Showing 24001 words to 27000 words out of 84238 words
Chapter 9 - ROYALTY (YAN SARAUTA) by Mrs Alamin.txt
d'auko littafin da Ahmad ya bata ta bud'e tana dubawa kafin Khairat d'in ta fito su tafi..........................
MRS ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË 🌹.
Manzon Allah Saw
Aminci ga muftahul jannatun naimah
Aminci ga kiblar bayi a ran qiyama
Aminci ga Mai shiryarwa cikin salama
Aminci ga duk Mai matsayi dakai ya samu
Aminci ga duk Mai girma dakai ya samu
Aminci ga duk Mai daraja dakai ya samu
Aminci ga fatuhul Akbar aya imamu Yusrah Musa ce tare dani da gaisuwa ta🙏
Ka tausayawa zuciyata naganka ko sau d'aya a rayuwata.
Thanks for ur supports 🔥 nagode masoya ana tare insha Allah.
TYPING📲YMA DUTSE NEW WORLD 🌏 YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨✨💯.
👑 Royalty 👑
A*W*A
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta haka taken mu yake tafiyar mu babu rago babu maci amana tsantsan gaskiya muke nunawa.
STORY WRITTEN ND EDITING
✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR
Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 🌺.
6~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Taibanah.
Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿
@YUSRAHMS CE
Page 11 & 12
Tsabar yadda Baby tasa tafiyar Ahmad a ranta har mafarki tai wai ya tafi kuma harda su a rakiya saida asuba bayan sunyi sallah sunyi karatu Baby ta kalli Khairat dake shirin komawa ta kwanta duk da gari yayi haske sosai tace "Aunty Khairat kinsan wani abu? Kai Khairat ta girgiza tana kallon ta itama taji wanne irin mafarki tai harda tashi zaune tana gyara zama tace "ina jinki wanne irin mafarki kikai"? Kai Baby ta jinjina tana cewa "uhm inji me ciwon baki abun ba'a magana waifa mafarki nayi wai ya Ähmäd ya tashi tafiya mune 'yan rakiya" d'an zaro ido Khairat tai tana sakin dariya tace "tabd'ijan ahh dole kice ba'a magana wannan lamari yafi karfin mu wane mu" mi'kewa Baby tai tana cire hijab d'in jikinta ta aje tana cewa "um gane min hanya Aunty Khairat indai ba mu 'ka'kalowa kanmu dukan ban kwana ba mezai kaimu inda ya Ahmad yake randa zai tafi musamman idan ya sako kayan soldier d'in nan nasa wani irin kwarjini yake ko daga nesa na hangoshi da gudu nake 6uya kamar naga abun cutarwa haba gaskiya ya Ahmad yana lokaci muna shan kallo yau dai zamu huta please Aunty Khairat karki manta da partyn da zamuyi" Baby na rufe baki cikin tsokana Khairat tace.
"To zamuyi party amma saidai yanzu muje muyi masa sallama".
"Wa zamuyi wa sallama amma dai ba ya Ahmad ba"?.
"Shi mana ba shine zaibar masarautar ba".
"Amma da wasa kike Aunty Khairat mune zamuje yiwa ya Ahmad sallama aiko daya sallamar damu".
"No babu abinda zaiyi mana shima yau yana busy bazai bi takanmu ba tashi ma muje maybe muyi masa rakiya damu".
"Dawa za'ai rakiyar? Amma bada niba wallahi bazanje ba nida ya Ahmad saidai idan ya dawo na ganshi amma banda yau".
"Idan baki tashi munje ba baza muyi partyn ba" Khairat ta fad'a da serious face kamar gaske ta d'auka Babyn idan taji haka zatace suje sai taga ta kwanta a kusa da ita tana cewa "a fasa kawai indai sai naje gurin ya Ahmad da muyi kawai a barshi yafi" dariya Khairat tai tana cewa "humm ai baki iyaba Baby da kince ni d'in naje ni kad'ai nima fa ba iya zuwa zanyi ba kawai Ina tsokanarki ne ban fad'a miki ba tun a jiya ya Shadad ya turo min kud'in da zamuyi partyn dashi amma baisan partyn murnar tafiyar ya Ahmad bane 'karya na sharara masa ya turo min" baby dake lullu'be tace.
"Oh kice zamuyi kenan"?.
"Kwari zamuyi dan tun a jiyan na baiwa ya Hamid kud'in na fad'a masa abubuwan dazai sayo mana idan ya fita kinsan mu baza'a barmu muje ko'ina ba daga school sai gida".
Tashi zaune Baby tai tana cewa "amma gari fa ya waye haske ya fito sosai nasan maybe yanzu ai ya tafi mu tashi mu tafi part d'in Momy nifa yau da yunwa na tashi domin jiya da dare banci abinci ba iya fab-choculate d'in nan naci dan Allah Aunty Khairat tashi muje amma idan zamu shiga mu tsaya mu saurara tukuna kar muje mu fad'a muga Yaya boss" tashi Khairat tai tana dariya tace "tab kina fad'ar haka na hasko wata mugunta ace muna zuwa kofar parlon Momy kin bud'e zaki shiga ni kuma na turaki ciki da 'karfi kuma ace ya Ahmad d'in yana parlon a zaune" bud'e baki da ido Baby tai tana komawa ta bayan Khairat tace "please kar kiyi haka indai ba so kike yau nayi wunin zazza'bin wahala".
"Ai dama bayi nace zanyi ba misali nayi miki".
"Misalin jinsa nayi kamar gaske shiyasa nima nace haka" daidai sun karasa bakin kofar part d'in Momy basu shiga ba saida suka tambayi masu tsaron kofar ko Ahmad yana ciki sukai musu albishir cewa shikam tun asuba yabar masarautar nan prince Hamid ne yayi masa rakiya jin wannan daddad'an labarin yasa da gudu suka bud'e kofar suna shiga ko jira a bud'e musu basuyi ba Momy tana zaune ita kad'ai sai gani tai sun fad'a mata da gudu suna zama suka saka ta a tsakiya kowa na fitar da huci da mamaki take kallonsu da ace Ahmad yana nan sai tace ko shine ya korosu suke irin wannan gudun tashin hankalin to yanxu kuma da baya nan lafiyarsu kalau kuwa..............
Katse mata tunani Khairat tai har lokacin numfashinta bai dawo daidai ba tace "Momy ya Ahmad ya tafi ne ko yana nan"? Tun kafin Momy ta bata amsa Baby tace "Momy wai ya tafi inji securities d'in dake tsaye a bakin kofar part din nan haka ne"? Murmushi tai tana kallon su tad'an girgiza kai tana cewa "ok shine dalilin da yasa kuka shigo a haukace saboda kunsan me gyara ku baya nan ko"? Daidaita numfashi Baby tai tana cewa "da alama ya tafi kenan Momy"?.
"Eh ya tafi ko wani abu zaku bashi irin wannan nema haka nasan idan yana nan ba haka kuke ba yau kuma saboda kun tabbatar baya nan shine kuke tambayar sa"?.
Kai Khairat ta girgiza tana cewa "a'a Momy ba haka bane kawai dai mun tambaya ne amma tunda ya tafi munji dahir masha Allah da sau'ki Allah abun godiya sabuwar rayuwa ta dawo heheheee shagaliii yau zamu shana" jinjina kai Baby tai tana cewa.
"Humm wallahi yau yadda kika san sallah Aunty Khairat haka nake jin farin ciki har wata sabuwar sansanyar iska ce take ratsa ni da Yaya Ahmad ya fita daga masarautar nan shikenan kuma mun huta kafin ya sake dawowa ya sake sakamu a gaba" murmushi Momy tai tana cewa "wato a gabana kuke farin ciki da tafiyarsa ko? d'ana nefa bakusan yadda ni kuma nake jin kewarsa a raina ba amma kunzo kun sakani a gaba da maganganun ku wannan ai saiku sani kuka" tana rufe baki duk su biyun suka zaro ido da sauri Baby ta girgiza kai tana cewa.
"Please Momy kiyi ha'kuri dan Allah ya Ahmad d'in ne ba'a iya masa wallahi muma ba'a son ranmu muke masa hakan ba dole tasa saboda irin hanamu sakewar da yake".
"Ai idan ma yana nan ba hanaku sakewa yake ba kune kuke Hana kanku duk tsiya idan bakuyi laifi ba bazai dake kuba".
Ha6a Khairat ta ri'ke tana kallon Momy tace "Eh haka ne Momy amma wallahi ba mu bane muke hana kanmu ba muna son mu ri'ka wargi baya barinmu saidai yazo ya tsare gida yadda motsin kirki bazaka iya yi ba yayita muzurai yana hahhad'e rai wai shi ala dole soja haba jama'a wannan matarsa zata sha wahala indai akace itama irin takurar mu zai nuna mata".
"Kwarai Aunty Khairat idan yace d'auko min ruwa me sanyi saita d'auko tun kafin ta karaso zaice bamai sanyi ba ta mayar ta d'auko masa d'an tsakatsaki ko marar sanyi dan naga alama ya Ahmad koba nefa caji yake yanzu zaisa mutum yai shokin da tashin hankalinsa" Baby ta fad'a tana maida fuskarta kalar tausayi dariya Momy tai tana cewa.
"Lallai wato saboda kunga baya nan yayi nisan kiwo shine kuka zauna kuka kafa gulmarsa ko aiko indai mukai waya saina fad'a masa duk abinda kuka fad'a a kansa har qari sai nayi".
Yarfa hannu Baby tai tana ri'ko hannun Momy tace "Innalillahi dan Allah Momy karki fad'a so kike ya d'auki hutu saboda mu akan wannan maganar ya dawo gida yaci ubanmu ya koma kenan" kai Momy ta girgiza tana murmushi tace "a'a bazai dawo gida ba saboda daku saidai tunda ba nisa yayi ba zaisa a saka masa ku mota a kaiku inda yake yaci 'kaniyarku acan son ransa sannan yasa a d'auko ku a dawo daku gida" Momy na rufe baki Baby tace "a wuce damu asibiti dai ya Ahmad d'in ne zaisa a kaimu har inda yake kuma hukunci zai bamu harmu dawo mu samu damar iya cigaba da rayuwa batare da munga likita ba tab uhmm Allah dai ya rufa mana asiri.
"Amin Khairat tace tana cigaba da cewa "ai Baby ko zamu samu d'an hutu da sassauci a gidan nan maybe sai yayi aure kila ko muma ma huta dan ko 'ya'yan bayi bazamu fad'awa hutu ba tunda su babu wanda yake takura musu mu kuwa fa kullum kana ankare sai kace wanda kake filin ya'ki Allah yasa daya dawo gida yayi aure kawai a wuce gun".
Da sauri Baby ta d'aga hannu tana cewa "Amin ya Allah Aunty Khairat Allah yasa yayi auren nan da wuri indai hakan zaisa hankalin mu ya kwanta aidai dole zai rage matsa mana lamba yana part d'insa zai rage zirga-zirga a gurin Momy da part d'in Mami ta Nan zamuji dad'in abun" dariya Momy tai tana kallon Baby datai maganar kawai ta girgiza kai domin tasan akwai guguwa a gaba duk ranar da Baby ta fahimci Ahmad ita yake so kuma ita zai aura wai za'a kwashi 'yan kallo bata jin hakan zaizo da sau'ki sau'kin d'aya tunda Abban Baby din Sultan Ashraf ya hana yace kada a sanar mata sam a rabu da ita suje a haka iya daga ita sai Khairat sune basu sani ba amma kowa ya sani daga Momyn har Abba da Mami su Sultana Addah da Sultan Sharfaddeen mai martaba duk sun sani.................
"Momy" Baby ta fad'a ganin ta fad'a tunani dawo da kallonta Momy tai kan Babyn tana cewa "na'am" "tunanin me kike yi zamuyi breakfast"? Kaita d'aga tana cewa "ok kuje dinning man kuci tunda naga ku bakwa son masu aiki suyi serving d'inku ko meyasa oho" mi'kewa sukai Khairat na cewa "saboda tsaro Momy gara hakan kinga nan gaba a gidan mazajen mu mun riga mun saba da kanmu zamuyi nikam girki ma dan baza'a barni bane da yanzu Ina zuwa kitchen ina ganin yadda akeyi na koya amma duk da hakan alhamdulillah tunda wata rana muna fakar ido mu shiga kitchen d'in Mami mu d'an girka wani abu idan mukai searching muka gani".
Basu dad'e da zama a dinning ba prince Hamid ya shigo yana aje musu kayan da Khairat ta fad'a masa ya sayo musu baisan me zasuyi ba yana zaune suna zance da Momy yaga sun fara gyara gurin suna hura balloons suna d'aurewa ga cake da suka aje d'an karami mai kyau anyi masa kwalliya a jiki an rubuta happy valentine day da mamaki ya kalli Khairat yana cewa.
"Ummul-khairi wai wannan d'in na mene naga dai yau ba ranar valentine day bane ku kuma na me zakuyi"? Dariya Khairat tai zatai magana Momy tace "murnar tafiyar Ahmad suke shine harda had'a walima a gabana kuma na fad'a musu ni d'ana ne kewar tafiyarsa nake ji kamar nayi kuka su kuwa farin ciki suke gashi nan ka gani har party zasu had'a kuma a gabana" da sabon mamaki prince Hamid ya sake kallonsu jin abinda Momyn ta fad'a yana cewa.
"Oh duk wannan murnan tafiyar Ahmad ne lallai kun kyauta amma meyasa bakuyi jiya ba kuka bari sai yau a gabansa ya kamata kuyi ya gani amma kwazo kuna ihu bayan hari mu amfanin me zaiyi mana ko taya ku zamuyi"? Ya tambaya yana kallon dukkan su biyun Baby da take jera grapes da yankakkun Apple red and green tana yiwa cake d'in kwalliya tace.
"Yaya Abdul-Hamid murna ta zama dole yau sabuwar rana ce a garemu zamu sha shagali muyi komai muke so babu mai takura mana koda ya Ahmad ne ya dawo yau sai mun gwangwaje yasin" kai prince Hamid ya jinjina yana sakin murmushi yace "anya Baby idan Ahmad yana nan zaku iya yin wannan abun sannan yasan dashi kuke"? Cikin 'kwarin gwiwa Baby tace "kwarai ya Hamid zamuyi" ok kawai abinda yace mata bai sake magana ba Momy tana kallonsa ya zaro wayarsa ya fara daukarsu video batare da sun sani ba murmushi tai tana d'an sakin dariya wato yanxu kuma da zasu d'ago su gani maybe valentine d'in da baza ai ba kenan saidai suyita bada ha'kurin a goge videon murmushi prince Hamid yake yana ta tsokanar su suna magana duk basu san abinda yake ba har suka gama had'awa ganin zasu d'ago yai sauri yai saving yana aje wayar yace.
"Wow gaskiya cake d'in nan yayi kyau bari na dau'ki photonsa na d'ora akan DP (difi) d'ina ya fad'a yana d'auko wayarsa ya d'auka yana cewa "wannan valentine d'in ba iya ku kad'ai zakuyi ba harda ni saboda idan yana takura muku nima Ina jin babu dad'i idan kin fara Khairat ko ke ko Baby wata da kirani a waya" yana rufe baki Baby tace "ni ya Hamid bani da waya ya Ahmad ya hana na ri'ke yace sai nayi aure" ta fad'a tana zun6ura baki juyawa yai zai fita yace.
"Ok Ummul-khairi ki kirana".
"Tom" tace tana mi'kewa ta kalli Baby tana cewa "muje muyo wanka wannan abun dole saida kwalliya ina Sultan please mu kar'bo aron mp d'insa mu gwangwaje da ita".
"Mu fara yin wankan tukuna sai muje mu kar'bo maybe bazata wuce tana parlor ya sakata a caji ba dan shima yau ranarsa ce tunda ya boss baya nan muje mu fara shiryawa" wucewa sukai suka bar Momy ita kad'ai a gurin tana kallon yadda suka tsara abun nasu kamar masu yin birthday party a ranta tace "bari sai sun fara zan kira Ahmad video call batare da nayi magana ba yaga yadda ake party da murnar barinsa gida maybe idan yaga haka ya canza ya daina takura musu.
Wanka sosai su Khairat suka d'auka sun saka kaya iri d'aya an soke d'aurin kwali anyi makeup kowa da bayyanan nan farin ciki a fuskarta suka fito har lokacin Momy tana zaune wucewa sukai suna tafiya 6angaren Mami humm tun daga harabar shashin suke jiwo tashin kid'a kallon juna sukai suna dariya domin ko ba'a fad'a ba sunsan Sultan ne shima yake nasa partyn suna shiga kuwa suka ganshi zaune ga mp a gefe sai kad'a kai yake ganinsu yasa Mami tai murmushi tana qare musu kallo tace.
"Tofa 'yan matan Momy wato kuma Ashe kuna kan hanya inayiwa Sultan maganar ya rage qarar mp nan tayi yawa ku kuma wanka kuka d'auka kowa da kiwon daya kar'beshi kenan"? zama sukai Baby da har kamar tafi kowa jin farin ciki tace "Mami ba dole yau muyi tsalle mu jujjuya ba ya Ahmad ya fece ya bamu filin shan iska yau ranar gud'a ce muyi farin ciki muyi shewa yanzu ma mp Sultan muka zo mu ara zamuyi valentine a parlon Momy harda cake mukai saboda murnan ya tafi please Sultan bamu aro dan Allah" Baby ta fad'a tana mi'ka masa hannu bai kashe wa'kar da yake jiba ya mi'ko mata yana cewa.
"Baza'a yi babu mu ba Aunty Baby ku tashi muje yau akwai buduri a gidan nan nima ina da chocolate gida guda bari in d'auko mu tafi da ita ku jirani" ya karasa maganar yana wucewa ya shiga bedroom d'insa kallonsu Mami tai tana cewa "yanzu ku da ace saikun fara ku ganshi ya dawo kamar a mafarki ya zakuyi"? Had'a ido sukai tare da jinjina kai a ransu suna hango irin hukuncin dazaiyi musu Baby tace "sai muce ba farin cikin tafiyarsa muke ba mu farin cikin yau wacce rana ma"? Ta tambaya tana kallon Khairat amsa ta bata "yau laraba".
"Yauwa Mami kinga yau laraba sai muce murna muke taya Sultan tunda kinga ranar labara da dare aka haifeshi".
"Ai kuma ba watan bane baku da yadda zaku kare kanku a gunsa" Mami ta fad'a daidai Sultan ya dawo yace "muje muyi partyn nan dan Allah ni harna fiku 'kaguwa" zasu fita Mami ta mi'ke tana cewa "bari nazo naga wanne irin shiri ku kaiwa tafiyar d'an nawa" ta fad'a ta biyo bayansu dariya sukai Khairat na cewa "gaskiya kam Mami ya kamata kizo ki gani kar ayi bake Momy kam dama tana gurin".
"Nima ina biye daku yau zanyi kallo".
Suna shiga suka ga prince Hamid a zaune ga Momy data kallesu taga harda Mami suka gayyato kawai tai dariya tana girgiza kai zama Mami tai tana kallon Momy tace "um muna can ashe suna nan suna shagali abinsu wai murnar tafiyar Ahmad suke"? Kai Momy ta d'aga tana cewa "eh haka suka ce gashi nan harda gayyatoku kuma mukam dama an dad'e da gayyarmu tun d'azu" murmushi Mami tai tana gyara zama tace "humn rabu dasu zanyi maganinsu" ta fad'a tana saita wayarta ta fara musu video duk abinda suke rufe baki Momy tai tana dariya Mami kam duk wani abu da suke tana d'auka Baby ce mai gabadatarwa kamar gaske Khairat ita da Sultan suna zaune kowa ya d'ora kafa d'aya kan d'aya idan tai magana sai su tafa mata harta gama Khairat ma ta kar'ba itama ta nuna murnarta da ranar 'yanci da suka samu sannan suka yanka cake duk abinda suke Mami tana tayi musu video Momy kuma datai sa'a Ahmad yana online tai kiransa video call duk abinda suke yana gani tsabar yadda suka bashi dariya har baisan lokacin daya saki murmushi ba gashi sun qure mp yaga harda prince Hamid dama yasan shine yake gayon bayansu kaiya jinjina yana katse kiran ya kira ta normal call yana cewa.
"Momy kice ina magana dasu" kallonsu tai da murmushi akan fuskarta tace "Khairat da Baby ku kashe mp nan Ahmad zaiyi magana daku" Momy na fad'a d'iff