambayarki na yi".

Jiki a sanyaye ta ce"Wannan bai kai dalilin ƙara aure ba, kuma ma na ga..."

"Ya isa, gwada ki na yi fa" Ya katse ta.

Ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi ba don ta yarda da cewar gwajin ba ne, da wannan tunanin ta kwana a ranta.


GIDAN HARUNA

Kasuwa Haruna ya nufa kai tsaye, don yaron shago ne, kasancewar babban shago ne ana biyansa daidai gwargwado, sai dai wannan halayyar tasa da ta zame masa katankatana ita ce take lamushe duk wani abu da zai samu, duk a zatonsa idan ya yi aure shi kenan matsala ta mutu, da farko kamar gaske sai daga baya ya ji ya rage samun nutsuwa da Halima, sannan ma sam ba ta da wayewa ta wannan fannin, ta ƙi sakin jiki da shi, su na bazan sun fi ta iya komai da yake so, shi yasa ya fi samun nutsuwa da su. A duk inda ɗan bariki ya haɗu da ɗan'uwansa ba ya ɓuya, don haka tun a satin farko da su Zainab suka tare a gidan ya gane ita ma ƴar hannu ce, kamar da wasa wataran zai shiga wanka tana zaune ya tsaya yana kallonta, sai ya ga ta ɗage masa gira tana kashe ido, ya yi murmushin jin daɗi don tun a ranar farko da ya fara ganinta ya kwaɗaita da ita, bayan an kwana biyu yana ƙofar gida ta zo za ta shiga kawai ta shafa bayansa za ta shige, ya taso da sauri yana miƙa mata wayarsa, ta saka masa lambarta, kuma tana shiga gida ya kira ta, su ka yi ta waya kamar sun saba, daga nan suka fara chart na musayar kalaman banza don kar ta san kar babu wani abun ɓata lokaci, sautari idan zai shigo gida yakan taho mata da leda tsire ko balangu ko dangin kayan sanyi, kafin ya ƙaraso sai ya yi mata waya ta same shi a zaure, ya lalube jikinta ta karɓi leda ta shige gida, sannan shi ma ya shiga kamar ba a yi komai ba, duk ranar da bai taho mata da komai ba ba ya faɗa mata ga shi nan zai shigo, ita kuma da safe sai ta daidaici fitarsa sun haɗu a zaure, don tana da mugun son banza, irin matan nan ne ma su yi wa maza kankat idan suka shiga komarsu.

Yau ma hakan ce ta faru, ya samu alheri a kasuwa babu laifi, don haka ya ƙunso mata balangu mai zafi da yogurt, ya sayi taliya leda uku, sabulun wanka da omon wanki, don ya ragewa Halima.

A zaure ya tsaya ya kira ta ba ta ɗaga ba, don lokacin tana tsakar gida wayar tana ɗaki, tana ganinsa ta taho da sauri za ta rungume shi, ya kauce yana kallon ɗakinsa ya ce"Haba Zee mene ne haka?"

"Naki yana zaure" Ya faɗa yana saurin shigewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login