Showing 1 words to 3000 words out of 21816 words

Chapter 1 - WANI AUREN BOOK COMPLETE BY SADIYA ABDULL.txt

12 Sep 2025

26

[7/30, 5:30 AM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*



BY
SADIYA ABDULRAZAƘ



FIRST CLASS WRITERS


Page 1



GIDAN ALI

Lokaci zuwa lokaci take kallon agogo tana ƙwafa, kana kallon fuskarta za ka gane cike take da ɓacin rai, ƙarfe tara tana cika cif ta ɗauki hijjabi ta saka ta ɗakko mukullin gidan ta fita ta kulle, ta ja tinga ta tsaya a ƙofar gidan, ba ta yi minti goma ba ta jiyo ƙarar babur, tana juyawa ta ga shi ne ya shawo kwana kamar yadda ta yi zato, ta ƙara haɗe gira hannunta harɗe a ƙirji. Ali ya ƙaraso yana haɗe fuska "Maryam idan ba za ki buɗe mini ba na koma inda na fito!". Ya faɗa ganin ba ta da niyyar buɗe gidan tana binsa da kallo, ta girgiza kai ta buɗe sai da ya shiga sannan ta bi bayansa ta saka sakata, cike da mita yake cewa"Wannan wane irin hali ne, ki dinga cewa kina jin tsoron zama ke kaɗai, saboda tsabar raini sai ki fito ƙofar gida ki tsaya masu wucewa suna kallonki kina kallonsu wannan ai raini ne!".

Maryam tana cire hijjabi ta ce"Duk yadda ka ɗauka, ni dai ba zai taɓa yiwuwa ka fita tun safe sai dare ba kuma ace daren ma wai ba ka da lokacina sai ka gama fira a majalisa, ka ɗakko ni a gidanmu mai cike da jama'a ana raha ana dariya ka zo nan ka kulle ni kai kana majalisa? Kar ka ga ina tsayawa a ƙofar gida, wallahi duk ranar da ka yi sake na gano majalisar nan taku sai dai a fara zaman da ni..."

Ransa ya ɓaci ya ce"To bisimillah ai ga hanya nan, wallahi Hamza sai ya kai sha biyu a waje, amma dayake shi yana da ƴanci matarsa ko waya ba ta isa ta yi masa ba, ke da nake dawowa takwas da rabi ba za ki godewa Allah ba?"

Ta taɓe baki ta ce"Ita ta ga za ta iya, don ni wallahi duk ranar da ka kai ƙarfe goma a waje ka saka a ranka babu kai babu kwana a gidanka, don wallahi tabarma zan kai maka shago kafin ka dawo!". Daga haka ta fita ta ɗauki bokiti ta zuba masa ruwan wanka ta kai masa banɗaki tana ci gaba da mita "Ni an isa a dawo min gida sha biyu, sai ka ce ƴar iska mutum ya ajiye? Tab".

Kafin ya fito daga wanka ta kawo abinci falon, ta zuba musu, suna gamawa nefa suna kawo wuta, ta ɗauki wayarta ta jona, za ta ɗauki tashi ya ce ta bar shi yana da caji, ta kunna kallo a ƙaramar tv dake falon, tana kuma jansa da fira yana mazewa, ganin hankalinsa ba ya kanta ya sa ta tattara hankalinta kan tv.

Shi kuwa Aliyyu jinsa yake tamkar a kan ƙaya, hankalinsa sam ba ya gidan da yake a zaune, fargaba ce fal zuciyarsa, saboda sanin halin Reza wacce ya karya mata alƙawarin haɗuwar da za su yi yau don ya ba ta rabin kuɗinta ya kuma ba ta haƙuri kan sauran kuɗin, amma saboda sanin halin Maryam dole ya haƙura ya dawo gida, wayar ya ɗauka ya saka a silent, babu jimawa kuwa sai ga kira yana dubawa ya ga Rezar ce, gabansa ya faɗi, ya ɗan tura wayar ƙarƙashin kujera, amma hankalinsa yana kanta yana ta ganin haske na kawowa yana ɗaukewa, sai jan tsaki yake cike da fargabar furucin Rezar na cewa yau har gidansa sai ta zo akan kuɗinta. Maryam wacce tsakin ya fara ba ta mamaki, ta juyo tana haɗe gira ta ce"Wai ni kam Love tsakin me kakr ta jerowa ne? Na lura tun da ka dawo ba ka da nutsuwa".

Ya sauke numfashi ya ce"Wallahi Love mantawa na yi ban siyo biredi ba, shi ne duk abin ya dame ni".

Lokaci ɗaya ta haɗe rai, don ta san indai ya fita siyan biredin nan fa sai an gan shi, ta ce"Ka bar shi kawai, a dafa indomi".

Ya ce"Ai kuma shayin nake son karyawa da shi, wallahi minti biyar ya yi yawa, kin ji?" Ta juya kai ba ta ce komai ba, hakan ya sa ya gane ta yarda ya fita amma ba da son ranta ba.

Ya tashi zai fita, ta ce"Ara min wayarka".

Ƙirjinsa ya buga, ya ce"Ai fa yau ƙaraf na dawo gidan, transfer zan yi wa mai biredin".

Ya fice yana jin salama a ransa, sai da ya yi nisa da gidan sannan ya kira lambar Reza, tana ɗagawa ta fara masifa"Wai kai Ali ni za ka rainawa hankali saboda ka yi aure ko? To idan ban kashe auren ba Allah Ya..."

Kafin ta ƙarasa ya katse ta da faɗin"Subhanallah! Haba Reza, ke me yasa ba ki da uzuri? A ina za mu haɗu?"

Tana faɗa masa gidanta zai kai mata ya kama hanya jiki na rawa saboda da ɗan nisa, kamar zai yi kuka saboda takaicin fitar da kuɗin ya ba ta dubu biyar yana ba ta haƙurin gobe zai cika mata dubu biyar, duk da ya san ba zai taɓa yiwuwa ya bata a goben ba, don wannan biyar ɗin ma da ƙyar ya haɗa ta, ya bar gidan zuciyarsa fal ƙunci, a hanya ya tsaya ya sayi biredin ya koma gida da ƴar fargaba.

Har ta yi bacci saboda an ɗauke wuta kuma ya daɗe, ya ɗauki radionsa dake kan mudubi, ya haska ta a ransa yana cewa'fitinanniyar yarinya', sosai yake jin daɗin saurin baccinta, saboda daren ne kawai yake da lokacin wayarsa inda yake cin karensa babu babbaka da ƴan matansa, falo ya koma ya kwanta ya kunna radion ya ajiye, don haka yake yi idan Maryam za ta takura masa kan ya zo su kwanta, sai ya ce shiri yake ji, ko ta yi zaman jiransa jin radion ba ya ƙarewa, sai ta haƙura ta je ta kwanta. Data ya kunna ya shiga chart da Baby Farha wacce jiya suka haɗu da ita a wani group ɗinsu mai suna ƴan hutu, sosai jiya ya ji daɗin haɗuwarsa da ita kuma daga ganin hotonta ƴar hutun ce da gaske, saboda haka bai yi ƙasa a gwiwa ba ya shiga sharara mata ƙarya da nuna shi ma ɗan hutun ne kuma babban ɗan kasuwa, suna ta fira idan zai yi mata voice sai ya kashe radionsa ya narke murya yana iyayi kamar mace, shi a dole ɗan hutu.

Sai ƙarfe ɗaya Maryam ta farka, yana jin ƙarar ɗaukar buta ta shiga banɗaki, ya yi maza ya kashe wayar duka ya baje a ƙasan kafet yana jan munshari. Ta leƙo ta haska shi tana mai jin tausayinsa, ta san a gajiye yake saboda yanayin aikinsa na kafinta, ga shi wuni yake a can, ta kira sa da 'Love' Ya tashi a firgice yana mirtsika ido ya ce"A...wai bacci na yi a nan? Ikon Allah kin ga fa radio nake ji ashe bacci ya ci ƙarfina". Ya kashe radion da ke ta shuuuu don tuni sun rufe gidan radio, ya kulle falon.

Kafin ya shiga ɗakin gadon har ta kwanta, ta baje don ci gaba da baccinta, a hankali ya kai hannunsa jikinta, wanda ta ji saukar hannun kamar saukar wuta a jikinta, idan da abin da ta tsana a aure to wannan fannin ne, tsam ta cire hannunsa daga jikinta ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, wai sau nawa zan faɗa maka duk wani abu da ya biyo bayan bacci haramun ne?".

"Hmm!" Ya sauke ajiyar zuciya, yana matsawa gefe, don shi dai ba wani zurfi ya yi a islamiyya ba, ganin ita kuma ta yi karatun ya sa shi zaton wannan hadisi ne, cewar ba a tashin mace a neme ta idan ta riga ta yi bacci, ajiyar zuciya ya sauke, ya juya mata baya, a zuciyarsa yana ta hango surar Baby Farha wacce yake so yana samun wasu kuɗi da yake jira ya ziyarce ta, idan Allah Ya taimake shi ƴar hannu ce sai ya san yadda zai ɓullo mata.


GIDAN SADIQ

Riƙe yake da hannun ƴaƴan nasa biyu mata wanda ya karɓo su daga maƙota, Afna har ta fara bacci aka tashe ta, ita ma Fanan daga gani baccin ne a idonta, ya buɗe gidan suka shiga zuciyarsa sam babu daɗi, kaca-kaca ya tarar da falon, ya yi ƙwafa ya kalli yaran ya ce"Kun ci abinci?" Suka girgiza masa kai alamar ba su ci ba, ya shiga kitchen, nan ma ya tarar da wanke-wanke a zube, nan ya duba kuloli da tukwane ya fahimci ba ta yi girki ba ta fita, idan da sabo ya saba da yin girki, don haka ya kunna gas sai ya ga ashe ya ƙare, tsaki ya yi ya ɗakko flas ya ga wayam babu ruwan zafin ma"Allah na gode maka!" Ya faɗa yana buɗe wani ɗan bokiti ya ɗauki plate ya zuba cake ɗin da ke ciki, ya dawo falo ya buɗe firji ya ɗakko lemo ya zauna yana janyo yaran jikinsa, ganin duk sun noƙe yasa shi ƙirƙirar murmushi ya ce"Ku zo mu ci ko".

Fanan da ita ce babba ta ɓata fuska ta ce"Daddy da rana ma fa shi muka ci, da safe ma da shi muka je makaranta, kuma ma Afna ba ta so, ni ma ya ishe ni".

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Ku yi haƙuri ƙawayena ku ci kun ji? Babu kyau kwanciya da yunwa".

Da ƙyar ya lallaɓa su, Fanan ta ci, ita kuwa Afna sai shayi ya haɗa mata da ruwan sanyi, shi ma tun safe babu komai a cikinsa, don haka ya ci cake ɗin, yana son duba littafansu ko da home work amma ya san bacci suke ji, ya yi musu shimfiɗa a ɗakinsu ya kwanta a ƙasa su suna gado, bayan ya yi musu addu'a sun fara bacci, ya janyo wayarsa ya kira lambar mahaifiyarsu.

"Hello Masoyi sorry yanzu nake shirin kiranka". Ta faɗa ta cikin wayar cike da kulawa.

Jin ya yi shiru ya sa ta sake cewa"Ina yaran, ka dawo gida?"

Ya ce"Yusra me yasa gas ya ƙare ba ki faɗa min ba?"

Ta ce"Oh my God! Wallahi na manta, na so ma na aiko Nura ya ɗauka sai na sha'afa".

Ya ce"Amma me kike yi tun da rana a gidan?"

Cike da gajiyawa ta ce"Oh! Yau fa na zauna sosai a kemis, kuma na je wani gida karɓar haihuwa, sai magriba ma na shiga asibiti a latti".

"Ok sai da safe" Ya faɗa yana shirin katse kiran.

Ta ce"Na gode Masoyi".

Ya ajiye wayar yana tunanin kalar rayuwar gidan nasa, da haka bacci ya kwashe shi, yana dawowa daga sallar asuba ya ɗora musu abin karyawa a electric kasancewa akwai nefa, shi ya shirya yaran suka ci abinci ya saka musu wanda za su tafi da shi, ya bar mata nata, ya jira mai mashin ya zo ya tafi da su makaranta, shi ma ya tafi shagonsa na provition da babu nisa da gidansa.

Bakwai da rabi Yusra ta koma gida, don ta tsaya jiran wacce za ta karɓi dutyn safe, saboda tana bawa wata mai naƙuda kulawa sosai, ba ta so ta barta sai ta damƙa ta a hannun wacce ta san za ta kula da ita, duk saurinta ba ta tarar da su a gidan ba, bacci ne fal idonta amma haka ta haƙura tana ajiye jaka ta shiga kitchen ta fara wanke-wanke, sai da ta gyara ko'ina gidan ya dawo hayyacinsa ya ɗauki ƙamshi sannan ta ci abincin da ya ajiye mata, ta yi wanka ta ɗauki waya ta kira shi, "Ina kwana?" Ta gaishe shi bayan ya ɗauki wayar.

"Kin dawo?" Ya tambaya ba tare da ya amsa gaisuwar ba.

Ta ce"Na dawo".

"Ok anjima kaɗan zan kawo cefane". Ya faɗa yana sauke numfashin da ta san fassarsa.

Ta ce"Ka bar shi, wake da shinkafa zan yi ai, kuma Nura zai zubo gas".

"Zan zo dai" Ya faɗa.

Ta ce"Masoyi da ka haƙura dai, wallahi jiya ban samu bacci ba, yanzu ina dawowa na hau kan aikin gida, bacci zan yi kafin na tashi ɗora girkin rana, kaina har ciwo yake".

Yana haɗiye ɓacin ransa ya ce"Amma yau ma fa dutyn dare za ki fita, ba kya tunanin..."

Ta katse shi da faɗin"Don Allah Masoyi, gobe ina gida fa".

"Ok" Ya faɗa, yana katse kiran. Ita kuma ta gyara kwanciyarta ta fara bacci hankali kwance. Sai sha biyu ta tashi, ta kira yaronta Nura ya sako mata gas, har ma da cefanen kayan miya, don ba ta son zuwan mijinta shi yasa ta ce masa ba sai ya kawo cefane ba, saboda ta san idan ya zo hana ta bacci kawai zai yi, shi ma ya katsewa kansa kasuwa, a gurguje ta yi shinkafa da miya, tana saukewa ta ɗora tuwon dare don shi a son samunsa kullum ya ci tuwo da daddare, amma ba kullum take samun damar yi masa ba, saboda aiki, ƙarfe ɗaya aka dawo da yaran daga makaranta, suka ci abinci ta yi musu wanka, sai da suka saka unifom ɗin islamiyya sannan ta fito da littafansu suka yi home work, tana sauke tuwo ta yi wanka, ta shirya ta ɗauki abincin Sadiq ta haɗa kansu ta kai su makarantar da babu nisa da gidansu, sannan ta wuce shagonsa don kai masa abincin.

Gefe ta tsaya sai da na ciki suka fita, sannan ta ƙarasa murmushi ɗauke a kan fuskarta ta ce"Sannu da aiki Masoyi".

Ya yi guntun murmushi yana kallon yadda ta yi kyau tana zuba ƙamshi duk da ba kwalliya ta yi ba ya ce"Na gode". Ta ajiye masa kular tana cewa"Ya kake, komai ƙalau ko?" Ya gyaɗa mata kai yana ta kallonta.

"Kemis?" Ya tambaye ta.

Ta gyaɗa kai ta ce"E zan je na ɗan zauna, na gama aikin gidan, har tuwo na yi maka".

Ya ce"Kin kyauta kuwa, sai goben". Ta yi murmushi ta fice, yaran sun sani daga islamiyya maƙotansu za su shiga, sai ya dawo bayan sallar isha'i ya ɗakko su, duk da ranar da ba ta nan ne yake katse kasuwar, amma a ƙa'ida goma da rabi yake tashi.


GIDAN HARUNA

Ƙarar alarm ne ya karaɗe ɗakin, hakan ya sa Halima tashi a firgice, ta janyo wayar da ke kusa da ita ta latsa alarm ɗin ya mutu, bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci ta miƙe zaune, ta dafe kanta tana jin yadda ya sara mata, tun dare ta kwanta da ciwon kan, ga shi har yanzu bai sauka ba, sakkowa ta yi daga gadon ta fita tayo alwala ta dawo ta canza kaya ta kabbara sallar da ake yi ta asuba, tana lazimi tana gyangyaɗi har bacci mai ɗan nauyi ya kwashe ta daga zaunen, a firgice ta tashi ta ga gari har ya yi haske, ga kukan tsuntsayen da suke faɗa mata lokaci ko da babu agogo, da sauri ta fita ta kunna murhunta na gawayi, sannan ta dawo ɗaki ta fara firfito da kayan sana'arta ta wainar fulawa, wata matashiya ce ta fito daga ɗakin dake kusa da nata tana cewa"Ashe kin fito, yanzu nake cewa yau Halima ta makara".

Halima ta yi murmushi ta ce"Zainab ina kwana? Wallahi yau baccin ya yi mini nauyi ga ciwon kai tun jiya".

Zainab ta ce"Ai ke ce ba kya hutawa Halima, sai ki sha magani kafin ki hau suyar nan".

Jin ba ta bata amsa ba ya sa ta san ba ta da maganin, ta shiga ɗaki ta fito hannunta ɗauke da kofi da kuma maganin, kunun alkama da ta saba damawa ne ta miƙawa Halima tare da maganin, ta karɓa tana godiya, ta kwankwaɗe sannan ta sha maganin, Zainab ta ce"Zauna ya ɗan tsarga miki Halima bari na fifita miki wutar".

Ba don kan ya daina ciwo ba ta tashi ta hau suyar wainar, mutane suna ta shigowa suna siya, yawancinsu ƴan makaranta ne, sai da ta gama tsaf sannan ta saka a farantai biyu ta miƙawa Zainab ta leƙa ɗakin da Zainab ɗin ta fito wanda kakarta ke ciki tana jin radio ta miƙa mata, suna gaisawa.

Ta dafa shayi ta juye a flas ta ɗauki wainar da ta zuba a wata ƴar kula ta kai ɗaki ta ajiye, tana nan zaune a tsakar gida tana wanke-wanke yaron da yake kai mata tallar wainar makaranta ya zo ya ɗauka ya tafi, bayan ta share tsakar gida ta shiga ɗaki ta auno shinkafar da take dafawa ta siyarwa ta fito ta fara tsince ta, sai da ta gama ta ɗora tukunya ta saka wake, sannan ta koma ɗaki ta tarar mijinta ya tashi, ta kalle shi cike da takaici ko sallar asuba bai yi ba, sai yanzu zai yi idan har an yi sa'a yana da niyyar yi a ranar, ta kalli yadda daga tashinsa har ya ɗauki waya duk da ta san halayyarsa ce amma tana takaicin abun.

"Ga wainarka da shayi" Ta faɗa tana tura kayan gabansa

Ya ce"Ki ɗan dafa min taliya da ita zan karya, wannan wainar kuma ki samu leda ki saka min".

Ta ce"Taliya ai ka san ta ƙare".

Ya yi tsaki ya tashi ya fita don yin wanka, daga shi sai gajeren wando, wanda har zuciyarta ba ta son hakan, ko don Zainab da ke zaune a tsakar gidan kullum daidai wannan lokacin, ta yi masa ƙorafi har ta gaji, ta lura abun ya bi jikinsa ne.

Yana gama karyawa ya fara sosa kai, tsaki ya ja fuskarsa ta nuna alamun damuwa, Halima da ta san kwanan zancen ta ce"Lafiya kake tsaki?"

Haruna ya ce"Wallahi Halima jiya zero na shigo gidan nan, wannan shinkafar ma bashi na karɓo ta, kin ga bai kamata yanzu na fita ban bar miki komai ba".

Ta yi guntun murmushi ta ce"Haba kar ka damu, Allah zai rufa asiri, watarana sai labari, ga wannan ka hau babur". Ta ƙarasa tana miƙa masa ɗari biyu

Ya karɓa ya ce"Na gode, kai ni kam na yi sa'ar mace ta gari, Allah Ya shi miki albarka".

Ta amsa da amin, shi kuma ya fice. Ta yi shiru tana tunanin kalar rayuwar auren da take yi, sam Haruna ba shi da zuciyar nema, dududu wata uku kenan da auren amma kullum a haka ake, dama a wurin da take siyar da abinci suka haɗu har ya aure ta, don haka da ta lura da irin mijin da ƙaddara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login