Showing 33001 words to 36000 words out of 84238 words

Chapter 12 - ROYALTY (YAN SARAUTA) by Mrs Alamin.txt

15 Aug 2025

2105

dawo gunta da zama kamar wani 'karamin yaro humm zaiyi maganinsa kuwa domin kome Hajiya Khubura zatai sai Khaleel yabar gidan nan.

Tunda Aiman yabar gida tun safe bai dawo ba sai bayan sallar la'asar yana shigowa da tasa motar Khaleel kuma ya fito daga gidan shima ya nufi tasa motar ya shiga yad'au wanka tsaki Aiman yaja ransa a 6ace da sauri ya karasa yai parking kafin ya fito har motar Khaleel taje bakin gate saboda dama me gadin bai mayar da gate d'in ya rufe ba tsaye Aiman yai yana bin motar da mugun kallo harya fice karasawa gurin me gadin yai yana cewa.

"Daga yau karka qara bud'e masa kofa ko yanxu ya dawo kace na hana karya kuskura na qara ganin motarsa a gidan nan" yana fad'in haka ya juya da karfi ya shiga gidan zuciyarsa tazo wuya yana shiga Hajiya Khubura ta fito daga part d'inta ransa a 6ace yace "wannan gardin da kika kawowa mutane cikin gida kuma waye shi daga Ina"?.

Wata uwar harara Hajiya Khubura ta sakar masa tana cewa "sannu d'an masu gida dad'in abun ma ba haka kawai ya shigo ba uwarsa ce ke aure a gidan kaga kuwa yana da 'yancin shigowa ko ba'ai masa izini ba kuma yana da gurin zama ko ba'a bashi ba".

"Ok yana da gurin zama ko ba'a bashi ba kikace ko? To bismilllah yazo ya zauna d'in na rantse da Allah saina 6allashi idan na sake ganin 'kafarsa a cikin gidan nan saboda kina gadarar d'anki ne shine zai shigowa mutane gida kai tsaye haka da dagara yana wani hura hanci da bubbud'a kafad'u to bari kiji karya kuskura yace zaiyi mana hauka a gidan nan ina daidai dashi sannan karya kuskura ya ri'ka yin abinda zai sa6anta hankalina tsaf zanyi masa abinda zakiji ciwon sa domin niba shashasha bane irinsa bai isa yazo yace zaiyi abinda bai gamshe niba".

Wani kallon sama da 'kasa Hajiya Khubura tai masa tana cewa "au sannu d'an me gida idan ya sake shigowa me zakai masa masa zaka dake shine"? Kai ya jinjina yana cewa "fad'a 6atawa idan kuma kina ganin nayi 'karya dan Allah ki kirashi yanxu kice ya dawo ya shigo gidan nan wallahi tallahi saidai a d'ebe shi zuwa asibiti" yana rufe baki Hajiya Khubura take "wallahi baka isa ka hanashi shigowa gidan nan ba saboda kaima ba gidan kune d'an karere ne dan haka kuwa baka da bakin cewa wani bazai shigo ba kaima alfarma akai maka".

"Haka kikace"? A masife Hajiya Khubura tace "nace hakan kai abinda zakai".

"Zakiga abinda zanyi d'in kuwa tsautsayi ya dawo dashi gidan yau zaiga hauka da d'anyan kai wallahi" ya fad'a yana shirin wucewa da sauri Hajiya Khubura tasha gabansa tana cewa "me zakai masa"?.

"Bai shafe kiba nidai na fad'a miki sa'ko na zuwa gare shi ki sanar masa kar tsautsayi yasa naga wani abu sa6anin hankalina zaiga fushina akansa.

"Wallahi baka isa ba dan gidan wan ubanka ne kace 'ya'ya na bazasu taka rawa da bazarsu ba dole su sakata su Wala a gidan nan tunda har Alhaji ya aure ni kai kuma babu yadda ka iya dasu sun zame maka ciwon ido idan ma ba'kin ciki kake da aureta da Alhaji saidai ka mutu babu yadda zakai ni dashi mutu ka raba" wucewa Aiman yai yana cewa "shikenan ni kuma zan gwada miki isar tawa Allah ya dawo dashi gidan zakiga yadda zanyi dashi" yana fad'in haka ya wuce da kallo Hajiya Khubura tabi bayansa harya fice tsaki taja tana cewa "jimin d'an mara mutunci to sainaga uban me zakai masa bari ya dawo gidan zansa yayi maka dukan halaka idan kaji wuya rainin da kake min zai ragu" ta karasa maganar tana wucewa domin yau dangin saurayin Nadiya zasu zo gidan kawo akwatun lefe Hajiya Khubura ta gayyaci manyan 'kawayenta suzo su kar'ba shine dalilin dayasa yau bata zauna ba tun safe take aiki har la'asar kuma abinda bata gane ba sannan bata damu ba da sukace sai dare zasu zo kawo kayan bata nemi dalili ba ita dai kawai su kawo.

Bayan sallar magriba suka zo da kayan masu yawa kuwa wanda kowa mamaki take a cikin 'kawayen Hajiya Khubura wanne irin mutum Nadiya zata aura me kud'i haka Hajiya Khubura kam sai d'add'aga hanci take tana tausaya kai ta kalli nan ta kalli can har suka gama abinda zasuyi suka tafi zuwa bayan sallar isha da Daddy ya dawo sai sannan ta shiga part d'insa yana zaune ta sameshi itama zaman tai fuskarta fal da farin ciki dan harta manta warning d'in da Aiman yayi mata tana taso Daddy ya dawo ta fad'a masa saii kuma wadannan ba'kin suka zo shiyasa ta manta da wancan shafin kallonasa ta bakinta kamar zai yage ba sannu ba ya aiki da gajiya kawai abinda ke ranta take son fad'a kamar wani zai rigata tace.

"Uhm Alhaji na manta ban fad'a maka ba d'azu dangin su Sabit sunzo baka nan naso kiranka amma kuma hidima ta hana saidai Kai fatan alkhairi" da alamar tambaya Daddy yace "su waye kuma dangin Sabit"?.

"Saurayin Nadiya fa nake magana akai d'azun daf da zaka dawo suka tafi".

"Ok aure zaki mata"?.

"Eh har an gama komai ma rana tayi nisa d'an lokaci ya rage" kai Daddy ya jinjina yana cewa "amma baki ta'ba fad'a min ba kunyi bincike a kansa ne d'an waye shi"? Kai Hajiya Khubura ta girgiza tana cewa "ai Alhaji sun dad'e ba wani bincike da za'ai tunda kusan shekaru hud'u baya da suka wuce yana sonta".

"Ba maganar dad'ewar da sukai nake ba magana nake akan kunyi bincike a kansa ne"?.

"A'a bamuyi ba".

"To meyasa"?.

"Alhaji gani nayi Nadiya tasan yaron nan sani na ha'ki'ka nima na sanshi yawancin lokuta tana kawo min shi ya gaishe ni gaskiya yana da nutsuwa bashi da gurin kushe ko kad'an nasan zai ri'keta da kima sosai" kai Daddy ya sake girgizawa yana cewa "wannan fa duk ba hujja bace Khubura maganar sun dad'e suna soyayya kema kin sanshi duk bazai gamsar ba abinda ya kamata shine kuyi bincike kafin ku fara komai wannan shine ya asalinsa yake ya mu'amalarsa da iyayensa take bawai kawai kice min kin sanshi yawancin lokuta yana zuwa gaisar dake ba gaisuwa da lokaci kad'an dazai tashi ya tafi taya zakisan halinsa yaron kirki ne ko na banza sannan idan ya aureta zai ri'ke miki ita ke duk bakya tunanin wannan"? Tunda ya fara magana Hajiya Khubura take faman murgina kai ta juya nan ta juya can ta ta'be baki alamar maganganun sa basu samu kar6uwa ba jin yayi shiru ta d'ora nata.

"Alhaji naji duk abubuwan daka fad'a wannan gaskiya ne haka yake saidai kar kace ban bi shawararka ba ko ban dau'ki abinda ka fad'a min da muhimmanci ba a'a na yarda da dukkan komai abinda kace amma fa ni na riga na yanke hukunci koma waye shi sai Nadiya ta aureshi saboda da alama ba d'an 'kananun mutane bane iyayensa suna da 'kazamin kud'i idan na samu Nadiya ta aureshi bani ko jikanu naba hatta tatta6a kunne na sai sun taso sunci irin dukiyar kaga kuwa ina zan sake ya kubce mana abu nefa ake nema sai gashi yaso har gida kasan ko bazan sake ba dole nema Nadiya ta auri Sabit ko bataso balle itama masifar sonsa take kamar ranta" tunda Hajiya Khubura ta fara magana Daddy ke girgiza kai cikin yanayin rashin jin dad'in son zuciyar data nuna 'kiri-'kiri har takai aya kafin ya kalleta dakyau yaga bil hakki tsakanin ta da Allah tayi maganar ta kuma babu batun komawa da baya ko ace wannan maganar auren ta wargaje a 6angarenta.

"Khubura" taji Daddy ya kira sunanta amsawa tai tana 'kureshi da kallo domin taga sauyin yanayi a fuskarsa da alama dai neman hanata samun wannan d'aukakar data sameta yake shirin yi jin a karo na biyu ya sake cewa.

"Khubura" bata amsa ba sai caraf datai tana cewa "Alhaji wai me kake nufi ne amma ba hana auren nan ne niyyarka ba gaskiya nikam ina so kuma yarinya ma tana so dan haka babu wata magana kawai ka bimu da fatan alkhairi a gani na zaifi" ta karasa maganar harda irin d'aga kafad'ar nan.

Ganin ta riga tayi nisan da baza taji kira ba Daddy yace "Ok ai shikenan Allah ya sanya alkhairi Allah yasa gidan zamanta ne Allah ya bada sa'a" kawai shine abinda yace daga haka yai shiru saidai abun nacin ransa kamar 'yarsa ta cikinsa Hajiya Khubura take shirin yiwa haka amma tunda ta nuna 'yarta ce shi bai isa ya fad'i magana a kanta ta d'auka ba zai zuba mata kamar yadda ta bu'kata a yayin da wata matsala ta shigo ciki shima lokacin zai nuna mata Nadiya ba 'yarsa bace 'yarta ce babu ruwansa a ciki.........................

Ganin yayi shiru yasa Hajiya Khubura ta kalleshi tana cewa "Alhaji dama ina so na fad'a maka Khaleel ma yaga Ayrah ranar da tazo gidan nan d'iban kayan sawarta yace yana sonta na fad'a maka idan zaka bashi aurenta"?.

Numfashi Daddy ya fitar yana cewa "mezai hana indai Allah ya 'kaddara matarsa ce shikenan bani daja Allah ya za'ba mana mafi alkairi a rayuwar mu" yana rufe baki Hajiya Khubura ta saki wani irin murmushin jin dad'i ganin shima ya amince shikenan kwanan nan zata zama Hajiya Khubura billionaire mai nairori tayi suna a yankin Africa da yankin yirof ko ina a santa ayi da ita ta kafa kamfaninnika ta zuba ma'aikata yau tana wannan kasar gobe tana wancan wannan shine burinta iya tunanin hakan datai ya sanya mata wani jin dad'i da sanyi yana shiga zuciyarta mi'kewa tai cikin 'kwarin gwiwa tana cewa.

"Yauwa Alhaji muna godiya da wannan karamcin naka bari naje na fad'a masa wannan daddad'an albishir d'in" ta fad'a tana ficewa da sauri kamar zata kifa ta shiga wani part data baiwa Khaleel matsayin ya dawo gidan da zama saboda ta had'a Aiman da Daddy ya hanashi yace ya 'kyale kar yayiwa Khaleel magana shiyasa yanzu Aiman baya shigowa gidan ko kad'an sun daina ganinsa tunda dama Ayrah bata nan tana gidansu yanzu shi damuwarsa lokacin tafiyarsa Beijing yayi kawai yabar Nigeria ya huta da kallon kayan ba'kin ciki da takaici.

Khaleel yana zaune a parlor ya 'kure sauti kamar ba dare ba kana ganinsa kasan sai a hankali d'an sharholiya ne hutu kawai ya sani bayan haka baisan komai ba saidai yaci yabi lafiyar gado yana wannan halin Hajiya Khubura ta shiga ganinsa zaune yana kad'a kai alamar sautin kid'an yana tsuma shi ga wani arnen d'an mitsilin wando a jikinsa mai kamar da d'an diras cinyoyinsa sad'a-sad'a a waje maimakon ace tayi masa fad'a sai murmushin ya burgeta d'anta wayayye ne data saki tana zama ta kalleshi idonsa a rufe da 'karfi tace.

"Khaleel" bai bud'e idon nasa ba balle yasan tanayi saida ta sake 'kwalla masa kira tana d'an ta'ba kafarsa sannan ya bud'e ido yana tashi zaune daga jinginen da yake ya kalleta yana cewa "Umma yaushe kika shigo kin sameni ina shan DJ" murmushi tai tana d'add'aga hanci ala dole ita mai d'a tace "dama zuwa nayi muyi magana Khaleel ko Alhaji zai kiraka na akan maganar kana son Ayrah ka tsaya ka nuna masa sosai kake sonta saboda Naga shi haka shine damuwarsa na riga na fad'a masa cewa kana sonta zaka aureta" da mamaki Khaleel yace "amma meyasa Umma nifa bana jin son yarinyar nan a raina meyasa kika ce masa haka"? Gyara zama Hajiya Khubura tai tana cewa "kasan dalili kaga niba haihuwa nayi da Alhaji ba ga 'kazamin kud'i daya tara kamar qasa kasan idan ya mutu iya tumuni zan samu gabadaya dukiyar ta Ayrah ce amma abun hikimar anan shine idan akace ka aureta ta zama matarka saiya mutu to kaga komai yana hannun mu dukiyar ma ta zama tamu karshe saimu samu mu kashe Ayran batare da sanin kowa ba mu mallake komai kasan wannan shawarar tawa tayi sabida kaima kana son ka inganta rayuwarka ko amma me kace"? Shiru yayi zuwa wani lokaci ya d'ago yana jinjina yace.

"Tabbas Umma wannan shawara taki tayi kwarai zan aureta ko yanzun nan ne na shirya ki sameshi ki sake fad'a masa sannan ki nuna kawai nine na ganta nace ina sonta ba kece kika fad'a ba sannan maganar daga ni take" ajiyar zuciya Hajiya Khubura ta sauke tana cewa "yauwa Khaleel ko kaifa har kasa naji dad'i wallahi bari na koma kar Alhaji yaga na barsa shi kad'ai" ta fad'a tana mi'kewa ta fita da kallo khaleel yabita harta fita daga baya ya sauke ajiyar zuciya yana sakin murmushi tare da mi'kewa ta tafi jikin window ya d'aga labule yana kallon waje a ransa yana cewa.

"Gaskiya Umma kin iya had'a shiri ban ta'ba kawowa a raina zan kalli wannan yarinyar ba saboda yayan nan nata Aiman masifaffe ne amma yanzu tunda har Daddyn ta ya shiga ciki na sake samun 'kwarai gwiwa ta yadda zan tareta da karfina duk sanda nake so" kaiya jinjina yana cije lips ya murza yatsunsa suka bada sautin 'kas 'kas kafin ya cika bakinsa da iska yana firzarwa a fili yace "muje zuwa shiri nagaba na kusa taka wani matsayi da nake son zuwa" bai baro jikin windown ba yaci gaba da tsaiwa a gurin kawai yana kallon waje iska tana shigarsa yana lumshe ido yana bud'ewa cikin yanayin da rabon daya jinsa a irinsa harya manta sai yau da yaga ya samu dami a kale Hajiya Khubura tai masa hanyar samun cikakkiyar budurwa yana zaune batare daya sha wahalar komai ba.

***Bayan sati biyu Aiman ya gama komai nasa lokacin tafiyarsa Beijing yayi saidai a yau d'in dazai tafi sai yaji wani 6angare na zuciyarsa yana riya masa baya so ya tafi yabar Ayrah baisan wanne hali zata shiga ba Allah yasa bayan tafiyarsa kar Hajiya Khubura ta zuga Daddy yasa Ayrah ta koma can itama Ayran a nata 6angaren duk hankalin ta ya tashi tasan idan har Aiman yabar gari zai wuya Daddy baisa ta koma can gidansu ba ita kuma hakan ne bata so musamman ranar da taje d'iban kayanta taga khaleel a parlor ga wani irin shu'umin kallo da yake binta dashi yana d'age mata gira yana lashe baki tun da taga haka tsoro ya kamata bata sake zuwa gidan ba har yau shiyasa take tunanin tafiyar Aiman d'in har wata ramar rashin kwanciyar hankali tai gashi a hakan ma tana gidan hutu ne babu me takura mata da ace a gidansu take maybe da yanzu ta kamu da ciwon bugun zuciya.

Duk suna zaune a parlor suna jiran fitowar Aiman suyi sallama kowa ka kalla fuskarsa fal dake da damuwa shi kanshi Aiman baisan wannan tafiyar yanzu zaiso ace a qara masa lokaci zuwa gaba amma dai kawai ya danne duk yadda yake ji bayan ya gama shiryawa ya goyo jakarsa a baya hannunsa kuma ri'ke da trolley yana ja ya fito ganinsu zaune fitowarsa duk sun zuba masa ido yasa ya d'an dakata yana sauke numfashi kafin ya karaso yana zama ya kalli mahaifiyar sa murya a nutse yace.

"Aunty Umma lokaci yayi zan tafi ina so kimin addu'a sannan magana ta karshe dan Allah duk yadda zaki karki bari Ayrah tabar gidan nan karta koma gidansu komawarta can akwai had'ari barazana ce ga rayuwarta wadannan yaran suna matsa mata baya da haka yanzu wani saurayi yazo gidan wai shima d'anta ne harda part aka bashi a gidan ya d'auko kayan sawarsa da motarsa da komai nasa ya dawo gidan kuma Daddy ya sani amma bai hana ba shiyasa ni nake fargabar barina gari domin indai Hajiya Khubura taji labarin tafiya ta saita zuga Daddy yasa Ayrah ta koma dan Allah Aunty Umma karki bari ta koma" ya karasa maganar yana kallon Ayrah wacce zafafan hawaye suka zubo mata shiru yayi zuwa wani lokaci ya sake d'agowa yana cewa.

"Ayrah kiyi hakuri komai ya zafi maganinsa Allah ki daina kukan nan haka insha Allahu nasara tana tare dake babu wanda zai samu d'aukaka saiya sha wahala sannan ba'kin ciki yana tare da farin ciki tsanani yana tare da sau'ki ki ri'ke wannan a ranki kullum ki kasance mai godiya ga Allah domin wannan yanayin da kike cike hakan ma baiwa ce karki fushi ki zama mai godewa Allah a kowanne hali ubangiji maji ro'ko ne idan kika tsaya a kofarsa zai kar'be ki idan kika nufesa zai cika miki burinki karki sare karki nuna karaya wata rana wannan kukan da kike zai zama miki dariya mai d'orewa ki dauwama a cikin farin ciki gaba kinji" jiki a sanyaye Ayrah ta d'aga kai tana shasshe'kar kuka ta kasa magana sosai ran Aiman ya dagule amma bashi da yadda zaiyi yana fatan tafiyarsa ce mafi alkairi akan zamansa sannan yana fatan Ayrah a duk inda ta tsinci kanta ubangiji ya zame mata kariya da garkuwa.

Mi'kewa yai bayan Aunty Umma ta gama yi masa addu'a da fatan samun nasara karatun da yaje nema ya samu Allah ya dawo dashi lafiya shigowa Abba yai yana kallonsu da yanayin fuskokinsu kafin ya mayar da hankalinsa kan Aiman da shima fuskarsa a 6ace take yace.

"Lokaci yayi Aiman ka gama sallama da Umman taka da 'yan uwan naka ne"? A hankali Aiman ya d'aga kai tare da mi'kewa bai sake kallon inda Ayrah take ba muryarsa da rauni yace "na tafi" bai jira amsar kowa ba yayi waje Abba yabi bayansa hannu Ayrah ta d'ora aka tana fashewa da kuka a susuce ta mi'ke zata fita itama ko mayafi babu a jikinta balle takalmi da sauri Aunty Umma ta ri'keta tana girgiza mata kai babu bakin magana domin idan har tace zatai magana tofa kuka ne sakamakon dazai biyo baya kawai jawo Ayrah jikinta tai dan ta samu nutsuwa ta fara shafa bayanta a kunnensu sukaji tashin motar Abba da zai kai Aiman airport inda abokinsa yake yana jiran zuwan su.

Kwana biyu da tafiyar Aiman Hajiya Khubura ta hura wutar dole sai Daddy yasa Ayrah ta dawo gidansa yasa ta baro gidansu Aiman farko Daddy ya share tun yana baiwa iska ajiyarta harta isheshi da 'korafi kullum bata da aiki sai yi masa mita gabadaya tabi ta d'aga masa hankali ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login